FreeArewaPen original
BA SONTA NAKE BA
- 1views
- 19chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
Da sauri ta sunkuya tana mai dafe tarin takardun dasuka watse zuwa ƙasa wanda hakan yayi dai dai da shima sanda yakai nashi hannun zuwa ƙasan cikin rashin sa'a kuma hannunsu ya sarƙe dana juna atake anan taji wani baƙon yanayi ajikinta mai wuyar ta fassara shi.Saɓanin shi dayay saurin ɗauke hannunsa daga saman nata gefe guda kuma yana jefa mata kallon raini da ƙasƙanci.Sam bata lura da hakan ba face ƙarasa tattare mai takaddun nashi datai tana sakin wani irin lallausan murmushi.Hannunta har yanzu rawa yake sakama kon baƙon lamarin daya faru agareta yanzu.Seda ta kammala tattara mai sannan ta ɗago fuskarta cike da murmushi mai ƙayatarwa ta dube shi da matsakaitan idanunta.Wanda kallo guda tayi masa takasa cigaba da kallon nashi murya na rawa kamar zatai kuka ta furta!"Afuwan yallaɓai ban kula ba"Tafaɗa tana mai janyo maganar da kyar tsintar kanta tayi dajin wata irin wawiyar faɗuwar gaba marar misali acikin kirjinta zuciyarta kuma kamar zata fasa kirjinta ta faɗo dan tsabar rawan data keyi.Bai amshi takaddun ba kuma bai dena kallonta ta ƙasan idanunshi ba yarinyace wadda batafi shekaru goma sha takwas ba sanye take cikin ɗamammun kaya waɗanda suka bayyana baiwar kyan surar da Allah ya bata gawani dogon gashi data zubo dashi har gaba da dokin wuyanta kallo ɗaya yayi mata yagane ainihin itan wacece.Tayi mai kama da karuwa marar aji kokuma tantiriyar ƴar iska marar aji! Abin da ya faɗi kenan aranshi yana mai lumshe kyawawan idanunshi.Totaly batafi sa'ar ƴar ƙaramar ƙanwarshi ba to mai yasa zata ɓata rayuwarta ta nakasa kanta."Yallaɓai ka amsa hannuna"Taja maganar cikin ƙosawa.Tana mai tsareshi da nata idanun wannan lokacin ta ɗan ƙare mai kallo kaɗan.Ataƙaice Shiɗin dogon namijine ƙaƙƙarfa baƙi mai ɗauke da manyan idanu da yalwatacciyar gira kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin jerin maza masu aji tare da izza da taƙama uwa uba kuma hutu gayu da ƴaƴan banki sun sami muhalli atare dashi.Har yanzu hannunshi na naɗe a saman kirjinshi idanunshi lumshe wanda shi kallonta yake batare data farga da hakan ba."A'a ya subuhanallahi A'A yana ga baka ƙarasa ciki ba"Maganar wani magidancin farin namiji daya karaso wajansu yanzu wanda hakan yasanya yarinyar zube mai takaddun ajikinsa ta ƙara gaba cikin sauri tabar wajan.Cikin sauri yarinyar take sauka ƙasa har tana haɗawa da ɗan gudu kafin ta fita compound na hotel ɗin wata baƙar mota ta buɗe da sauri ta shiga taja murfin tana maida numfashi."Ke Ummul lafiya naga duk babu nutsuwa atare dake kodai...?"Bata bar wadda ke mazaunin drivern tai magana ba tai saurin tarar numfashinta."Ameera ja mota mutafi yau nai gamo da ƙaddarata"Wadda ta kira da ameerah itake mazaunin driver wadda daga gani zata girmewa ummul da sauri tai revars haɗi da nufar gate ta fita a hotel ɗin baki ɗaya.Titi tahau tare da kunna redion motar.Seda ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.