AMATURRAHAMAN

28

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 28

*بسم الله الر حمن الر حيم*

....…...Washe gari Zayyad ya wuce China da rakiyar Sojojinsa da suke a matsayin security a gare shi duk inda zai je suna biye da shi. Cikin maida hankali ya shiga gudanar da abinda ya kai shi cike da ƙwarewa ya samu ya kammala ya turo su gida shi kuma ya wuce Poland ba tare daya koma gida ba.

Kaya sun iso gida cikin aminci inda Muzaffar ya tsaya akan aikin sai da aka tsara komai yanda ya kamata kafin ya koma gida. Alhamdulillah Company ya kammala an kuma zuba dukkan wasu kayan aiki sannan an fara ɗaukar ma'aikata abinda ya rage kawai shine dawowar mai Companyn a gudanar da bikin buɗeshi a can Kanon kafin su fara aiki.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

A ɓangaren Doctor Farhan kuwa duk yanda yaso ya shawo kan Dady game da maganar aurensa da Amaturrahaman abin ya gagara domin kuwa Dady da Yaya Turai sun kafe akan bai fa isa ba. A tsakaninsa da Suhaima kuwa duk yanda yaso ya dai-daita abubuwa a tsakaninsu abin ya gagara domin kuwa bashi da cikakkiyar natsuwar da zai bata kulawar da take so daga gare shi, saboda hankalinsa yana kan Amaturrahaman da yanzu ko fitowa bata yi in yaje saboda dama Kawu Isa ne ke fito masa da ita, yanzu kuma shima ya sauya shawara ballagazar ƴarsa yake son ya manna masa saboda son zuciya.

Wannan dalilin shi ya ƙara lalata masa nutsuwarsa duk yabi ya zare tamkar ba Doctor Farhan ɗangayu da ƙwalisa ba, domin ba da wasa soyayyar ta kama shi ba. Har ta kai ko Asibitinsa ya daina zuwa kullum yana hanyar Matazu shi ɗinma baya iya tsinana komai bayan ƴanmatan dake binsa har can yana mua'amala dasu domin rage damuwa. Rikici sosai suka kwasa da Kawu Isa akan maganar Salaha da ta bala'in kamuwa da sonsa take jin in ba shiba bazata iya auren kowa ba, koda Kawu Isa ya ƙara tararsa da maganar shine fa yayi masa rashin mutuncin daya sa su kawu Isma'il da su Amaturrahaman dariya domin kuwa suna jin yanda abin ya kaya.

Haka suka rabu baran-baran Kawu Isma'il yana kwasar dariya saboda yanda Kawu Isa ya dinga ɗaga masa kai shi ga surukin mai kuɗi dole a riƙa girmama shi.

Koda Dady yaga abin na Doctor Farhan ba mai ƙarewa bane don duk ya lalace damuwa ta masa yawa ga rikici suna kwasa da Suhaima kullum akan maganar Amaturrahaman da bakinsa baya gajiya da kiran sunanta koda kuwa mua'amalar aure yake yi da ita. Haka take zuwa da kuka riris ta sanar da Mahaifiyarta ita kuma taje ta sanar da Dady.

Wannan dalilin yasa Dady yanke shawarar sama masa aiki a wani babban asibiti dake India ta hanyar wani amininsa dake can, dole yasa suka tattara suka wuce shida Suhaima da zataci gaba da karatu a can suka wuce ba tare da an barshi yaje Matazu kamar yanda yaso ba.

____________★

A ɓangaren Dugaz kuwa da Alhaji Tanimu ya Bama aiki akan Ya Nafi yana can yana bincike a kanta, sai da ya san komai a kanta sannan ya fara shirya plan ɗin yanda za'a yi ya kamata saboda yanda Alhaji ya matsa akan aikin yake kuma sakar masa kuɗi.

Gaddafi kuwa da hankalinsa yaƙi kwanciya da abinda Mahaifinsa ya shirya mata, gashi ta toshe duk wata ƙofar da zasu haɗu bare ya ankarar da ita ta kula, saboda tace ɓatawa kansa lokaci yake don ba zata bada M card ɗin ba ko me za'a yi kuwa, a firgice yake a cikin tashin hankali yake saboda ya san rashin imanin Dugaz, tunda Dady ya bashi wannan aikin to sai yaga ƙarshensa don haka kullum yake roƙon Dady akan ya janye aikin dayaba Dugaz a kanta shi zai amso masa kayansa.

Shiru kawai yake masa don ya gaji da jira ga Dugaz ɗinma shiru kuma bai taɓa jinkiri ba akan duk aikin daya bashi.

A ɓangaren Dugaz kuwa ya gama shiryawa tsaf ya fara bibiyaryar Ya Nafi ba tare data sani ba, so yake kawai ta shiga inda ba idon mutane yayi ram da ita. Sai dai har yanzu Bai samu wannan damar ba don kamar ta sani ta rage yawo sosai a kwanakin nan, ƙoƙarin haɗa duk wasu kuɗaɗenta take tana son buɗe babban account ne wanda zata zuba manyan kuɗin data samu wurin Alhaji Tanimu da shi Gaddafin kansa. So take ta zuba su a account ta aje wanda zata yi hidimar karatun Amaturrahaman don tana gab da kammala secondary har ma tayi Jamb, sauran kuma so take ta sayi kaddara ta aje saboda in lokacin auren Amah yayi tayi mata irin kayan da akewa ko wace ƴar gata. Domin kuwa ta san itace zatayi komai saboda basu da kowa itace Uwa da Ubannta harma da danginta, domin su kawu Isa ko tsinke ba zasu saya mata ba.

Duk wannan faɗi-tashin da takeyi ba don kowa take yiba sai domin ƙanwarta ƙwara ɗaya da iyayensu suka bar mata. Ta samu an buɗe mata account da sunan Amaturrahaman sannan ta saka kuɗaden da take buƙata ta damƙawa Amaturrahaman ɗin ATM da pin da komai tace ta ɓoye shi tayi mata bayanin dalilin buɗe shi ta kuma sanar da ita shawar data yanke game da sauran kuɗin.

Kuka Amaturrahaman ta fashe mata dashi lokacin data gama mata bayani tace "Ni bana buƙatarsu Yaya Nafi, ke shike nan bazaki duba taki rayuwar da yanda zaki gyarata ba sai ni kaɗai. Kin san yanda nake jin ɗacin in na ganki cikin irin wannan rayuwar Ya Nafi?, so nake ki tuba ki samu Miji kiyi aure na san zai faranta ran Umma koda bata raye, sannan kuma idan kika tashi aurar dani ɗin zanfi samun daraja in akaga Uwata a ƙarƙashin inuwar aure ba yawon bariki ba. Dan Allah Ya Nafi ki ajiye komai ki tsayar da Miji kiyi aure saboda bana jin daɗin yanda ake zagar min ke zan iya fasa bakin ko wanene idan yayi kuskuren zaginki a gabana." Ta ƙare maganar cikin tsananin raunin daya bayyana har saman fuskarta.

Rungumeta Ya Nafi tayi suka saki wani tsumammen kuka mai ciwo a tare, saida sukayi mai isarsu sannan Ya Nafi tayi ƙoƙarin danne nata ta share hawayenta sannan ta sharewa ƙanwarta hawayenta itama ta fara rarrashinta, da ƙyar ta samu tayi shiru sannan ta fara magana muryarta da alamun kukan da tayi tace "Nayi maki alƙawarin dainawa in sha Allah domin gyaran rayuwarki, saboda ba abinda ba zan iya sadaukarwa domin taki rayuwar tayi kyau ba. Duk abinda kikaga ina yi saboda ke nake yin sa, ina yin komai ne domin samun abinda zan tsaya na kula dake kamar yanda Umma ta bar min amana. Dalili na biyu kuma shine cika alƙawarin dana ɗauka akan Maza irinsu Gaddafi kuma ko yanzu Alhamdulillah domin na saka da yawansu a cikin tashin hankalin daya fi ƙarfinsu kuma ina kan hanyar gara duk wanda ya tunkaroni da irin buƙatarsu. Zan bisu ɗaya bayan ɗaya ina firgita rayuwarsu tamkar yanda na firgita ta Alhaji Tanimu da abokan harƙallarsa na hana musu bacci cikin kwanciyar hankali, ki kwantar da hankalinki ƙanwata nayi maki alƙawarin duk sanda na samu Mijin daya amince zai aureni a yanda nake zai kuma riƙe min ke to zan karɓesa da hannu bibbiyu na aure shi na kuma yi masa biyayya." Ta ƙare maganar tana dafa kafaɗar Amaturrahaman dake kuka riris.

"Zaki samu Miji Ya Nafi, in sha Allah zaki samu Mijin marainiya wanda zai ƙaunace ki a yanda kike ya kuma yi ƙoƙarin saita rayuwarki a hanyar data dace, abinda zamuyi kawai shine barin garin nan muje wani wuri inda ba wanda ya san tarihinmu mu gina sabuwar rayuwa mu tsaya da ƙafafunmu kafin lokacin da zan wai-wayo gida domin yin hukunci wa mutanen da suka zaluncemu." Amaturrahaman ta ƙare maganar da iyakar gaskiyarta.

"Zamu bar garin in sha Allah da zarar na gama aikin dana fara ke kuma kin gama jarabawarki."

"Wane irin aiki ne kika fara ban sani ba?."

"Zan sanar dake idan lokaci yayi." Daga haka suka bar maganar suka shiga tattauna wata da ban.

★ Washe gari Ya Nafi tayi shirin zuwa Katsina domin fara binciken inda Aunty Halima (ƙanwar Mahaifinsu Allah yasa kun tuna ta). Ba tare da sanin Amaturrahaman ba domin so take ta nemota idan tana nan ta miƙa Amah a hannunta kafin ta fuskanci faɗan dake tsakaninta da Alhaji Tanimu domin ta shirya miƙawa ƴan'sanda memory card ɗin nan domin tona asirin tsiyar da suke tabkawa ba tare da sanin kowa ba. Ta san zai iya yin komai domin hana shaidar dake hannunta fita, ita kuma bata so ko kaɗan wani abu ya samu ƙanwarta mai tarin mafarkai masu kyau da take son cikawa ta dalilin rikicin data janyo tunda ta san a kaf faɗin garin Matazu basu da mai tsaya musu sai Allahn ɗaya halicce su. Hatta sauran dangin Babansu dake JIƘAMSHI su kawu Isa sun gama lalata sunansu a wurinsu, dama kuma dangin ba wani yawa ne dasu ba manyan duk sun mutu sai ƴaƴa da jikoki kuma ba wani zumunci ake ba tunda Iyayen suka rasu kowa ya kama gabansa.

Shiryawa tayi tsaf cikin shiga mai kyau ta baƙar Abaya ta naɗe fuskarta da kallabin Abayar, tayi kyau sosai abinta domin kuwa itama ɗin kyakykyawar ce. A ƙafa take takawa kafin ta samu abin hawa da zai kaita tasha, tunda ta fito daga gida ta lura da wata baƙar mota dake binta a baya cikin ƙwarewa don in baka da maida hankali ba zaka taɓa tunanin cewa bin nata take ba.

Tayi tafiya mai ɗan nisa dai-dai inda hanya ta rabu wacce zata kai mutum bayan gari motar tazo ta sha gabanta da ƙarfi, da sauri ta matsa gefe saboda saura kaɗan motar ta taka mata ƙafafu. Ƙoƙarin buɗe baki take zata soma masifa don ta ɗauka irin ƴan iskan nan ne masu tare ƴanmata a hanya taji horn daga bayanta, a fusace ta juyo don ganin wane ɗan rainin hankalinne kuma daga bayanta. Kafin na cikin motar dasuka sha gabanta su fito aka buɗe wacce ke bayanta, sojoji ne guda biyu suka fara fitowa sai kuma Muzaffar shima ya fito yana kallonta da murmushi yace "Wa nake gani kamar Yayar ƙawar Auta?." Itama murmushi ta saki tana cewa.

"Lah kaine ashe ɗan gidan Sojoji, ina ƙanwarka da kuma bos ɗin?." Murmushi ya saki yace.

"Bos baya nan amma shi ya aikomu, Haneen kuwa tana can tana ɓata rai saboda Ammah ta aiketa shi yasa bamu taho tare ba duk da taso hakan don ta haɗu da miskilar ƙawarta." Murmushi ta saki tana cewa.

"Ai Amah ba sauƙi in dai miskilanci ne ta ƙware, don nima in ta ƙumeni da takaici sai na samu na maka mata zagi muke shiryawa." Dariya Muzaffar ya saki sosai harda ƙyal-ƙyalewa saboda shi mutum ne mai fara'a ga zolaya bashi da matsala ko kaɗan.

Juyawa Ya Nafi tayi don ganin motar data kusa kaɗeta amma sai taga wayam bata nan ta bar wurin. "Kai ina ƴan balaja'un da suka kusa kaɗeni?." Ta faɗa tana ciza baki alamar ba haka taso ba.

"Oh wai dama kaɗeki ta kusa yi? Ai mai motar yayi tafiyarsa tun tsayawarmu." Muzaffar ya bata amsa...

Abinda ya faru shine lokacin dasu Dugaz ke ƙoƙarin fitowa daga motarsu domin kama Ya Nafi sai kawai sukaga Sojoji sun fito daga motar data tsaya a bayanta shine fa suka ji tsoro suka arce ba tare da sun gabatar da abinda suka yi niyya ba.

"Kaico!." Dugaz ya furta cikin ɓacin rai yana dukan sitiyari lokacin da ya tabbatar yayi nisa daga inda yaga sojojin, sosai yaji haushin rasa wannan damar da yayi, domin kuwa kusan sati ɗaya yana dakonta yana son ta fito ta shiga inda zai iya ɗauketa ba tare da an gansu ba. Sai yau ya samu damar amma wannan sojojin suka zo suka ɓata komai, ga takurar da Alhaji Tanimu ke masa don bai taɓa sa shi wani aiki aka samu jinkirin kammala shi kamar wannan ba. "Sorry Oga ta tsallake yau, amma a gaba bazata samu mai cetonta ba." Wani da ake kira na kalala a cikin yaran Dugaz ya faɗa.

Tamkar Alhaji Tanimu ya san halin da ake ciki kuwa sai ga kiransa cikin wayar Dugaz, sai da ya saki mugun tsaki kafin ya ɗaga yayi shiru bai ce komai ba. "Ya ake ciki ne Dugaz? Ina fatan dai an kammala aikin?."

Ya faɗa da zaƙuwar son jin labari mai daɗi.

"Ana gab da cika aikin dai aka samu matsala sojoji suka biyo ta hanyar." Ya ƙare maganar cikin muryar riƙaƙƙun ƴan daba. Ai kuwa masifa Alhaji Tanimu ya shiga zazzagawa yana cewa "Ka san irin matsi da takurar da nake sha akan wannan aikin kuwa, amma shine ka tsaya wasa da shi? Kaga Dugaz idan bazaka iya bane ka sanar dani a samu wanda zai iya, haba don Allah!." Ya ƙare maganar a fusace.

"Amma dai ka san baka taɓa bani aiki na kasa cikawa ba ko? Miye na gaggawar akan wannan ɗin?." Dugaz ya ƙare maganar cikin jin haushin tsawar da Alhaji keyi masa a kunne. Kwantar da murya Alhajin yayi saboda ya san halin Dugaz baya ɗaukar raini, kuma sannan shima faɗa yake bashi da wanda ya kai Dugaz iya cika masa aiki duk cikin yaransa. Don haka yace "Ba haka bane Dugaz nima ina cikin takura ne, mai gida ya sakoni a gaba akan na bari aka samu matsala abin nan ya fita to in kuka da kaina shi yasa nake a birkice."

"Za'a cika aikin tamkar yanda aka saba." Yana gama faɗa ya yanke kiran yana jan dogon tsaki ya ciro sigari ya kunna mata wuta ya shiga banka ma cikinsa. (Allah ka shirya mana zuri'a ka hane su aikata ɓarna).

A ɓangaren su Muzaffar kuwa tambayar Ya Nafi yayi akan inda zataje tace masa Katsina. Cewa yayi "Me zai hana ki jira mu gama abinda zamuyi a gidan gonar Akhi sai mu wuce tare tunda ba daɗewa zamu yi ba." Shiru ta ɗanyi tana nazari kafin tace "Shikenan to muje." Buɗe mata baya yayi ta shiga shima ya shiga ya zauna kusa da ita, sojojin kuwa a gaba suke ɗaya ke jan motar ɗaya kuma a kusa da shi. Baba Alhaji ne yasa shi tahowa dasu su masa rakiya zuwa matazun gidan gonar Zayyad ɗin da zai je su fitar da raguna da shanun da za'ayi walimar buɗe sabon Companyn Zayyad ɗin dasu.

Shine ya saka sojojin suyi masa rakiya saboda rashin kyan hanyoyi da ake fama dasu a ƙasar, sunzo dai-dai kwanar da zasu shiga shine sukaga mota ta tare hanya suka fito domin dubawa yaga Ya Nafi, shine silar cetonta daga hannun su Dugaz......

***