7
by @sadiyanasir
RIKON SAKAINA
YA FARU A GASKE
NA
SADIYA NASIR DAN
Arewa Book
sadiya Nasir
SHAFI NA BAKWAI
Tunani mai zurfi na shiga akan Uncle Naira, zuciyata sam ta kasa aminta da cewar bada mugun nufi yazo gareni ba. "Malama mun iso layin a Ina zan ajiye ki?" Muryar mai adai-daita ta dawo dani daga duniyar tunanin dana fad'a. "In da motar can tayi parking". Nayi masa nuni da motor Uncle Naira.
Kamar mai jira ina fitowa yayi saurin bud'e motor ya fito fuskarsa d'auke da murmushi, had'a ido mu kayi yayi min signa ya k'araso in da nake, kauda kai gefe nayi nace "Ya kamata mu shiga harabar gida ko?". To yace yayi gaba ina biye dashi. A step d'in da zai sadamu da Maine parlor na gidan naja na tsaya, ganin haka yasa Uncle Naira ya dubeni. "Khadija maganar da nazo da ita tana da matukar mahimmanci bai kamata ace a tsaye anan mukayi taba, any way! kin riga kin min mummunar fahimta yasa dole nayi hakuri da yanda ta kasance, ya kamata mu ɗan zauna tsayuwar ba zai yuyuba gashi kin d'auko gajiyar makaranta". To nace na zauna shima ya zauna nesa dani kaɗan. Ya kai Akallah mintuna biyar yana kallona har sai da na tsargu nayi gyaran murya kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya soma magana. "Da farko dai ina mai baki hakuri akan abinda ya faru last tsakanina dake, wallahi banyi haka da nufi ba, ko min shashanci na Khadija ba zan tab'a aika mummunar Abu akanki ba, hasalima ba haka halina yake ba, yanayin dana tsinci kaina a ciki ne yasa hakan ta kasance.
Khadija wallahi tun ranar da idona ya sauƙa akanki naji hankalina ya kwanta dake nake ji a jikina na samu Macen Aure irin wacce na jima ina Addu'a da burin samu, amma kuma sai naji tsoro saboda nasha wahala da Matan da suke fakewa da shiga ta mutunci da kamala ta addini suke tsula tsiyarsu, infact Akwai wata yarinya har sadakinta na kai magana ake ta Aure bai zai wuce wata guda ba na sameta da cin amanata, gudun karna sake afkawa cikin tsaka mai wuya yasa nayi miki gwaji kuma Alhmdullah nayi nasara samun irin Macen da nake da burin Aure, don girman Allah Khadija ki fahimce ni, wallahi Ina kaunar ki". Ya k'arasa maganar murya a raunane.
Ajiyar zuciya na sauƙe mai karfi saboda harga Allah ban tsammaci abinda zai fito daga bakin uncle Naira kenan ba, kallon sa nayi sau d'aya na sunkuyar da kai k'asa ina jin zuciyata na wasiwasi akan zancen sa, sam yanayin uncle Naira bai nuna cewar mutumin kirki ne shiba, baya ga haka bana jin zan iya son shi a zuciyata, uwa uba kuma babu maganar soyayya agabana saboda Daddy karatu yake so ba Aure ba, jin shurun nawa tayi yawa yasa yayi gyaran murya, ɗan murmushi nayi da bai kai zuciya ba nace. "Kayi hakuri Uncle Naira a halin da ake ciki ba zan iya karb'ar soyayyar kaba saboda karatu ne agabana, kaga kai kuma Aure kake so". Shu'umin murmushi yayi yace. "Karki damu Khadija Amincewa ki kawai nake nema, matukar na samu goyon bayanki zan iya jiranki har ki gama karatun ki, don Allah Khadija kar kice a'a?". Shuru nayi bance komaiba Uncle Naira ya cigaba da magiya, sosai na takura da zama a inda yake saboda har ga Allah warin sigari yake min, ga bakar yunwa da gajiya da suke jikina, hakan yasa nace. "Shikenan komai ya wuce, abinda nake so dani da kai shine mucigaba da Addu'a Allah ya zab'ar da abinda yafi alkairi". Murmushin jin daɗi yayi ya amsa da Ameen, sallama nayi mishi na mike na shiga cikin gida. Abinci na fara ci kamin nayi wanka na rage gajiyar dake jikina, zama nayi gefen Sahura dake goge kayan Aunty Aliya muka cigaba da hira, anan Baby tazo ta samemu itama ta zauna aka cigaba dayi da ita.
Bayan isha'i muna zaune a palo muna kallon TV Hajiya Indo ta sauƙo cikin takun kasaita, da sauri na sauƙa na zauna a k'asa, bayan ta zauna munyi mata sannu da fitowa kallo na tayi na y'an mintuna kafin ta tab'e baki tace. "Dadyn ku yana hanya gobe in sha Allah, zaki koma sama da kwana, kuma na rantse da Allah naji wata magana a bakin Alhaji idan ya tafi zaki raina kanki, don ku marayu akwai munafurci da haddasa husuma". Shuru nayi ina mai tsananin jin zafin maganganun ta. "Don kutumar ubanki ina magana kin min shuru idan uwarki ce zaki mata haka?". "Aa Mommy kiyi hakuri". Na ambata a tsananin firgice, dogon tsaki taja tace. "Tashi ki koma gun Sahura zan maganan tu da yarana". Da sauri na mike har ina had'a kafafu na wuce ɗaki, gefen gado na samu na zauna na saki marayan kuka, zuciyata tana karaya da zagin cin mutunci da Hajiya take min da take had'awa da iyayena, hanun Sahura naji a jikina hakan yasa sautin kuka na kara fitowa, rungume ni tayi a jikinta ta soma lallashina. "Khadija kiyi hakuri kinji? Babu abinda yake tabbata a doron k'asa sai sarautar Ubangiji, watarana sai labari kicigaba da hakuri kinji?". Share kwallah nayi na dubi Sahura. "Ban san me nayi wa Hajiya ba ta tsaneni Sahura, babu abinda yake min zafi da ita irin zagina da takeyi ta had'a da iyayena da basu a doron k'asa". "Tabbas babu daɗi amma idan kinyi hakuri watarana zai wuce, kuma babu mai tabbata a duniya itama watarana zata mutu za taje inda iyayen naki suke, don Allah ki daina d'aga hankalinki"? To nace na cigaba da sharar kwallah Sahura na lallashina da kalamai masu sanyata zuciya. kallon da ban koma ba kenan nayi alola na d'auki Qur'ani nacigaba da karatu ina jin sanyi a zuciyata, harna idar da karatu na kwanta Baby bata shigo ba, ba mamaki Hajiya ta b'ata mata rai tayi ɗakin su.
Washe gari tun karfe hud'u na asuba Hajiya ta tashemu muka soma aiki da Sahura, saboda jirgin su Dady karfe goma zai sauƙa, Aunty Aliya da Baby suna ɗaki suna bacci, nida Sahura da Hajiya ne a kitchen tana bamu umurni muna aiki, bamu muka samu kanmu ba sai kusan karfe tara da rabi, sosai na gaji sam bazan iya zuwa makaranta ba, shiyasa nayi wanka bayan nayi breakfast na kwanta, ina tsaka da bacci naji muryar Daddy da mutanen gida ana masa sannu da isowa, cike da murna na fito nima na isa gareshi na durkusa na gaisheshi had'e da masa sannu da dawowa, kai tsaye sama ya haura shida Hajiya abinci ma ɗakin tasa aka kai mishi, da la'asar haka ya kwashe mu gaba d'aya harda Hajiya muka tafi makaranta su Khalifa, sosai naji daɗin yanda Muhammad ya jasu a jiki babu wani banbanci, sai kusan magrib kafin muka bar makarantar muka dawo gida.
Harga Allah na saba da kwana a ɗakin Sahura saboda nafi sakewa, amma haka na daure saboda umurnin Hajiya na nufi ɗakin su Baby, koda wasa ban hau musu gado ba, shinfida nayi na kwanta abina, dake akwai gajiya a jikina tuni bacci ya d'aukeni, Ina jin tashina da baby takeyi Amma nayi biris saboda harga Allah babu abinda zaisa na hau gado Aunty Aliya tazo taci zarafina. Washe gari da hantsi Muna zaune da Dady a palo cikin dabarar yake tambayata ina jin daɗin zama ko akwai abinda akemin, fuskata d'auke da murmushi nace. "Wallahi Dady bakomai Ina Jin daɗi sosai". Yaji matukar daɗin Jin furucina, kwana Uku yayi ya koma, Muna dawowa daga rakiyar airport Hajiya tasa na kwaso kayana na mayar ɗakin Sahura.
Ta bangarena da Uncle Naira kuwa tun daga ranar da mukayi magana na ɗan saki jiki dashi, idan ya kirani ina d'auka amma baya ga gaisuwa bana iya tofa masa kalma d'aya cikin maganar sa. Duk bayan kwana biyu yake zuwa gidan saboda ya ganni amma sam bana bashi fuskar muyi zance, na fake masa da maganar Daddy na zurfin karatu da yake so muyi.
A cikin wannan yanayi muka soma shirin rubuta final exams, sosai na mayar da hankalina akan karatu na fita tsabgar Uncle Naira, saiya kirani sau biyar a rana baifi sau d'aya zan d'auka ba, wannan shariya da nayi wa Uncle Naira sosai ya tashi hankalin sa. Ranar wata Alhamis na fito daga school ina neman napep wata karamar motor kirar Honda Accord ta tsaya a gabana, ɗago ido nayi na kalli motor mu kayi ido biyu da saurayi da ba zai wuce shekara 33 ba, wani irin fad'uwar gaba na tsinci kaina dashi nayi saurin sunkyar da kaina k'asa na matsa kaɗan daga gun motor, fitowa yayi ya nufo gareni da sallama da sassanyar muryar sa. "Wa'alaika salam na amsa a takaice na cigaba dasa hanu wa masu napep. "Baiwar Allah barka da rana, yauwa na amsa ba tare dana kalleshi ba, sunana Ibrahim, kiyi hakuri nayi miki magana a hanya, dole ce tasa haka saboda idan na bari kika kauce min ban san Ina zan sake ganinki ba, ki taimakeni ki saurareni kona minti d'aya ne?". Ban san meyasa na kasa yi mishi musu ba na tsinci kaina da tsayawa. "Ina jin ka?". Na ambata fuska babu walwala. "Allah ya miki albarka, don Allah ki taimakeni da number wayarki da sunanki, sauran bayani zan miki a waya tunda makaranta kika dawo bai kamata na tsayar dake a cikin rana haka ba". "Bana da waya". Na ambata nasa kai zan wuce, da sauri yasha gaba na. "Don Allah nace? ki dubi girman Ubangiji ki bani number ki?". Tsayawa nayi cak saboda girman Allah daya hadani dashi nace "A Ina zan rubuta maka?". Wayarsa ya fito dashi cikin aljihu ya miko min, rubuta masa number nayi na mika masa. "Nagde sosai suna fa?".
"Khadija". Na ambata nasa kai na wuce.
Uncle Naira Ashe duk abinda ke faruwa akan idon sane, ganina tare da bakon mutum yasan ya tsaya bai k'araso ba, karb'a waya da nayi nasa number ta sosai ya tashi hankalin sa, haka ya tashi motor yabi bayana zuciyar sa na kitsa masa munanan Abu akaina. Ina sauƙa a napep na hango sa ya had'a fuska, ko a jikina nasa kai zan wuce ciki. "Khadija?". Ya ambaci sunana. "Na'am na amsa na ɗan tsaya. Murya a dake yace. "Shigo motor magana za muyi?".
"Aa yi maganar ka ina sauraron ka". Iska mai zafi ya furzar. "Wani gardi ne kika bashi number wayarki a bakin hanyar school d'in ku?". "Nima ban sanshi ba". Na ambata a takaice. "Wow shine har zaki d'auki number wayarki ki bashi? Wannan shine burin da kike so ki cika wa Alhaji Kabiru na son yin nisan karatu? Tun ba'aje ko Ina ba kin fara tara samarin y'an ashawo?". Ɗago ido nayi na kallesa. "Ikon Allah naga hakan ba laifi bane uncle Naira don na bada number ta ma wani, kuma a...." Hasken wuta dana hango shiya hanani k'arasa magana saboda zafin Marin da uncle Naira yamin. "Ni kike bawa amsar cewa ba laifi bane don kin bada number? To wallahi karya kikeyi Khadija baki isa wani ya shiga tsakanina dake har ya hanani cikar burina akan kiba". "Shine zaka mareni?". "An mare ki har dukan ki zanyi useless kawai". Kuka na fashe dashi na wuce cikin gida zuciya ta namin zafi...