AMATURRAHAMAN

26

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 26

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Wani sanyi taji a ranta na kulatan da yayi don haka ta ƙara matso hawayen tana ƙara marai-raicewa, dawowa yayi ya zauna saman kujera ya nuna mata wuri yace "Zauna in ji minene."

Kasa ɓoye farin cikinta tayi ta matsa ta zauna kusa da shi "Minene matsalarki ne wai?." Ya tambaya fuska ba walwala.

"Kaine matsalata Abban Jalila gaba ɗaya na kasa gane maka a kwanakin nan, baka saurarata in nayi girki baka ci, baka zama kayi hira dani ko kaji matsalata, ga yara basa nan kaɗaicin ya min yawa." Ta faɗa da alamar har cikin zuciyarta abin ke damunta.

Iska ya furzar kafin yace "Amma ai kin san ina cikin damuwa ya kamata ki bar ni naji da abinda ke gabana ba ki ƙara min wata damuwar ba da wannan ƙorafi da mitar naki." Ya faɗa yana dafe kansa dake masa ciwo.

"Amma Abban Jalila dan kana cikin damuwa sai ka riƙa shiga haƙƙina kana tauye ni akan wata Macen dako auren nata baka yi ba!." Ta faɗa cikin tsananin damuwa da kishin dake danƙare a cikin zuciyatra.

"Ba sai kin yi magana a kanta ba, ya kike so ayi yanzu." Ya faɗa don baya buƙatar aja maganar har ta faɗi abu marar kyau akan abinda yake so azo al'amurra su ƙara lalacewa kuma.

"Ga abinci can na shirya maka muje kaci." Ta faɗa tana nuna masa table ɗin data shirya masa.

"Bari na watsa ruwa sannan." Ya faɗa yana hayewa sama.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

Isasshen bacci ya yayi a yinin ranar ba inda yaje, sai da yaje sallar magrib a masallaci suka haɗu da Uncle Maina. Sai bayan sallar isha'i suka fito tare suka nufi sashen Baba Alhaji tare da Uncle Hashim da Uncle Yusuf da Abba har su Muzaffar gaba ɗaya Salim ne kawai babu sabo da baya ma gidan bare yaje masallacin yana can yawon gantali da abokai da ƴammata sai barr Kabir da baya gari.

A babban palonsa suka samesu shida Hajiya Iya da take haɗa masa abinci sai Rashida da yaranta ke kiranta da Mammah wanda hakan yasa sunan ya bita gaba ɗaya haka kowa ke kiranta a mansion ɗin.

Rashida (Mammah) itace auta a cikin duka yaran Baba Alhaji ƴar matarsa ta biyu ce mai suna Safina su biyu ta haifa a gidan Allah ya mata rasuwa, Barrister Kabir shine ɗanta na farko wanda bata ƙara ba sai akan Rashida wacce a wurin haihuwar ta ne Allah ya amshi ranta.

Hajiya Iya ita taci gaba da kula da Rashida tun tana jinjira tamkar ita ta haife ta, ta haɗa Kabir da Rashida ta riƙe tamkar itace ta haife su don idan ba faɗa maka aka yi ba baka isa ka gane ba. Wannan yasa gaba ɗaya yaran suma suka tashi kansu a haɗe babu wani ban-banci.

Gaba ɗayansu a can sukayi dinner cikin sakewa da shaƙuwar dake tsakaninsu Hajiya Iya na mitar data saba akan rashin auren Zayyad harma da Salim da Muzaffar gaba ɗaya, Uncle Maina na kare masa da nuna mata cewar lokaci ne bai yi ba saboda Zayyad ɗin ɗan gidansa ne yana matuƙar ƙaunarsa tamkar ɗan daya haifa da cikinsa don hatta wasu ɗabi'un a wurinsa Zayyad ɗin ya ɗauko, hakama ra'ayinsu na zuwa ɗaya a lokuta da dama har akan zaɓin aiki ma.

Shi da ake yi a kansa ko kai bai ɗaga ya dubeta ba bare ya bata amsa wanda hakan shi ke ƙara ƙuleta da shi tayi ta sababi tana kiransa da dunkum ɗin wofi mai abin haushin tsiya.

Suna haka Zaheera da taci uwar kwalliya taje ɓangaren Zayyad da sunan kai masa abinci ta samu baya nan shine ta nufo nan don ta san ba zai wuce nan ɗin ba don Fatima ta sanar da ita baya wurin Ammah don suna can tare da Haneen suna kallon Koriyan movies abinda suka fi auki a kai.

Da sallama ta shigo tana yauƙi sai dai ganin gaba ɗaya Iyayensu yasa taci birki tana kallon su. "Ƙaraso mana ja'ira kika tsaya kina kyafta ido sai kace mara gaskiya." Hajiya Iya da taga shigowarta ta faɗa.

Gaba ɗayansu ɗagowa suka yi don ganin dawa Hajiya Iya take amma banda shi da kansa yake a ƙasa yana shafa wayarsa. Ƙarasowa tayi tana tura baki gaba jin abinda Hajiya Iya ta faɗa.

Wuri ta samu ta zauna ta shiga gaishe da Iyayensu kafin ta matsa kusa da shi tace. "Ina yini Ya Zayyad, an dawo lafiya."

Ba tare daya ɗago daga abinda yake yi ba yace "Lafiya Alhamdulillah." Ba haka taso ba, so take ya ɗago ya kalleta yaga kwalliyar data kashe kuɗi aka yi mata duk don ta burgeshi amma yaƙi ko kallon inda take bare yaga wata kwalliyarta.

Haka ɗabi'arsa take bai cika kallon mutane ba, ko Haneen da suke ciki ɗaya baya tsareta da kallo idan ba laifi tayi masa ba shine zai hukunta ta da idanunsa.

Kamar haɗin baki sai ga Anisa itama tare da sauran ƴanmatan sun shigo da hayaniyarsu sai dai suna shigowa suka yi tsit sakamakon wanda suka fara cin karo da shi.

A ɗarare suka ƙarasa suka zauna suka shiga gaishe su a natse tamkar basu ne suka shigo da hayaniya ba. "Ƴan ƙwal Uba, wasa ma wuri gare shi ashe." Hajiya Iya da bakinta baya shiru ta faɗa.

Yana jinsu bai ko ɗaga kai ba bare ya kalle su sai ma amsa gaisuwar da suke masa da yayi a dake, tashi yayi yayi musu sallama ya fice don zuwa ya gaishe da Iyayensu mata kafin ya wuce wurin Ammah yayi hira a can yasan tana son hakan ko bata faɗa ba sabo da karar da take masa.

Bayan fitar sa ajiyar zuciya suka shiga saukewa kafin suka ƙyal-ƙyale da dariya suna sauke ajiyar zuciyar samun saken da suka yi don ƙwaƙwƙwaran motsi ma nasa sakewa suyi in yana wuri.

"Ja'iran yara ni na rasa irin wannan tsoron da kukewa Mazan fama, ga shi dai ba duka ba zagi amma kunfi jin tsoronsa fiye da kowa a gidan nan." Baba Alhaji ya faɗa yana tsokanar jikokinsa.

"Ai boss ɗin ne Baba kwarjininsa kaɗai ya isa ya ladabtar da mutum." Muzaffar ya faɗa yana murmushi. "Mazan gaske kenan." Uncle Maina ya faɗa cikin raha.

Zaheera kuwa yana fita tabi bayansa da sauri tana haɗawa da gudu don ta samu ta cimma sa.

Jin kamar ana binsa a baya yasa shi dakatawa ya juyo kaɗan don ganin mai bin nasa, ƙarasowa tayi tana haki tace "Yaya dama abinci na kai maka baka nan, ko in je in kawo maka yanzu?." Ta faɗa tana tsare shi da ido. Kallonta yayi na ƴan seconds yana nazarin yanda yarinyar take shishshige masa sosai da sosai da alama har yanzu tana nan da shirmen da take a kansa.

Ɗauke kai yayi yana cewa "No bana buƙata." Daga haka bai ƙara ba yaci gaba da tafiyarsa. Jin kamar taci gaba da bin nasa ne ya wai-wayo yace "Kina buƙatar wani abu ne?."

Tsayawa tayi ta langaɓar da kai tana jin zuciyarta ba narkewa a kansa. "Ba buƙatar ki bini ok?." Ya kuma faɗa a taƙaice yana zuba mata ido don ya san ba cikakken hankali ne da yarinyar ba zata iya binsa har can, da sauri ta gyaɗa kai ba tare data shirya ba.

Tafiyarsa yaci gaba dayi har ya ɓacewa ganinta tana nan a tsaye ta kafe hanyar daya bi da kallo tamkar taje ta rungume shi take ji ko zata samu samu sauƙin azalzalar da ƙaunarsa take mata a zuciya da ruhi.

"Allah ka mallaka min wannan bawan naka kasa ya zamo nawa ni kaɗai!." Ta faɗa tana jin son sa mai girma yana ƙaruwa a cikin zuciyarta.

"Ba Ameen ba!." Taji an faɗa daga bayanta wanda hakan yasa ta juya don ganin wace mai tsaurin idon ce.

Anisa ce data kasa samun natsuwa ganin Zaheera ta bi bayansa hakan yasa ita ma ta sulale ta fito don ganin abinda zata yi. Dama ita tayi tunani don ta lura yarinyar tafi kowa tsaurin ido a gidan don haka ta juyo a matuƙar fusace tana jin tamkar ta wanka mata mari tace.

"Ke! Ina wasa dake ne wai!?." Ta ƙare maganar cikin fushi tana nufo ta.

Murguɗa baki Anisa tayi zata fara rashin kunya su Abba suka fito hakan ne yasa ta tsuke bakinta tayi gaba tana maganar zuci. Itama Zaheera fasa nufarta tayi ta wuce da saurin tana jin duk sanda ta kama yarinyar nan sai ta koya mata hankali.

***** A cikin sati biyun da Zayyad yayi a gida Zaheera ta dage sosai wurin samun kusanci da shi wanda baya bata damar hakan, ji take kamar zata yi hauka idan taga yana nunawa tamkar bai san da ita ba ko ƙudirinta a kansa.

Hakan da Anisa ta gani ne yasa itama ta yi ƙoƙarin rage tsoronta ta tunkare shi da niyar sanar da shi tunda Momy ta kasa yin komai ga Aunty Zaheera na yiwa kanta fighting, don haka itama zata yiwa kanta yaƙi.

Yana Zaune a cikin ƙaton gerden ɗin gidan dake can bayan part ɗinsa yana duba wani sabon design ɗin da Companynsu suka fitar na haɗa jaka da takalma wanda shida Abba keda kaso tamanin 80% na hannun jari a cikinsa, 20% shine sauran da abokan kasuwancinsu suka zuba.

A hankali take takawa jikinta na rawa duka ƙwarin gwiwar data tattaro yana zagwanyewa ba tare data shiryawa hakan ba. Sai da tayi Namijin ƙoƙari ta ƙarasa gabansa ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya tamkar wadda tayi tseren gudun neman ceto.

Jin tsayuwar mutum a saman kansa yasa ya ɗago kansa daga saman laptop ɗin ya zuba mata idanunsa masu tsananin kwarjini wanda suka idasa ruɗata kawai ta zube ƙasa ta fashe da kuka don bata da abinda ya fiye mata hakan.

Kallonta yaci gaba dayi mamakinsa na ƙaruwa da tunananin abinda ya sameta take irin wannan kukan haka.

"Wani abu ya faru ne?." Ya faɗa a taƙaice cikin muryarsa ta kai tsaye.

Da kyar ta buɗe baki cikin muryar kuka tace "Don Allah Yaya ka taimaki rayuwata ka aureni wallahi ina tsananin sonka zan iya rasa rayuwata idan ka barni ka auri wata!." Da ƙyar ta iya ƙarasa maganar tana shiɗewa tsabar kwarjini da tasirin idanun daya zuba mata suka yi mata, sai dai koba komai ta samu ta amayar da abinda ke wahalar da zuciyarta.

Zayyad kuwa mamaki ne ya kusa kashe shi a zaunen da yake ya zubawa Anisa dake duƙe a gabansa ido yana lissafa shekarunta duka da basu haura ashirin ba amma ta samu ƙwarin gwiwar zuwa gaban Namiji ta roƙe shi ya aureta, Namijin ma shi da yake Yaya a gare ta.

Da ƙyar ya iya danne ɓacin ransa ya nuna mata hanya yace "Wuce gida." Ba musu ta miƙe ta wuce tana waigensa da jin sanyi kaɗan a zuciyarta, koba komai ta riga Aunty Zaheera dama duk masu sonsa furta masa tana son sa, ko iya haka taci rabin yaƙin.

Ya daɗe yana juya abin a ransa bayan tafiyarta yana mamakin yanda aka yi sakaci da tarbiyyar yaran suka zama haka, kwanaki ɗayar taje ta daki ƴar mutane da sunan tana son sa, ganin bai hukunta ta ba yasa ita kuma wannan ta samu kwarin gwiwar zuwa ta faɗa masa da kanta, idan yaci gaba da zuba musu ido bai san me zasu yi ba a gaba don haka zai takawa abin birki tun wuri.

Da dare bayan sallar magrib yana zaune a parlon Hajiya Iya ya aika mai aikinta yasa ta kirawo masa gaɓa ɗaya ƴanmatan gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci suka hallara kowacce jininta a farce da tunanin me suka yi masa.

Sai da ya gama shan ƙamshinsa har Hajiya Iya na masa maganar ya aje yara bai ce musu komai ba ya bar su da fargaba.

Sai da ya mula don kansa kafin ya ɗago ya ƙare musu kallo gaba ɗayansu ba wacce bata isa aure ba don wasu sun kammala karatu wasu kuma suna cikin yi ne. "Na baku sati biyu ko wacce ta fitar da wanda take so a aura mata, tunda kun riƙa har kun iya roƙar Namiji ya aureku!." Ya faɗa a natsensa yan ɗauke kai tamkar bada su yake ba.

Hantar cikin ko waccensu ce ta kaɗa suna jin wani irin tashin hankali wai sati biyu su fito da Miji a musu aure.

"Kai ɗan nan lafiyarka kuwa? Wane irin su fito da Miji a sati biyu a musu aure tamkar an gaji da su." Hajiya Iya ta faɗa.

Baba Alhaji kuwa dake zaune saman kujera murmushi kawai yayi don ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya tunda ya san komai game da son da yaran ke masa, da rigimar da suke yi a kansa. Har zuciyarsa yake so yaga Zayyad ɗin ya aje Iyali amma hakan ba zai sa su aura masa wacce baya so ba musamman a cikin ƙannensa don gudun lalacewar zumunci.

Kallonsa ya maida saman fuskar Hajiya Iya yace "Eh haka na faɗa, a binda suke so kenan ai."

"Allah Yaya ba so muke ba." Haneen ta faɗa hawaye na cika idonta don ita yanzu ne ma ta fara karatun a makarantar koyon aikin jinya wato School of Nursing kuma ko samarin ma bata kulawa sabo da Ammah ta hanata tace ta maida hankali tayi karatunta a natse tukun.

Zaheera kuwa kamar an matsi bakinta tace "Ni kai na fitar Yaya." Tsit akayi tamkar ɗaukewar ruwa aka zuba mata ido yayinda tayi fiƙi-fiƙi da ido tana kallon mutane.

"Shike nan kaga faɗuwa tazo dai-dai da Zama Hajiya Iya ta faɗa.

Da sauri Anisa ta amshe da cewa "Allah ƙarya take nice nake sonsa kuma har na faɗa masa ma."

Lokaci ɗaya rigima ta ɓalle tsakaninsu sun ma manta da a gaban wanda suke sai da Mammah da saukowarta kenan ta tsawatar musu. Sannan suka saurara.

Gyaran murya yayi kafin ya shiga yi musu ƙwaƙwƙwaran kashedi akan hakan ya kuma ce duk wacce ta ƙara sai ya aurar da ita wa ɗaya daga cikin sojojinsa. Ransa a ɓace ya fice daga gidan inda Mammah ta ɗora da musu faɗa tana cewa.

"Don baku da hankali shi ɗin sa'anku ne da zaku je masa da wannan shirmen, kun ci sa'a ma da bai ɓalla maku ƙafafu ba har yanzu."

Kuka sosai suke yi Anisa na cewa "Allah Mammah son sa nake da gaske kuma zan iya mutuwa akan son da nake masa."

Buɗe baki Zaheera take ƙoƙarin yi Mammah ta daka musu tsawa tace.

"To kun dai ji abinda yace sai ku maida hankali, ku tashi ku bani wuri sakarkarun banza, Ni na rasa yaushe yaran nan suka zama haka? Ko don laifin Iyayenku ne da basa tsawatar muku a kan ko wane shirme."

Baba Alhaji da Hajiya Iya dai na jin su basu ce komai ba har suka fice kafin Hajiya Iya tace "Allah ya kyauta, ba don abin zai zama rigima ba ai da sai ya zaɓi ɗaya a aura masa don na gaji da ganinsa haka yana gantali ba Mace."

"Haba Hajiya sai kace wani ƙaramin yaro, in ma banda tsaurin idon irin na yaran nan ya za'a yi su iya tunkarar Son da wannan shiriritar." Mammah ta faɗa.

"Allah ya kyauta to."

Suna fita sauran ƴammatan suka yi ca!!! Akan Anisa suna mata Allah ya isa akan abinda ta jawo musu suna zaman zaman su. Yanzu ba don Allah ya taimake su Hajiya Iya tasa baki ba da shike nan aure za'a musu ba tare da sun gama more ƴanmatancinsu ba.

Ita dai da gudu ta nufi part ɗin Iyayenta tana rusa kuka don tayi tunanin Hajiya Iya zata saka shi dole ya aureta saboda itama auren take so yayi.......

Dokajo Mansion fa ya ɗau zafi don ƙura na tafe.