KURURUWA A KUNNEN KURMA

3

by @oumameer2671

KURURUWA A KUNNEN KURMA 🥀 🥀

   A 2025NOVEL

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

     (OUM AMEER)

Wattpad:@ Ummu-Ameer

Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa

From d experience writer of:

Zaytoonah

Abarwa rai

Gudun wuce sa'a

Kibiyar so

Kulsum

Bahiyya

Nuudarr

& Now Kururuwa a kunnen kurma

Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏

FREE PAGE 3

    Deen na shigowa harabar gate ɗin gidan su suka yi ido biyu da Xunnurain.

Cike da murmushi ya isa gare sa tare da miƙa masa hannu ya ce.

"Yah Usman kai ne tsaye a nan? Ina Safnar? Miyasa baka shiga daga ciki ba...."

Murmushi Xunnurain ya yi sannan ya ce.

"Ba komai ai, na yi ta kiran yayar ka ne bata ɗaga kira na ba may be bata kusa, pls ka dubomin ita ina jiranka"

Da sauri ya nufi cikin gidan na su yana faɗin.

"Matar da ta ke very addicted to phone ace ba ta ɗaga kira, bari na dubo na gani"

Gaisawa suka yi da Haris, sannan kowa ya ci gaba da latsa wayar sa.

Deen kuwa yana shiga ya taradda Mama tana waya, sai da ya jira kusan shuɗewar mintuna sun kai goma, wanda duk iya yanda ya so ya gane kan wayar da ta ke yi ya faskara ya dai ji ana ta zancen kuɗi.

Bayan ta kambala ne ya gaisheta sannan ya ce.

"Zancen miye wai kike haka Mama? Naji ki na ta ambatan millions of money..."

Kallon sa ta yi da kyau cikin ido sannan ta ce.

"Ba abinda ya shafeka ba ne Shamsudden, wata ce ta ke so ta siya sarƙar gold...."

"To ki ce ta cimma na a shago mana, miyasa sai ta tsaya tana ta damunki... Kinga Mama, bani numbernta ni zan kira ta da kaina in ji wace iriya ta ke so..."

"A'a, ka bar shi, idan ta ta shi zata zo daman tana so kawai ta tambaya ne"

Remote ɗin TV ya ɗauka ya na mai rage volume ya ce.

"Mama Ina Safnah ne? Tunɗazu mijin ta yazo yana jiran ta a waje...."

Wani kallon ta bi shi da shi sannan daga baya ta ce.

"Na aikata gidan Hajiya Binta kuma ba yanzu zata dawo ba, yana iya bari sai gobe ya dawo...."

Juyawa yayi yana faɗin.

"OK..."

"Shamsudden!"

Juyowa yayi kawai ya kalleta ba tare da ya amsa ba.

"Sa'adu ya kirani ya faɗamin yana kan  hanya kada ka kwanta masa a ɗakin sa..."

Gyaɗa kansa yayi ya ce.

"Tau yayi Mama.."

"Deen ba tauyayi ba kada ka kwanta masa a ɗaki na gaya maka da wuri kada sai ya zo ku fara rigimar nan ta ku ta tsiya"

Hannun sa ya ɗaga sama alamar amincewa ya na mai rintse ido sannan ya buɗe ya kalle ta ya ce.

"Mama! Ki yarda da Deen mana, na rantse miki ba zan kwanta masa a ɗakin sa ba"

Daga haka ya fito ya zo ya samu Xunnurain ya ce.

"Yah Usman Mama ce ta ɗan aike ta, kuma ashe ta manta wayar a gida, amma dan Allah ka ƙara haƙuri Mama ta kira can in da taje ɗin ance tana tahowa yanzu"

Gyaɗa kansa ya ce masa.

"Thank you"

Hanyar Parlour ya nufa shi da abokin sa Haris yana faɗin.

"Yah Usman ka shigo daga ciki mana"

Girgiza kansa yayi ya ce.

"No I'm OK, I will wait here"

Suna shiga Deen ya zauna ya miƙe ƙafafunsa yana ta famar farin ciki ya ce.

"Tsuntsu daga sama gasasshe...wannan irin liyafa haka..."

A ɗan ɗosane Haris ya zauna murya a darare ya kalli Deen ya ce.

"Deen baka tunanin Aunty Safnah Yah Usman ta shiryawa wannan abincin..."

Girgiza kansa yayi ya ce.

"A'a Haris, ɗaxu ta faɗamin ba shi aka yi wa ba, yanzu kuma Mama ta ce min in ce masa bata nan ya je sai gobe ya dawo, kaga kenan da walakin goro a miya, ɗayan biyu ne; ko dai wanda aka shirya domin shi bai zo ba, ko kuma yazo amma bai taɓa komai ba, daman ina nazarin ta kwana biyu gaba ɗaya ta sauya. By the way! Wannan ba abinda ya shafe mu ba ne, muci abinci kawai mu fece, amma kafin nan bari na ɗibarwa ɗan uwana Mama ta ce yana hanya "

Daga haka ya janyo plate ya zuba ya zubawa Haris ɗin sannan ya rufe sauran abincin a gefe suka shiga cin abincin suna yi suna fira.

                   🪐🪐🪐

Xunnurain kuwa, duk inda ran sa ya ke ya kai ƙololuwa wurin ɓaci, Allah ya sani yana son Safnah sosai, ita kanta tana cikin mutum ta farko da zata bada shaidar cewa mutum ne wanda baya son wulaƙanci, baya wulaƙanci kuma baya bari a yi masa, duk wata hanya muddin zata zo masa da cin zarafi da ƙasƙanci ya fi so ya yafe koma miye wannan.

Turbar da Safnah ta ɗauko a yanzu ta fara ba shi tsoro. Tunda suka rabu a ɗaxu bai fi minti goma da isa gida ba ya fara kiran wayar ta har yanxu bata ɗaga ba, kuma yanxu ma akan kiran na ta yake har a cikin gidan na su line busy amma shi ne Mama zata ce wai bata je da waya ba....yana nan dai ya saƙa ya warware ya na yi yana duba agogon wayar sa kwatsam sai ga ni na turo ƙofar gate ɗin na shigo. Turus nayi tare da mugun haɗe rai tamkar ban san wanda ya ke a gabana ba. Shi ma dai haɗen ran ya yi domin ba ƙaramin harzuƙasa na yi ba.

Kallon kallo mu ka Shiga yi wa juna, ganin bai da alamar yi man magana yasa na kama hanya da nufin shigewa,cikin wata kakkausar murya a mugun fusace ya ce.

"Wai Safnah miye ya ke damun ƙwaƙwalwarki ne?"

Waigowa nayi ina facing ɗin sa ta tare da ɗaukar sa da ido na watsar sannan na ce.

"Abin da ya ke damun taka ƙwaƙwalwar..."

Ɗan ƙara matso ni yayi kaɗan yana mai bina da kallon mamaki ya ce.

"what?"

Ƙara maka masa harara na yi sannan na ce.

"Usman Shaheed ka na fa ɓata min lokaci na, idan ba ka da abin yi to ni gaskiya ina da shi"

A hankali ya matsa jikin gini ya jingina domin ji yake ƙafafuwansa sun kasa ɗaukar sa, hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa yana mai ƙara zuba min idanu murya can a ƙasan maƙoshi ya ce.

"I'm not a kid Safnah, and I don't have time to waste, a yanxu dai kin fi sani na fiye da kowa, wannan yawan surutun ma da kike sakani ba ƙaramin ciwon kai ya ke sanya ni ba, just come in a straight way ki faɗamin miye ya ke ranki a kaina...."

Kai tsaye na ce.

" Na faɗa maka ina so muyi aure nan da wata ɗaya zuwa biyu shi ne matsaya ta"

Rintse idanuwansa yayi tare da girgiza kansa a hankali jin har ya fara masa ciwo.

Ta fi kowa sani cewa baya da yawan magana sannan kuma baya son yawan surutu, Safnar da ke fitowa su sha firar su ta soyayya cikin nutsuwa da zallar madarar soyayya yau ita ce ta ke iya tsayawa a gaban sa tana masa ihu tamkar zata fasa masa dodon kunne.

Girgiza kan sa yayi jin yanda ransa ya ke ƙara tsananta ɓaci idan yana ƙara tuna wa su abubuwa.

A hankali ya buɗe idanuwansa a kaina ya ce.

"Yanxu ya kike so a yi Safnah?"

Kai tsaye na ce.

"Ka faɗawa iyayen ka su zo wurin Baba a mayar da auren nan kusa kamar yanda na ce, sannan na sake tsara jadawalin kayan lefe na kuma ka tabbata an kawo su kafin bikin,..."

Katse numfashi na yayi yana mai ƙure ni da kallo ya ce.

"ko ɗaya ba za ki samu ba Safnah...."

Taɓe baki nayi tare da sakin wani malalacin murmushi sannan na ce.

" Mutumin da ya siyar da mashin ɗin sa ya sayi kwano aka rufe masa ɗaki biyu da parlour da kitchen gudun kada ruwan sama ya zube masa gini ai na san ba shi da halin aure nan da wata biyu, ga gidan kaji an yi asara, an kwashe jari baki ɗaya an sayi kaji sun zo sun mutu......"

Cikin wani sabon ɓacin rai ya sake kallo na ya ce.

"To kin san da haka amma ki ke min wa su zantukan banza. Look Safnah! Ka da ki bar tsawon shekarun da muka kwashe su je a banza please, dan Allah idan ma wani abu ki ke ji ko kuma wani ne ya ke hure miki kunne ki yi haƙuri ki daina sauraren su, Soyayyar gaskiya muka ƙulla ni da ke,kuma ke ce kike ganin shekara ɗaya a matsayin wani abu mai tsawo a gare ki, wanda idan kin kwantar da hankalinki kamar gobe ne za ki ga taxo..... "

Juyawa na yi kai na tsaye na shige gida ganin yanda kiran Naseer ke ta shigowa wayata ba ƙakkautawa.

A yanzu duk sanda nayi ido biyu da Xunnurain wallahi ji ni ke yana ɓata mini rai na. Mutum ba kowa ba sai shegen faɗin ran tsiya da nuna isa, kuma kai baka isa ɗin ba, ga shegen Jin ƙamshi da jan aji wanda da ƙyar ya ke buɗe baki yayi magana kamar wani sarki. Mtws!

Xunnurain ba ƙaramin shock ya shiga ba ganin irin bajen haukar da Safnah ta manna masa tayi shigewar ta gida.

Ya daɗe zaune a bakin wani dakali a Layin su sannan ya kira abokin sa Kanoma wanda shima gwauro ne kamar sa yace ya zo ya sauke sa a gida.

Ni kuma ina shiga na fara masifa na ce.

"Mama wai waye dan Allah ya tsayar da wancan shashashan a nan? Yazo sai wani nuna min izza ya ke tamkar wani ubana...."

Riƙe haɓa Mama ta yi cike da mamaki ta ce.

"Au! Daman bai tafi ba?"

"Ina ko ya tafi, maye kawai"

"Ina Deen ya ke? Shi fa na ce ya faɗa masa cewa bakya nan ya tafi sai gobe ba yanxu zaki dawo ba..."

Sai yanxu tunani ya harɓa a ƙwaƙwalwata cewa tabbas na hango takalmi a ƙofar parlourn Baba ta waje, cikin wani sabon ɓacin ran na ce.

"Ai kin san Deen munafukin Sa ne Mama, yanxu haka bai faɗa masa yanda kika gaya masa ɗin ba"

Daga haka na fito ban tsaya ko ina ba sai a tsakar parlourn.

Raina bai ƙara ɓaci ba sai da na kalle su na tabbatar da cewa sun cinye komai kaɗan ne suka rage wa su abubuwan. Ƙugu na riƙe cikin masifa na kalli Deen na ce.

"Ubanwa ya ba ku izinin ta ɓa wannan abincin?"

Naɗiɗiye ƙafafunsa Deen yayi tare da kallon Haris ya ce.

"Mun shigo mun tarar da mijin ki, na buɗe masa parlour na ce ya shigo, yace a'a, nayi ta kiran sa ina janyo masa hannu amma ya ƙi ya shigo, to shi ne muka ga abincin na shirin lalacewa muka cinye miki kada a yi a asara...."

Tsawa na daka masa na ce.

"Deen! Bana son iskancin banza, tun yaushe na sanar maka cewa wannan ba abincin Xunnurain ba ne?"

Miƙewa yayi a tsaye yana kallo na ya ce.

"Au! Haka ne? To idan ba nasa ba ne kenan na waye abincin? Sabon saurayi kika yi ko kuma ƙawayenki mata ne za su zo, idan mata ne miye na shirya musu abinci a parlourn waje? Idan kuma saurayi ne ai lokaci ya ƙure masa domin kuwa lokatun firar ki sun ƙare.... "

Wasu hawayen takai ci ne suka wan ke min fuska ta,Juyawa na yi kawai na yi shigewa ta gida domin ban san wata hujjar da zan ba shi ba. Idan ba haka ba yanxu sai mu fara sai da hali gaban Haris kuma ba iyawa zan yi da shi ba.

Deen shi ne ƙanina da ya ke bi na, mutum ne mai mugun zafi, duk da cewa ni ce a sama da shi tun muna yara ban taɓa buge shi idan muna faɗa ba, da muka fara girma kuma duka ya ke min sosai wani lokacin sai in wuni ina kuka, a yanxu kuma da hankali ya shige mu bama faɗa na haɗa ƙarfi domin ba zan ma fara ba sai dai muyi ta fatar baki, yayi mugun tsanar a ce masa ni ce yayar sa, duk da haka idan wani abun ya haɗamu sai dai in yi shiru in ƙyalesa.

OUM AMEER