AMATURRAHAMAN

29

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 29

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Sun isa Katsina cikin aminci Muzaffar ya buƙaci ta faɗi inda zata je su kaita, cewa tayi su ajeta kawai zata hau adai-daita sahu. Dagewa yayi ta faɗi unguwar da zataje ɗin su kaita, unguwar da tasan su Aunty Halimar na zaune a cikinta kafin tafiyarsu Istanbul ta faɗa masa suka kaita har can sannan ta sauka tayi musu godiya. Kuɗi ya ciro masu yawa ya bata sai chocolate masu yawa a cikin wani ɗan boxs mai kyau yace ta kaiwa Amaturrahaman.

Amsa tayi tana masa godiya sosai saboda Ya Nafi bata wuce tayin kuɗi saboda azabar rashinsu da suka ɗandan a rayuwa yasa duk inda ta same su amshewa take ba tare da banbance halacci ko haramcin su ba. "Kamar ka san kuwa mutuniyar akwai shan zaƙi." Ya Nafi ta faɗa tana murmushi.

"Kinga shike nan ta samu, amma fa kada tasha da yawa yayi mata illah."

"Da alama kanaji da ƙawar autar nan." Murmushi kawai yayi yace "Sai an jima, ki gaisheta idan kin koma."

"Zata ji da kyau, ka gaishe da auta da Ammah."

"Ok bye." Ya faɗa yana ɗaga mata hannu daga haka suka wuce. Ajiyar zuciya Ya Nafi ta sauke tana tunanin ta inda zata fara neman gidan domin kuwa sau ɗaya suka taɓa zuwa tun tana yarinya, gashi unguwar ma ta canza mata tamkar ba waccen unguwar da suka taɓa zuwa ba lokacin da Ummansu taje gidan da ita.

Kan junction ɗin da wasu samari ke zaune suna hira ta ƙarasa da sallama suka amsa mata. "Don Allah tambaya nake?." Ya Nafi tayi musu tambayar.

"To Allah yasa mun sani." Faɗar ɗaya daga cikin samarin da duk suka zuba mata ido suna kallon kyakykyawar budurwar da tayi kyau cikin shigar Abayar da tayi.

"Nace don Allah nan ne ƙofar marusa?." Cikin sauri wanda ya fara mata magana yace "Eh nan ne, gidan wa kike nema?.

"Gidan wani Alhaji Kabiru Ahmad Datti." Ta faɗa saboda ta riƙe sunan mijin Aunty Halimar.

"Kai anya kuwa a nan unguwar?."

"Eh haka ne sunan, amma yanzu basa ƙasar sun tafi Istanbul ban sani ba ko sun dawo." Ya Nafi ta faɗa da fatan dacewa.

"Oh na gane, wanda suka zauna a gidan can na layin baya, gaskiya basu dawo ba don har yanzu gidan a rufe yake." Ɗaya daga cikinsu ya faɗa.

"Dan Allah to gidan Iyayensa fa?".

"Gaskiya ba a nan unguwar suke ba sai dai ki tambaya gaba." Godiya tayi musu tayi gaba ta shiga tambayar mutane.

Ranar haka Ya Nafi ta gama zagayenta a cikin Katsina ba tare da ta samu abinda tazo nema ba, haka ta haƙura ta koma da nufin zata ƙara dawowa.

Koda ta dawo ta samu Amaturrahaman kwance tana fama da zazzaɓin daya zubar mata don ko tashi ba'a yiba yau a Makaranta ta taho gida ta kwanta ta rufa da bargo sai faman kar-karwa take.

"Subhanallah! Amah me ya sameki haka?". Ya Nafi ta tambaya cikin damuwa tana yace rufar da tayi. Da sauri ta jawo abin rufar tana ƙoƙarin mayarwa ta sake rufa.

"Tashi, tashi maza ki cire uniform ɗin asibiti zamuje." Ya Nafi ta faɗa tana hanata sake rufewar.

"Sanyi nake ji Ya Nafi, ki rufeni."

"A'a tashi in taimaka maki." Kamata tayi ta tashi zaune sannan ta nufi wurin kayanta ta ɗauko mata doguwar riga mara nauyi da hula ta aje mata ta fita waje domin duba kofi ta haɗa mata tea ta bata kafin su wuce. Shigowa tayi ɗauke da cup ta samu har ta saka rigar ta koma kwanta.

Inda suke aje kayan shayin ta nufa bayan ta tsiyayi ruwan zafin da basa rabo da shi a plaks saboda basa amfani da ruwan sanyi tun Umma na raye, ita ce ta koyar dasu kuma suka tashi akan turbar har bayan ranta. Tea ɗin ta haɗa ɗan madai-daici ta miƙa mata tana cewa "Maza shanye mu tafi."

"Na ƙoshi Ya Nafi, amai zan yi in nasha."

"Ba za kiyi ba, maza daure kisha." Ya Nafi ta faɗa tana sa mata cup ɗin a baki. A hankali ta buɗe baki ta shiga kurɓa a hankali har ta ɗan sha da yawa sannan ta ɗauke kai.

"Bari na kira Gaddafi yazo da mota ya miƙa mu."

"Ba zan bisa ba." Amah ta faɗa a taƙaice.

"Kin fiye rigima Amah, shike nan muje mu hau adai-daita sahu ya miƙa mu. Ba musu ta miƙe da ƙyar Ya Nafi ta riƙe hannunta suka fita ta kulle ɗakin saboda shigowa da ake ana musu ɗauke-ɗauke idan basa nan.

A ƙarƙashin biyar tsakar gidan suka samu matan gidan da yaran suna hutawa, da kallon banza Babar Salaha da Salahar suka raka su suna jin baƙin cikin rasa Doctor Farhan da suka yi domin kuwa kwata-kwata sun daina ganinsa. Gashi Babar Salahar taje ƙauyensu ta amso magunguna wanda Salahar zatayi amfani dasu ta tunkari Doctor Farhan ɗin da zarar sun haɗa ido kuma ya shaƙi ƙamshin turaren da boka ya bada shike nan magana ta ƙare.

Sai dai tunda ta dawo suke baza idon ganin Doctor Farhan ɗin yazo wurin Amaturrahaman suyi amfani da damar Salaha taje ta gudanar da abinda bokan yace. Sai dai shiru bashi ba labarinsa har tsawon sati kusan biyu, sau uku Salahar na zuwa asibiti nemansa ana ce mata bai shigo ba dole suka haƙura suna jiran dawowarsa daga koma inane yaje, domin kuwa sun riga sun ƙwallafa rai a kansa dole sai sun cika birinsu.

Aunty Rakiya dake ƙullin kayan miya na sayarwa ita kaɗai ta tambayi Ya Nafi abinda ke damun Amah ɗin, ta sanar da ita cewar zazzaɓi take zata kaita asibiti tayi musu fatan samun lafiya suka fice sauran na binsu da harara da tsaki ƙasa-ƙasa.

Suna fitowa suka samu abin hawa suka wuce Asibitin inda cikin sa'a ba kayi don haka ba ɓata lokaci aka dubata. Ba wani abu bane ke damunta maleria ce sai damuwa da likita ya sanar da Ya Nafi cewar Amaturrahaman ɗin na barin damuwa a ranta tana damunta su suka haɗu suka saukar mata zazzaɓin, sakamakon aman da tayi da yawa aka jona mata ƙarin ruwa laida biyu da allurai.

Ruwan na ƙarewa aka rubuta mata magani aka sallamo su suka koma gida lokacin magriba tayi, suna zuwa wanka Ya Nafi tasa Amaturrahaman yi ta tsareta ta ɗanci abincin da ta sayo musu a hanya. Da ƙyar ta samu ta ɗanci kaɗan ta bata magani ta kwanta barci ya ɗauketa sannan Ya Nafi ta shiga wankan itama

Katsina.......

A can Dokajo Mansion kuwa kamar yanda Uncle Maina ya faɗa Abdulmajid yazo ganin Anisa, tunda Mahaifinsa yace ya shirya yaje ganin ƴar gidan amininsa da yace yana so Mahaifinta ya bashi izinin zuwa su ga juna.

Ba ƙaramin farin ciki yayi ba saboda da dama ya daɗe yana neman irin wannan damar mahaifinsa na dakatar dashi.

Cikin zumuɗi ya shirya cikin kyakykyawar shiga irin ta matashin saurayi ɗan gata mai ji da Naira ya nufi gidan kasancewar ya san gidan ba baƙonsa bane domin suna zuwa da Dadynsa lokaci zuwa lokaci idan ana wani abu a mansion ɗin ko kuma da bikin Sallah. Wanda a nan ne yaga Anisar wani zuwa da sukayi shida Dadyn duba Baba Alhaji da yayi rashin lafiya.

A kallo ɗaya daya mata ya kamu da soyayyarta saboda Anisa itama kyakykyawa ce ba laifi, ga iyayin tsiya da ɗaukar kanta tafi kowa saboda ganin irin gidan data fito. Lokacin da ya mata magana bata wani kula shi ba saboda ta riga ta ƙwallafa rai akan Marshal Zayyad ɗin.

Koda ya samu Dadynsa da maganar yayiwa abokinsa maganar cewa yayi ba komai in har sun dai-daita kansu shi zai yi farin ciki, sai dai kuma yana so Abdulmajid ɗin ya ɗan dakata har Anisar ta kammala karatunta saboda ta samu yinsa cikin nutsuwa.

Ba don yaso ba ya haƙura saboda ba ƙaramin so yake mata ba, amma duk da haka yana kiranta a waya sai dai bata wani kula shi. Yau da akace yaje da izinin Mahaifinta su gana za'a saka musu ranar aure shi kaɗai ya san irin farin cikin da yake ciki, don haka ya tafi zuciyarsa wasai.

___________★

A ɓangaren Anisa kuwa saɓanin Abdulmajid ne domin kuwa tana cikin tsananin baƙin ciki da tashin hankali, ba irin roƙon da bata yiwa Dady ba amma yace ya gama magana, ta kuskura kuma yaji cewar ta wulaƙanta Abdul ɗin sai yayi mummunan saɓa mata.

Ita da Momyn gaba ɗaya ya haɗa ya bigewa warning ya kuma ce su shirya tarbar baƙon. Zuciyar Momy ba daɗi ta bawa masu aikinta umarnin shiryawa baƙon abin tarba ta kuma lallaɓa Anisa ta shirya bayan ta mata alƙawarin cewar ba zata bari a aura mata wanda bata soba, zata san duk hanyar da zata bi ta lalata wannan haɗin da Dadyn ke ƙoƙarin yi.

Haka tana tura baki tana komai ta fita ko ƙwalliya bata yi ba iya Abayar jikinta ta fita da ita. Tunda ta shigo ɗakin baƙin da aka sauke Abdul ɗin ya zuba mata ido yana jin yanda soyayyarta ke ƙara yi masa illah, duk da cewa fuskar a turɓune take ba fara'a shi tayi masa kyau sosai a hakan.

Da ƙyar ta iya buɗe baki tayi sallama ciki-ciki shima saboda gargaɗin da Dady yayi mata ne domin tunda akace Abdul ɗin zata aura taji wata muguwar tsanarsa wacce bata jiba a baya, a maganar gaskiya Abdulmajid ɗin bashi da wata makusa domin kuwa kyakykyawa ne ba laifi sanan kuma ɗan gayu, uwa uba kuma suma suna da ƴaƴan bankin, sai dai in aka haɗa shi da Zayyad ɗin shi ba komai bane shi yasa taji ba zata iya amsar shi ba.

Da ace babu Zayyad ɗin babu abinda zai hana ta amshe sa domin kuwa shima yana da qualities ɗin da ƴanmata ke buƙata wurin zaɓen mijin aure.

Sai dai kash Ya Zayyad ɗin na da banne dake wahalar samu a cikin dubban maza, kamewarsa da tsananin kwarjininsa kaɗai ya isa yasa zuciyar ƴanmatan dake ji da kansu matowa a tsan-tsar ƙaunarsa ba tare da sun farga ba.

Wuri ta samu saman kujera ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta shiga karkaɗasu. "Barka da zuwa sarauniyar zuciyata." Abdul ɗin ya faɗa yana sake mata murmushi.

Wani malolon baƙin ciki ne yazo ya tokare maƙoshimta jin abinda ya faɗa, don haka ta watsa masa wani mugun kallo tace. "Ka nemo sarauniyarka tun kafin dare ya maka, domin kuwa wannan sarauniyar tafi ƙarfin ƙasƙantaccen sarki irinka sai dai gawurtaccen Sarki wanda ya amsa sunan shi."

Yaji matuƙar zafin kalamanta domin kuwa hakan cin fuska ne a gareshi, amma da yake shima gogagge ne sai ya danne komai ya saka murmushi a fuskarsa yace. "Gawurtaccen Sarki sai gawurtacciyar Sarauniya wacce ta dace dashi, amma wannan Sarauniyar da wannan ƙasƙantaccen Sarkin ta dace domin kuwa shine dai-dai ita, am kinga ni zan wuce amma ina son sanar dake cewar ki fara shirin zama mallakin ƙasƙantaccen Sarki nan da ƴan kwanaki, domin kuwa tuni Mahaifinki ya mallaka masa ke!." Yana gama faɗin haka ya fice daga palon cike da jin zafin wulaƙancin data yi masa, a ransa ya ƙuduri aniyar nuna mata iyakarta domin kuwa soyayyar da yake mata bazata hana shi koya mata hankali ba tunda ya lura rashin mutuncinta kullum ƙara gaba yake.

Anisa kuwa kasa motsi tayi daga zaunen da take, zafi da ɗacin maganar daya faɗa mata su suka kusa tsayar da bugun zuciyarta. Data rasa abin yi kawai sai ta fashe da kuka ta fice daga ɗakin ta nufi Momynta dake can ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman kai kawo take........