12
by @autarmanya
Mayar da hankalin shi yayi ga tuƙin shi sedai ta cikin kunnen shi yana jiyo sautin fitar ajiyar zuciyarta akai akai lumshe kyawawan idanunshi yayi ya kuma waresu bisa kwalta yana jin jan ajiyar zuciyar tata har cikin ranshi.
Ba jimawa wahalallan bacci yayi gaba da ita ta langwaɓar da kanta a jikin kujerar motar tare da cusa hannunta a tsakiyar cinyoyinta kamar mai jin tsananin sanyi.
Ta wutsiyar idanu yake kallon yadda take sauke numfashi da alamun kukan data yine ya sanyata wannan baccin, sanya hannu yayi tare da ɗan ƙara ƙarfin na'urar sanyaya motar kana ya kunna rediyo ya cigaba da bin karatun alkur'ani mai girman dake tashi ta cikin rediyon daya kunnah.
Ahaka har suka ƙarasa cikin unguwar yayi parking a ƙofar gidan hajja Tare da kashe motar yayi jugum sabida rashin sanin yadda zeyi wajan tashinta daga baccin data keyi.
Wajan mintina biyar suna zaune cikin mota ganin lokaci naja yasa a hankali ya soma kiran sunanta kamar yadda ta gaya mai kuma hajja ma tagaya masa.
Murya can ƙasa kamar baya so yake furta.
"Khairy! khairy!! khairy!!! wanda seda ya kirawo har sau uku amman ummul ko gezau batayi ba sema sabon fitar numfashin dake fita ta cikin hancinta.
Tsaki yaɗan ja kaɗan aranshi yana ayyana matsalarta yawa gareta.
Sannu a hankali yakai hannun shi saman fuskarta yaɗan taɓa kumatunta kaɗan da sauri kuma ya janye hannunsa.
Tura baki tayi tana wani yamutsa fuska kamar yadda yara keyi idan suna mafarki cikin baccinsu.
Idanunshi ya tsira a saman fuskar tata yana kallon ikon Allah babu ko ƙiftawa yana mamakin yadda wani bin idan tayi abu take komawa kamar ƴar ƙaramar yarinya.
A hankali ya kuma kai hannunshi saman nata ɗumi yaji a saman fatar hanun.
A hankali yasanya bayan hannunshi ya shafi saman fatar hannunta yana furta.
"Khairy wake up"!
Saukar sassanyar muryarshi taji acikin kunnenta tamkar cikin mafarkinta.
A hankali take buɗe kyawawan narkakkun idanunta waɗanda sukayi ɗan ja kaɗan suka kumbura sabida bacci da kuma kuka se hakan yasanya fuskarta ta ƙara cika da wani irin sahihin kyau mai shiga zuciya.
Cikin nutsuwa ta sauke ganinta a saman hannunshi daya ƙi ɗaukewa daga saman nata hannun wata irin kwantacciyar suma ce a kwance ajikin hannun nasa sannan kuma hannunshi yafi nata girma nesa ba kusa ba ahankali taɗan motsa kaɗan tana cino bakinta gaba kamar yadda take ma hajja ko bamu.
Kafin tayi wata irin hamma ta koma jikin seater ta jingina.
Da sauri ya ɗauke hannunshi a saman nata yana mai sosa kanshi da ɗayan hannunshi.
Ya wani basar tare da furta.
"Mun iso gidan hajja fitar min a mota"
Sannu a hankali ta wani juya kai tana kallon saitin windo babansu na waje yana wa yara faɗa kirjinta taji ya bada sautin dam! da karfi kwalla ta taru cikin idanunta.
"Khairey kina ɓata min lokaci na"
Wani irin mutuwa jikinta yayi ta wani kwantar da jikinta a jikin glass ɗin motar dama ze dauwa ma yana kiran sunanta a haka tunda take bata taɓa jin wanda ya iya bawa sunanta haƙƙinshi kamar shiba.
Tsananin faɗuwar gaban ganin abbanta da kuma sanyin jikin kiran sunanta dayayi yasanya jikinta ya soma karkarwa ahankali sanyi ke ratsa saƙo da lungu na cikin gangar jikinta.
"Khairyyyyyy"
Ya kuma jan sunan a wannan karon daɗan zafin rai kaɗan.
Juyowa tayi tare da yin ƙwalƙwal da idanunta batare data iya furta mai ko kalma guda ɗaya ba se faman girgiza mai kanta data ke faman yi
"Dallah malama kimin magana ko kifita ina miki magana zaki mayar dani mahaukaci yaushe na zama abokin wasanki daga jiya zuwa yau zaki shiga rayuwata ki tarwatsan farin cikina"
Yafaɗi maganar tare da ware mata girman idanunshi masu sanya marar ji saurin nutsuwa.
"Dan Allah ka fita ka barni anan zuwa anjima babanmu ne a waje bani so ya ganni"
Tafaɗa tana wasa da yatsun hannayenta idanunta na zubar ƙwallah!!
Ɗan kallon ta yayi na mintina biyu kafin ya kawar da kanshi.
"Ni ban yarda ba ki fita kawai wani uban ne ze ƙi son yaga ƴarshi indai ba baki da gaskiya ba wato laifi kika ma mahaifanki shiyasa na ganki a hotel ko? ƙilan baya son yawon da kike ne shiyasa bakwa shiri"
Yafaɗa tare da kafe fuskarta da kallo yana son gano rashin gaskiyarta.
Rintse idanunta tayi don ko kaɗan bata son kallon daya ke mata hakan yana sanya zuciyarta tsalle tamkar zata faso ta fito mata daga kirjinta sannu a hankali ta sakar masa kyakykyawan murmushi mai ciwo tare da saurin ɓalle murfin motar ta fita.
Ya jima yana auna yanayin yarinyar kafin ya girgiza kafaɗun shi alamun su ta shafa tare da ɗaukar ledar drugs ɗin ya fice.
ƙofar karamin gida mai ginin ƙasa na kusa da gidan hajja ya ƙarasa tare da ɗan rissuna wa yana gaisar da wani dattijo fari dake faman masifa ga wasu ƙananun yara kamar ze duke su jin muryar Barrister yasan ya yaɗan sassauta tare da miƙawa Aliyu hannu suka gaisa kallon dattijon Aliyu yayi sosai wanda shigarshi ma kaɗai ta nuna talaka ne futik don babu alamar wadata atare dashi sedai akwai tsantsar kamanni atare dashi da waccan yarinyar.
Miƙewa yayi daga rissunawar tare dayi mai sallama yabar wajan wanda har lokacin dattijon bai dena masifar daya kema yaran ba.
Lokacin da ummul ta shiga gidan hajja ta tarar da wata mata fara zaune a saman kujera suna hira da hajja da ɗan sauri ummul ta ƙarasa wajan matar wadda bazata gaza shekaru 40 ba ta wani ɗane jikinta tare da sanya kuka tana furta.
"Bamu shine baki zo da wuri ba ko?"
Cikin tsananin tausayawa wannan matar da ummul ta kira da bamu take shafa kan ummul tana furta.
"Kiyi haƙuri Umminah nima ban so nakai wannan lokacin banzo gareki ba to kinsan halin gidan namu ne yanzu ma fakar idanun mutan gidan nayi na shigo"
Da sauri ummul ta ɗago tana furta.
"Aikam naga abba a waje yana sana'ar tasa wa yaran mutane"
Da alamar tsoro bamu ta ware idanu tare da furta.
"Hasbinallahu wani'imal wakil ya rabbi ka rufan asiri"
Tafaɗa tare sauri sanya hannu ta share zufar data karyo mata.
Dai dai nan Aliyu Dikko ya doko sallama cikin kamilalliyar muryarshi.
Duk suka amsa da hajja da bamu wadda ummul ke zaune ɗare ɗare saman cinyarta.
Ɗan rissunar da kanshi yayi tare da gaisar da bamu sannan ya mikowa hajja ledar tare da furta.
"Zani inda na sauka seda anjima zan dawo dan na makara a komawa gida yau"
Da sauri ya furta hakan kamar mai tsoron abin da ke kusa dashi.
Ba sakewa yabar falon hajja ta take mai baya tana furta.
"To bazaka tsaya kaci abinci ba?"
Murmushi ya sauke mai ƙayatarwa.
"Haba hajja wani abincin zanci kuma bayan wanda naci?"
Ɓata rai hajja tayi kana tace.
"Ai kace bakai kalacin safiya ba to kaga akwai na rana tunda wancan na safiya kaci ay"
Zira hannayen shi yayi cikin aljihun wandonshi.
Yayi taku ɗaya zuwa biyu
'zan dawo anjima kimin sakwara miyar agushi, waccan ledar kuma maganinta ne aciki za'a sami ruwa mai ɗumi a gasa wajan sannan a shafa maganin ɗayan kuma tasha Allah ya sawaqe"
Yafaɗa tare da cigaba da tafiyar shi.
Godiya hajja tayi masa kana ta koma ciki da murna hajja ke gayawa bamu cewar wannan fa jikanta ne Aliyu ɗan wajan ɗiyarta.
Sosai suka faɗa hirar Aliyu ita da bamu wanda ita kuma ummul ta lafe jikin mahaifiyarta tana jin ƙaunarta na ratsa mata jikinta.
Seda akai la'asar sannan bamu taima hajja sallama tare da godiya ta wuce gida.
Da ƙyar ummul tayi sallah taci abinci taɗan kwanta dan wajan na mata zafi sosai.
Wajan yamma ƙannenta suka shigo a sace sukai mata sannu suka koma.
Abu kamar wasa ummul taƙi shan magani duk da irin faɗan da hajja ke mata ga uban zugin da wajan keyi mata saka makon taɓawar da likita tayi, zuwa magariba zazzaɓi da ciwon kai ya kamata har tana sheƙa amai hankalin hajja yayi masifar tashi dan ko sallar magariba ma azaune tayi ta bayan ta idar ta jibga uban bargo ta kwanta saman gadon hajja tana rawar ɗari har tana shiɗewa faɗan duniya hajja tayi shi wanda ita bata san daman ummul ciwonta haka yake ba sam bata shan magani se taji kamar zata mutu.
Shiko Aliyu ya koma hotel cikin nutsuwa yayi wanka ya shirya cikin kayan shan iska coffee yaɗan sha sannan ya kwanta bacci wanda bashi ya farka ba se wajan karfe huɗu alwalwa ya ɗauro ya tayar da sallar la'asar bayan ya idar ya ɗauko system ɗinshi yana aiki da ita.
Bai tashi daga wajan taba se magariba alwala yayi tare da sauya kaya zuwa jallabiya fara ƙal mai dogon hannu tare da baƙin 3qtr acikinta sallah ya tayar bayan ya idar ya zauna karatu wanda a kwanakin nan kusan kullum seya yi.
Seda yayi sallar isha'i wajan ƙarfe 8:30 ya miƙe tare da nade sallayar yaɗan ƙara fesa turare ya ɗauki wayarshi da keyn mota ya fita.
A hara bar hotel ɗin ya kalli sararin samaniya walkiya tana tashi hadari na haɗowa alamar ruwan sama na gab da sauka.
Yana son yanayin damuna sedai baya son dukan ruwan sama dan muddin ruwa ya taɓa shi seyayi zazzaɓi ko mura mai zafi
Da sauri ya shiga motar ya kunna ya ɗauki hanyar gidan hajja
Dayake yayi sauri yasa ya ƙarasa wajan ƙarfe 9:00pm sabida akwai tazara nesa ba kusa ba a tsakaninsu parking ya gyara a kofar gidan tare da fitowa waje bayan ya kashe motar hadarin unguwar su hajja ma har yaso yafi nacan inda ya baro ɗin tura gate ɗin yayi ya shiga daya ke hajja tasan zezo shiyasa bata rufe gate ɗinta ba.
Sallama ɗauke cikin bakinshi ya shiga falon hajja.
Da sauri hajja dake zaune tai tsuku duk al'amarin ciwon ummul ya ɗaga mata hankali ta ɗago tare da amsa mai sallamar cikin kulawa.
Tsaida kallon sa yayi a fuskar hajja yana nazarin ta kafin ya furta.
"Hajja ta lafiya na ganki cikin rashin walwala? daman nace ma ammi a yaran can wani ya dawo nan tace kinki amman zaman kaɗaicin bai da daɗi"
Yafaɗa yana mai zama a gefenta.
"Kai nifa salame na zuwa yau ma biki taje shiyasa bata zo ba,nifa duk damuwata akan ummi ne kaganta can a gado se wani abu take gudu nake kar yarinyar mutane ta mutu"
Tafaɗa tana share hawayenta.
Ɗan jimm yayi tare da cewa.
"Au hajja bata sha maganin bane wani abunne kuma?"
Yafaɗa batare da ya nuna hakan ya dame shiba.
"Babu yadda banyi da ita ba wallahi taƙi sha gaya can zazzaɓi ya kamata tana ta rawar sanyi"
Hajja ta faɗa tare da share ƙwallar dake zubo mata.
Da mamakin yake kallon hajja wannan wace irin ƙauna take ma waccan yarinyar kosu in suna ciwo bata ɗaga hankalin ta haka.
Daɗan ɓacin rai ya dubi hajja.
"Ki dena kuka! dan iskanci abata magani a asibiti sannan taƙi sha dan ta rena ki, ina maganin yake?"
Yafaɗa cikin rashin walwala.
Da hannu ta nuna masa ledar da tunda ya ajeta babu wanda ya ɗauketa.
Da matiƙar ɓacin rai ya sanya hannu ya ɗauki ledar tare da nufar bedroom ɗin hajja wanda ummul ɗin ke cikinsa a kwance............