NUR FIRDAUS

34

by @surayyahms

NUR FIRDAUS...34

@SURAYYAHMS

follow @Arewabook.

wann babban hatsaniya dayafaru a filin makaranta ya jefa malamai da dalibai cikin wani sabon yanayi na rade rade.

maqiyan nur na fili dana boye suna famar dabbaka zancen layla nacewa nur tay cikin shege,masoyanta kuma suna wankewa da batun adnan na cewa sharrin layla ne musmn ma jadida wanda itace a farko wajen fayyace halin layla wa dalibai tace tabbas dama saida tay zargin cewa layla tana son adnan tana boyewa.

hankalin malamn makarantar ya tashi bana kadan ba, cos nur firdaus has been an extra ordinary student kuma ita din babban misali ce ga sauran dalibai dake tasowa dan haka dolene suje su nemo gaskiyar wann lamari..

ata dayan bangren kuwa a hannu ahannu adnan ya dawo da nur firdaus gida aka bata gado tare da daura mata ruwa. baiy kasa a gwiwa ba yahau fayyace ma Dr surayya da kakarsu didi abunda layla taje tay ma nur a schl, tsabar yana son ya nuna musu wacece layla harji yake kamar basa gane meyake fada.

ana cikin maganan sai ga nan laylar ta dawo daga asibiti anduba mata wuyarta da haryanxu da shatin hannun adnan akai

tana zuwa Didi suka tutsiyeta da masifa Dr surayya harta wanka mata mari amma ba shi ya hana layla tay denaying din komi tanuna musu cewa ai bada mummunan nufi tay maganan ba kawai sudden anxiety attack ne yasata fada.

cacar baki ya kaure tsakaninsu da adnan dan yaki amincewa da karyan layla sam ta dinga kuka tana karyata shi shikuma yaki sam hatsaniyar su ya tada nur firdaus

wanda dede tafito kenan saiga mrs Haseena ta shigo da hawaye akan fuskarta tana kwala mata kira, tana cewa nur nur nur dan ubanki bayana kike son gani da zaki kama ki fita kije makaranta? yanxu duk balain da kika jawo min agari be isheki ba sai kinyi yawo agari dan neman tona min asiri..? zuwa tay ahaukace zata fixgo nur din Didi tay sauri ta riketa tace meya haka Hasesna meya faru???? kin haukace ne..yrinyar da aka dawo da ita a sume pls behave urself...

nan mrs haseena ta fara musu kuka tace mama wallh yarinyar kasheni takeso tay, nanta fara basu labari cewa tun tana can office dinta malaman makarantar su nur din sukazo suka tutsita da tambyoyi waiko dagske ne yarta tay cikin shege snn suna fita yan jarida da bata san daga ina suka billo ba sukazo suka fara fadin maganganu

suna cewa sunji kishin kishin cewa babban yarta tay cikin shege ana boyewa duk dai ta gaya musu kalar cin mutuncin da aka mata

Dr surayya tace mata ai ba lefin nur bane layla ce ta kawo wann idean, layla tace sam ita bada nufi tay ba tay hakanne dan ta cire yar uwarta a zargi daga schl sai kuma anxiety attack yasata furtawa.

ta inda mrs Haseena take shiga bata nan take fita ba...

tsabar sonkai sai ta aje maganan lefin layla agefe ta koma kan nur da zagi tana cewa tajawo mata fitina da bala'i da kuma abun kunya yanxu duk duniya sai anji cewa yarta tay cikin shege wa barayi

Su didi suna kkrin calming din mrs haseena amma ina sai masifa take tana cewa tagaji tagaji da rufawa nur asiri kawai gara ta hada kayanta tatura ta yola wajen didin suje can ta raine cikin barawon acan...

baqin cikinta duk ta fara saukewa akan nur sai zaginta take kamar so take tace ai lefinta ne ma datay cikin.

ran Nur firdaus ya mugun baci wani karfi taji yana shiga jikinta haseena nakan mata ihu kawai aka ji tafara amsata da zafi zafi

...dan taga babu amfanin rufa ma haseena asiri tun da gashi harta fara mata gori da tozarci tana kirar cikinta da sunan cikin barawo...kawai taga gara ta gaya mata cewa in ma wani ne barawon to mijinta sadaat ne kuma shine uban abunda ke cikinta..

tunda nur tafara amsawa wajen ya dada kaurewa da hayaniya nan nur ta haubada labarin abunda ya faru tana gaya musu cewa sadaat ne jikin kowa awajen sai ya fara kaduwa da mamaki

barinma Haseena data kangare dan kamar mutum mutuminta akayi ta kafe nur da idanu kamar zata hadiyeta.

jin yadda nur take borataccen kuka tana gaya mata cewa itace ta kawo musu bala'i da mumnan qaddara agidansu da rayuwar su ba ita ba, inkuma bata yarda da itaba tace ayi bincike akan kowa, snn abinciki sadaat aji meyasa yau ana neman sati uku kenan da afkuwar komi amma ba asame sa koda awaya ba

..why is he not home yet,nd why hiding if he is clean?

nur firdaus na kuka tace mummy ina darajaki matsayinki na mahaifiyata shiyasa narike abun araina ban iya furta miki gatsau cewa mijinki bane yazo da wani mutum suka mana wann abun agaban mutane,ive tried many time to tell you amma kika maida ni kamar me tabin hankli..i cannot keep quiet any longer...duk sanda kikaji aranki kina da bukatar tozarta ni ko zagina akan wann cikin toh kisani cewa mijinki sadaat shine ya aikata min wann abun..

basu hankara ba ji kawai sukay fassss wani irin gigitaccen mari daga haseena ya sauka akan fuskar nur

Adnan yay sauri ya daga nur yajata jikinsa Dr surayya ta riko haseena dake bari tana kyarma tana kuka at same time tanajin kamar kanta na kuncewa..

a mugun zafafe tace ke wallhi kinyi kadan kima mijina sharri nur firdaus, aniyarki ta biki munafuka, muguwa

..snn idan kika sake furta wann maganan akansa wallh wallh wallhi saina tsine miki albarka

tana fadin hakan ta haura sama tana rusa kuka Didi ne tabi bayanta Dr surayya Da adnan suka rike nur dake kuka sosai har suka zaunar da ita.

layla na tsaye tana kallonsu duk ta kasa motsi she was like so sadaat was really the father of nur's unborn child????? sai kuma taji wani haushi ya kamata.

muryan adnan harna rawa rawa yake kara tambayar nur akan batun sadaat, nur kuwa bata boye masa komi infact anan ne ma ta asalin bude musu kan maganan ta fayyace musu dalla dalla yadda abubuwan suka faru..

she said she cant even feel like she is being raped,amma kawai akace wai tana da ciki..kawaide ta dau hakan a matsayin qaddara tun da bata san meyafaru da ta suma ba.

badon kwaya da adnan yasha dazu ba da hala he wont be this calm dan iyaka abunda yake son yaji kenan, haka ya dinga lallashinta yace mata zaije wajen babanshi dama yace masa zai taimaka masa akan duk wanda yay wann abun nd he wll make sure ankama sadaat

daga haka ya barta a hannun Dr surayya ya fita agidan, layla ta haura sama da sauri ta samu didi tana tana kan buga kofawa mrs haseena dake fashe fashe da ihu a daki ita daya dan ranta ya mugun baci da furucin nur akan sadaat duk dama batayarda da nur amma tasan nur bata furta karya dole ne da akwai abunda bata sani akan sadaat ba.

layla na zuwa wajen ta buga kofar tace mum, mummy, mummy dan Allah kibude kiji wai adnan zaije ya gaya ma babansa kuma zasusa a kama miki mijinki..i am sure he is not at fault..mummy u have to do sumtin abt uncle sadaat kar yaa nur ta saka akamashi

amasa hukunci akan abinda bema sani ba.

baki sake didi ta tsaya kallon layla can kuma saiga mrs haseenan tabude kofa gabaki daya kamar barm mrs haseena ba tsabar madarar haukan datay

nan take dukansu suka shigo ciki Didi na tsaye a tsakiyarsu taga yadda laylan take zuga mrs haseena akan maganan abun sai ya mugun daure ma tsohuwar kai bana kadan ba.

suna cikin haka sai ga kirar hajy mairam

Haseena har tsoron dauka mrs haseena takeyi daga bisani dai tay shahada ta dauka din,...

nan take hajiya tahau gaya mata cewa an sun samu wani labari cewa sanata farida bala tana da hannu acikin abunda ke faruwa dasu, anama zargin itace ta aiko barayin amma kuma tanada wani shiri nadaban da zatyishi agidan telebijin domin ta tona musu asiri, so, tana son kafin sanata farida tay shirin, lallai ayi auren layla da adnan nan da 4 days inyaso bayan an daura auren zasu kama sanata farida balan ta wani hanyar da batay tsammani ba, sann auren ne zai goge dukkan wani sharri da tarkon dataci nasarar kulla ma y'ay'an haseena tunda dama ba asan asali wacece adnan yake so acikin yaran ba, it wont really matter to the media in sunga eh harma anyi auren.

nan ma tama hasina alkwari cewa yau yau zatasaka goge batun cikin shege da akace nur tay abakin dalibai da dedekun mutane harma da makaranta..

they will debunk the news in every way possble ita minister ce dan haka she have ways to use NCC na nigeria to her own advantage akan duk wata kafafen yada sako na kowani kalar media kuwa, har na wayar salula.

sann in return tanason hasinan tay duk yadda za'ayi tasan yadda za'ay cikin nur din ya fita kafin nan da wani lokaci.

hajiya mairam tana so lallai ta wanke mrs hasina sabida tasan idan har babu mrs haseena akusa da ita hala tenuren ta akan kujerar mulki bazai yi tasiri ba, kuma dama sunshirya abubuwa da yawa da zasuyi domin cimma next target dinsu, gabaki daya ta duba manyan mata bataga dai wacce zata iya mata wayannn abubuwan ba inba mrs hasina ba

shikenan kuwa hasina ta amshi qudurinta dan aduniya babu abunda takijini kamar abun da zai xubar mata da kimanta da mutuncin ta a idon duniya inde zaa goge mata tabon nur tayi cikin shege a media ai koma me akace tay zatayi.

agefe kuwa yadda kasan an tsoma layla a aljanna haka taji wani mugun dadi da taji ance nan da four days aurenta da adnan da wani irin murna ta bar dakin tabarsu ita da didi.

Didi ta sauke ajiyan zuciya bayan tagama bin bayan laylan da kallon tausayawa ta kalli yarta tace ke amma Haseena kibi duniya a sannu, kin san ni de bazan iya ce miki komi ba, sabida nasan wanda yay nisa bayajin kira, amma kiyi hankali kar kibari son zuciyarki ya saka ki kije kikashe yarki nur firdaus batare da kinbi mata haqqinta ba..snn ki tuna fa y'ay'anki amana ne agareki hanyar dakike daura layla akai ba hanyar nuna mata soyayya bane baki nuna mata lefinta snn baki nuna mata cewa abunda take furtawa akan yar uwanta makirci ne da gulma.

..wann auren dakikeso ki dorata akai hanyar cutarwa ce dan kuwa auren cushe wallhy bata daraja.

daure fuska Hasina tay tace naji, amma kuma kisani mama abunda zai ficceni shi kawai zanyi, inma nur ta mutu aishikenan sabida menene rayintan ya taba kara min a duniya banda baqin ciki da tozarci da mugun qaddara

tunda na haife nur firdaus ban huta ba, haka harouna ya zabi ya tazorta kansa akan kulawa nur, how many times did he ruined my career sabida nur firdaus, dan nice na haifeta shikenan sai kawai in bauta mata kodan sabida ita kawai nazo duniya?

gabaki daya kudinsa yasaka da sunanta bai barmin komi ba yace nur zata kula da layla, ni inyi takaina, mama har harouna yabar duniya zagina yake akan tarbiyanta, toh gashinan ta yi cikin shege, yau ina yake sai yafito yazo yaga yarsa me tarbiyan. wai har ace yau nur tana budan baki tana lakawa mijina sharrin wai shine yazo har gidan nan ya mata fyade ya mata ciki?? kisan kuwa cewa nur bata kauna ta.., hala sunyi da ubanta cewa itace zata kashe ni da baqin ciki kuma wallh kafin ta kasheni saina kasheta,..dede nan ta fashe da kuka sosai Didi ta kyabe baki tay shiru tanata kallonta batace mata uffan ba

bayan tafiyar adnan Dr surayya takai nur daki tana dan lallashinta hr hanklinta ya dan dawo jikinta,around bayan azhr nur tay wanka ta zauna sanye da hijabi tana karatun qur'ani hawayenta na sauka ahankli dan itakadai tasan me takeji aranta ynxu.

ji take She really need her phone dan tasan inda zata same javeed to babu shakka zai iya taimaka mata wajen nemo gaskiya dake lullube tsakaninta da haseena da kuma sadaat.

after 2 days, Layla ta dawo zama jikin mrs haseena sosai suna gefenta sunata shirin aure agidan batare da sunyi involving din kowa ba. Didi ne kawai tasan shirinsu Dr surayya bata san me ake ciki ba, saida nur ta fara matsawa akan tanason wayarta kafin Dr surayya tace lallai sai tagaya mata me zatayi da wayan kafin taje ta roki hasina abata wayar.

tanata tsoron kar nur tace zatagudu cos she feel like nur is really depresed iyaka karatun qur'anin ne kawai yake riketa.

nur bataso gayawa kowa labarin javeed ba amma matsuwa yasata tace mata akwai wani mutum ne datakeso ta nemeshi dan tasan shikadai ne zai taimeketa wajen fayyace gaskiyar cikin dake jikinta wa Mrs Haseena.

Dr surayya tace ba damuwa dama itama tana da wasu yan tambayoyin da take so tay mata in bazata damu ba nur tace ba komi. nan tace ma nur tasake maimaita mata labarin abunda ya faru adakin bayan taga fuskar saadat sabida da akwai wani abu datakeson tayi confirming ranar hanklinta atashe ne bataji sosai ba.

aikuwa nur batay kasa agwiwa ba tafara zayyana ma Dr komi

sai taga dr surayyan na murmushi dan jawota jikinta tay tace shikenan its okay naji abunda nakeso din dama inaso ne in tabbata cewa sun miki allura, zanje asibitin sabida i ask them to save ur old blood sample a laboratory sabida in kara gwada cikin in yakai wata guda,yanxu ma zan sake daukar jininki kinji cos i need to investigate sumtimg inhar nagama bincike na zan sanar dake koma minene.

ahnkli nur ta lafe jikin dr surayya tanamai gyada kai cikin sauke ajiyan zuciya.

*********

Kaduna state nigeria

yau aka cike sati biyu da dawowarsu Alhaj abubukar ciroma kaduna bayan jinyar da sukayi a egypt shida iyalansa.

yau ranar monday rana na farko kenan da yafita offishinsa since after the break bai jima a offishin ba kuwa akace mai yay bako, and he cudnt belive it dayaga Sultan ne,take duk jikinsa ya dau rawa dan yasan koda ka kasance kana da yawan gaskiya kagawai sultan ya tunkaroka dolene kaji hanjin cikinka ya tsure dan baka san da wani irin babban magana zai tunkaro ka dashi ba.

sultan irinsu ne da ake hiring suyi abubuwan da hankali ma bazai dauka ba, he is almst connected to all the gvmnt tiers tun daga local, civil har military

,politicians, criminals, war lords, terrorist, da cartels,kuma duk inda sirri yake yakan iya kakalo shi cikin sauki.

snn shine kadai aboki na kud da kud da javeed mufasa yake dashi a duniyan nan.

isowarsa kamfanin ma wani abun kallo ne sabida irin shegun bullet proof bunkers din nan yakeja yau shikadansa ma yazo

sultan na shigowa office alhaj ya bashi wajen zama suka gaisa, gashi dai babban mutum amma shine yake ma sultan din fadanci sosai.

bayan sun samu nitsuwa kai tsaye sultan yagaya masa cewa Bg Javeed mufasa is seeking consent with his doter razia abu, amma kafin wani maganan aure ya shigo, javeed din yana son ya hadu da ita one in one a private yatch dinsa dake can lagos for a small talk. nan ya dauko wata jaka shake da kudi ya aje masa akan table tare da bashi wani file me dauke da sirrin razia na kkrin shiga fashion nd movie academy aboye, ata daya bangaren kuma location ne dakuma lokaci daga nan ya mike tsaye yace masa shizai wuce sai sunga yarinya on the 8th.

fitar sultan din bada jimawa ba alhaj abubakar yashare zufar dake tsatsafo masa akai ya dau file din ya dudduba ya nata mamakin yadda yarsa razia take wasu abubuwan harda turo hotunanta datakeyi da cvs dinta into movie and fashion world abayan idonsa bayan ya riga ya hanata..

kai hatta chats dinta da movie producers duk sai da suka aje masa awajen ya gaggani.

bayan nan ya bude jakar yaga kudine shake aciki kamar wanda ba ason su. mamaki ne ya rufe sa dan sosai yake da cikakken tarihin ahalin mufasa, wai harme suka gani acikin nashi karamin duniyar da suke son hada zuria da shi.

toh amma da yabar razia taje duniya tana saka tsinannun kaya akan fashion run ways ko tana tabe tabe da iskanci da maza da sunan yar film gara kawai ya mata auren a inda yasan baza'a bartta take yin irin wann mafarkin nata bama.

he knws mufasas are underworld mafias daga zarar sun hada zuria toh ba lallai bane sukara ganin yarsu razia idan ace javeed ya aureta.

atake kawai ya yanke hukuncin koma miye javeed yake bukata zai basa muddin ba zina bane ko wani sabon Allah, which he knw is even highly impossble for the mufasas to involve demselves in such low acts, sabida mutane ne masu ilimi, kamiya da daraja kansu bana wasa ba.

aikuwa yana komawa gida baiyi kasa agiwa ba ya tattauna batun da matayensa sai dai abun mamakin shine tundaga wann ranan sai ba a sake samun zaman lafya agidan ba..razia taji baqin ciki da aka tona mata asiri akan plans dinta nq cikar babban burinta and she doent even knw who the hell is that javeed mufasa, so how on earth zata auresa..

mahaifyta kuma ba matsalarta ba kenan, babban matsalarta shine tasan inhar aka bada razia wa ahalin mufasa kusan an rabasu kenan na har abada, sabida kowa fa yasan ahalin mufasa they are alwys like a ghost family, they barely relate to the outside world sabida sirri da kuma kare jinin wanda suke muamala dasu

kawai ji tay bazata iya sadaukar da razia ba,

dan razia is der only child, koma yaya ne tanason razia ta aure normal mutum, wanda zasu na ganinta duk sanda suke so, and they will even bond with their grand children.

alhaj abububakr kuma gani yake da yabar razia tay film ko taje tana yawo kusan tsirara akan fashion runways gara ya aurar da ita acan.

kullum hatsaniyar da ake samu kenan agidan, iyaye matan duk sukabi bayan razia, shikuma yace dolentane sai ta masa biyayya akan javeed mufasa..sn inhar javeed yace zai aureta ko taki ko taso zai bada ita. razia has been depressed ever since maganan nan ya fito babanta kuwa sai shiri yake kowani rana kuma sai ya tuna mata cewa in few days time she wll be going to lagos to meet javeed mufasa kuma babu fashi akan haka.

haryau ya kasance saura kwana biyar hakan ya faru tunanin duniyarn razia tay na yadda zata kwace kanta acikin wann cakwakiyar harde ta amince da shawarar kawarta molly ta bata wajen gaya masa gaskiya cewa ita da mamunan ta basuson auren babanta ne kawai yake so and she planned to beg him to let her live her dream koma yayane ai ta dan tattambaya tarihinsa few ppl dat knw him ance famlyn mufasa suna da addini so she thinks she wll likely make him understand that auren dole babu kyau a musulunci.

she planed all this and just chill bata kuma fasa dena turawa hotonanta wa fashion house da stunt dinta wa producers ba.

********

Abuja..

nur firdaus ta shiga wani sabun damuwa dan tun ranar da adnan yace mata zaije wajen babansa sai bata sake ganin ya dawo ba kuma gashi babu waya a hannunta aynxu bare taji meke faruwa. A fannin adnan din kuwa tuni yay amfani da agent din babansa batare da ya sanar da baban nasa bama, sabida so yake shidakansa ya hukunta sadaat tukun yahuce dan bayaso a zo akamshi a mika sa wa hukuma, wann qudurin san yasa ya hada kai da abokinsa abrar dake yaron gagarrare ne yana kuma saida kwaya hrda irinsu cocaine snn yana harka da manyan hooligans

Adnan yana zuwa gida aranar yaje dakin mamansa ya dau katon jaka ya bude safe dinta ya kwashe kudi ya cika jakarsa dashi snn ya saci jiki ya fita, daga ranar babu wanda yasan ina yaje..ko awaya basa samunsa ba, hada kai yay da gayun ya nuna musu kudi suka masq shige dafice in less than 3-4 hours aka kwamuso masa sadat tundaga niger cikin dare suka suka kaisa wani jeji inda suke kazamin harkansu ta drugs din aboye, anan ne adnan yafara amsar shaye shaye arayuwarsa har abun tafara shigarsa, suka daure sadaat jikin bishiya suka fara ma sadaat din mugun ta na fitar hankali. dan kowani bayan mintina sai ya konasa da ruwan acid awani part na jikinsa dan yaji irin ciwo da zafin daya dandana ma zcyar nur dinsa dis few days, ga duka da gayun suke masa da itatuwan itace manya manya.

saboda ba acikin hayyacinsu suke ba kuma yarane kanana da iyayensu ke daure musu gindi duk basufi 20-24 yrs ba, it was so easy for them to get him sabida drugs connection da suke dashi a niger din kawai waya sukayi sukasa bounty wa yan jagaliyar gari sai gashi nan kuwa an kamo musu shi.

rantsuwar duniya sadaat ya musu cewa baiyi raping din nur firdaus ba amma suka maidashi mahaukaci

suka faffasa masa jiki

duk sanda adnan ya sha cocaine din kamar haukacewa yakeyi, he was pure evil baya jin kai baya tausayi bayama jin me sadaat din ke cewa.

azaba suka dinga gana masa har na kwana biyun, da suka lura da cewa za'a iya nemansu sai suka yanke hukunci gamawa da sadaat din.. arana na biyun da tsakar dare karfe daya da rabi suka tube sadat tsirara, suka kaisa cikin wani container suka turasa acikin wani drum wanda zallan ruwan acid ne aciki suna tsaye har yagama sullubewa namar jikinsa ya narke suka bar zallan kashinsa acikin drum din wanda suke tunanin shima kafin nan sa safiya zai narke koda anzo bincike wajen bara agane waye aka narka bama.

wajajen asubah suka tattara komi nasu snn sukay proper clean up againts any evidence awajen suka daddawo

cikin gari, wasun su a safiyar ranan suka bar nigeria, abune wanda adnan bai tabayi a rayuwarsa ba amma kuma koda yaga sun ma sadaat haka sai yaji kamar sai yanzu ne hankalinsa ya dawo jikinsa.

he totallly changed ya fara shan cocaine din sosai just to clear his head off the memori na cewa sun kashe sadaat murus shida abokansa.

sai after two days din da yamma sai gashi ya dawo gida bai kula kowa ba dan tambayr duniyan nan babansa ya masa akan inda yaje kwana biyu amma yaki sam ya fada saima kulle kansa dayay adaki ya cigaba da shaye shayensa dan babu karya in besha ba yasan zaina tuna cewa sunyi kisan kai wanda yasan bazai taba nadama akai ba koda wata rana an kamashi.

yadda yake son nur firdaus he feel he cud do more for her sake

washe gari ana saura kwana daya daurin aurensa bema sani ba anata shiri sassafe ya fito zaije shi gidan haseena domin ya dubo nur mahaiyarsa ta tsaresa da hayaniya

ko kulata baiyi ba yaje gidan ya samu daga didi sai Nur haseena da layla sunfita wajen bridal fittings na daurin auren layla basu gayama kowa ba

hanklin Nur sosai ya kwanta dataga adnan agidan itama tambayar duniya ta masa akan inda yaje kwama biyun amma bai gaya mata komi ba, but she noticed how much he changed sai kawai ta dauka ko abubuwan da suke faruwane suka zanca shi.

tun ranar da abun ya faru basu taba samun momemt na farin ciki arayuwarsu ba sai yau din dan kuwa a garden suka zauna suna ta hira, wani abun dariya wani abun tausayi wani hirar har ya sakasu kuka, they have no idea this moment wll be their last.. sosai nur firdaus ta gode masa irin soyayya na amana daya nuna mata dan abune wanda bazata taba iya mantawa ba.

tunda suka zauna awajen sallah ne kawai ya ke daga su sai can da yamma kafin nan babansa ya kirasa awaya, nur ta rakashi har gate ya shiga motarsa ya tafi yanamaice mata gobe da safe zai dawo

tun bayan tafiyarsa Nur tana zaune a garden din tana karatun qur'ani tana kuma tunanin yaushe dr surayya zata dawo

daga asibiti dan tun dazu ta debe jininta ta fita basu kara jinta ba

ana kirar magrib ta wuce ciki domin gabatar da sallah

tana kkrin yin sallama kenan taji ihun mrs hasina daga waje da kamar bazata fito ba wani abu yace ta leko aikuwa tana lekowa tagasu Didi da dr surayya data shigo yanxu itama suna kan kokowar danne mrs haseena acewarta

an aiko mata sako da private number cewa mijinta saadat is gone missing amma wat eva d outcome of the investigation gobe ne zataji.

nur batasan sanda taja tsaki takoma daki ta chigaba da tasbihin ta ba.

anyi asan waya tura ma mata sakon ba sani ba..amma sosai haseena ta daga hankalinta gashi kwana biyun nan kwana take tana tashi da fushi da kuma kishi akan abunda nur ta fada na cewa shine ya mata fyade.

daren yau be ma Adnan dadi ba sam dan darene wanda yakejin kamar har rayuwarsa ya kare bazai taba mancewa ba,dan kuwa yana komawa gida iyayensa duka biyu suka sanar dashi cewa gobe da karfe biyu na rana zaa daura aurensa da laylah..and the weding is very important for the reputation of his family dan ceto alaqar hajy mairam shehuri da kuma mrs haseena kamar ceto siyasa da mutuncin gidansu ne.

babu irin dokokin da basu saka ma adnan dan su tsoratashi ya amince ba amma haka dai ya musu taurin kai yace inba nur zai aura ba ya gwammaci, su disowning dinsa, su rike arxikinsu, da siyasarsu su koreshi a cikin family duk ya amince ammade bazai aure wata layla ba.

hajiya mairam tay fadan tay lallamin harta gaji amma adnan baima san tanayi ba, koda tace zata tsine masa yace mata she shud go ahead..haka yabar su anan yaje daki ya debi zallan wayarsa zai bar musu gidansu, hajiya mairam ta dinga kuka tana birgima dan bata san yadda akayi har adnan dinta ya dawo me tsananin taurin kai haka ba, hanklin kowa yatashi dan wann hayaniyan ya jawo abubuwa dayawa yafaru, da sukaga haikan adnan din zai barsu dagske duk suka razana suna binsa abaya suna rokonsa ya dawo a sasanta amma yaki sam, nan take kuwa babansa ya yanki jiki ya fadi with a serious cadiac arrest wanda badon likitan gidan na kusa ba da an rasa shi kenan. wann lamarin ne kawai ya bawa hjy mairam wani babban dama,nan kuwa ta hada baki da likita tace marmasa su tursasa maganan ciwon inda zaisaka adnan ya rusuna ya amshi qudirinsu. ai kuwa hakanan akayi they use every words possble to blackmail him emotionally akan ciwon babanshi har adnan din ya amince just for his dad to be alive amma badon haka ba ji yake koma me zai faru saidai ya faru amma bazai aure layla ba.

saidai tunda ya amsa batun yakoma dakin sa shikenan basu sake gane waye adnan ba,he got very high on drugs ahaka ya kwana yay sallah ba acikin hayyacinshi ba yaki ya fito har washe gari ranar daurin aurensan.

gabaki daya hankalin iyayen nasa ba a kwance yake dashi ba amma hakanan dai aka dinga managing dinsa..

daga gefen nur da safe dr surayya tazo suka gaisa tace mata tay haquri haseena taqi saurararta akan batun wayarta amma zuwa can anjima da yamma the result of her new tests datake running akanta will be ready dama an dan samu delay me wajen karban dayan jininta dake asibiti saidai bazata bata wani hope ba sai ta gama komi. nur ta gyada kai dan tasan kowa na tausaya mata sosai ayanayin datake ciki.

yau hanklin Mrs Haseena rabi nakan jiran news na bacewar sadaat rabi nakan shirya layla domin daurin aurenta da zaayi karfe biyu

haka kuwa bata gaya ma kowa ba didi ma datasani bata ce musu uffan ba har saida lokcin daurin auren yay za'a je masallaci a daura snn

mrs haseena ta shigo musu sashen da layla lokacin har an mata wani irin kwalliya na amare an saka mata wani irin tsadadden french lace fari kal da stones ajiki an mata duk wani shiri da ake ma amarya lalle ga jeweries ubansu.

layla tay kyau bana kadan ba, Su nur suna zaune a daki ita da dr surayya da Didi saiga su nan sun shigo..

cikinsu Didi ne kawai bata sha mamaki ba kawai ta dauke kanta dan tafi kowa sanin yarta haseena da taurin kai da rashin imani, hasina has since been rebellious and determine, inhar kace zaka gaya mata gaskiya to saidai kuyi tone tonen asiri, kawai tana rike baqinta ne da girmanta dan kada ta furta wani abunda zai zubar ma haseena kimarta na har abada agaban yayan cikinta

Nur ta mike tsaye tana kallon layla all glamed up in her bridal attire looking breathtking.

tajima batay murmushi amma koda taga irin kyan da layla tay saida tay mata murmushi me sanyi...Tace "little sis u look beautiful"..

layla ta zubawa nur din ido batace komi ba sabida she knew she is about to hurt her feelings amma kuma aikowa kansa yasani ko??

Dr surayya ta kasa haquri tace haseena wann irin shiga haka ina kuka nufa ji yadda layla tay kyau kamar wata amarya..

Cikin sauke ajiyan zuciya mrs Haseena tace baki bata ba Dr..ai layla amaryace ayau.

nan ta kalle nur cikin yanayin harde rai snn tace" kowa yasan dq cewa Qaddara babu ydda bata aje mutum. kuma akace matar mutun kabarin sa.da ace mutum nada iko akan qaddararsa da nasan nur fiddaus bazata amince ta zauna da cikin wani barawo ajikinta ba, nima kuma bazanso ama y'ata fyade ba. amma abune daya riga yazama wani rubutacce kamar yadda auren layla da Adnan shehuri ya zama rubutaccen al'amari ayau..

gaban nur firdaus atake yay mummunan fadi idanunta suka wani irin ciko da wasu zafafan hawaye dan ita direct mrs haseena take kallo datake furta wann magangnun...

baki bude Dr surayya tace "Adnan.."wani Adnan? hasina kinsan me kike fada kuwa

sanda hawaye suka fara sauka a idon nur ma bata sani ba kawai ji tay jikinta na wani irin kakkaryewa ta ciki kamar ana sasareta ba gatari.

lumshe ido tay tana jin mugun zafin kishi tareda ciwon rasa soyayyarsu da adnan din na ratsata

tanaji mrs haseena tahau musu bayani, bata boye musu komi ba ma yadda iyayen adnan sukaki jinin nur firdaus sann suka nace sai an basu laylah.. duk ta gaya musu komi, tace tasan zasuce tabi sonkai da son zuciya ta raba nur firdaus da masoyinta. amma koda hakan zaiyu ita bazata iya bada nur wa famlying da already sunki jininta akan qaddararta ba amma tunda sunce suna son layla, kuma layla dama tana son adnan din shine kawai ta basu...Allah yasaka hakan shine zabin Allah! ita bata son aja wata magana me tsayi akan wann batun kawai nur din tay haquri.

tana cikin bayanin nur firdaus takama hanya jiki a sanyaye zata fita waje tabar musu dakin dan bata son tay kuka me yawa agabansu she just feel like she need to be alone dan har wani duhu duhu tafara ganin agabnta..

tana daga kafa kuwa layla ta wani rugo da gudu tazo tarike mata hannu tawani narke fuska da muryan kuka tace 'Big sis, yaa nur pls dont leave, say sumting to me. bana son kiyi zaton na ci amanarki, kema fa kinsani i truly love and cherish you. adnan was since meant for me, qaddararmu ce, kuma namiki alkwari zan kula dakaina da kuma Adn..nan. nd i will din everthing to make sure he is happy big sis in auren nan ya bata miki rai dan Girman Allah kiyi hakuri kiyafe mun ure the mother i neva had i knw u wll understand how i feel big sis pls say somthing to me.

jikin nur na rawa rawa dakyar ta iya hadiye wani gulluton baqin ciki daya tsaya mata a wuyarta tadaga kai ta kalle laylan yadda babu abunda ta tuna face yadda kowa yake gaya mata cewa layla tana kishinta, kuma ta dade tana makirtanta, ta jima tana boye wani abu na sirri a ranta game da alaqarta da adnan.

itadei tasan harga Allah bata taba cutar da layla ba, but wat eva happen here yasa ta tagane cewa dama she was all alone in her world, sorrounded by ppl dat neva apreaciate or even like her for a bit. sai yau ne taji mutuwar babanta ya kara hitting inta hard, he was the only one that truly truly love her afteroll and he is gone. ji take kamar ta harzuka ta rusa ihu koda baqin ciki zai ragu mata amma inaa ta kasa.

hawayenta na zuba sosai at same time saitay murmushi me mugun sanyi wa laylan muryanta na rawa sosai tace laylah, in har na taba cutar dake cikin rashin sani dan Allah kiyafemin, all i eva wanted was to love u and protect u bcos ure my only sister. but its okay now..'Its ur wedding day little sis. bani da wani abinda zance miki, i wish u gudluck with life and pls "congratulations".

tana fadin hakan ta kwace hannunta ahankli tana baza sassanyar murmushi hawayenta na kuma zuba cikin sauri tay waje.

kakarsu Didi ne ta tashi da sauri tabi bayanta tun da fita ta zube akasa awajen garden dinsu ta dinga kuka kamar ranta sai fita..

Dr surayya ta dinga kallon layla da hasina da wani irin shock

da har zatace wani abu sai tafasa iyaka jakarta kawai ta juya tadauka azazafe ta rataya ta kalli hasinan cikin ido snn tace mata Haseena karki mantq duk abunda kika shuka in sha Allah shi zaki girbe. i get ure mother, kuma ke kadai kikasan dalilinki nayin abunda kikeyi wa nur ynxu..i wish u gud luck on ur favorite doters weding. nan tama laylan wani irin kallo

with so much disgust

wanda ko jiran wani reaction dinsu batay ba ta bangaje mrs haseenar tay waje tabar gidan abunta

Aka bar mrs haseena daga ita sai amarya layla dake kan kakalar kuka dan gashi dai ba bakaar magana ko ihu nur ta mata na amma kuma sai taji gabaki daya hanklinta ya mugun tashi..

haka mrs Haseena ta rarasheta tace mata ta sharesu zasuyi subari, nan sukaje quest house anan wasu kawayenta na siyasa sune suka rufa mata baya har akayi karamin walima by 2:30pm on d dot famlyn shehuri daga maidaguri suka hallara har aka daura aurensun aka gama batare da ango ya zo wajen ba.

adnan yana gida yana kwance ya gama shan cocaine babu ko karfi ajikinshi kuma yasan duk tsiya de ba zaa barshi ya fita ba tunda har aka daura aurensa be jeba. he wrote a very long emotional letter yanata kuka da yamma can ya tura ma nur firdaus dinsa

yace lallaine yanason yaga reply inta dan gani yake idan har baiji daga gareta ba hala zai kashe kansa kafin ayi hidmar auren dan tun jiya yake fama da wasu irin suicidal tots he just cant belive zai rasata.

nur kam tuni tay kukan ta abun har ya fice mata arai, atleast she knew dat was the best for them, dan tasan akarshe koda sunyi auren ma kayan baqin ciki da wahala zata zame masa so Allah knows what best

bayan magrib daga ita sai kakarta didi ne agidan su haseena suna can guest house inda aka aje amarya layla cos in this week to come zaayi events kala kala har guda biyar na shagalin biki kafin akaita gidan mijinta anan abujan amma a can sabon gidan sa a maitama wanda iyayen suka gina masa zasu zauna so basically auren kawai aka daura dan awargaza duk wani makamashin shirin da sanata bala zatay gobe da safe.

Nur tana idar da sallah ta zauna tahau rubuta reply dinta ma Adnan with calming words dat is carefully writen with so much love and gratefulness,

tay baqinciki amma aciki sai tanuna masa cewa kamar tafi kowa fahimatrsa,kuma bata dau hakan a matsayin cin amana dga garesa ba, tajawo masa wasu ayoyin qur ani dayawa wanda tasan zaiyi reflecting akai dan ya gane cewa qaddarar su kenan. komi daya kamata tagaya masa wanda tasan zaisaka shi yanitsu yakwantar da hanklinsa akan auren saida ta gaya masa in the most beautiful way ever.

sai datagama kuka sosai sann ta fito ta roki malam liman akan ya taimaka mata ya kai masa yau din nan da dare.

adnan yana daki yana kwance wajajen karfe tara aka kawo masa lettern,jikinsa na rawa ya karba wanda harse daya gama karantawa snn ya iya busar numfashi dakyau yaji wani bangarena jikin sa ta dawo aiki dede

tasakashi ya mata alkwarin cewa zai yi auren ne domin Allah domin kuma biyayya wa iyayensa sann zai kula mata dakansa bazai kuma yi fushi da qaddarar rayuwarsa ba, duk wann ya amince aransa zaiyi dominta amma batun wai zai kula mata layla anan kam yasan bazai taba yuwa ba.

he just wanted her to come to him first dan haryanxu bai gama tsara irin zaman da ya shirya mata zatay da shi ba duk duniya yakejin babu wacce ya tsana kamar ita.....

SURAYYAHMS

***

COMBACKSERIES

2024/2025