BA SONTA NAKE BA

5

by @autarmanya

005

Ta tsaya.

A gaban shi tai masa tsaye a bayan shi tana kallon shi cike da tsananin soyayyar shi gare ta.

Mai ya ɗauko zai shafa karaf ya ɗaga idanu ta cikin madubi ya kalleta cike da mamakin ta yadda ta iya ƙaraso wa gaban shi ya aje man ba tare daya shafa ba.

A zuciye ya juyo gareta ya saka hannu ya ture ta ta faɗa gefen gado tana faman zare idanu.

Mai ya shigo da ita ɗakin sa? in ma wayarta zata amsa mai yasa bazata masa waya ya fito ya bata ba wannan salon rashin ɗa'a ne tabbas zai koya mata hankali wanda bazata kuma gigin aikata irin haka ba.

Shigowa ɗakin mutum babu izini kamar tana da alaƙa da shi.

Ya tunkaro ta fuskarshi da zallar rashin imani tamkar bai taɓa wata aba wai ita dariya ba.

Raɓe take a gefen gado sakamakon jefawar dayay mata ta haifar mata da buguwa a ƙugunta wanda bata jin ko yatsa zata iya ɗagawa a halin yanzu bare ta iya fita daga ɗakin duk da tsananin tsoron shi dake nausarta wanda tana jin tamkar ta arta aguje domin ceton lafiyar jikinta.

Duk takunshi ɗaya zuwa gabanta yana mai dai dai, da dokawar kirjinta mai ɗauke da tsananin tsoronshi gami da wata irin kwantacciyar soyayyarshi dake huda mata dukkan sassan jikinta.

Agabanta ya zube tare da dafe hannunshi a ƙasa yana mai ƙureta da kallonshi mai nakasa dukkan sassan jikin ma'abocin kallonshi.

Tura kanta tayi tsakanin cinyoyinta tama kasa jure kallonshi gareta.

"Mai ya kawo ki ɗakina?"

Saukar sassanyar muryarshi ma'abociyar nutsuwa kamala da haiba ta dirar mata cikin kunnenta.

Bai jira amsarta ba ya cigaba da cewa.

"Kamar yadda kike gurɓa tacciya shine nima kike son gurɓata mini rayuwa? kamar yadda kike najasa shine kike son nima na zama najasa zaki biyoni har ɗakina kinemi cillani a tarkon shaiɗan?"

A wannan karon muryarshi cike da tsantsar ɓacin rai yake faɗin maganar sedai tsabar nutsuwar shi yasa bai ɗaga murya ba, inma ka gansu bazaka ɗauka magana yake jefa mata ba seka rantse maganar arziki suke duba da yadda yake fitar da maganar a sautin hankali da nutsuwa tare dayin ƙasa da murya tamkar mai yin raɗa.

"To zan baki shawara in ma kina ganin hakan waye wa ne to sam ba waye wa bane sema naƙasu daze janyo miki tare da zubewar mutunci kamarki yarinya ƙarama wadda a tsarin ilimi ba lallai kin kammala karatun secondry ba amman ki zaɓi wannan harkar ta jagaliyanci wadda baxata fusheki komai ba se taɓewa da wahalar rayuwa, ban taɓa ganin shaiɗaniya irin kiba hakan yasa na baki muhalli na matsayin karuwa ƴar jagaliya marar kamun kai daƙiƙiya marar tunani naji ina tausaya miki da wannan makauniyar rayuwar da kika zaɓa ma kanki tabbas idan kika yarda na kuma saka idanuna akan fuskarki zan sauya maki halittar zubinta zan maki mugun tabon da ƴan gidanku bazasu ƙara shaidaki ba"

yafaɗa tare da saurin tashi ya wurga mata wayarta se yanzu ya tuna ashe ɗazu garin sauri bai saka ma ƙofarshi key ba wannan dalilin ya bata damar ratso mai ɗaki.

Daga zaunan datake ta yunƙura kaɗan tana matse fuska alamar har yanzu akwai zafin buguwa a tare da ita amman hakan bai sa ta zauna ba seda ta cigaba da tashi har Allah ya bata ikon miƙewa gaba ɗaya tare da taimakon dafe bangon datai ta kai duba gareshi ya bata baya tare da zira hannu cikin aljihun jallabiyar jikinshi.

Murya can ƙasa mai cike da kukan nadamar abin da tai take furta.

"Nima ba laifina bane laifin zuciya tace wadda batai min adalci ba don ta kaini inda bazata sami muhalli ba! nagode da dukkan furucinka gareni amman kasani atun haɗuwarmu dakai a ɗazu naji duk duniya bani da Aminin zuci idan ba kai ba Ina sonka! ina son ka!! ina Sonka!!! wanda soyayyar ka ce tajani na afka maka kuma ka riƙe a ranka har abada Ummul khairi mai son kace.........

"Ƙarya kike munafuka ƴar iska ba sona kike ba sha'awa ta kike irin na matan bariki marasa aji irinki! to ki sani Ni ALIYU DIKKO nai miki nisan da har abada bazaki kamoni ba Domin wuta da ruwa basa haɗuwa kin taɓa ganin tsafta da najasa sun haɗu? to ni dake babu maganar soyayya domin bakya cikin types na matan dana ke burin mallaka a rayuwata"

Yafaɗa yana mai nufota kamar ze shaƙeta.

Da wani irin sauri ta juya har tana ƙara yarda wayarta a karo na biyu tai saurin nufar ƙofar fita muryarta a dakushe ta furta.

"I love you for ever Aliyu"

Tana faɗin hakan ta fice a ɗakin tare da datso ƙofar ta silale a wajan tare da sanya kuka! mai ƙarfi na jimamin Rashin Aliyu na har abada anya zata jure........?