9
by @sadiyanasir
RIKON SAKAINA
YA FARU A GASKE
NA
SADIYA NASIR DAN
Arewa Book
sadiya Nasir
SHAFI NA TARA
Murd'a handle din kofar tayi ta shiga, ajiyar zuciya ta sauk'e mai karfi ganin da'bi'ar data jima rabon da taga Alhaji cikin ta wato shan sigari, tabbas duk abinda ya had'a Alhaji da Uncle Naira to ba k'aramar abu bace. Dogon numfashi taja ta k'arasa in da fridge yake ta d'auko ruwa mai sanyi had'e da cup ta isa inda yake zaune ta durkusa ta tsiyaye ruwan ta mika masa. "Ko yaushe idan nayi fushi kai ne mai bani shawarar yanda zan tausashi zuciyata na samu sanyi, don girman Allah ka ajiye sigarin nan ka amshi ruwan nan, ina mai tabbatar maka zaka samu nutsuwa cikin zuciyarka fiye da yanda baka zato, please Alhaji na?". Ta karasa maganar da murya mai sanyi". Iska mai zafi Baffa Kabiru ya furzar ya karb'i cup din ya kafa kai sai da ya shanye ya dire. "Na rantse da Allah sai naga uban daya take wa Mustafa Naira a garin nan, wallahi yanda ya shiga gonata sai na wulakanta sa yaga tozarci mafi muni, zan ajiye masa tarihin da har ya koma ga Ubangiji ba zai manta ba".
"Subhanallah! Meye haka kake fad'a Alhaji?".
"Indo abinda nake so dake kar ki kuskura kice zaki shiga cikin wannan case, bare kiyi tunanin hakurin ki zai saka na sassauta masa, wallahi billahi kinji rantsuwar da nayi? Zan wulakanta Mustafa, babu wani mahaluki da zai shiga gona ta na kyale sa, cin amana haka? Mustafa ya shigo har gida na ya nemi ya keta wa d'iyata haddi? na rantse daga kaina ba zai sake yunkurin aikata haka ba, wannan case har gaban Major".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um! Alhaji wani irin furuci kake haka, don Allah kasa wa zuciyarka salama, shin meye Mustafa yayi maka haka da zafi?".
"Duk iskanci da bad'ala da rashin tarbiya da Mustafa yake aikatawa a waje bai ishesa ba har sai ya shigo gida keta min mutunci? Shikenan da Allah baiyi shigowata gidan ba sai dai naji labari mai muni akan Khadija? A bani amanar yarinya yazo har gidan ubanta yace zaiyi rapein dinta? tirr da haihuwar bunsuru irin Mustafa?".
"What rapein? Hajiya Indo ta ambata gamida dafa kirji?"
"Kwarai kuwa shigowata gidan shiya hana faruwar abinda yaso aikatawa". Ya labarta mata yanda abin ya kasance".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um amma Alhaji bai kamata ka yanke hukunci cikin fushi ba, ai Khadija ba yarinya bace tayi girman da Mustafa ba zai iya far mata ba tare da amincewar taba, mace ita take zubar da mutuncin ta, ba mamaki sun saba sheke ayarsu ganinka yasa ta juya al'amarin saboda ta kare kanta, amma ko giya Mustafa Naira yasha ba zai shigo har gida yace zaiyi wa Khadija wani abu ba, gaskiya ina da jaaa akan al'amarin nan akwai lauje cikin nad'i, wallahi zuciyata ba za taba aminta da haka....
Mari mai kyau Baffa Kabiru yayi mata wanda yasa ta saki ihu mai k'ara ta dafa wajen. "Me yasa baki da Imani Indo? Yanzu idan Aliya ko Baby ce hakan ta kasance akansu kalmar da zata fito a bakin ki kenan? Wato saboda Khadija bake kika haifeta ba shiyasa kike so ki kare azzalumin k'anin ki? To ki bud'e kunnen ki da kyau kiji abinda zan fad'a, wallahil azim ki kayi k'okarin kare Mustafa zaki tarwatsa Auren ki, ina mai baki umurni da kar na sake jin bakin ki a maganar nan". Yana gama fadin haka yaja dogon tsaki ya d'auki key din motor ya fito.
Durkushewa Hajiya Indo tayi a wajen ta saki wani irin kuka, shekara ashirin da biyar kenan suke rayuwa da Alhaji bai tab'a marinta ba! amma yau sanadin rikon marayu zai mata mari sai kace ya samu jaka?
Wayyo Allah ta ambata da karfi ta dafa zuciyarta tana jin tsananin tsanar Khadija.
****
Baffa Kabiru yana fita kai tsaye area command ya nufa, uncle Naira ya bugu har baya iya magana sai numfashi da yake fitarwa da kyar, ganin halin da yake ciki yasa commander din ya bada umurni a kaisa asibiti mafi kusa don duba lafiyarsa. Baffa Kabiru sai da ya tabbatar ya biya kudin komai ya gama dasu kafin ya koma motor ya kira number wani abokinsa da sukayi secondary school Captain Emanuel, wayar bata d'auki lokaci tana ringing ba ya d'auka, bayan sun gaisa anyi raha ta yaushe gamo nan Baffa Kabiru ya bijiro da bukatar sa na son ganin Major ya kuma sanar dashi dalilin da yasa yake so suyi zama. "Oh my God abin baiyi kyau ba, Amma kayi hakuri Major ya tafi gida gobe da misalin karfe goma kazo zaka ganshi". Nagode Baffa Kabiru ya ambata ya kashe kiran.
*****
Tunda muka shigo da Sahura na nemi waje na kwanta nacigaba da kuka tamkar raina zai fita, hakuri kawai Sahura take bani ita kanta taji zafin abinda ya faru, ganin bani da niyyar yin shuru yasa ta mike ta fita cigaba da aikin ta, haka nacigaba da risgar kuka ina tausayin rayuwata har sai da naji kiran sallar la'asar kafin na tsagaira na mike na shiga toilet, ruwan sanyi na zuba wa jikina sosai har gashina sai da na jika ko zanji sanyi kafin nayi Alola na fito, sallar azahar na soma da ban samu yinta akan lokaci ba, kafin na idar Sahura ta kawo min kunun gyada mai zafi da funkaso, bayan na idar murmushi nayi na kauda abincin gefe, a yanda nake Jin zuciyata ba zan iya cin komaiba, kalmar fasika mai raba jikinta wa maza a waje shike min yawo a kwakwalwa yasa naji duk duniyar tafita kaina, meyasa Uncle Naira zai jefeni da mummunar kalma haka? Ina tsaka da tunani naji ringing din wayata, da kyar na iya mikewa na isa inda take, ganin number Ibrahim yasa nayi murmushi na dauka. "Matar so da fatan kin shiga gida lafiya?"
"Alhmdullah Yaya Ibrahim ya jikin Mama?"
"Jiki Da sauk'i, Mama sai maganar ki take, tace ta samu nutsuwa dake tana goyon baya na Aure ki". Murmushin jin dad'i nayi nace. "Allah sarki Mama ta, Ubangiji ya bata lafiya"
"Ameen! Khadija baki da lafiya ne? Naji muryarki wani irin?"
"Eh Yaya Ibrahim kaina ke ciwo amma nasha magani, na tabbata zuwa anjima zai sakeni".
"Subhanallah Ubangiji ya baki lafiya, bari na kyale ki ko zaki kwanta kila kiyi bacci ba". "Shikenan nagode Yaya Ibrahim". "Allah ya k'ara sauk'i ya ambata ya kashe wayar. Runtse Ido nayi wani sanyi na shiga zuciyata, Ina kaunar Ibrahim Ina burin muyi rayuwa dashi ta har abada. "Ya Allah kaci kamin burina". Na ambata a hankali na ajiye wayar.
****
Hajiya Indo na baje a carpet ta sak'a wannan ta kunce wannan wayarta dake cikin aljihun rigarta ta soma ringing, dogon numfashi taja ta fito da wayar, ganin wacce take kira yasa ta sauk'e ajiyar zuciya ta d'auka. "Hello Aminiya tun d'azu hankalina ke tashe na kikkira wayarki sau babu adadi bai shiga ba , tunda ki kace min gidan ki ba lafiya na gaza samun nutsuwa?".
Hawaye Hajiya Indo ta share murya a dishe tace. "Meye ma bai faru ba Aminiya, yau akan Khadija yar riko Alhaji yasa hanu ya mareni, kuma yake ikirari zai iya rabuwa dani na har abada akanta".
"Alhajin......? Hajiya Turai ta ambata gamida dafa kirji? "Kwarai kuwa haka abin yake, na rasa me yake min dad'i a duniya? To wai meye ainihin abinda ya faru?" Nan Hajiya Indo ta labarta mata komaiba, ajiyar zuciya mai karfi Hajiya Turai ta sauk'e tayi shu'umin murmushi. "Tabbas Aminiya sai fa kin tashi tsaye, wallahi idan ba haka ba wannan marainiyar sai ta kashe miki Aure, kin san marayu da sharri kuwa? Bana raba d'aya biyu tayi haka ne saboda zancen Aure da Mustafa yayi mata, tasan idan ba gagarumar sharri ta had'a ba zaiyi wahala bata Aure shiba".
"Ai kuwa ba zata tab'a Auren saba matukar ina numfashi, yaushe zan had'a zuri'a da munafukai, tirr wallahi".
"Abinda nake so dake Aminiya ki nutsu please? Kar kice don Alhaji ya mareki koya miki barazana ba zaki shiga case din dan'uwanki ba, Musfata duk duniya bashi da kamarki, idan zancen nan ya koma cikin family d'in ku laifin ki zasu gani, kinga komai na iya faruwa, ke kika san hanyar da kike bi ki shawo hankalin Mijin ki idan yayi fushi, ki manta da zancen mari ki taimaki dan uwanki, Amma kar ki yarda ki tunkaresa a yau, ki bari gobe idan kin fito office mu nemi station din da Mustafa yake ya sanar damu ainihin abinda ya faru, ta hakane za musan hanyar da zamu shawo kan matsalar, don fa dole kisan yanda za'ayi ki kori shegiya a gidan ki". Hawayen bakin cikin Hajiya Indo ta share. "Shikenan Aminiya sai goben".
"Allah ya kai mu ki nutsu please?". In sha Allah ta ambata ta kashe wayar.
Number Sahura ta kira ta bata umurni ta had'o mata shayi ta kawo mata, tana ajiye wayar ta fito ta koma d'akin ta, toilet ta shiga ta d'auro Alola ta gabatar da sallah, tana idarwa tayi addu'a sosai akan Allah ya kawo karshen zamanta da wa'innan Marayu kafin su kasheta su huta. Sahura ce ta bud'e kofar ta shigo a nutse, ajiye shayin tayi ta mike zata fita. "Ke zo nan?".a ladabce Sahura ta jiyo ta durkusa. "Ki sanar dani abinda ya faru tsakanin Uncle Naira da Alhaji har ya mishi duka ya kira hukuma?".
"Na rantse da Allah Hajiya ban san komaiba, shigowata gidan kenan Uncle Naira ya aikeni ciro kud'i na samu ana wannan tashin hankali shine na kiraki". Sosai Hajiya Indo ta kalleta kafin ta kauda kai gefe. "Jeki". Da sauri Sahura ta mike ta fita.
****
Ta bangaren Hajiya Turai kuwa tana ajiye wayar Hajiya Indo waka tasa a wayarta ta soma taka rawar murna, cikin sauk'i burinta na gaf da cika, sai da tayi mai isarta kafin ta fashe da wani irin dariya ta zauna. "Shegiya Indo dani kikeyi, ki rubuta ki ajiye zaki kunshi bakin cikin da yafi wanda kike ciki a yanzu.......