35
by @surayyahms
NUR FIRDAUS....35
SURAYYAHMS
@surayyahms AREWA BOOKs/ wattpad.
FINAL EPISODE.
Book1.
Duk yadda nur taso kar da tasaka komi aranta sai da hakan yaci tura dan auren saurayinta Adnan da kanwanta layla ayau din saida yahanata runtsawa duk dama abubuwan dake faruwa da ita yasa ta dena shiga shock sosai sabida tunda akace an mata fyade kuma tana da cikin nan ta hakura takara mika zuciyanta da kominta wa Allah S.W.A kamar yadda mahaifinta ya mata nasiha a mafarki.
komi da ya faru na qaddara, the hatreds, the losses, the rape the pregancy trauma, karatunta kam ma yanxu bata san ina ta dosa dashi ba, hala kenan saita haihu tabi didi can garin yola taje inda ba asanta ba snn tay karatu inta samu miji awajen kawai sai tay aure.
adayan bangaren kuwa sanata farida bala ta nemi sadaat sama da kasa,kudu da arewa bata samesa ba kawai sai ta kudura aranta cewa tabbas su mrs Haseena suna da hannu abacewar sa duba da duk wani abunda ta shirya na tozartasu a social media sun dakileshi.
baqin ciki da damuq kamar sai kasheta da bata ga sadaat ba dan bata da wani yaro acikin yaranta datake mutuwar sonsa akan harkan gado kamar sadaat gabaki daya sai hankalinta ya tashi sosai.
washe gari sassafe kuma sai ta tashi da labarin cewa wai har anyi auren Yar gidan haseena da adnan shehuri, wann news din ma ya girgizata dan ji tay kamar zata haukace,atake ta kira gidan telebijin din ta canceling din shirin data shirya snn takira ussy tace mai maza yaje nigeria yaje ya bincike doctor din nan kode acikinsu wani ya tona mata asiri ne bata sani ba.
Nur bata wani samu bacci ba dan haka washe gari da safe ta tashi da wani irin zazzabi didi ne ta dinga kulawa da ita harsai can yamma snn su mrs haseena suka dawo gidan ita da amarya layla
a cewarta zata shirya layla kafin azo events sabida akwai wasu abubuwan al'ada da akeyi in zaa kawo su lefe da kuma tsaraba gashi bata da wani isasshen kudi duk sundawo hankalin su atashe didi dai batace musu uffan ba.
Daga schl din su nur kuwa anyi gulma dq rade raden case inta har angaji an dena dake Allah ya rufa mata asiri abun sai beyi tsanani kamar yadda maqiya ke zato ba dakema haryau babu wani shaida akan zancen cikin sai dai yuwar auren adnan da layla sosai yay spiking wani sabon gurmi da gulmace gulmace da cece kuce a tsakanin yan makaranta.
Hankalin jadidah yaki kwanciya dakyar ta roki malam liman ya barta ta shigo gidan ta same nur firdaus da maganan auren.
koda nur firdaus tay confirming mata ta kuma dauko lettern adnan ta bata tagani da idonta bakaramin kuka jadida ta musu ba. ta jinjina cikin jimami sanin cewa tabbas wann shine qaddarar ubangiji.
saidai haryau Nur takasa gaya ma jadidah cewa she is pregnant and the story behind it duk dama zuwan jadidan ya kawo mata sauki dan sosai ta debe mata kewa daga tunanin da ciwon datakeji na rasa adnan dinta. layla tana gidan tana zama a dakin Mrs haseena ana ta shirin tsara events na aurenta amma gabaki daya borin kunya ya hanata ko lekowa waje.
har saida jadida tazo tafiya snn laylan ta fito da wani lullumi tafara ma jadidan magana jadidah tay kamar bata san ta ba ta wuce ta kara da gaba batare da tace mata uffan ba. Nur firdaus tajuyo kenan zata wuce ciki laylan tabiyota abaya da sauri tana kiran sunanta big sis big sis
gabaki daya nur sai tanajin kamar laylan tariga tafice mata arai amma hakanan dai ta daure tatsaya dede
cikin falo tanamai saurararta
layla tadan sunkuyar dakai tafara umm ummm can de tay shahada tafara cewa dama, dama, big sis inasone ki dan bani aron abayarki wanda kikasa a kaduna ina so na saka ranar da zaa kawo lefe na, and i also have few oda things naki danake so kiban aro kinga auren yazo mana wani iri agaggauce i havent done anything abt it mummy kuma bata da kudi sosai, familyn adnan sunata demanding din abubuwa, but we cant really afford it big sis, i really need ur help with some things..
tun kafin nur fiddaus ta budi baki amsa Didi dake jinsu ta harzuka tasauko kasa rai abace tace keeee laylah kinci uwarki kenan ashe baki da mutunci baki da hankali?..kema ashe mugun jinin hasinan kika kurba baku da kunya baku da tausayi waike layla harkina da baqin karban aron kayar nur domin yin hidiman aurenki shegiya kawai marar imani
rai amugun abace layla tace haba grand ma, ni me nayi miki dan Allah kike min wann zagin, kayanki nace zan karbi aro ko na yar uwata, toh yau naga ikon Allah da can wajen waye zan je na karbi abu in ba wajen yar uwata ba
ko sokike naje nay aro awani waje ehhhhh
...bazata didi ta wanka ma lebben bakinta mari tace "kikace yar uwanki? aida a yar uwanki kika dauketa ko akafa aka daura miki adnan zakice a'a sabida ai ko ba komi ana barin halal dan kunya,.ga nan yar uwarki tana fama bata gama warkewa bama daga ciwon iftila'in daya afka mata, but dake you clearly dont care abt her well being ai gashi kin aure mata saurayi..toh wallahi kisani layla namiji ba a masa dole, inma kina tunanin kunyi amfani da wann daman kunci nasarar rabasu toh kijira kiga irin rayuwar da zakiyi dashi. ranar kukan ki na nan zuwa marar hankali kawai.
wani irin gullataccen kuka mai cin rai laylan tafashe dashi daga can sama Haseena dake jinsu itama nan takarasa saukowa tace haba mama, shikenan kinsata kuka hanklinki ya kwanta fisabillahi wann irin mugun baki kike ma layla haka,ita meye lefinta? naga de ba ita tsarawa kanta wann qaddrar ba Allah haka yaso itace matar adnan.
Da wani irin bacin rai Didi ta kalli idon mrs haseena tace na rantse da raina karya kikeyi Haseena, qaddarar karya wanda kika kirkiro mata shi ba?yarinya bata da hankali,bata san me kemata ciwo ba muguwa wacce bata san kunya da halacci ba.
koda shike kece kike daure mata gindi haseena kuma kinsani cewa wann tsinannen gurbataccen alaqa da kuka kulla bazai daure ba, auren da bbu daraja, babu kima, babu soyayya aciki sai cushe. ta kalli laylan dake kuka tace haqqin yar uwarki saiya kamaki cos u can neva be happy or win on another women tears. Kuka kam bakima fara ba layla kukanki na nan gaba shashasha kawai marar imani..
da wani irin ihu mrs Hasina ta katseta haba Mama haba mama, duk kin gama tsinewa auren nan albarka waime haka ne kam? yanxu kenan ni bazaki fahimce ni ba, duk abunda nake yi is for their own good..
A masife Didi tace ehm ehm dnt tell me that nonsense dan
kowa ya sani ure doing dis for ur own selfish reason dan baki kaunar political reputation dinki ya baci, dahakan ya faru kim gwammaci gara kigwara kan yayan cikinki, daya kin kasa yi mata adalci daya kuma kin chusata zaman aure a inda bata da gwarjini.
mrs hassena enuf mama, enuf..ya isa haka..dan kawai ina darajaki ina miki shiru shine zakina gayamin bakaken magana agaban yarana mama
...what make us apart
..inma am selfish mother aikece kika haifeni..bambamci na dake shine i choose to rise and shine, ke kuma kin zabi ki kashe kanki awajejen da ba asan darajarki ba, layla tana son adnan, kuma nasan shima zaizo ya sota, babban misali shine kamar rayuwar aurenki..
Didi tay dariyar takaici snn tace eh kimin gori da rayuwar aurena agidan ubanki haseena, na yadda bani da wayo kamarki, yes..bcos i choose to stay in my abusive husband house to raised you,you ingrate. ban kyaleki kin shiga wani hali kamar yadda kika kyale naki yayan suka shiga wani hali ba..haseena menene wayewarki ya kawo miki,..har yanxu baki da gidan kanki, rayuwar karya dana siyasa shi yake rike ki har ke kin isa ki hada rayuwarki danawa?
Mrs Haseena ta fara kuka "why are u even here mama dama ashe kinxo ne dan ki zage ni kici mutunci na?dats why u deserve evrything dat has happen to you, if i failed as a mother u also failed as a mother.
Didi tace Fine Haseena. i failed.
amma kisani na riga na gaya miki gaskiya akan yaranki yau, yadda kike tafiyar da rayuwarsu cikin nuna sonkai,warayya da bambamci bai dace ba. sauran kuma ya rage naki. ni kinga wucewata.
Daga nan Didi ta wuce sama, Mrs haseena ta share hawayenta taja tsaki tace kifi ruwa gudu mana dama can bani nace kixo min ba. tana fadin hakan ta haura sama ranta a mugun bace tareda layla abaynta.
nur ce tabi bayan kakan nasu taje ta sameta ta kwanta agado tana sobbing ahankli, nur batace mata komi ba kawai tazo tadan rungumeta in a comforting way tsawon lokci suka kasance ahaka har saida tsohuwar ta samu nitsuwa...
tun bayan wann heated argument daya faru a tsakanin mrs haseena da kuma mahaifyarta Didi gidan sai ya dau shiru
nur tarasa meke mata dadi gashi Dr surayya bata dawo ba har sukayi bacci washe gari kawai tana idar da karatun qur'ani bayan sallahn fajr taga Didi tana tattara kayanta zata wuce yola abunta.
Babu kalar haquri da bakin da nur firdaus bata bawa tsohuwar ba amma tace sam bazata iya zama da Mrs Haseena ba dama can saboda su kawai tazo Abuja amma tunda komi ya lafa gara ta wuce gidanta dan bazata iya zama inuwa daya da haseena ba.
tun nur tana bata hakuri hartagaji ta dena, wajajen karfe takwas Didi ta gama shiryawa ko sallama bata musu ba ta fita nur tabita har gate tana hawaye, tausayin nur din duk ya cikata amma babu yadda ta iya sai kawai ta dan jawota ta rungumeta tay tabata haquri akan lamarin rayuwa sann tace mata in har tasan xamanta da hasina anan abuja zai zame mata cutarwa a wann conditon din toh maza itama tashirya taje ta kai kanta wa dangin ubanta..daga yin wann maganan Didi ta kama hanyarta ta bar Abuja.
sosai tafiyar Didi babu sallama yay ma Mrs haseena zafi arnta bana kadan ba, kenan ita kadai zata aurar da layla babu wani dangi na jini sai kawayen siyasa, she was so frustrated dan waliyan laylan ma da kyar tay convincing din wani abokin mijinta ka harhada mutane jiya aka karbi aure kuma tun daga nan basu sake dawowa ba.
dakyar tazo ta iya danne komi ta watsar snn ta cigaba da hidimarta abunta.
ranar da didi ta wuce yolan layla bata wani daddara ba haka ta sace kayan sawar nur kankararru taje bridal photo shoots dasu,
da kyar Adnan yaje wajen ahakan ma wai saida mum dinsa tay kamar zatay hauka koda yaje wajen yana ta babbasarwa layla taga ruwan walaqnci awajen dan adnan yaqi sam ayi wani style da zaisa ta matso kusa dashi amma ko ajikinta ana gamawa da wann da dare can suka dawo gida da wani uban rawan jiki tazo ta samu nur ta fito daga wanka kenan dan is almost 10pm na dare
tana zuwa kuwa ta fara nunawa Nur hotonan biki, abinka da rai da jini, dataga nur ta dauke kai bata kalla ba kuma bata kulata ba sai kawai ta hade rai ta fita kai kararta wajen mrs hasina, tana zuwa ta samu mrs hasinan nakan waya ana mata batun za'a kawo lefen laylan washe gari Duk hanklinta ya tashi dan bata da wani isashen kudi ahannunta da zata tarbesu yadda ya kamata dan karamin walima sukeyi anasu al'adar bakaramin kashe kudi akeyi ba wajen bada tukuici da sauransu.
ganin Hanklin mrs hasina a hargitse yake sai kawai ta koma dakin ta samu nur harta kwanta, kawai sai ta fara habaice habaice, tana cewa wai ai baqinciki ake mata akan aurenta daga karshe dei nur earpiece ta saka ajikin system dinsu na dakin tana jin karatun qur' ani har tay bacci.
washe gari sassafe Mrs haseena ta fita neman kudin tarban baki dukansu sun farka basu ganta agidan ba.
bangaren ussy kuwa tin jiya dayaje asibiti ya gudanar da bincike ya kira sanata farida awaya yace mata bai samu matsala wajen likita ba tace sam bata yarda ba, garin bincike yaji labari cewa Dr surayya ta amshi jinin nur taje asibitin datake aiki tana gudanar da gwaje gwaje akai
atake Sanata farida ta bashi oder akan ya nemi Dr surayya cikin daren nan ya kwace duk wani abunda ta samu sann ya gama da ita. koda yaje asibitin da dr surayya take aiki ya samu bata shigo ba tukuna mei aikin lab ya biyasa kudi nan yace masa aijiyan tana wajen meeting ne amma da safene zata shigo.
haka ussy ya zauna a asibitin har safiya yay disguising kansa as a patient, around 9:30 am na safiya sai ga doc surayyan ta taho sanye da hijab da gilashinta dake mata mugun kyau. kai tsaye tawuce cikin lab din da key inda ta boye results da duk wani sakamakon gwajin
nur dan bata yadda da kowa ba tana kuwa daukowa tawuce dashi offishinta duk bata san ussy yana kallon duk wani motsinta ba.
she is a gyneocologist dan haka bata bukatar wani ya fassara mata sakamakon test din,
tana sakawa a yar computerta ya fara nuna mata complte blood scan result for nur firdaus harouna
sample din jininta na farko yanuna yana dauke da high dose of human chorionic gonadrotropin mixed with progestrone injection.
shi HCG wani nauin hormone ne da jikin ya mace yake producing dinsa naturally idan ciki ya shigeta, snn duk wanda aka masa allurar HCG in high amount atake jikinsa zai fara wasu reacting kamar na me cikin gaske koda bai sadu da namiji na.alluran yana iya tricking bodyn mace into thinking cewa akwai embryo a mahaifarta koda kuwa babu komi. barema da aka mixer shi da progestrone wanda shikuma babban aikinsa shine ya saka symptoms na ciki kamar amai, su kumburin nono kasala da daukewar jinin al'ada sabida shi asali dama pregnancy supporting hormone ne. ana maka high dose na wnn allurar zai atake fara reacting within d first 24hrs,
sann bayan kwana biyu kuma zaka fara jin alamar shiga ciki early prenancy signs and symptoms haka zaiy ta worsening musmn inyakai 1-2 weeks and can even produce a false positive test result
in akaje gwaji.
Bazai kuma fasa nuna wa mace tana da ciki ba harse karfin alluran ya ragu sosai ajikinta nan ne in akaje akay gwaji za'a ga negative snn ahankli sai sign nd symptoms duk zasu washe. the main amfaninsa shine asaka mace taji kamar eh tana da ciki for a while dan a kawo wani rudani ko hatsaniya.
Dr surayya was soo shocked and excited at the same time sai kabbara takeyi tana gode ma Allah dan tsabar murna tama kasa rufe baki face sai dataga result na biyu na dayan jinin nur firdaus data dauka shekaranjiya aikuwa taga yanuna pregancy negative da alaman ruwan Alluran ya fara ficewa ajininta.
Da karfi tace masha Allah, Alhamdullahi ya Allah nan ta mike tsaye tace zama bai kamani ba masha Allah..cikin lumshe ido da budewa tace Allah mungode maka da ka cire yarinyar nan a wann fitinar..
wayarta ta dauka ta dinga shekawa mrs hasina kira dan ji take bazata iya ma jira takai musu result din ba, saidai mrs hasina na can acikin rubibin shirya shiryen tarban yan kawo lefen layla bata ma ji ringing din wayar ba.
ganin ta mata 6 miss call bata dauka ba kawai sai ta dauki files din da misalin karfe goma da rabi ta kama hanya zataje gidan mrs haseenan dashi aikuwa tana ficewa ussy ya dinga binta abaya, ya kira sanata ya gaggaya mata cewa ai yaga Dr surayyar da file tana haba haba ta fice da alaman gidan mrs haseena zataje..
atake ta bashi wani sabuwar oder nan ta turo wasu suka fara binsu, Dr surayya tana tuki akan hanya bata hankara ba kawai tag an wani yanka an shigo gabanta kafin tay control taga wata baqar motar tayo kanta da gudu ta mugun tsorata ta fara salati babu imani suka gwarata da kwalbet saida suka tabbata ta fadi ciki.
motar ce tay tumbul ta fadi da gefe take ta suma kafin mutane masu wucewa su tsaya dubata nan ussy yay sauri yazo ya cakka mata wani allura snn ya mika hannu ya dauke file din ya cusa a rigarsa sai kuma ya fara ihu yana cewa jamaa ataimaka ataimaka
duk masu wucewa sukayo wajen acikin rubibi ussy ya bace abunsa, ahanya ya kira mutuminsa na lab yace masa ya dauke laptop din Dr surayya sann ya share history na sakamakon gwajin
haka aka dauki Dr surayya aka kaita asibiti emergency direct bawani rauni taji ba amma atake ta shiga comma.
bayan sun cimma wann lami lafiya sukabar abuja da file din dan sanata ta riga ta bada aiki an bazama ana neman mata inda sadaat ya shiga.
Wajajen bayan azahar hasina ta dawo gidan a mugun gajiye batako duba wayarta ba bare taji meke faruwa ta shigo kenan ko zama batay ba saiga kirar hajiya mairam, dan ringing tone na daban tasaka mata dan haka kirar nashiga ta dauka jikinta na bari tafara gaisheta cikin girmawawa.
maganan kawo kayan lefe tay mata lkcin layla na gefenta tanajin yadda ake ma haseena lisafe lisafe abunda zata tanada
bayan haka kawai sai tasako maganan zubda cikin nur, cikin sassauto da murya mrs Haseena tace ranki shi dade likita ne yace mudan dakata cikin yay kwari sai acire in ba haka yarinyana zata iya rasa ranta. wani irin tsawa Hajy mairam ta daka mata tace kika ce mene? tun hseena bata gama budan baki ba..
hajya tafara masifa ke hasina ba haka mukay dake ba karki sake ki rainamin hankli wato dankinga an daura auren dana da yarki shine zaki maidani abun wasarki ko..to wallh bakaramin aikina bane insaka adnan ya maida yarki bazaura yau din nan.
atake mrs haseena tafara bata haquri
..cikin masifa da balbalin balai tace ni bandamu da wani case dinku da likita ba just find a way and abort it kafin ya zame mana cikas a hidimar bikin nan..haseena was shocked data ga kamar kawai de hajy mairam bata damu da nur tay rai ko kar tay ba. ahaka har suka katse wayar bata sake cewa komi ba sai toh
ganin ta sauke nannauyar ajiyan zuciya cikin matsanancin damuwa yasaka layla ta matso kusa da ita tafara bata baki da dadadan kalamai masu kwantar da hankali
ahaka ahaka ta shigo da maganan nur, tace mummy kinata neman kudi yaa nur fa tana da Dollars dayawa ajakrta wallh tun ranar nagani ta boyesu da wasu perfumes da wasu set na kaya masu tsada kuma king ai na roketa taki ta bani...gashi kinata shan wahalar neman kudi amma ya nur tana dasu taki tako taimaka mana hmmm
Baki bude haseena take kallon laylah da mamakin jin wann maganan layla kikace nur tanada ajiyayyun dollars? layla tace wallh tana dasu suna nan acikin box dinta da mukaje kd dashi in karyane kice mata ta kawo box din nan wajen aduba.
ahrgitse hasina ta mike zata je saiga kira ya shigo wayarta tana daukawa aka gaya mata cewa ai ga abunda ya same doc surayya harma ana zaton hala bazata yi rai ba tana sauke wayar sai kuma taga 6 miss call dinta bada jimawa ba, nan take mrs hasina taji ta mugun rudewa kawai saita rarumi jakarta ta kama hanya zasuje asibitin. sunfito kenan adede coridorn ta wajn kitchen suka hadu da noor firdaus ganin yadda suka fito yasata tambaye layla meke faruwa laylan ne tagaya mata ai dr surayya ne tay mmnan hatsari.
atake ta aje plate din itama ta bisu suka je asibitin koda suka ga yanayin Dr surayya rai a hannun Allah kusan kowannensu sai da jikinta yay mugun sanyi.
Kuka nur takeyi da tunanin hala itace silar dagawa matar nan hankali hartaje tasaka kanta a hatsari
aikuwa haseena tana fara tambaye tambaye aka gaggaya mata cewa ai test dr surry take running wa jinin nur firdaus, ta fita kenan da file din result din zataje gidansu shine aka kawota wai tay hatsari.
mrs hasina tasha mamakin jin hakan sai kuma ta jajanta sosai
agefe ta kira me lab ta dinga masa question akan test din shikuma bai boye mata yace ai tana reconfirming ne akan cikin nur firdaus amma dake ita daya tay abubuwnta shima besan outcome din ba gashi ance file din ma yabata a rububin hatsari. godiya kawai ta masa at around 3:0 pm suka bar asibitin
dukansu uku duk ta kullace abubuwa aranta game da nur
aikuwa isarsu gida kenan ko wani hutawa basuyi ba kawayenta sukazo sukaje mata masu kawo lefe na hanyar zuwa agurguje haseina tay wanka tun bata gama cancara adon bama sai ga mutane hilimi guda a motoci na alfarma sunzo, gabaki daya bata shirya ba gidan ma saida kawayenta sukazo suka dan saka mai turaren wuta suka kimtsa, babu komi face chops da drinks na alfarma da suka sisssiya, bayan haka duk abunda ala gindaya bata samu daman shiryashi ba
gashi manyan mata masu ajine suka rako kayan akwatunan lefen layla masu shegen tsada sunkai set 34 komi yaji dake harkan show off da pubclity ne komi da akeyi awajen ana daukawa for media sake. sai sum sum Mrs haseena take da abun kunya da suka isheta sabida komi anyishine na nuna iyawa da wani irin almubazarnci itakuma
harga Allah Capactyn ta bai kusa kai nan ba.
kyaun fuska da wayewar haseena shine kawai ya dan ceceta ayau dan duk yadda tay packaging
abun yakiyi sosai taji kunya awasu abubuwan musmm wajen maida tukuici dan milliyan goma akasa akasar akwati
few anties na adnan saida suka dinga ma haseena habaici masu ciwo acikin raha wann kawo akwatin layla bazata taba manta shi ba cos she actually feel insulted amma dai haka ta daure tana yake har aka gama aka watse bayan magrib.
kawayenta ne suka tayata tattara komi aka shiryasu a daki, wasu sun kasa haquri saida suka gaggya mata magana akan cewa dolene fa ta nemi kudin da zaty barazana wa mutanen na inba haka ba layla ta shiga uku da gori gashi dama auren hadi ne ba daukarta da daraja zasuyi ba.
magnganu dayawa suka taru sukama zuciyar haseena yawa gashi tana alhinin babban kawarta dr surayya dake asibiti rai a hannun Allah wanda duk tana alaqanta faruwar hakan ne da lefin nur firdaus aciki.
Daren yau gabaki daya dakyar Mrs haseena tay bacci, takaici da baqin ciki yabi ya cikata badan komi ba saidan abubuwan da suka faru worst ma shine nawajen karban lefe, sake sake ta dingayi aranta akan nur firdaus tasan dolene kawai gobe ta dau kwakwaran mataki dan gabaki daya takeji tagaji da ukubar da Nur firdaus take jawo mata a rayuwarta gabaki daya.
layla kuwa kusan kwana tay tana ta creating anynmous acct tana tura video na lefenta wa media pages kamarsu arewa blogs big big nigerian celebrity wedding an co, da captions kala kala #Aurensoyayya #LayAd20## lefen yar gata. laylanAdnan.
wani irin tsantsan farinciki takeji yadda ake yaba kyaunsu ana ta anticipating din event dinta a coment sections tana kallo just few bad comnts na wasu yan schl da suke cewa ta auri sauryin yayarta amma duk wnn be dameta ba. bata runtsa ba sai wajen karfe biyu na dare lkcin nur ta jima da yin baccinta acan gefe atakure.
washe gari sassafe Nur ta farka tay sallah haka ta dinga tashin laylan tanajinta amma taki motsawa harta dauki qur'aninta ta fita waje domin karatu.
nur tana ficewa da kamar minti biyar layla ta diro akan gadon ko sallan batay ba tasaka sleepers dinta ta wuce dakin mrs haseena kome suka kulla oho..
nur tana tsaka da karanta suratul yousuf
da muryanta me dadi sai ga nan layla tazo ta tsaya mata akai babu ko yar sallama bare gaisuwa tace
..."mummy tana kirarki tace kizo yanxu karki bata mata lokaci. nur tadago kai da mugun mamaki tanata kallon layla da already har juya tana tafiyarta abunta. karamin ajiyan zuciyane ya kufce mata batay kasa agwiwa ba ta rufe qur'anin gently ta kamo hanya cikin gida
ahnkli take tahowa dan tanajin jiri jiri ga wani dan banzan yunwa dataji ya fara damun cikinta duk de batajin dadin yanayinta.
tana shigowa ta same su a kofar dakinsu suna tsaye a wajen doguwar corridor da zakabi kaje kitchen mrs Haseena ta mugun harde ranta har tana girgiza kafa tana huci.
Nur tana zuwa ta rusuna kasa cikin ladabi tace ina kwana mummy...wani irin mugun kallo mrs hasina tamata a tsawace tace rike gaisuwarki babban munafuka muguwa
..nur wallh kin yi asara. ta inda take shiga batanan take fita ba, tace ma nur ai tsabar baqin ciki da kishin layla datakeyi yasaka ta tursasa Dr surayya akan aje asake mata gwajin ciki dan kawai ta wargaza auren layla da adnan ita kuma ace she is innocent
yau babu kalar zagin da hasina bata mata akan haka ba, she call Nur desparete evil and toxic, me kwadayin abun duniya tace wai nur batason cigaban yar uwarta layla sam sam.
Nur harta budi baki zata fara kare kanta
kenan sai ta tuna Mrs haseena bazata ma saurareta ba kawai sai tay shiru tana kuka ahankli.
kafin tagama hadiye zafin zagi da zargin da hasina take mata akan hatsarin Dr surayya kawai sai taji Haseena ta shigo da maganan karuwanci.
tafara cewa nur ai ta jima da sanin cewa suna zuwa yawon iskanci da adnan shiyasa suka kasa rabuwa da juna haryaje yana cusawa iyayensa baqin ciki akanta, ta kafa hujja da gulman da layla tagaya mata akan taji sunacewa zasuje su huta awani waje. snn tace ai agabanta ma wani me mota ranar yazo ya ajiyeta da asubah tafito a motar ko dankwali babushi akanta kuma agaban nebors yoo ina take zuwa inba yawon karuwancin dare ba?
tanata masifa kawai tasako maganan su abayarta data saka a Kd, dana kudin da nur take kashewa har dana komi ma, ta dinga zazzagawa nur firdaus din zagi yau din ta kirata da sunan karuwa awajen yafi sau akirga...tace ai fyaden da aka mata ma kamuwar Allah ne hakama cikin Allah ne ya tozarta dan mutane susan wacece ita.
duk dai nur batace mata uffan ba saida layla ta shiga dakin ta fara kwaso jakunan ta tana kawowa gaban mrs Haseena,..
ana budewa kuwa suka fara cicciro expensive gifts da hajy bilki da hjya saadatu suka bata
jeweries, da set na veil me takalmi da clutch dinsa akwali da turarruka masu tsada da qamshi na meduguri aikuwa sai ga tumin bunch bunch na Dollars har guda bakwai da wrapper na 1k me dauke da 200 thousand naira dan nur bata wani kashe kudinta duka ba.
ganin wayannan kayan yasaka hasina ta fasa ihu ta jawo nur tsakiya tafara kai mata duka kota ina tana gullin cikinta tana takata
wallhi baki isa ki kasheni ba saidai ke ki mutu munafuka kawai
algunguma kawai yau Allah ya toni asirinki.
saida tama nur dukan da bata taba mata ba, kafin nan ta kyaleta awajen suka kwashe dukka kudin da kayan sann suka wuce dashi dakin mrs Haseena suka barta akasa tana murkususu tanata kuka tanata kiran babanta cikinta ya fara murdawa jini ya fara bin kafarta sosai numfashinta harya zo ya dauke
saida layla ta fito sann taganta ahaka taje ta gaya ma mrs hasina tazo takira likita anan anguwansu aka kai nur wani private asibiti
anan ne aka mata gwaji likita yace ai shi bega wani ciki bama
Wani dadi mrs haseena taji da tunanin ai dukan data mata ne yasaka shegen cikin ya fita..
she was not even remoseful at all suka dawo gida nur batajin
karfin jikinta takwanta a daki ita dayanta maganganun mrs haseena na tozarci da muzantawa haka ya dinga dawo mata tay kuka bana kadan ba.
yaudai babu kalar tunanin da batay ba,
Mrs haseena tuni duniya ta zame mata sabuwa dan duk kudin na zasu isheta har ma su fiddata akunya inta juyasu zuwa naira, ga wann shegun jeweries da bridal veil da shoe da clutch komi ya zama musu deidei yau din nan sun samo abunda zai fiddasu a kunya saidai harynxu mrs hasina bata dena jin matsanancin mamakin inda nur ta samu wann uban kudin hartake ajesu a jakarta batare da saninta agidan ba..
Da yamma suka shirya tsaf suka bar gidan ita da layla, mrs hasina takai result ma hajy mairam dake nuna cewa cikin Nur firdaus din yama fita shikenan kuma komi ya dawo musu dede aka tsunduma hidimar biki, gobe zaa fara event za'ama laylan wankan lalle da turare na yan meduguri.
anata shiri basu dawo gidan ba sai wajajen 12pm na dare tazo ta samu nur firdaus tana tattara duka important files dinta tana saka su agefe, basuce ma juna komi ba sai can layla tafara cema nur ai yanxu kam cikin shegen dake jikinta ya zuba sai ta dena guilt tripping dinsu da emotional face ta saki jiki ayi hidimar biki dan kar ace sisternta batazo bikinta ba.
aidama itace tasha gaya mata cewa bazata rabu da ita ba komin rintsi inde hakane kawai gobe tabisu wajen sakun lallen.
laylah tanata zuba maganganu yadda kasan nur bata dakin haka tay banza da ita har tagaji tay shiru.
hanklin nur sosai ya dan dawo jikinta da taji cewa ai dukan da hasina tay mata tayta zubar jini jiya yasaka cikin ya zuba atleast now she can make a move dan tagama tunani taga babu amfanin zamanta da su inba de kashe kanta takeso tayi da baqin ciki agidan ba.
washe gari da asubahi
ta dauki wani jakarta na baya, acikin wanda Adnan ya taba kawo mata dayajeshi dubai siyayyar sport wears na shi. gucci schl bag ce me kyau amma tana da dan xurfi da girma. tana kammala karatun qur'ani ta kwashe muhmmn files dinta na schl da komi data ware tunjiya da dare ta shiryasu acikin jakar da duka inne wears dinta da farin rigar javeed.
snn ta hada duk wani abu da babanta ya siya mata sai few abaya datasan kudin mrs haseena bai shiga ciki ba ta saka aciki basufi kala biyar ba,sauran duk wanda tasan idon laylah nakai tabarsu a wadrob din da dukkan wani abu data mallaka nakayan duniya da layla take saka mata ido akai tana kishinta, harma da wanda mrs hasina ta siya musu duk bata daga ko daya ba. acikin manyn hadadun hijabanta ma befi kaloli biyu kawai tadauka ba sai wanda ta'aje akan gado zata saka ajikinta.
karfe takwas ta fita basu san inda ta nufa ba, da kafa taje cikin wani 24/7 jeweries store a anguwarsu
takai tallan wani abun wuya da dan kunne na gwal da ta siya da kudinta da aka bata kyauta awani gasar makaranta..
kudinsa ya kama 400k a lalace, bata damu ba ta karbi kudi ta saka a hijabinta ta boye snn ta siya abinci da pain relievers around 9:30am tadawo gidan saida ta tabbata suna can dakin snn ta boye kudin acikin kaya tay wanka taci abincin snn tasha magani ta shirya kanta tsaf...
can ta ta fito daga ita sai jakar bayanta sai handbag dinta, kai tsaye taje dakin Mrs Haseena wanda ko sallamarta bata amsa ba,itama hakanan taqi ta gaisheta tace musu wayarta tazo abata.
nan Haseena ta mike tsaye da mamaki tace wa nur ina zataje da jaka? tafara kkrin zata kwace jakar tava meye aciki, nur ta ture hannunta da karfi
cikin tsaurin ido ta fara mata magana da wani irin busashen ido
tace karsu taba mata jakarta ita bata dauke komi nasu ba suje daki gasucan kayan duniyar datay yawon karuwanci ta samesu tabar musu su siyar suyi hidiman biki in hakan zai saisaita musu zuciya.
then she begin to tell mrs hasina everything na yadda ta samu kudaden da kayan datake zaginta akai, yau nur taki ta rufawa layla asiri, duk wani abunda ya wakana wanda Mrs haseena bata sani ba nur ta fayyace mata tace mata kuma bata damu da ko ta yadda da ita ko bata yadda da ita ba, itade kawai wayarta tazo karba zataje kaduna dan bazata iya zama da uwar da take nuna mata tsana a fili snn take tozarta ta ba.
baki bude kuma akangare mrs hasina ta dinga kallon nur ganin yadda yau ta tsaya agabanta take gaya mata magana masu zafi with no filter or ounce of respect, nur ta bushe idon ta gaggaya ma mrs hasina kalaman da inaji harta mutu wasu kalaman bazata iya mancewa dasu ba.
..sann ta dada jaddda ma mrs hasina cewa tabbas mijinta saadat shine ya aikata musu hakan kota ki, kota so wata rana zata gani.
layla duk ta rude da hayaniyarsun tana ta kuka tana karyata nur amma ko ajikinta.
kusan cacar baki sukeyi da mrs hasina
akan karda nur taje kaduna inma barinsu take so tay taje yola kawai wajen didi amma nur ta tubure tace inda taga dama zataje kuma wallh ba'a isa ahanata ba.
ganin baza'a bata wayarta bama yasa ta wuce afusace ta fara wargaza kayan mrs hasina tana watsi dasu a tsakar dakin kamar ba nur din ba har saida ta tsamo wayarta acikin wani drawar tadauki abunta batay wata wata ba ta kama hanya zata tafi
har waje Suka biyota mrs haseena tanata masifa kamar zata daga gidan...
wallh nur inkika fita agidan nan karki sake ki sake dawowa dan bazan karbeki ba...
dama can baki da kunya gashi yau halinki na boye ya fito fili, butula, duk abunda nake miki da rashin kunya saki sakamin? har nine kike cewa zakije kaduna konaki konaso to dan ubanki kije su kasheki kamar yadda suka kashe ubanki...inhar kika tafi nide wllh karki sake dawomin..
nur firdaus bata ko juyo ta kallesu ba
kuma ko hawaye bata sauke ba itakanta tasha mamakin kalar bacin ranta tun jiya kawai tasa aranta mrs hasina ta mugun tsanarta hakan bazai taba canzawa ba inta cigaba da zama da ita wata rana hala zata kasheta gara kawai ta tafi inda zata rayu.
har bakin gate layla tabiyo nur tana ririketa tana kuka tafara rokonta wai karta tafi kaduna shikenan yanxu bazata tsaya taga aurenta ba.
a fusace nur ta fincike hannunta a tsawace tace wani auren naki da kullum sai kince min ina miki baqin ciki akai layla? tou ai nice kika dauka a matsayn babbar maqiyanki kuma be kamata na kasance aranakun farincikinki ba dan haka kiyi aurenki lafya
kayan duniya kuma gasu can nabar maki
a daki, all the shoes jeweries harma da abayan dana saka a kd..take them. let them give u the happiness and love dat i cudnt give you.
tana gama blasting din layla ta fita abunta
mrs haseena ta dinga ihu tana masifa tana kwala mata kira kamar kanta zai tsage yau bakaramin mamaki nur firdaus ta bata ba dan bata taba tsammanin haqurin yarinyar nan zai kare hartay behving haka ba.
nur kuwa har saida tay nisa takai bakin titi sann ta fashe da wani irin kuka me radadi dan abunda tay kusan abune me matukar wuya ita bata iya raini da rashin kunya ma babba sai yau gashi tay ma mahaifyarta
sann ta raba kanta dasu fatan ta shine kar Allah ya kamata da lefi, saidai kuma in ta tuna cewa Allah ya baka cikaken dama raba kanka ko nisanta kanka da mutanen da suke cutar dakai sai taji wani sanyi.
ta tari mota kenan ta kunna wayarta wanda har hooking yake yi tsabar sakonnin da suka shishigo da sauri ta dudduba da bataga wanda yay kama dana javeed ba sai kawai ta maida wayar jakarta ta aje. basu ko yi nisa ba taji tafara bleeding jini na shirin wanke mata kafa duk sai taji tamugun tsorata haka tafasa tafiyar taje ta kama wani motel 20k per night ta zauna anan ta hada ruwan zafi ta shiga ciki ta wanke kanta snn tasha maganinta da tazo dasu, Rigar javeed datazo dashi ajaka shine mata kadai marar nauyi haka tacire tasaka ajikinta tasaka pad ta dan kwanta tay bacci me dan nauyi sai yamma ta farka taga jinin be dauke duka ba tasake wanka snn ta fita ta siya abinci tazo dakin ta zauna taci
ata daya bangaren kuwa tunjiya mutanen sanata farida suka samu rigar sadaat daya gama wankuwa sa jininsa ya turmushe sa datti ya bushe da kyar ma suka gane nashi ne, tun anan ka tabbatar mata cewa da wuyane in sadaat yana raye babu tantama tunda an samu rigarsa ajeji to hala har anjima da kashe sa. bakaramin baqin ciki da haukan gaske sanata farida tay ba, ji tay kamar asarar datayn ya mata yawa, ita bata ci kujera ba, bata samu ta tozarsa haseena yadda ranta ke so ba gashi kuma ta rasa shakikin yaron gidanta sadaat. zafin hakan yasa kawai ta bawa ussy oder akan duk inda akaga yaran mrs hasina abisu a akashe su karma abarsu su raye..
yau da safe ussy ya fito farautarsa saidai bai samu damar samun mrs hasina da layla ba dan tunda Nur firdaus ta rabu da su suka gama jimamin su na lkci kalilan snn suka share kashinta suka tsunduma hidimar biki dan mr haseena ta hau dokin zuciya tace sam bazata sake bata lkcinta akan ryuwar nur firdaus ba tunda tazabi taje wajen dangin ubanta in sha Allah bazata taba nemanta ba harsei tazo ta nemi gafaratta a abuja.
abun nadan sosa mata rai amma ta danne dan yau akwai kudi da abubuwan duniya a hannunta sai kawai ta tsunduma wajen harkan karya da nuna ma dangin Adnan cewa itama watace dan ta goge abun kunyar datay awajen karban kayan lefe da akaga tanata barin kudi akan layla duk sai anata mamakinta.
ussy yasan be isa yaje ta wajen hidiman ba sabida security dan haka yazo kofar gidan ya tsaya daga nesa ya samu dede maman saeid ta fito zataje gidan mama hauwa
samunta yay da magana yana son ya san ko nur firdaus haryau tana kumshe a gida koma ta mutu.
maman sa'iid tace masa ai yau din nan da safe taji suna hayaniya nur firdaus
ma ta wuce kaduna
wajen dangin ubanta
har maganan da be tanbayeta haka ta dinga zuba masa
yaji dadi sosai data masa wann barbadan harya dau dubu talatin ya bata kyauta sann ya tafi
tun ahnya ya gayama sanata farida cewa ai nur bata tare dasu mrs haseena awajen biki dan haka itace first target, nan danan kuwa tay amfani da mutanenta aka fara neman nur basu samu excat location dinta ba sai can da yamma ana daf da magrib nan da nan kuwa yazo shi gate djn motel din ya tsaya yana jiran dare ya dadayi da wata silencer ajikin bindigarsa yadda zai harbeta ta mutu basai anji karar bindinga ba.
ita kuwa nur tun bayan dataci abincin yamma takara shan magani tay wankan ruwan zafi takunna Data a wayarta tanata kallon hidimar bikin layla sai hawaye dake zuba a idonta, ga wajen ya dau shiru har wani tsoro tsoro takeji na shiga jikinta not knwing dat tun data bar gidansu she is being surounded by spys na javeed mufasa dan suna ganin signal din trackerta ya dawo suka hau aikinsu na bibiyarta duk inda tay motsi batare da saninta ba.
wajajen 10pm bacci ya fara damunta ta aje wayar ta saka karatun qur'ani tayi shiru tanaji dede wann lkcin ussy ya fito cikin sanda baiko lura da spy suna binsa ba
dake sun kware atake suka gane cewa akwai bindiga ajikin sa daya acikinsu ya kira javeed
ya sanar masa cewa sunga wani guy dat looks suspicious a motel din har sun dau hotonsa sunyi bincike sunga cewa stray dog din politcal rival dinsu mahaifiyar nur firdaus ne.
atake javeed yace musu inhar wajen nur ya dosa karsu bata lokci kawai su harbeshi.
aikuwa kamar antunxira su hanklin ussy akwance ya shiga ta baya zaije dakin nur ya kasheta
baiko hankara da takun gayun abyansa ba yana miko hannu zai saka master key yabude kofarta yaji saukar wata shegiyar military riffle akansa
koda ya juya ya kalle gandama gandaman gayu masu damatsu ajiki saida yaji cikinsa yay kuuuu dan kamar zaitsaki fitsari ajikinsa haka ya tsomare jikinshi yana rawan dari zai magana dayan gayen yace masa "shushhh..kakr sake ka jawo hanklin madam lets go to your car ryt now.
dama gashi awajen duhu duhu ya aje motar tasan, suna kaiwa wajen dayan gayen ya wani buga ma ussy gindin bindigarsa aciki sai dayay aman jini atake
suka matseshi suka fara tambayrsa meyake nema da yarinyar bakinsa na bari yace shima besanta ba cewa kawai akayi yazo ya kasheta by her mums political rival...yafara rokonsa akan su masa rai karsu kashe shi. aikuwa da bindigarsa daya saka silencer suka karba sai dau dayan gayen yaharba masa shi akansa, suka dauke gawansa cak suka bude booth dinsa suka sakashi aciki
nan ya kira javeed ya gaya masa, javeed yace su rubuta sako su hada da gawar akai ma sanata farida let her know dat in ta sake turowa akashe yarinyar nan she will be the next person to die and he wont mind wasting her entire generation wnn gargadine ya mata danma wai ita mace ce.
aikuwa yadda ya fadi haka suka aikata sanata farida tana zaune a daki da dare aka kirata da wayar ussy akace tazo ta amsho sako akofar gidanta...tana fitowa ta samu motar ussy a bude amma babu kowa aciki ta mugun tsorota tayta dube dube har takai both a mugun kangare ta koma baya dataga gawan ussy da takardan gargdi ajikinsa a mugun tsorace ta dauka ta karanta..
tsabar ta tsorata acikin daren ta tattara inata inata tabar nigeria saida taga ta tsira snn ta turo sako acikin yaranta suka dauki gawan ussy akaje aka toni rami aka binneshi..
Duk wann hidimar da akayi nur firdaus bata san anayi ba, bayan data gama jin karatun qur'aninta she slept peacefully hartay mafarki babanta yazo mata sun zauna suna tahira har tana famar kyalkyala dariya.
hakan yasa washe gari koda ta farka taji zuciyarta yay fayauu batajin wnn damuwa da baqin cikin dake kumshe a ranta.
koda tay wanka sai taga jinin kamar ya dauke duk da haka dai ta saka pad abunta ta dawo dakin ta shirya tsaf snn ta dauki wani baqin abaya plain acikin jakarta ta saka
tanata tunanin ko zata kira kawunta ne ta sanar dashi zuwanta amma kuma tana tsoron karyace mata a'a sabida case dinsu na kotu dan takulla aranta cewa inhar be karbeta ba, da ta dawo gidan mrs Haseena gara ta kira lambar hajiya mammy snn taje gidanta ta roketa akan kome aikin shara da wanke wanke a dauketa xata mata har sai ta cika 18yrs din.
haka dai ta qudura aranta kafin ta fito taje ta siya abincin kryawa
ta zauna taci bayan nan tadan kwanta akan gadon kadan sabida ciwo dataji cikinta yafara mata
ata daya bangaren kuwa Alhaj abubakr yana kwance akan makaken italian bed dinsa har sun gama waya da Agent din Sultan kenan cewa yau da karfe 2 bayan azhar jirgin helicopter zaizo ya dauke Razia izuwa mufasa's private yatch in lagos
komi da suke bukata an tanadar musu tun jiya da dare yay ma yarsa Razia nasiha akan kartaje ta bashi kunya agaban mutane inde tana daraja shi
ya aje wayarsa kenan sai ga wata baquwr lamba na kiransa da can kamarma bazai dauka ba amma sabida yanayin yau din kawai saiya dauka
bakaramin shock ya shiga ba daya ji muryan Didi wato mahaifyar mrs haseena, acikin mutuntawa suka gaisa dan sun balain jimawa basu ga juna ba. hanklin didi ne be kwanta akan nur firdaus ba, sai tana ganin kamar inda aka bar nur agidan ita kadai taredasu mrs haseena hala zasu kasheta da baqinciki
tunjiya ta nemi lambarsa kawai ta yanke hukunci gara ta gaya masa meke faruwa dan yazo ya dauki yar dan uwansa kafin hasina da yarta layla su kasheta.
alhj abbkar yana tambayarta ko lafiya
kawai Didi ta fashe masa da kuka..
jin haka yasaka call din a recoding dan dama yana neman duk wata evidence akan mrs haseena ai kuwa Didi ta fara zuba masa labarin halin da ake ciki bata boye masa ko da full stop ba, tafara rokonsa akan yayi haquri yazo kawai ya dauke nur ya tafi da ita dan itakam tanaji ajikinta cewa nur bazata iya zama agidan can akarkashin haseena ba. tsaban kuka da rokon da didi tay masa har saida jikinsa yay sanyi ya dinga bata haquri yana lallashinta yace mata in sha Allah yau ko aiki bazaije ba zaije ya samu lawyer su tattauna zuwa yamma ko anbashi dama ko ba a bashi zaije ya dauko nur ya dawo da ita hannunsa. godiya ta dinga masa sede suna gama wayar ya fashe da kuka muryan sa harna fita waje jin tsananin baqin ciki da tashin hankalin daya rufesa dayaji wai barayi sunshiga gidan hasina sunma nur firdaus fyade hartay cikin shege kuma ana zrgin wai wawan mijin hasenan ne ma...
salati ya dingayi yana kuka a dakin kamar karamin yaro yana maganganu yana cewa dan uwansa ya yafe mishi...jin ciwon zuciyarsa na kkrin tashi yay sauri ya jawo maganimsa ya sha harya dan samu yay bacci kadan.
matansa sunzo dakin suka samesa ahaka amma gabaki daya ba sugane masa ba, dan Alhaj baiya bacci da safe, duk dai basusan baqin ciki da damuwa bane kawai yasakashi shuting down din kansa for a while..
koda ya farka wajajen karfe goma baiwani kulasu ba kawai ya shirya kansa yawuce offishin lawyernsa kai tsaye sukuma matan suka tsaya akan raxia domin a shirya ta duk sunyi tunanin ko hala sune suke bata masa rai akan maganan su na mufasa duk sai suka damu dake sun san yana da ciwon zuciya.
wann yanayin yasa razia ta haqura ta saki jikinta tay shirinta me kyau danma ta faranta ma babanta rai yau din professionals ta kira suka shiryata tsaf wani kankararen steve meden flowing gown me stones da furrs suka kawata jikinta dashi takalminta da jakarta kuma duka na alexander MC queen
gashi de english wears ne amma babu wani waje ajikinta dake bude face fuska da hannu da kafarta satin scarf me tsada aka mata mata rolling shi bakaramin kyau tay so simple ba.
saidai har 1pm yay babantan be dawo gidan ba kuma basu samesa a awaya ba bare suji daga garesa cikinsu kowa ya damu sosai, 1:30pm on d dot sai ga agents din sultan aka zo aka dauke razia suka wuce da ita lagos a helicopter na mufasa.
bangaren nur kuwa tunda cikin ta ya fara ciwo sai tay bacci bata tashi farkawa ba sai can wajen karfe uku saura na yamma sai kuma taji kanta garau batajin wani ciwo ko motsin zuban jini.
aiko wanka bata sakeyi ba agurguje ta gyara fuskarta daya dan nuna alaman kumburin bacci ta wanke bakinta ta tattara inata inata ta fito ta kama hanyar tashan da xai kaita Kaduna
duk a tsorace take yadda taga mutane suna juyowa suna kallonta, harta dauka ko wani abune face sai da taji wani dan karamin yaro da bazai wuce 6 yrs ba yanata ihu yana ce mata mamansa ga wata kyakkawar anty acan me kama da aishwariya rai...
Nur ta sunkuyar dakai dan tsabar damuwa harta fara manta wai tana dama kyau irin haka, sauri sauri tay ta isa tashar ta samu motar karshe ne ma kuma baifi saura mutum biyu ya cika ba.
kawai frm no where taga wani mutum yazo ya biya musu kudin motar, shima ya zauna agefenta wai zaijeshi kaduna.
tunda ta gode masa taga ya dauke kai akanta yanata latsa wayarsa, sai taji hanklinta bai kwanta ba dan gabaki daya dama tajima tanajin kamar ana bibiyarta tun yau da safe da ta fito siyan abinci..
amma dake akwai mutane a motar kawai sai tay relax mutumin ma taga ko kulata bai sakeyi ba he was just pressing his phone non stop.
2:00 on d dot razia ta isa lagos, tun anan take ganin formalities kala kala irin wanda sai a film kadai take gani dan suna sauka wasu dalla dallan kyakwan yan mata ne su uku da well toilered torquise blue colour uniform dinsu gasu nan kamar ethiopians sunsha light make up sunyi tsaf sukazo suka amsheta da fara'a dan ko jakarta da wayarta ba abari ta rike da kanta ba.
she was lead to walk like a queen kowa na biye da ita ana mata duk wani formality daya dace, kai tun anan ta fara jin taraina kanta gabaki daya dataga yadda wasu abubuwan a duniyar mufasas yake like a fairy tale ko a kasar waje bataga irin wnn extra ultra luxury life din ba.
she was looking foward to meet javeed in his yatch waiting for her, sai taga an kaita wani filin da ake buga wasa daga javeed din sai wani mutum sunsaka fararen high ends polo shirts da p.caps idonsa toshe da shade suna buga wasar golf a fili.
wani tsayuwar cak tay tazuba musu ido jin hanjin cikinta yana dan rawa rawa dataga kalar haduwar javeed mufasa din, sai yanxu ta dada tabbatar makanta yes sunan mufasan yakai ajishi akoina dan komi awajen abun kallo ne
after like five minutes da tsayuwarta aka kaita wani shade ta zauna duk yadda taso takama ajinta kamar yadda ta kwarance amma ta kasa sai satar kallonsa takeyi
gani tay yanata buga golf dinsa cikin kwarewa da nishadi kamar baisan tazo ba
masu aiki ne ke zagaye da ita suna serving inta varieties of drinks harda wanda bata taba gani ba duk wayewartan nan.
taci minti talatin tana zaune kafin nan ya gama wasar ya wuce ciki ya watsa ruwa ya shirya acikin wata simple casual fari kal din shirt na steffano richie da beige sweat pant dinsa me laushi rigar bata da nauyi dan hatta butoranta ba dukane arufe ba amma yay tucking so he look very simple and smart sai wani irin shegen qamshi turarensa na mufasa noir dake bibiyarsa
dakansa yazo shade din yay inviting dinta izuwa private yatch dinsa dake kan tekun dake zagaye da wajen.
nan din ba asalin gidansu bane, gidan hutawarsa ne. yadda razia ta kurewa nur kallon kurilla shima haka ta dinga kure masa kallo saidai tanayi tana kama aji sabida idanun securty dake kanta.
suna zuwa cikin yatch din taga an setting musu table da varietie na abinci, tana zama aka fara serving inta da duk abunda ke gabanta batace uffan ba sabida ta dan rude
dataga ba a wani yi wani romantic decoration special sabida zuwanta ba
gashi ta jima tana shige shige takuma kwarewa wajen sanin rayuwar masu kudi amma bata ga irin sanyin aji da kyau da kuma kwarjini dake yawo ajinin javeed mufasa din nan ba.
tun da suka zauna banda drink bata taba komi ba, she actually tot intazo zai mata maganan ta auresa ko wani abu na kasaita da gadara cos he is so damn cute and super wealthy tasan dole ne irinsu suna da izza gadara da mulki.
sai kuma taga kamar he is truly just a gentle men duk kamewar datake tana batsewa baisan ma tanayi ba.
saida yaci abinci kadan snn suka fara magana akan zuwan sultan wajen babanta,
duk Ya lura ta matsu taji asalin menene yake so awajenta besides auren dole
amma dataga kamar ba fadan zaiyi akan lokaci ba sai kawai ta fara fada mishi nata ra'ayin cos she is a very smart modern and confident lady.
kamar yadda ta tsara tahau gaya masa komi na cewa she had her own life and ambition and she want to chase it kuma iyayenta mata ma they want dat for her not marriage, saidai in zai bari tazama yar film da fashion agidan su toh she wll go and think about it...
saida ta gama bayani javeed yace mata shi ba abunda yasa ya kirata ba kenan, alho marriage is also part of his plan,amma sai baice mata ita xai aura ko ba ita ba dei a murmude yay mata maganan dan tasan she might be d one he will marry by proxy if she fail him.
suna cikin maganan taga ya daga hannu sai ga wani mutum yazo da files guda biyu sai ya karba file din ya mika mata ta bude taga komi nata ne aciki including all her qualifications and all her personality profiles.
the way she think, talk, walk, eat, sleep, her life choices in every aspect, her friends, her secrets yadda take numfashi ne kawai babu aciki.
kawai saitaji ta mugun tsorata dashi..dayaga tay shiru yay smirking yace mata he want to offer her a job.
da mamaki tace mishi wani irin aiki kenan? saida ya dan ja kafin nan yace he want to use her service to take care of his Twin flame...
"...tace service? twin flame..sir i dont understand you.
hankalinsa kwance yace i went tru ur personality profile nd u have wat it takes to take care of a little girl
...you a smart girl zaki gane menake nufi.
raxia tay rau da ido da mamaki tace "you mean u want me to stalk a girl for you??
babu ko shakka yace yah, like a quardian angel just teach her wat you knw abt personality and you can name any price..
mamaki yasata kara relaxing bayanta akan chair wani tattausar murmushi me aji ya kufce mata, dan shiru tay snn tace "and in return i get wat??
saida ya mata irin kallo snn ya dauke kai yace... 'money...any amount of money. and your Freedom..of course.
cikin bude ido da lumshewa tace i wll take freedom..u can keep ur damn money
dan karamin dakkyr murmushi yay yace
"As expected! ya dau drink dinsa ya kurba ahnkli snn yace so,
"we have a deal?
ahnkl tace yes, kay alkwari zan samu cikar burina. so, what abt the weding?
batare da ya kalleta ba yace "let me worry abt that". inna gamsu da aikinki..ur dreams nd ur fredoom is urs.
tace okay, "what if i dint?? will you forcely marry me.
ahnkli ya daga ido ya kalleta yace yes.... "forcefully.
kwarjini tare nauyin dake ciki kwayar idanunsa yasata dauke nata idon ta kawar gefe cikin sauke ajiyan zuciya tace okay fine i need ur girls picture
yace "sure.
kirjinta har bugawa yake tanata jira taga ya bata hoton sai taga kuma ya basar da ita.
for almost 30 min yana latsa wayarsa
har ta gaji tafara taba abincin dake gabanta kadan kadan sabida qamshin turarensa ya kama dagula mata lissafi har wani jika taji tanayi taciki...
she just ate little oysters to take her mind off him sabida gayen kure haduwa ne babu karya yaune rana na farko data raina ajinta da kanta agaban wani namiji.
saida tagama cin abincin snn taga ya kalle time its almost 4:30pm,zaije sallahn asr kuma yay latti nan yace ma mr aqeel su kira agent a maida razia gida.
sai har da tamiqe zata tafi snn ya dau zanen hoton ya bata, koda ya bude taga nur ne twin flame din nasa saida tay kamar 12 minutes cikin shock kafinnan ta kalleshi baki bude
zatay magana cikin datsar numfashinta yace 'just do the job"
kasa magana tay tana kallonsa kawai sai ta gyada masa kai cos she really want her freedom duk dama batayo dandanin tsammanin cewa abunda zatazo ta tarar bakenan and the worst part ma wai cousin sisternta nur firdaus ohh damn.
tun anan javeed ya barta bata sake ganin me kama dashi ba kuma, its like he doesnt really send her, irin de mace tasan ta kure haduwa amma namiji yay kamar bema ga wani abu special ajikin tan nan ba haka taji yau a yar meeting dinsun nan dashi.
wasu yan mata na daban masu kirki sune suka zo rakata wajen jirgi, suna biye da ita da jakanta da wayarta
duk dama taki karban komi nashi me sunan kudi amma ba shi ya hana aka kai bita da goma na arxiki gida ba.
kanta gabaki daya ya daure ta rasa me zata fassara javeed dashi, gashi baiy kama da wanda zaka cikasa da surutu ba bare ta tambayasa, kai tun ajirgin ta dinga tunani shin a wani duniya ne yasan yar uwarta nur firdaus har ta dawo twin flame dinsa. dat means he is neva going to live witout her in his life cos a twin flame is a twin soul. kenan koda ya aure wata mace na daban he wll still be with nur firdaus for life weda as a wife or not, abundai ya dada mugun daure ma raxia kai bana wasa ba.
so he called her all the way to offer her a job to be a qurdian slave to his twinflame? its feel kind of insulting to her amma inta tuna
cewa he promise her dreams and freedom
sai taji koma miyene zata iya dan shine last hope inta yanxu..
takardan zanen daya bata ta daga taga cewa he even wants her to do everyrhing in privacy that means nur doent need to knw about all this, sede tasan shikm zai iya sanin komi da suke ciki dan yanxu bakaramin kure mata tunani taji yay ba da yanuna mata yadda suke da record na yadda take aikata komi a rayuwarta
this means he is damn dangerous and well connected, toh dolene tay kominta ahankli karyaje ya lalata mata rayuwa.
tasan dai javeed baice mata zai aure nur firdaus direct ba itama baice mata ko bazai aureta ba, amma dai ta fahimce shi sosai is like he needed nur firdaus for sumting emotionally intense wanda batasan meye bane.
she just feel like is better she shud do her own part of the deal if not tasan dolene da akwai mummanan abunda zai iya biyowa baya inta saba masa.
tunani da lissafe lissafe sunkai hamsin wanda ta juyasu aranta can dai ta sauke nannauyar ajiyan zuciya tay shiru taga ma ashe saura just few minutes ne su iso kaduna.
wajajen karfe biyar da rabi raxia abu ta samu isowa gidansu sede da mamaki tazo ta tarar da nur firdaus zaune a falonsu atsakiyar iyayenta harda baban ta da suketa nemansa dazu,
taga kowa acikinsu yay jigum akanta anata bata hakuri tanata kuka tana gaya musu abunda ya faru da ita acan abuja..
spy din javeed daya bita a mota har gidan ya rakota batare da ta sani ba, tazo ta samu dede kawunta ya gama ma matayensa bayanin cewa kotu ta bashi oder zaije ya dauko nur firdaus sai kawai ga nur din ta shigo musu da jakar kayanta ahannu
nur tazo daf ana musu zuwa daukota alhaji yana ganinta jikinsa ya fara bari yaje ya rungumeta yafara kuka dan sosai abunda akace an matan ya taba masa zuciya shikadai yasan ma meyakeji dan ya jima a kotu yana tada bori akan cewa lallai kawai sai anje an kama masa haseena an kulleta sabida awajen sa ganganci ne yasata tabar su nur agida har aka lalata mata rayuwa.
abunda yajawo ya jima kenan a kotu dan dakyar aka lallashe shi aka basa grant din daukotan kawai sabida yanxu mrs hasina tana tare da hajya mairam kuma sune da mulki gashi sunhada zuria in akabi na tayar da hatsaniya fadar tsakaninsu baxai taba karewa ba.
koda alhaj ya fara kuka yace ma nur ai yaji labarin komi yanxu ma wajenta zasuje she felt really vulneralable sai kawai taxauna tahau bashi labari, anan sukaji cewa mrs Haseena ta mata dukan tsiya cikin ma ya zuba.
Razzy tashigo lokcin ana kan rarrashin nur iyayenta matan kusan kowa acikinsu na kuka ana bawa nur haquri,
razia taji kamar mafarki takeyi da sauri tazo ta rungume nur firdaus din tana mata wani irin extra friendly face har saida kowa yasha mamakin yadda razia abu tay murnan ganin nur..
batamasan meyafaru suke kuka ba itama ta jonasu ta dinga bawa nur din haquri har tay shiru aikuwa nan da nan tattara jakar nur ta wuce da ita sama
tasaka maid ta hada mata ruwan wanka me shegen qamshi da dumi bayan nur taci abinci sukadan samu bacci.
washe gari sassafe lokcin nur din bata farka ba raxia taje gaishe da dad inta anan ne ta sameshi da mummys inta suna hirar abun harya saka musu recording din wayarsu da Didi suka ji.
bakaramin sanyi jikin razia yayi ba sai kawai taji asalin tausayin nur din ya kama mata zuciyatta bana wasa ba har kuka tay dataji wai any raping inta an mata ciki kuma kanwarta layla ta aure saurayinta all at same time abun sai ya dameta sosai, tafaraji aranta toh kenan ba zallan aikin javeed zatay ba, nur yar uwarta ce kuma yarinya karama duk wani me imani ai dolene yay wani abu na musamman da zai cireta dan uwansa a damuwa...tanaji iyayen suna alkwari tsakninsu cewa har nur ta tsufa inde suna raye daga yau sune zasu zame mata uwa da uba da duk wani gata tunda dai mrs haseena ta muzanta ta.
share hawayenta tay jikinta a sanyaye ta fita ta barsu awajen ta koma dakinta inda ta same nur ta takure kanta waje guda tana bacci..
koda ta zubawa nur din idanu wani sabon kuka taji yazo mata tun daga cikin kokon ranta tana imagining in itace akamata wann abun ta tuni ta hadiye ranta ta mutu...
tahowa take jikin gadon tana kallon innocent fuskar nur firdaus tana sobbing profusely feeling so so sorry for her..
agefenta tazauna daf tana ta kallon fuskarta sai tay murmushi cikin ranta tace oh god she is so young i wonder how she survive all dis pain.
saikuma ta lumshe idonta ahnkli tace."
nur namiki alkwari bazaki zama makullin cika burika na kadai ba...in sha Allah i will make you smile and so happy, untill you are heal...Nd i wll make sure of that little sis. ahnkli ta dan rangwafo snn ta daura mata sassnyar karamin kiss asaman goshinta kafin nan ta mike tana dan share hawayenta cikin sanyin jiki sai tafita cikin ayyana wasu tunani masu nauyi....
#Hmmmm Nikaina Danaga script din book2 saida Na shiga cikin shauki wayyooo soyayya😭❤️❤️❤️
#ALHAMDULLAHI...
ANAN NAKAWO KARSHEN NUR FIRDAUS KASHI NA FARKO. KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA.
KASHI NA BIYUNSA
NA KUDI NE.
zamu fara on FRIDAY NIGHT, KO SATURDAY morning babu tsaya wa harse an gama bizinallah .
IS ONLY AVAILABLE IN👇🏻
1- WHATSAP PAID GROUPs 500 naira
(single post per day)
2: VIP GROUP ON TELEGRAM ONLY
2k(multiple pages mon-satuday)
3: AREWA BOOKS @Surayyahms SPECIAL POST AT AFFORDABLE PRICE
DAN ALLAH KAR WATA TAXO TA TAMBAYENI COMPLETE COPY DINSA HAR SE NACE NA GAMASHI GABAKI DAYA IF NOT I WLL JUST IGNORE UR MESSAGE..
ZA'A BIYA ANAN👇🏻
9132352275 mohd surayya sule, opay
or 0152983148 mohd surayya sule GTB
👇🏻
EVIDENCE ***
DAN ALLAH DO NOT CALL ME JUST CHAT ME...
NAGODE SOSAI MASOYANA❤️❤️❤️