Zanzabira
by @maidambu41
A Royal politics🔥
An yanka ta tashi.
Ramlat Ar Manga
Mai_Dambu
Dandano
Runaway Bride
"Kamin alƙawarin babu abinda zai tab'a had'aku, kai ban yarda ka haihu da ita ba balle har wani abu ya shiga tsakaninku Please idan kayi min haka ba ruwana da aurenka da ita tunda hoto ce ni kuma xan zame maka baiwa ga duk wata bukatarka!"
Murmushi irinta gogaggen likitan ƙwaƙwalwa da suka girma cikin gogewa da iya tafiyar da sha'anin mahaukata da masu hankali ya kashe mata idanu, wato idan ana niman Dr romance aka samu Salman magana ya kare.
"Na ji ke yaushe zaki haihuwa?" Gabanta ne ya fadi. Tashi tayi daga jikinsa "My prince ya batu haihuwa?" "Ok baki shirya haihuwa ba?" "No mu yi Adopted Yaro mana ko yarinya?" Kallon renin hankali ya mata domin yasan abinda take kokarin binnewa ba mai yiwuwa ba ce. "Ba ce kome ba?" "Hmm me zance?" "Ka ce kayi alƙawarin babu abinda zai haɗaka da ita!" "Ok!"
****
"Uwais!!" Na kira sunanshi da mugun ƙarfi, wani irin karo muka yi da motar da yake gabanmu, na dai ji lokacin da motarmu tayi wani irin juyi kamar an cillata sama, kafin ta kifa daga nan ban kuma sanin me ya faru ba.
****
Murmushi yayi yana kallon Dattijon da yake gabanshi, wanda a baya can aminin mahaifinsa ne amma a yau da ya koma makiyinsa zalla gani yake kamar idan ya kyale shi Allah zai tsine mishi albarka ya tab'e ya lalace ya zama mara amfani a cikin al'umma. "Da fatan kafin shiga da fice kana fahimtar meke faruwa a wannan duniyar! Bumm!" Bai rufe baki ba daya daga cikin bodyguard din dattijon ya shigo da gudu. "Yallabai mai gida Khalifa ga shi can yana ihu da hauka!" "Khalid?" Ya furta da karfi zai mike. "Koma ka zauna!" "Kai Salman?" Ya daka mishi tsawa, hannu ya saka a kunnensa ya sosa kafin ya cire ya hure hannun, sannan ya saka hannu a aljuhun gaban rigarshi ya fito da wani kwalbar allura Gamma-Gamma-Aminobutyric Acid (GABA) "Yallabai yana ihu!" Masu kula da lafiyar Khalifa suka fada da ƙarfi. Murmushi yayi ya ce mishi." Regulates mood, stress, and fear
For our brains to operate effectively, the brain releases neurotransmitters that communicate with the rest of the nervous system. The way this process works is, wanann shine halin da danka yake ciki, ba mamaki idan ya kasance ba dukka kwalbar na juye mishi zai dauki short term kafin ya sake shi, idan kuma aka yi dace nan da sati daya yana hauka." Sannan ya mike ya zuba mishi idanu. Ya kai tsaya biyu idanunsa da hannu ya ce mishi. "Ina kallonka idan kaso kada ka bada kai. Ni kuma sai na tabbatar da, bummm." Sannan ya juya ya bar gidan.
***
Bude idanun nayi da suka yi nauyi, na kalli dakin me dauke da haske sosai. Sannan na kara lumshe idanuna a karo na biyu na kara bude shi. Juyawa nayi na ganshi zaune harde da kafarshi wato yayi Crossing leg yana kallon wayarshi. "Kin gama gudun?" Tashi nake son nayi amma na kasa, wannan wani irin mutum ne da bai san tausayawa ba, sai bakar magana. "If you like ki fadi kome!" Bude idanun nayi ina jin kwalla na cika min idanu. Mikewa yayi. " Ai nasan ke ba jahila ba ce, da aurena akanki zaki bi a wani namiji."
***
"Dame ka dogara ne!" "Allah" ya furta yana murmushi. "Zan baka mamaki!" Murmushi yayi kafin ya ce mishi. "Alhaji Nafi'u bana tsoron mamakin da zaka bani, na fi tsoron irin mamakin da zan baka kawo kunnenka!" "Bummm!" Ya furta a hankali. "Kai kai kai..." "Shiii kai ta kanka!" Ya fada yana barin harabar masallacin juma'ar da take kofar fadar Zanzabira.
Yana tafiya amma murmushi yake, ga wata irin tafiya me cike da kasaita da izza, wata irin nishadi yake ji. Bai bar wurin da taku goma ba aka kira Alhaji Nafi'u, wani irin ƙara yayi tare da dafe kirjinshi.
Ihun jama'a bai saka shi fasa tafiyar ba, yana murmushi idanunshi sun yi jajjur.
Cizon lips dinsa yayi bai gama ba, mahaifinsa, Alhaji Saddam, Matarshi, da aka ci zarafinta, sai ya yaki duk wanda yake da sa hannu a tab'a Nasabarsa da kimarsa..
***
Cirko-cirko suka yi a gaban emergency, manya da Yara, sai kuka suke domin wannan shine karon farko da aka kawo Mai Babbar daki asibiti. Idan ka kalle shi sai ka É—auka babu jini a jikinshi ne. Shigowar matansa biyu yasa shi zuba musu idanu. Kafin suka iso gare shi.
Rab'ewa nayi gefe domin nasan ni ce mai laifin. Duk abinda ya same Mai Babbar daki ni ce. "Yaya Salman me tazo yi asibitin? Tazo ta kara kashe mana Uwa ne?" Kallon kanwarshi yayi da idanu. Kafin ya juya kaina ya kalle ni. "Gaskiya ta bar asibitin nan ko mu dauki mataki a kanta." Yadda suke harzuke, ya sa shi takowa gabana ya ce min. "Ki koma gida!" "Ka.... Bar...ni na wanke kaina." "How?" Ya tambaye ni yana zare min idanu. "Da gaske ba hotona ba ne?" "Waye zai yarda? Bayan ni da nake Mijinki guduna kike?" Ya fada kasa kasa yadda babu me iya jin amon kalmar. Da sauri na d'ago kaina ina kallonshi. "Idan na yarda ka bincika zaka wanke ni?" Duk da halin da yake ciki sai da ya kara min kallon ban dariya. "Ikhlas a zahirin gaskiya kin bani kunya, ace kina wife of crown prince a ce har an fitar da nude dinki! Kuma Prince Salmanun haka zaka cigaba da kallonta a matsayin mace." Inji Iram wacce ta shigo asibitin ita da Mommy Turai. "Wallahi ba nawa ba ne?" "Ku fita kafin na dauki mataki akanku!"
Wani irin kuka ne ya zo min, taya xan iya cewa bani bane. Haka na juya a hankali ina tafiya. Na bar cikin asibitin karar horn naji na tsaya ashe Uwais ne.. "yan mata shigo na kai ki gida ai na gaya miki ba sonki suke ba."
Yana tsaye ya ga lokacin da ta shiga motar Uwais. "Na gaya maka yarinyar nan bata sonka, duk abinda ya faru amma zata bi wancan dan iskan gayen!" Murmushi yayi ya kalli Nadiyyah. "Ni kuwa sai nake ga kamar Nadiyyah Chiroma da na sani bata damu da rayuwar wasu ba, tafi damuwa da niman kuÉ—inta da duniyarta yaushe kika fara damuwa da kishiyarki? Ko akwai wani abu da yake fishy ne ban sani ba?" "A'a... A'a no never!" Ta fada da sauri.
---------------
"A yau gwamnati mai ciki na jahar zanzabira ta tsige sarki Attahiru Shehu Yayari a kujeransa na Sarkin yanka. Sannan ta nad'a Alhaji Rilwani Abubakar Yayari a matsayin sabon sarkin ZANZABIRA. Ana kira ga al'ummar jahar zanzabira su yi mubaya'a ga sabon Sarki."
Tsaki wani dattijo yayi yana faÉ—in. "Aikin kenan, tunda Alhaji Saddam ya rasu shi kenan, masarautar Zanzabira da shi kanshi Sarki Attahiru Shehu Yayari ya zama abin tausayi, waye ya sani ko akwai hannun wasu a cikin jinyar da yake yi a kasar Jamus!" "Tabbas Baba Mati, nima na zargi haka sannan shi gwamnan ma ai bai da ikon kanshi saka shi ake yi, Allah ya kyauta kana ganin Sadauki zai bar wannan batun?"
"Yaron da aka ce babu abinda ya dame shi da sarauta, ba zai damu ba don ba damunshi tayi ba."
"Amma tow bari nayi shiru!"
-----------
"Ku tabbatar kun kashe shi ku batar da gawarshi, wannan yaron bala'i ne idan ya girma sai yafi Attahiru Shehu Yayari masifa!"
--------
"Ku kashe mana Saddam ku daura laifin akan Junaid Gobir, sannan Attahiru Shehu Yayari na saka an rufe mana babinsa ko.yana raye ba zai amfana ba. Zai ma mutu"
****
Kafin zuwan turawan mulkin mallaka, sarakunan gargajiya suna da wata irin karfi da fad'a aji, sarakunan suna iya kafa dokar da babu wnada ya isa tsallakewa bayan har zuwan turawan mulkin mallaka, sun sami wannan dokar na sarakunan gargajiya! Domin kuwa Muslunci da jahadin Shehu Usman danfodiyo ya kafa sarakunan Musulunci wanda suka kasance sarakunan gargajiya! A da can baya kafin shehu usman danfodiyo ya samu damar mamaye yankin Arewacin Najeriya, Malamai sukan zo gari kafin su shiga gari sai sun nime Izinin sarki da jama'arsa, haka yasa koda mamayar jahadin Shehu Usmanu danfodiyo ya zo sai aka samu sassaucin karban addinin Muslunci! Bayan Muslunci ya shigo cikin gidan da al'ummar sassan arewa sun amsa hannu bibbiyu! An yi ta samu malamai masu zuwa garuruwa domin tabbatar da da'awa da yad'a Muslunci! Haka ya taimaki ainun wurin kafuwar Musulunci a ko'ina! Shigar Muslunci lungu da sakon arewa wani abu ne da ya kara habbaka addinin, haka yasa garin Zanzabira! Take daga cikin yankin arewacin najeriya da Muslunci ta shiga cikinsa har sarakunan wancan lokacin suka rike babban Malamin da ya shiga yankin Zanzabira!
(Zanzabira gari ce da na kirkirota a cikin najeriya da kasar hausa gabakidaya)
2004
_Ƙarƙashin sassanyar inuwar bishiyar mangoro da yake yalwacce a gidan gonar Sarki Attahiru Shehu Yayari, kishingiɗe yake yana hutawa tare da wasu daga cikin manyan hadimansa. Musamman Salama wanda kowa yasan amintaccen hadimin sarki ne, domin ana yawan faɗin. Kafin ka ga Attahiru II fara isar da sakonka ga salama. Wayar tafi da gidanka da yake aljuhun Salama ce tayi ƙara, ya kalli Mai Martaba cikin kulawa da niman izinin. Murmushi yayi cikin dattaku irinta manyan mutane ya ce mishi. "Har sau yaushe zaka fahimci girmanka Abdulfatihi?" Kasa da kai yayi cikin girmamawa ya ce mishi. "Lafiya toron giwa, lafiya Mazaje, Giwa mai tafiyar kasaita. Na gaida Angon Mai Babbar daki, Mijin kilishi, Mai dakin mai daki wato Fulani karama, Babba dan babba namiji Babban Salmanun Faris, Garnakaki Garko na Turaki! Gaba Salama baya salama mijin Maryamu Uban Maryam, Uban Fadimah, Angon Balkisu. Miji ga Khadija, Baban kubra, na gaida Mijin Zainab Abu Fulani karama baban AbdulHafiz!." Cikin murmushin da yalwatu a fuskarshi ya ce mishi. "Salama dauki wayarka!" "Na gode Salama yana godiya!" Ya mike da sauri ya matsa kaɗan ya amsa. "Alhamdulillahi, mai martaba yana nan lafiya, muna gidan gonarshi. Wanda yake wajen gari." Ya fada yana murmushi tare da shafa gemunsa. "Alhamdulillahi tow Allah ya kawo shi."
Ya kashe wayar yana murmushi, sannan ya koma wurin Mai Martaba ya zube gabanshin yana faɗin. "Allah ya taimaki had'arin dare malafar duniya, Alhaji Nafi'u yana tafe tare da tawagarsa." Murmushi yayi yana kallon hanyar da zata dauko mutum izuwa inda yaƙe, ya ce. "Ubangiji ya kawo su lafiya, rabona da shi tun wani haduwar da aka yi na sarakunan yankin arewacin kasar!" Ya furta yana murmushi domin mutum ne mai matuƙar son zumunci. Hakazakali yana matukar son abokanshi guda ukun nan, Nafi'u Abubakar Shaiba, Saddam Tanimu Jatau, Sheikh Imam Junaid Gobir. Su din abokai ne na faɗa aji wanda suka yiwa kansu lakabi da Four Friends, Four Pillars, Four Empires, wannan taken nasu ya saka ko tari suka yi tow kowa yana iya shiga hankalinsu.
Sun gina juna a tafarkin soyayyar iyaye da kakanni, sun tsayawa junansu cike da wajensu,yadda ba ka tab'a iya gano meke faruwa me ke a tsakaninsu. Sunyi alkawarin bawa junansu kariya. Da dukkanin zukatarsu. Haka yasa babu wanda zaka iya gulmar dan uwansa ya kyale ka, domin kana gulma dayansu zai saka s kira shi a kuma kiraka a kuma maganar a gabanka. Haka yasa suka gina tsoro da firgici a zukatan magautarsu.
Darajar kowannensu.
Alhaji Nafi'u Abubakar Shaiba. Attajiri ne da yake da manyan kamfanonin a cikin gida da kasashen waje, kuma dilalan mai ne babba na kasar nan. Sannan yana da mata daya Hajiya Khareema da yara hudu.
Saimah
khalisah
Khalifa
Iman
Alhaji Saddam Tanimu Jatau. Dan kasuwa ne mai shigo da kayayyakin masarufi kuma yana fita da na gida waje ya shigo da na waje gida, yana da manyan gidajen Store na zamani a cikin fadin najeriya, sannan yana da gidajen Mai me suna STJ and Son. Yana da mata biyu Hajiya Atika da Hajiya Jamilah yara bakwai.
Uwais
Fadil
Usama
Halima
Safiyya
Tanim
Ikram
Sheikh Iman Junaid Gobir, babban manomi idan aka ce manomi ana nufin noma ba irin nomar abinda za a ci ba, a'a noma ce sosai wacce har fitar da ita ana yi , yana nomar fruits wanda ana ana fita da ita manyan kamfanonin haɗa abin sha, suna saya ana musu drinks, yana nomar kaji da kifi, yana da babban kamfanin yin madarar gora irin Yorghurt da sauransu, sannan makiyayyi ne da yake kiwon dabbobin kana da manyan, awakai, tumakai, shanu da Raƙuma sannan babban malamin Jami'a ce wanda tashi ce ta kanshi. Allah ya albarkaci Imam Junaid Gobir da Yara kasancewarshi daga yankin maradi na kasar Nijar ya fito. Yana da mata uku Malama Hajara, Hajiya Asma'u, Hajiya Turai yara Tara.
Hudu daga cikinsu yaran Malama Hajara ne, wacce ake kira da Maluma.
Abid
Nawwas
Yunus
Ikhlas
Yaran Matarshi ta biyu kuwa Yara uku ne.
Nuraim
Nu'aymah
Sajida
Yaran Amaryansa kuwa.
Iram
Tauhid
Babban malami ne da yake koyarwar addinin Musulunci, wanda dayawa malamai suna mishi adawa da kiranshi Sheikh din masu kuÉ—i, wato almajirin masu kuÉ—i. Sannan sauran Malaman gani suke duk abinda yake samu daga jikin abokansa masu kuÉ—i ne shi yasa ya ware kanshi yana musu asiri tsafi yana lalata iliminsa da cin Amanar addini.
Dr Attahiru Shehu Yayari ll
Mai Martaba Sarkin Zanzabira kenan, wanda yake rike da madafar iko, dogo fari mai farin aniyar Garnakaki namijin gaske, bijimiin Zanzabira, wanda a tsawon shekarun mulkinsa har yau ake mishi fatan yayi nisan kwana irin mahdi ka ture, adalin sarki da ya gaji Sarautar daga mahaifinsa. Ba don abokai ukun nan ba da yau sai dai ya zama wani na fada ba dai Sarkin alumma ba. Mai martaba yana da Yaran goma sha biyar. Mata huÉ—u.
Hajiya Maryam mai Babbar daki, Yaranta shida.
Salmanun Faris
Maryam (Aneesa)
Dawlatu Khaltum
Abdullahi (Mai Kano) Takwaran Sarkin Kano.
Sulaiman (Mai Bauchi) Takwaran Sarkin Bauchi.
Fahad auta.
Hajiya Balkisu Turaki tana da Yara uku.
Fatimah
Abdul Hafiz
Salim
Hajiya Khadijah Kilishi tana da Yara uku.
Kubra Hadizah
Mu'azzatu
Hisham
Hajiya Zainab Abu Fulani karama..
AbdulHafiz
Amir
Ilham
Wadannan sune iyalan mai martaba Sarkin Zanzabira.
___________________________________________
Yau taron yau ya sha ban domin kuwa a cikin wannan shekarun Allah ya albarkaci rayuwar abokai hudu da samun karuwa, kowannensu ya samu haihuwar Yara mata,, idan ka cire Sheikh Iman Junaid Gobir da shi kusan haihuwa biyu ne, amma baya farin cikin kamar yadda ya samu haihuwar Ikhlas, wacce sunanta Ummu Habibah, amma ake kiranta da Ikhlas. Bayan kaman minti talatin sai ga baki na shigowa daya bayan daya, Alhaji Nafi'u da mutanenshi, can sai ga Alhaji Saddam da na shi jama'ar, can kuwa Imam Junaid Gobir ya iso, anan suka zauna aka fara gaishe gaishe, cikin farin ciki da jin dadi.
"Ba don ƙaruwar da muka samu ba, bai zama dole mu hadu anan ba ko?" Mai martaba ta tambaye su, cikin murmushi ya ke kallonsu. "Kasan hidimar tayi yawa, ga al'umma idanunsu yana kanmu!" Inji Imam Junaid Gobir. "Haka ne wallahi, shi yasa muka kirkirowa kanmu bawa juna yar tazarar da ba zata hana muna haduwa lokaci zuwa lokaci ba." Inji Alhaji Saddam. "Haka ma yayi!"
Kallon Alhaji Nafi'u mai martaba yayi kafin ya ce mishi. "Nafi'u da magana a bakinka?" Gyada kai yayi ya ce mishi. "Kwarai kuwa mai martaba, abinda nake son faÉ—a ta yadda zamu kulla alakar zumuncin da tafi wanda muke kai." Kallon kamar ya suka mishi. "Ni ina da Da namiji Khalifa, ina nimawa d'ana Khalifa auren Yar wurin Saddam Ikram," kallonshi kowa kafin ya sake magana. "Amma kana ganin haka zai yiwu kuwa?" "Yiwuwar a wurinmu ne." Ya fada da kwarin gwiwa.
"Tow ni na nimawa Uwais auren Iman, shi kenan ka É—auke min Y'a na dauke maka Y'a an raba kenan."
"Sheikh baka ce kome ba!" Murmushi yayi kafin ya ce mishi. "A'a ni yanzu lokaci zamu jira, idan Allah ya bamu lafiya nan da dubu biyu da goma sha hudu sai mu ga abinda ya dace."
"Ka ji me wayo ko?"
"A'a ba wayo ba ne." "Tow ni ina kamun daya daga cikin yaran da aka haifa maka!" Da sauri ya kalli mai Martaba."Ban fahimta ba. wa kanka ka kamawa?" Rausayar da kai yayi cikin dattako ya ce mishi. "Laifi ne? Ita yar wurin Turai nake kamunta!" Dariya suka saka. "Wato zaka mana wayo kenan na haifawa abokina y'a shi kenan na baka."
"Ni na zata Salmanun Faris zai nimawa ashe wa kansa yake nimawa." Dariya suka saka bakiÉ—aya. Wanann ita ce zaman da suka yi wanda yake cike da nishadi.
--------------------------------
2014
Bayan shekaru goma yau gasu nan, a zauna a gidan gonar, sai dai yau kana ganin fuskokinsu kasan rai a b'ace yaƙe. Cikin fusata Alhaji Nafi'u ya ce. "Kun yi shiru baku ce kome ba? Kuna jin Saddam yana shirin cutar da ni ba zaku iya tsawata mishi ba."
"Ka ga Nafi'u wannan abin ba fa wani tashin hankali ba ne, sannan kafin ku zo nan Saddam ya same ka har office ka ki bashi damar kuyi maganar fahimtar juna. Wannan abin da ya faru kuskure ne babu wanda baya kuskure amma ka kasa fahimta. Sannan shima ya tafka asara fa, idan don kudi ne zamu mai da maka kayi hakuri." Cikin sanyi murya Alhaji Saddam ya ce mishi. "Mun taso tare mun girma tare,a tsakaninmu akwai yarjejeniyar auratayya, amma yau akan dan asarar da na san zaka iya bar min, kake tashin hankalin kanka? Shi kenan na gode xan mai da maka dukkanin abinda aka yi asararsa dama ban zo nan ba sai da shi." Ya tura mishi. D'agawa Imam Junaid Gobir yayi ya ce mishi. "Ka je da shi gidan ka biya kai zaka iya samun karayar arziki, shi kuma zamu hada mishi rabi shekarar nan sauran rabin zamu bashi shekara mai zuwa please mu bar maganar nan!"
Wannan shine karon farko da aka samu matsala a tsakanin,sai dai ransu su huÉ—un akwai abinda Allah kaÉ—ai ya sani.
*****
2019
Wanda taso da wata irin guguwar da ta rusa kyakkyawar ganuwar da take tsakanin manyan abokai hudu.
Abokai hudu
Masu ra'ayin hudu
Masu buri hudu
Wadannan abokai hudu, sun taso da wani irin kaunar junansu ne tun iyaye da kakanni! Kasancewar kowannensu ya bude idanu da zumuncin ahali hudu haka yasa dukkansu suka yi imani su din zababbu hudu ne! Buri irin tasu yasa gina kansu su har zuwa yau! Kowannensu zai iya bada rayuwarsa domin dan uwansa, wannan zaman na 2004 ba yau aka fara ta ba, yau ita ce zama na uku da akayi, wanda suka fara tun shekaru 1984/ shekaru goma, 1994/ yau 2004. Sun fara zaman ne tun lokacin da sarki Usman Attahiru Yayari, ya rasu aka so daukar sarautar gidan zuwa wani tsagi na daban, suka taya abokinsu yakin da sai da suka tabbatar da shi a matsayin shugaban al'umma. Kwarewa irin tasu na abokai uku! Yasa ake shakkar jayayya da kowannensu domin suna da goyan baya! Sai dai kash an wayi gari Abokai hudu! Suna yakar junansu sama da yadda suka so junansu a baya!
"Kamar yadda kuke da hannu a kashe Mahaifina da Alhaji Saddam, tare da rufe wasu boyayyun al'amari shine na maka kyautar wannan alluran kamar yadda na fara akan Baba Salama da Baba Rilwanu Abubakar Yayari!" Ya fada yana dariya wanda zaka fahimci ciwo a dariyar."
Haka ya bar dakin ya bar asibitin yana dariya, mutumin da bai kasance mai yawan dariya ba, shine yau yake dariya. Koda ya iso, kallonshi nayi na ga yana dariya sosai. Rike hannunshi nayi na ce mishi. "Kayi kuka don dariyarka ba dariya ba ce kuka ce! Kayi kuka forsake of Allah kayi kuka ka rage nauyin da kake dauke da shi na tsawon shekaru yi kuka domin Babynmu!....... D'ago kai yayi hawaye ya zubo mishi. A hankali yake kuka yana me kuka sosai. "Kuka ba ragwanta ba ce, asalima yare ce da zuciya take fitarwa idan kayi zaka samu sauki ka sani tunda kai likitan ƙwaƙwalwa ne. Yi kuka sadaukina....
________
HALIMATOU= SHATU TA KWALAM
CHEF ZEEY = AZIZAH HAMZA
A ROYAL POLITICS= RAMLAT MANGA, Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
5921536136,
RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN,
Moniepoint MFB
1-₦500
2-1000
3-1500
Mun dawo....