AMATURRAHAMAN

25

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 25

*بسم الله الر حمن الر حيم*

******* Washe gari Abba ya sauka a Kano a gidan da Zayyad ɗin ya sauka suka tattauna sosai kafin suka fita suka nufi inda za'a fara gudanar da aikin.

Ranar haka suka yini shige da fice akan aikin sai dare suka koma masauki, cikin sati ɗaya kullum sai sun fita inda aka kama aiki gadan-gadan kuma yana tafiya cikin tsari.

Sai da komai ya kan-kama aikin ya fara nisa kafin suka wuce Katsina ya ɗanyi kwana biyu ya huta kafin tafiyarsa China shigo da wasu manyan ingina da Company ke buƙata.

****** A mota suka wuce Katsina tare da Abba sai sojojinsa, tunda safe suka wuce hakan yasa suka isa da wuri, sun samu gidan an shirya musu tarba sosai musamman ma Ammah dake farin cikin dawowar yaronta daya kwana biyu bai zoba ga kuma Miji da yake a ɓangarenta, don haka basu huta ba ita da Haneen da masu aikin ɓangarenta har sai da suka tabbatar komai yayi dai-dai.

Ɓangaren ƴammatan gidan suma ba a barsu a baya ba don wannan lokacin ko waccen su ta shirya tsaf don yaƙin samun soyayyarsa musamman da a kullum yake ƙara bunƙasa a harkar Kasuwanci bayan aikinsa da yake da babban matsayi. Tako ina ya gama haɗuwa bai da makusa, duk wacce tayi nasarar samunsa ba ƙaramin kamu tayi ba.

A ɓangaren Iyayensu mata kowacce ta shirya taya ƴarta yaƙin don haka ko wacce take ba Tata ƙwarin gwiwa da bata tabbacin itace mai nasara, waɗan da kuma basu faɗa ba amma suna nuna alamu suma suna nan kowa da abinda ya aje a zuciyarsa.

Bangaren Hajiya Ruƙayya kuma ba ƙaramin baƙin ciki da ɓacin rai take ciki ba akan aikin da aka fara gadan-gadan, ga kuma yanda taga hankalin kowa a mansion ɗin ya karkata kansa bayan ga ɗanta nan yana gallafiri ba wanda ya damu da shi bare a bashi muhimmanci.

Sauƙin data samu ɗaya ne na ganin aikinta ɗaya bai tashi a banza ba tunda har yanzu ko maganar aure baya so bare akai ga yin auren, don haka ta zage take ƙarawa malamanta kuɗi akan a hakan don tayi Alƙawarin sai dai ya tabbata a haka ba aure bare ya samu magaji ko iya haka ta rama baƙin cikin da Hajiya Busaina ta ƙunsa mata.

Zaheera....

Yau tana cikin matsanancin farin cikin da bazata iya misaltawa ba na dawowar sanyin idaniyarta, tunda ta samu labarin zuwan nasa da dalilin zuwan a bakin Dady yana sanar da Momy taji kanta ya ƙara girma. Burinta ɗaya a yanzu shine na zama mtar Marshal kuma attajirin ɗan Kasuwa, matuƙar hakan ya tabbata ta san ta gama more wa kowa sai dai ta riƙa kallonsa a ƙasanta a cikin ƴammatan gidan.

Tana komawa ɗakinta ta ɗau waya ta kira ƙawarta Samra ta sanar da ita "Ke gobe fa Marshal zai dawo nake nan zaune ba wani shirin da nayi."

"Haba da gaske? To miye plan ɗin ki?." Samra ta tambaya tana jin daɗi na cika zuciyarta sabo ko ba komai zata samu damar ganinsa ta hanyar zuwa wurin Zaheera saboda itama ba'a barta a baya ba cikin waɗanda suka mato masa.

"Yanzu dai kizo muje wurin gyaran jiki zanyi gyara kafin komai don so nake wannan lokacin na doke ko wacce yarinya dake ƙulaficinsa a gidan nan don naga waccen yarinyar sai wani rawar kai take yi!." Zaheera faɗa cike da kishin dake danƙare a zuciyarta.

"Ok ina zuwa hakan yayi kyau ƙawata kar ki daga ƙafa." Samra ta faɗa tana hararar wayar tamkar Zaheera ce a gabanta. Tana kashe wayar tayi tsaki tana faɗin "Aikin banza kawai, sai ta riƙa nunawa tamkar don ita kaɗai aka halicce shi."

Tashi tayi ta shirya don itama gyaran jikin zata yi tayi kwalliyar tunda allura ne a cikin ruwa mai rabo sai ya ɗauka. Da haka taje ta ɗauki ƙawarta ta a motarta suka nufi wani haɗaɗɗen wurin gyaran jiki inda manyan Mata ke zuwa akayi musu duk abinda ya dace har da kitson attachement aka yiwa Samra.

****

Zayyad kuwa bayan sun iso ɓangaren Baba Alhaji suka nufa shida Abba suka gaishesu kafin suka nufi sassan Ammah ya gaisheta ya wuce ɓangarensa don kintsawa kafin ya dawo cin abinci don duk a ɓangaren Abba zasu yi zaman cin abinci gaba ɗayansu har Hajiya Ruƙayya da iyalanta don duk sanda Abba ya dawo daga tafiya haɗuwa suke gaba ɗaya suci abinci kafin mai Miji ta amshi mijinta.

Ammah ma ɓangaren Abba ta bishi ta taimaka masa ya shirya kafin suka yi zaman cin abinci da suka gama shiryawa ita da Haneen, bayan sun kammala suna hira ne Ammah ta kasa riƙe abinda ke ranta ta kalli Abba tace. "Amma Abbansu baka ganin ya kamata kayiwa Yayansu magana akan fito da mata yayi aure saboda naga idan aka ƙyaleshi bai da niyar yin hakan!." Ta ƙare cikin damuwa da alama itama rashin auren nasa yana damunta dannewa kawai take.

Ɗagowa Hajiya Ruƙayya tayi ta kalleta kafin ta ɗauke kai a zuciyarta tace 'har abada ba zakiga wannan ranar ba matuƙar ina raye.'

Ɗagowa yayi ya kalli Ammah jin abinda ta faɗa sai yaga da gaske take maganar har cikin zuciyarta don ta wani marai-raice tana kallon Abba da jiran jin abinda zai faɗa.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "To kaji kai abinda Mamanku tace don haka sai ka maida hankali ka fitar da mata tun kafin ta bada kai sadaka." Ya ƙare da sigar zaulaya. Ai kuwa dariya Muzaffar da Haneen suka saka suna ƙunshe baki ganin boss ɗin ya watsa musu wannan kallon nasa mai sawa su shiga tai-tayinsu.

"Daina harararmin yara ba laifinsu bane." Abba ya kuma faɗa kasancewarsa mai barkwanci da sakewa cikin iyalansa. Hajiya Ruƙayya da yaranta tamkar basa wurin ɗin ko tari ba wanda yayi.

A natse ya buɗe baki yace "In sha Allah Abba."

"To kinji, sai ki saki fuskar." Ya kuma faɗa yana kallon Ammah data sauke ajiyar zuciya tana jin har cikin ranta ya kamata ya aje iyali ko don samun nutsuwarsa da tasu baki ɗaya don ta gaji da ƙansnun magan-ganun dake yawo a cikin familn.

Miƙewa yayi ya musu sallama ya fice don yana buƙatar hutawa kafin ya shiga gaishe da Uncles ɗinsa. Ɗaya bayan ɗaya kowa ya fice aka bar Ammah da Mijinta.

♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️

Tana kwance saman katifarsu da ita kaɗaice shimfiɗe a tsakar ɗakin nasu daya sha shimfiɗar ledar tsakar ɗaki sai labulaye sai kuma lokar kayan sawarsu dake can gefe ɗaya. Litattafanta na makaranta take dubawa saboda jarabawar Jamb da zata zana wacce Ya Nafi ce ta biya mata kuɗin, tayi nisa sosai cikin calcution ɗin da take gwada wa na Chemistry Ya Nafi ta shigo da ƙatuwar laida riƙe a hannunta.

A natse ta ɗago ta amsa mata sallamar da tayi tana mata sannu ta maida kai ga abinda take ba tare da tabi takan ledar da ta aje mata a gabanta tana cewa. "Amah ki duba waɗannan kayan kiga waɗanda kike so."

Aje pen ɗin hannunta tayi ta zuro ƙafarta ƙasa ta jawo ledar ta shiga ciro kayan dake ciki, kayan sawa ne dogayen riguna ƴan kanti sai abayoyi masu kyau ta mayar ta aje ta kalleta tace. "Ya Nafi a ina kika samo wannan kayan haka?."

Kallonta Ya Nafi tayi tana raya cewar 'To Babata yanzu zata tsare ni da tambayar yanda aka yi na samu.' a fili kuwa cewa tayi Alhaji ne ya kaini shopping shine na ɗauko maki kema." Bata bata damar ƙara magana ba ta janyo jakarta ta fito da wasu takardu ta miƙwa Amaturrahaman ɗin tana cewa "Duba wannan sune takardun gidan dana saya mana a can bayan layinmu zan kaiki ki gan shi, ko gobe muke so zamu iya tarewa a cikin sa. Amma sai dai bana son bawa Kawu Isa damar da zai sa Sule ya gyara nan ya saka Matarsa kamar yanda yake so domin haƙƙinmu ne gadon Mahaifinmu."

Amsa tayi ta shiga dubawa kafin ta miƙa mata tace "Allah ya sanya alkairi Allah ya jiƙan Umma, naso ace tana raye zuwa lokacin da zamu yi mata gata."

"Ameen ya Allah, harda Abba ma Allah ya masa rahama." Ya Nafi ta faɗa. Shiru Amaturrahaman tayi bata ƙara cewa komai ba tana tunanin rayuwa har Ya Nafi ta adana takardun a inda suke aje abubuwansu masu mahimmanci.

Sai da ta dawo ta zauna ta janyo ledar ta ware nata kayan ta miƙawa Amah nata sannan ta janyo ƙaramar ledar ta shiga fito musu da kayan ciye-ciyen da ta jido musu.

******* Kamar yanda Alhaji Tanimu ya buƙaci ganin Dugaz a office ɗinsa yaje ya same shi, Dugaz Babban yaronsa ne wanda yake masa mugayen ayyukan sa ba tare da an taɓa samun kuskure ba. Irin mutanen nan ne da kwata-kwata basu da imani bare tausayi a cikin zuciyarsu duk abinda aka saka su shi suke aikatawa basa saɓa umarnin iyayen gidansu.

"Barka da hutawa mai gida." Dugaz ya faɗa cikin kakkaurar muryarsa mara daɗi irin ta riƙaƙƙun ƴan daba wanda shaye-shaye ya gama lalata wa.

"Barka dai Dugaz." Alhaji Tanimu ya faɗa yana nuna masa wurin zama, bayan ya zauna Alhaji Tanimu yayi danne-danne a wayarsa ya kamo hoto ya miƙa masa wayar.

Amsa yayi ya ƙarema hoton kallo kafin yace. "Me kake so ayi mata mai gida?."

"Akwai abuna a hannunta, wannan abin da kuka amso a hannun wannan yaron shine ta samu damar ɗauka, so nake kota wane irin hali a amso shi a lalata shi ban damu ba da tayi rai ko ta mutu ita ta saya da kuɗinta ni dai buƙatata shine a lalata hujjar dake hannunta." Ya faɗa cikin rashin imani.

"An gama mai gida." Dugaz ya faɗa yana miƙewa ya nufi ƙofa bayan Alhaji Tanimu ya bashi bandir ɗin kuɗi. Da sauri Gaddafi wanda daya gama jin tattaunawar tasu ya laɓe a bayan ƙofa zuciyarsa na dokawa da ƙarfi saboda ya san rashin imanin Dugaz. Sai da ya wuce sannan ya shiga Office ɗin yana sauke ajiyar zuciya don duk tsagerancinsa yana tsoron dabar su Dugaz don basu da imani ko kaɗan.

Duƙawa yayi ƙasan kafafun Mahaifinsa ya riƙe ƙafafunsa ya shiga roƙonsa "Dad don Allah ka masa magana kada ya cutar da ita wallahi ina sonta, ban san cewa da gaske nake sonta ba sai yanzu na maka alƙawarin zan amso maka abinka da kaina amma dai a bar min ita aurenta zan yi!." Ya faɗa hawaye na zubo masa saboda da gasken sonta yake kuma ya shirya aurenta idan ta yarda.

Da farko kawai ya ɗauketa ne a matsayin abokiyar jin daɗinsa, sai dai a hankali soyayyarta ta yiwa zuciyarsa mugun kamun da yaji ba zai iya rabuwa da ita ba. Da farko yayi niyar wulaƙanta ratuwarta akan mua'amalar da tayi da Mahaifinsa bayan suna tare, sai daga baya kuma yaji ba zai iya ba.

Ɗago shi Alhaji Tanimu yayi saboda yana masifar son ɗansa don shi kaɗai Allah ya basu, amma sai dai ba zai iya masa wannan alfarmar ba don yarinyar taurin kanta da tsaurin idonta shi yaja mata koma miye.

"Ya isa haka, tashi ka zauna." Ya faɗa yana riƙo kafaɗunsa.

"Dady zaka rabu da ita ɗin?."

"Kar ka damu zan masa magana ba zai mata komai ba, kawai iya abin zai amso." Ya faɗa masa don hankalinsa ya kwanta. Tashi yayi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya duk da dai bai ida yarda da Mahaifin nasa ba don ya san waye shi idan yayi niyar abu.

Yana fitowa daga Office ɗin yayi ta kiran wayarta bata ɗauka har kira kusan goma, bai gaji ba ya ɗauki mota ya nufi gidansu don ta bashi abin yanzu ya damƙawa Dady hankalinsa zai fi kwanciya da hakan.

Koda yaje gidan bai sameta a gidan ba har ta fice yawonta ji yayi tamkar ya fashe da kuka.

✨✨✨✨✨✨✨✨

Tun bayan maganar da suka yi da Momy yake jiran jin sakamako amma shiru bata ce komai ba, har yaran ya kawo mata kamar yanda ta buƙata ya zauna jiran ko zata masa maganar amma tayi shiru har ya gaji ya tafi gida. Gaba ɗaya a ƴan kwanakin nan yana cikin damuwar da ta ɗauke masa hankali daga kan ƴammatan da yake harka dasu, haka zasu yi ta masa naci yana rejecting ɗin su.

A ɓangaren Suhaima ma gaba ɗaya ta kasa samun kansa don ɗan kusancin da suka fara samu ma ƙoƙarin lalacewa yake, baya dawo wa gida sai dare. In ya dawo ɗin kuma ɗakinsa yake shigewa ya rufe yace mata baya son damuwa.

Tayi kuka har ta gaji ta tsinewa yarinyar data hargitsa shi sau ba adadi, koda ta sanar da Momynta kuma haƙuri ta bata ta kwantar mata da hankali akan cewa zai daina na ɗan lokaci ne zai manta da yarinyar suci gaba da rayuwarsu tunda aure dai ba yinsa za ai ba. Da wannan take ɗan samun natsuwa tayi haƙuri ta zuba masa ido.

Kamar yau ma data ɓata lokaci ta tsara masa girki tayi wanka tayi kwalliya ta zauna zaman jiransa, bai tashi shigowa gidanba sai dab da magrib ya shigo fuskar nan a haɗe ba alamar fara'a. "Sannu da zuwa Abban Jalila." Ta faɗa tana ƙoƙarin amsar jakarsa.

"Yauwa." Ya faɗa da ƙyar yana ƙoƙarin shigewa ɗakinsa "Abban Jalila na..." Hannun daya ɗaga mata ne ya hanata ƙarasa faɗar abinda tayi niyya ya shige ɗakinsa ya rufe.

Bai fito ba sai da aka kira sallar magriba ya fita, bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Ƙoƙarin shigewa yake ta kasa jurewa ta sakar masa kuka wanda hakan ya sanyayar masa da jiki ya dakata ya yujo ya kalleta yana faɗar miye kuma?."...

Oum Fatima