10
by @sadiyanasir
RIKON SAKAINA
YA FARU A GASKE
NA
SADIYA NASIR DAN
Arewa Book
sadiya Nasir
SHAFI NA GOMA
Baby dake yau sun tafi yawon bud'e ido a school d'in su a gajiye ta dawo gida, shiyasa tunda ta haura d'aki tayi wanka tayi sallar la'asar ta kwanta, sai gaf magrib kafin ta farka nan ma yunwa ce ta dameta, a k'asa ta samu Aunty Aliya ta hakimce a kujera tana canza chanel. "Kin samu tashi? ". "Ki bari kawai Aunty Aliya yau na wahala yanda baki zato, zan baki labari bari naci abinci nayi sallah naji ana kiran magrib". Ok ta ambata ta mai da hankalinta kan TV Baby ta nufi kitchen. Ganin har karfe takwas Khadija bata fito parlor kamar yanda aka sababa yasa Baby mikewa ta nufi d'akin. kwance tasameni gaba d'aya zazzabi ya rufeni, banda rawar sanyi babu abinda nake a cikin bargo. "Ya subhanallah Khadija meke damunki? meya sameki". Tayi maganar ta karaso in da nake da sauri ta yaye bargon, jin yanda jikina ya d'au zafi ta furta ya Allah ta fita da sauri tayi d'akin Hajiya.
Ko sallama ba tayi ba ta fad'a d'akin, a razane Hajiya Indo ta dubeta. "Ke lafiya kin shigo min a hargitse meya faru?".
"Hajiya Khadija ba lafiya jikinta kamar wuta sai rawar sanyi take. "Mts*** Indo taja dogon tsaki, to ina ruwana da ciwon dake damunta ta mutu mana sai me, kin wani birkice sai kace uwarki ko ubanki ne ba lafiya". Cikin Jin zafin maganar nata Baby tace. "Haba Momy wai meye Khadija tayi miki baki sonta, ba kiga jikin nata bane Momy don Allah kizo muje?". Tayi maganar idonta na zubar da kwallah. "Ko kin san yau akan Khadija Alhaji ya nemi ya sauwake min, tunda nake dashi bai tab'a marina ba Amma akan ta dubi kiga gefen fuskata? Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um garin yaya haka Momy? Uhumm Hajiya Indo tayi murmushin takaici ta kwashe komai ta sanar da ita. "Amma Momy uncle Naira baya ji kema shaida ce babu irin case din da baki kashe ba akan neman matan da keyi, kuma ni na jima da fahimtar mummunar kudirinsa akan Khadija". "Yi min shuru sha-sha-sha wacce bata da hankali. "Kina nufin har rashin hankalin Mustafa ya kai ya shigo har gida yace zai nemi Khadija? Karfa ki manta ga Sahura, wannan ma ba magana bace". "Shikenan yanzu dai Momy mu ajiye wannan zancen Khadija taimako take nema, a taimaka akaita asibiti tun kafin dare ya tsala please Momy?".
"Baki da number Ubanki ne? Ko ba yanzu na baki labarin abinda ya faru ba, ai kin san yana gari sai ki sanar dashi".
"Amma Momy....
"Ke ubanki, shegiya wacce bata da k'awa zucin Uwa, fita mun a daki kafin naci mutuncin ki". Tayi maganar a tsawace. Kuka Baby ta fashe dashi saboda yanda Hajiya Indo tayi mata tsawa sosai ya firgitata, d'akin su ta nufa Aunty Aliya ta fito a wanka tana k'okarin saka kayan bacci. "Lafiya Baby ke kuma dawa?".
"Mommy mana Aunty Aliya, har ga Allah bana Jin dad'i yanda Momy take nuna tsana wa Khadija".
"Ok wani abin ne ya faru?".
"Khadija ba lafiya naje na sanar da ita akan akaita asibiti, amma ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wai na fice mata a d'aki naje na kira Dady yazo ya kaita asibiti". "Dady kuma? Shi da yake wata uwa duniya ya za'a kirasa?". "Aa ya dawo d'azu har sun samu sab'ani da Mommy akan Khadija".
"Kuma? Lallai fa, to meye ya faru?"
"Yanzu ba wannan lokacin bari na d'auki wayata na kira Dady". "Ok Allah ya taimaka" Ta ambata ta k'arasa sa kaya ta fito tayi d'akin Momy Jin abinda ya faru.
****
Baffa Kabiru yana gaf da shigowa layin gidan nasa kiran Baby ya shigo, da sauri ya d'auka. "Barka da dare Dady kana Ina ne?" "Barka Uwata ya akayi?" "Dady don Allah kazo gida Khadija ce ba lafiya zazzabi sosai takeyi kar kaga jikinta yanda ya d'au wuta". "Subhanallah! gani k'arasawo ki taimaka mata ta shirya please". "Shikenan Dady Allah ya kawo ka lafiya". Tana ajiye wayar d'akin mu ta dawo. A yanda ta barni a haka ta dawo ta sameni babu abinda ya canza, haka dai ta taimakemin na gyara jikina na kwanta ina tsumayen zuwan Dady. A tsakanin minti shabiyar ya shigo gidan, Baby najin dirin motar sa ta fito da sauri ta tare sa a harabar gida. "Ina Khadijan? Kije kizo da ita". To Baby ta ambata tayi sauri ta dawo, kama hanuna tayi amma ina tashi naga waje yamin duhu sai ji nayi na buge kaina. "Wayyo Allah Baby ta ambata ganin yanda na zube a k'asa ta nufi gun Dady, Tare suka shigo da sauri ya d'auke ni cak sai motor, asibitin unguwar mu ya kaini bayan layin mu, babu b'ata lokaci suka bani gado aka jona min drip aka min allura tuni bacci ya d'auke ni. Sai a sannan Dady ya samu nutsuwa ya fara jefo tambayoyi wa Baby. "Yaushe ciwon ya fara Baby? Meyasa tun tuni baku kirani ba". "Dady wallahi ban sani ba, dake na dawo daga school a gajiye d'aki na wuce na kwanta kuma ban tashi da wuri ba, to bayan nayi sallar isha'i shine na leka d'akin su Ashe tana kwance ba lafiya, Sahura kuma bata sanar da kowa ba saboda Khadijan tace tayi shuru".
"Ban gane Sahura bata sanar da kowa ba? Wake da alhakin sanin halin da Khadija take tsakanin ke da Sahura? Wannan ma ba magana bace, ace house girl ce zata sanar daku Khadija ba lafiya to a wani dalili?".
"To ae Dady d'akin su d'aya, ni kuma wallahi ban sauk'o k'asa ba sai gaf magrib, shine dalilin da yasa ban san bata da lafiya ba".
"D'akin su d'aya? Kina nufin Khadija a d'akin Sahura take rayuwa?".
Hanjin cikin Baby ne ya k'ad'a, gaba d'aya ta sha'afa bakinta ya tattaro wannan zance ya furta. "Ba magana nake miki ba kin min shuru?". Dady yayi maganar a tsawa ce".
"Eh... Dady tare suke kwana, amma wallahi umurnin Mommy ce babu yanda banyi da ita akan Khadija tana kwana tare damu ba amma sam tak'i".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um". Dady ya furta lokaci guda idonsa ya k'ad'a yayi jaa. "Tabbas Maman ku tana nema na da bala'i amma gidan tazo ina dai-dai da ita". "Please Dady kayi hakuri don Allah karka sameta, wallahi zata min babu dad'i". "Uhumm kawai Dady ya furta ya jawo plastic chair dake gefe ya zauna ya rufe ido yana jin takaicin Hajiya Indo tare da tunanin irin hukuncin da zai d'auka akan ta don huce takaici.
****
Aliya da Hajiya Indo kuwa haka suka d'auki tsawon lokaci suna k'are min tanadi, zagi kam babu irin wacce ba suyi min ba, sai kusan karfe shabiyu kafin Aliya tabar d'akin saboda Saurayinta dake kiranta a waya. Bayan fitarta Hajiya Indo haka ta kwanta tacigaba da kulla munanan abubuwa akaina, wanda da kyar dai bacci ya d'auke ta saboda bakin cikin dake damunta. Washe gari da safe tun takwas Hajiya Turai ta kirata tace ta shirya zuwa 09:30 su had'u a office, shiyasa bata samu damar komawa bacci ba ta shirya ta sauk'o ko kallan d'akin Alhaji ba tayi ba, kunu kawai tasa Sahura ta dama mata tasha ta d'auki Jakarta ta fita. Da isarta office ta samu Hajiya Turai harta iso, babu bata lokaci suka nufi Area command, saboda tun a daren jiya Hajiya Turai ta kira I.G ta sanar dashi abinda ke faruwa, a daren yasa aka bin cika masa case d'in, office din Area command din suka nufa Hajiya Indo ta sanar dashi wanda ya turosu da kuma bukatarsu harta had'asu a waya, cike da girmamawa yace bakomai za'a bada beli amma yanzu ma baya station din yana asibiti yana karban medication. "Subhanallah Mustafan?" Hajiya Turai ta ambata tana binsa da kallo. "Kwarai kuwa".
"Uhumm ai abin yayi kyau ma da bai mutu ba, ke kinga irin dukan wulakanci da Alhaji yayi mishi kuwa, ai ko a titi suka had'u iya ka kenan". "Abu baiyi dad'i ba amma kiyi hakuri komai zai wuce, ranka shidade ya za'ayi mu samu ganin sa don Allah?". "Gaskiya sai dai kuje asibitin zan had'a ku da yara suyi muku jagora, shi kuma Alhaji Kabiru zan kirasa na sanar dashi bukatar I.G akan case d'in". "Shikenan mun gode ranka shidade, ga number ta duk abinda ake ciki ka sanar dani". Ba matsala". Ya amshi number sukayi sallama ya had'a su da jagora zuwa asibitin.
Sosai hankalin Hajiya Indo ya tashi ganin yanda Uncle Naira ya koma a lokaci guda, fuskarsa gaba d'aya ta kumbura. "Na shiga uku ni Indo, lallai Alhaji ya cika babban azzalumi, akan wata tsinanniya ga yanda ya dawo min da d'an uwa? Na rantse da Allah sai dai komai ya faru Amma ba zan bari wannan wulakanci da tozarci ya tashi a banza ba". "Ke matsalata dake saurin fushi, ki daina ganin laifin sa, babu mai laifi sai Khadija, shi anfani yayi da abinda ya gani, sharrin da aka shirya ya riga yayi tasiri, kafin ya gane gaskiya sai anyi da gaske".
"Daya gane da kar ya gane ni dai wallahi ba zan d'auki wannan cin mutunci ba". "Yanzu dai ba wannan ba, ya kamata muyi abinda ya kawo mu kin san ba lokaci, Mustafa ya jikin dai?". Da sauk'i ya amsa a hankali saboda bakinsa dake kumbure. "Yanzu muka fito station in sha Allah zasu bada beli, abinda nake so da kai ka nutsu ka kwantar da hankalin ka matukar ina numfashi sai na d'auki fansa akan abinda akayi maka, yanzu idan ba wanda yayi maka farin sani ba babu mai gane ka". "Meyasa baki d'aukar shawara wai? Nace ki nutsu komai a sannu za'abi, Mustafa ka sanar damu abinda ya faru har Alhaji yayi maka wannan duka?". Cikin yanayi najin azaba Uncle Naira ya soma magana. "Na fito cikin Destination hotel wajen wani friend d'ina kawai ido na ya sauk'a akan Khadija ta fito cikin motar wani ta saya Abu a shago, kuma wallahi cikin hotel din suka fito, saboda time din dana shiga hotel din motar tana ciki, shine nayi mata video nabi bayan su har gidanki, a bayan layin ku ya sauk'e ta a haka ma sai da suka kai kusan mintuna talatin a ciki, hakan yasa raina ya b'aci sosai saboda Auren Khadija nake so nayi, shine na shiga gidan nasa meta ta inda nake shiga ba tanan nake fita ba amma yarinyar nan tana bani amsa, sai da taga video din dana d'auka shine ta sauk'o tazo gareni ta fara shigewa jikina akan na goge video d'in duk abinda nake so za tayi mun, tuni shaidan ya rinjayeni, wannan shine dalilin da yasa na tura Sahura aike, kwasam muna tsaka da aikata sabon Allah mu kaji shigowar motar Alhaji, yarinyar nan saboda munafurci ta tureni ta d'auki towel tasa a jikinta ta fita da sauri, ni kuma na biyota ina kwala liran sunanta kawai naga Alhaji ne, to shine ya rufeni da duka, wannan shine abinda ya faru".
"Kinji dai, dama mena fad'a miki, wallahi ko giya Mustafa yasha ba zai shigo gida yace zai nemi Khadija ba tare da Amincewarta ba, gaskiya naji tsoron halin d'an mutum tirrr". "Allah ya kyauta muga video din? Hajiya Turai ta ambata, shiga video din yayi ya mika mata, sau uku tana kunnawa tana gani kafin ta sauk'e ajiyar zuciya. "Tabb wannan shine ana dara ga dare yayi, ko kin san d'an gidan waye sukaje hotel din dashi?"
"Aa Hajiya Indo ta ambata da sauri. "D'an gidan Liman mai rasuwa ne, yarane masu tarbiya da mutunci, lallai wannan yarinya shu'uma ce da har ta iya rinjayen Ibrahim ya aikata wannan rashin hankalin da ita, babban ma abin takaicin shine a ina suka had'u? Kinsan irin dukiyar da ubansu ya mutu ya bar musu? Wallahi barin yarinyar nan da yaron nan shine mafi girman kuskure daza kiyi a rayuwarki.....
Last free page's