AMATURRAHAMAN

22

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 22

*بسم الله الر حمن الر حيم*

"Ai kau dai ba zamu zuba ido yarinya tazo har ɗakin baccinmu ta zagi Iyayenmu kuma mu zuba mata ido ta fita haka kawai ba." Ai kuwa kamar sun san abinda zai faru suka fice daga gidan, Amaturrahaman ta tafi gidansu Salima tayi kwanciyarta bacci yayi gaba da ita sakamakon kanta dake ɗan sara mata.

Ya Nafi kuwa uzurin gabanta ta tafi hankalinta kwance ta manta da wata Salaha da abinda zai faru, koda Kawu Isa ya dawo ya tarar da abinda ya faru ba ƙaramin tashin hankali yayi ba. Masifa ya rinƙa yi baji ba gani har Iyayen Mukhtar da Asiya sai da ya kira su ya musu zagin ƙare dangi ya kuma yi rantsuwar sai ya rama mata dukan da suka mata. "Ai Malam kawai ka kore su daga gidan kowa ma ya huta!." Babar su Salaha ta faɗa.

"Da hakan mai yiyuwa ne da tuni an daɗe da wuce wurin, to kin san wannan fitsararriyar yarinyar ba kunya ce da ita ba, don idona ta kalla tace zata maka mu kotu a ƙwato mata haƙƙinta."

"Eh lallai yarinyar nan wuyanta ya isa yanka Malam, to yanzu haka zaka zuba ido suyiwa yarinya dukan ɓarawo?."

"Basu daki banza ba ai da Sule zan haɗa su ya rama mata tunda ita lussrar ba abinda ta iya!." Haka ya ƙaraci masifarsa Kawu Isma'il na jinsa bai tanka masa ba sabo da shi irin mutanen nan ne masu halin ko in kula akan abinda bai shafe su ba, Aunty Rakiya kuwa dama bata gidan tayi tafiya ganinsu don haka su kaɗai suka ci suka tsire.

Amaturrahaman bata tashi daga baccin data kwanta ba sai da aka kira sallar magriba sannan ta tashi tana jin kanta ya ɗan saki, alwala tayi tayi sallah kafin tayiwa Salima sallama ta fito zata tafi Maman Salima ke ce mata ta tsaya taci tuwo.

"Alhamdulillah na gode Mama." Ta faɗa tana yin hanyar waje, har zaure Salima ta rakata tana jin daɗin ziyarar da ƙawarta ta ta kawo mata yau duk da dai bata ci komai da aka kawo mata ba sai ruwa. Lokacin data isa gidan ba kowa a tsakar gidan kowa ya shige ɓangarensa don yin salla don haka ta wuce ba tare da kowa ya ganta ba.

Ya Nafi kuwa bata tashi dawowa ba sai lokacin data saba dawowa don haka tuni Kawu Isa ya gaji da jira yayi bacci ko Sulen da yake jiran zuwansa don ya faɗa masa abinda akayi bai zo gidan ba.

Da haka sukayi ta wasan ɓuya da Kawu Isa har maganar ta lafa sai dai fa sun sha zagi don da yana fitowa da tuni ya cika jikinsu.

******* A ɓangaren Doctor Farhan kuwa Mahaifinsa yasa wani Yaron dake aiki a Companynsa ya masa bincike akan yarinyar da Farhan yake son aure, asalin yaron ɗan garin Matazu ne don haka bai sha wahala ba wurin binciken ya samo dukkan bayanan dasuka dace.

A Office ya samu Alhaji Bilal ya masa dukkanin bayanin daya sani dangane da yarinyar da rayuwar da suke ita da ƴar'uwarta har ma da asalin Iyayensu. "To ba komai na gode zaka iya tafiya."

"To ranka ya daɗe a huta lafiya." Shiru Alhaji Bilal yayi yana nazari akan abinda aka sanar dashi game da yarinyar da Farhan ke son aura, kwata-kwata yarinyar bata da nagartar da za'a iya aurenta don haka dole Farhan ya haƙura ya nemo wata ya aura.

Da dare bayan ya koma gida ya kira Doctor Farhan akan yana son ganin sa, bai ɓata lokaci ba ya taho don ya matsu ayi wacce za'a yi a aura masa Amaturrahaman ya bata kulawa ya inganta rayuwarta data ƴar'uwarta idan ta bashi damar hakan.

Da sallama ya shigo parlon inda ya samu Momy na haɗa masa shayi ya samu wuri ya zauna ya shiga gaishe da Iyayen nasa, da kulawa suka amsa masa Momy na masa tayin shayin yace ya ƙoshi don a matse yake yaji dalilin kiran saboda ya san ba zai wuce akan maganar aurensa ba. Ganin Dady yaƙi cewa komai ne yasa shi faɗin "Dady kace kana son ganina."

"Eh haka ne." Dady ya faɗa yana ci gaba da shan shayinsa, sai da ya kammala sannan yace masa "Kamar yanda na faɗa maka zanyi bincike akan yarinyar da kake so ɗin to Alhamdulillah nasa an min bincike, sai dai sakamakon da na samu ba mai kyau bane don haka kayi haƙuri ka nemi wata ka aura don bata da kyakykyawan asalin da zan iya haɗa zuri'a da ita." Tunda Dady ya fara maganar yaji wata irin zufa na karyo masa saboda sanin da yayiwa mahaifinsa akan tsayawa a magana ɗaya, yasan tunda yace a'a zai yi matuƙar wahala ya amince da ita. Gashi kuma Allah kaɗai yasan yanda yake ji a game da yarinyar, don Allah ya jarabce shi da sonta wanda bai taɓa yiwa wani mahaluƙi irinsa ba.

Cikin magiya da roƙo ya matsa kusa da Mahaifiyarsa yana faɗin "Momy don Allah ki taimaka ki saka baki Dady ya amince Wallahi ina matuƙar sonta, kuma Allah Momy ita ba abinda take yi ba ruwanta Yayarta ce mara jin maganar, kuma Momy nima ai bana jin maganar ko?." Ya ƙare maganar zuciyarsa a matuƙar karye harda wasu ƙwalla ya tara a idanunsa.

Cike da tausayawa Momy take kallon yaron nata yana ƙoƙarin kuka a kan Mace, eh lallai soyayya ba ƙarya ba kuma ta tabbata ba ƙaramar soyayya yake yiwa yarinyar ba, ta san Allah ne ya kama shi akan abinda yake yiwa ƴa'ƴan mutane na lalata su ya kuma barsu ba tare daya aure su ba. "Alhaji a dai duba lamarin ko za'a samu dai-daito." Ta faɗa cikin son shawo kan Mijin nata.

"Na gama magana Hajiya ba wani dai-daion da za'a samu sabo da wanda na ɗora akan binciken ya tabbatar min da wan Mahaifin yariyar yayi Magana ya kuma tabbatar masa cewar itama ana zargin tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki."

"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!." Itace kalmar da Doctor Farhan ya shiga mai-maitawa yana jin wata zufar tashin hankali na karyo masa, lallai mutumin nan ya tabbata ƙasurgumin munafuki. Wato ta nan ya ɓullo masa don ya liƙa masa tasa ƴar da bai san wace kala ce ba. Da ƙyar ya buɗe baki ya fara magana "Dady Allah ba hak...." Bai ƙarasa faɗar abinda yayi niyya ba Dady ya dakatar da shi ta hanyar faɗin. "Na gama wannan maganar Farhan kaje ka nemo yarinya ƴar mutunci ka aura ba zan hanaka ba.

Jiki a saɓule ya tashi ya fice a ɗakin ba tare da yayi musu ko sallama ba, ƙoƙarin sake magana Momy tayi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin "Kar ki ɓata bakinki Hajiya, ba yanda za'a ina kallon kashi da rana kuma da dare inzon in taka shi." Shiru tayi bata ce komai ba sai dai hankalinta yana kan yanda ɗanta ya fita sabo da Mace ce mai son ƴa'ƴanta da goya musu baya akan abinda suke so.

Har wani duhu yake gani a idonsa tsabar tashin hankalin da yake ciki, a haka ya ƙarasa ya shiga Motarsa yajata ya nufi Asibitinsa don baya jin zai iya komawa gida a wannan yanayin. "Ba zai yiwu ba gaskiya, ba zan iya haƙura dake ba saboda kece Mace ta farko dana ji zan iya sadaukar da komai a kanki, a kanki ne naji zan iya barin komai ciki harda gyara halayena marar kyau."

Gwiwarsa yaji tayi sanyi daya tuna cewar bashi da mai taimaka masa a wannan yaƙin saboda wacce yake yi domin ta itama bata sonsa hasali ma ta tsane shi tsana mafi muni kamar yanda ta furta, gashi a halin da yake ciki yana buƙatar haɗin kanta. Da wannan tunanin ya isa Asibitin nasa kai tsaye ofishinsa ya nufa ya rufe kansa ya shiga tunanin neman mafita.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa nauyi saboda baccin daya yi mai nauyi na bayan sallar asuba, zaune ya tashi yana dafe kansa dake ɗan sara masa mafarkin daya yi yana dawo masa tamkar yanzu yake yinsa. Tunda ya dawo yake yawan ganta a mafarkinsa a cikin damuwa tana kuka tana miƙo masa hannu da nufin ya taimake ta.

Tun abin baya damunsa har yazo ya tsaya masa a rai, ya rasa meye haɗinsa da ita da zata hana shi natsuwa a cikin baccinsa. Tun yana ƙoƙarin watsar da abin har yazo yana damunsa yaji yana buƙatar sanin halin da take ciki. To amma a wane dalilin? Meye haɗinsa da ita? Wa zai tambaya?." Waɗannan sune tambayoyin da yake yiwa kansa idan yayi tunanin bincikar halin da take cikin hakan ke sawa yake watsar da abin duk da baya barin zuciyarsa kuma baya fasa yin mafarkin lokuta da dama.

Tsaki yayi a zuciyarsa yana faɗin 'azababbiyar yarinya kawai daga haɗuwa ɗaya kin bi kin liƙe min, daga ganin idanunta zaka san bata da kunya.' ƙoƙarin tashi yake ya shiga toilet kiran Haneen ya shigo wayarsa, sai da ya bari ya tsinke kafin ya kirata. "Barka da safiya Akhi." Ta faɗa cike da girmamawa.

Amsa mata yayi da kulawa yana tambayarta lafiyarta dasu Ammah duk da kullum sai ya kirata da safe ya gaisheta ita da Abba.

"Duk muna lafiya." Ta bashi amsa kafin tace "Dama dama...." Sai kuma tayi shiru ta kasa faɗar abinda take son tambayar.

"Menene?." Ya tambaya cikin dakakkiyar muryarsa da ba alamar wasa a cikinta.

"Dama so nake Ya Muzaffar ya kaimu gidan gona nida su Ameerah shine yace in tambayeka." Ta faɗa da ƙyar tana fatan ya amince."

"Me zakuyo a can ɗin?."

"Akhi kawai muna son mu fita shan iskane kaga weekend ne ba makaranta kuma ina son ganin dabbobi ne, don Allah Akhi ka amince." Tayi maganar a shagwaɓe tana marai-raicewa da fatan ya amince da buƙatar ta.

Shiru ya ɗanyi yana nazari kafin yace "Ok ki kula banda yawo idan kunje." Cikin farin ciki tayi masa godiya tana aje wayar ta buga tsalle ta kalli su Anisa dake zaune sun zuba mata ido da son jin abinda yace. "Ya amince." Ta faɗa tana doka tsallen murna, ihun murna suka kaure da shi har sai da Ammah ta leƙo tayi musu magana sannan suka tsagaita.

"Ƴammata kowa yaje ya shirya barin in kira Ya Muzaffar in faɗa masa ya amince." Haneen ta faɗa cike da ɗoki da murnar zata je taga ƙawarta da tunda suka dawo wancan zuwan ta ishi su Zarah da labarin kyakykyawar ƙawar da tayi a Matazu.

Kiran Ya Muzaffar tayi ta sanar dashi ya amince yanzu zasu shirya. "Toke da kike ta wannan rawar ƙafar in kinje Matazun ta ina zaki fara neman yarinyar da baki san komai akanta ba?." Muzaffar ya tambaye ta, gwiwarta taji tayi sanyi daya faɗi hakan don bayan Sunanta ba abinda ta sani. Ita dai Allah ne ya haɗa jininta da yarinyar da haɗuwa ɗaya suka yi taji tana sonta.

A sanyaye tace "Ba na san sunanta ba, ai tambaya zanyi."

"Allah ya bada sa'a." Ya faɗa shima yana fatan su ganta ɗin don maganar gaskiya shima yana son ganin nata don tun wacce ranar take masa gizo a idanunsa shi yasa ma da Haneen tazo masa da maganar zuwan bai mata musu ba.

****** A ɓangaren Zayyad kuwa bayan ya aje wayar bathroom ya shige ya sakarwa kansa shower ya lumshe ido yanayin daya ganta na faɗo masa a rai. 'ko meke damunta?.' yayiwa kansa tambayar a cikin zuciyarsa. Ture tunanin yayi a ransa yayi wankansa ya fito ya ɓata lokaci wurin shirya kansa kafin ya sauko ƙasa inda ya samu tuni kukunsa ya shirya masa table mai masa gyaran gida ma ya gama ya tafi sai Samuel dake zaman jiransa a parlon yana ta aiki a laptop ɗinsa.

Daddaɗan ƙamshin turarensa ya fara yi masa sallama don haka ya ɗago a hankalin yana kallon up stairs ɗin, cikin ƙaƙƙarfan takunsa yake saukowa jikinsa sanye da kakinsa na cikakken soja da yayi masa kyau sosai ya ƙara masa kwarjini. Tashi yayi ya ƙame yana sara masa lokacin daya ƙarasa saukowa ya nufi table ɗin ya zauna, amsa masa yayi cikin salon gaisuwarsu ta sojoji kafin ya zauna Samuel ya shiga savin ɗin sa breakfast.

A natse ya gama cin abincinsa kafin ya miƙe yana yiwa Samuel alamar zasu iya tafiya, da sauri ya kwashi tarkacen yayi gaba yana buɗe masa ƙofar ya fita sannan ya tsaya ya kulle ko ina yabi bayansa zuwa inda Motocinsa suke da sauran yaran dake ƙarƙashinsa waɗanda ke jiran fitowarsa.

Samuel shine babban yaron Zayyad kuma amintaccensa da yake iya shiga ko ina a cikin gidansa na nan Abuja da can Katsina, duk wani aikinsa mai muhimmanci shi yake bawa kuma ko wace ƙasa zaije da shi yake tafiya, a takaice dai shine na hannun damansa.

Dukansu miƙewa sukayi suna ƙamewa har ya ƙaraso suka sara masa tare da gaisuwa ya amsa sannan suka shiga motocin suka fice daga gidan, kai tsaye babbar headquarter da yake aiki suka nufa....

***

Oum Fatima