KURURUWA A KUNNEN KURMA

6

by @oumameer2671

KURURUWA A KUNNEN KURMA 🥀 🥀

   A 2025NOVEL

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

     (OUM AMEER)

Wattpad:@ Ummu-Ameer

Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa

From d experience writer of:

Zaytoonah

Abarwa rai

Gudun wuce sa'a

Kibiyar so

Kulsum

Bahiyya

Nuudarr

& Now Kururuwa a kunnen kurma

Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏

FREE PAGE 6

   Tunda suka tsaya suna jinjina maganar Yah Umar uffan bai ce musu ba, sai ma kallon Yah AbdulMalik yayi ya ce.

"Abdul ina mukullan mota na?"

Miƙa masa yayi tare da wayar sa da ya baro a ciki, kawai ya juya bayan ya karɓa da nufin tafiya.

Hajiyar Xuhrah ce ta kalle shi ta ce.

"Umar ya naji baka ce komai ba"

Waigowa yayi ya kalle ta cike da rashin jindaɗin abin ya ce.

"Hajiya what should I say? Baba Hayatu da kuma Alhaji sun goya mata baya sun ce hakan ba laifi ba ne, kinga kuwa duk abinda zan yi ba zai yi tasiri ba, Miƙdad ma ya kira ni but na gaya mishi ba yanda zamuyi namu kawai kallo"

Shima AbdulMalik cikin takaici ya ce.

"Wallahi da ace a gabana ne Safnah tayi wannan furucin wallahi da sai na mammare ta, wannan ai iskanci ne da wulaƙalanci, mutum ya shekara huɗu yana jiranki rana tsaka ki watsa masa ƙasa a ido, miye laifin Usman? Mutum mai mutunci, ita ko don yanda yake mutunta iyayen ta da dangin ta ai ba kyautu ace ta yi masa haka ba "

Cike da alhini ta ce.

"Uh uhm Kai co! To Allah ya kyauta"

Hajiyar Aydah ta ce.

"To amin Hajiya Saratu, Allah ya kyauta mana ya sa mu dace"

Duk suka amsa da amin, daga nan kowa ya kama gabansa ya tafi wurin nasa yi.

                🪐🪐🪐

Alhaji Ibrahim shi ne yayan Alhaji Hayatu, su en asalin jihar Zamfara ne, Mahaifinsu Malam Nuru ya daɗe da rasuwa tun kafin Alhaji Hayatu yayi aure, bayan rasuwar sa ne da shekara biyu ya auri Hajiya Shafa'atu wadda itama er jahar Zamfara ce amma a ƙaramar hukumar Mafara,bayan haihuwar Sa'adu ne da wata uku kuma Mahaifiyar su wato (Hajiya Rabi'atu) ta ra su itama. Miƙdad shi ne babban ɗan su sannan Safnah sai Deen sannan auta sa'adu, dukkan su a nan suka yi primary suka yi secondary,Miƙdad kaɗai ne bayan ya gama secondary ya tafi shi da Abdulmalik India sukayo degree na likitanci, wanda shi Abdulmalik ya karanci fannin dentist yayin da shi Miƙdad ya karanci fannin surgery Bayan sun dawo kowa cikin ikon Allah sai ya samu aiki a jihar sa, daga baya shi Miƙdad ya koma ƙaro karatu

yayin da Abdulmalik ya ci gaba da aikinsa, Safnah kuwa a FCet tayi NCE, sai Deen da ke da certificate ɗin secondary kawai domin ya ce shi ba zai ɓata lokacin shi wurin boko ba, kowa ya ja da shi dole sun haƙura shiyasa sai ragamar shagon mahaifinsu na kasuwancin zinari da ke Polo ya zama a hannun sa ga shi fannin Addini ma ba shi da wasa, Deen Allah ya yi mai baiwa da ilmi, a fannin kasuwancin su ma shi ɗin lamba ɗaya ne, ga iya mu'amala da mutane tamkar wani babban mutum,

wanda har gobe Alhaji Hayatu ya na jin ciwo sosai a ransa na ƙin ci gaba da karatu da yayi, ko fannin islamiyya yana da kaifin hadda da basirar ɗaukar ilmin litattafai.

  Sai Kuma Sa'adu da ke degree yanxu fannin Engeering a ABU Zaria.

Alhaji Ibrahim kuwa, Hajiya Hindou ita ce uwar gidan sa wadda ta Haifi, Umar, Rabi'atu, sai kuma Aydah, sai Hajiya Saratu da ke bin Hajiya Hindou wadda ita ce mahaifiyar AbdulMalik, Xuhra sai kuma autan gidan gaba ɗaya Irfan wanda shi ne yake Jss2 a secondary.

      Family ne mai cike da haɗin kai da son zaman lafiya, babu wani bambanci a tsakanin su, Alhaji Ibrahim yana da kuɗi sosai domin ya fi Alhaji Hayatu kuɗi, yayi fice a fannin kasuwanci daban-daban wanda shi kuma Baba Hayatu ma'aikacin gwamnati ne sai shagon sai da zinari ɗaya da ya ke da shi. Dukkan yaran gidan daddy a ƙasar waje suka yi karatu fannin deegre sai ma Xuhra ce kaɗai wadda ta yi secondary a can sannan daga baya tayi degree fannin nursing a John's Hopkins university, school of nursing baltimore USA, yayinda Aydah ta karanci public healths a University of North Carolina at Greensboro (UNCG) da ke USA. A Last 7month da su gaba ta ne Xuhra ta dawo wanda a yanzu ta na service ne a nan Sokoto, ya yin da Aydah kuma saura mata 2 semesters ta kambala.......

                    🪐🪐🪐

  Komai tamkar a mafarki na ya ke zo min, kasancewar komai ya faru yanda muka tsara ni da Naseer babu wata hatsaniya da tashin hankali.

Cikin sati biyu aka saka mana rana nida Naseer, a sati na uku a kawo kayan an gani ana so da lefe gidan Daddy da ke Sokoto, akwatuna set ɗaya ne kamar yanda muka tsara komai an yi shi saffa-saffa.

    Yau ma tunda na tashi muka shiga hidima ni da Mama domin Naseer ya sanar min cewa na shirya na kuma gayawa su Mama cewa yana nan zuwa ya zo ya gaishe su.

Shiyasa na tashi tun asuba na shiga gyaran gida, ƙarfe goma na shirya na fita kasuwa wurin yin cefane.

  Sai kusan 12pm na dawo, ina shigowa muka hau aikace aikace wanda ko da ƙarfe uku ta buga na gama shirya komai parlorn Baba.

  Ina wurin wanka suka iso wanda Deen ne yayi musu jagora shi da abokin sa.

Bayan sun zauna Naseer ya kalli Deen ya ce.

"Deen?"

Gyaɗa masa kai Deen yayi ya ce.

"I'm Deen Hayatudden"

"Nice to meet you Malam Deen,Allah yasa ka yi na'am da ni?"

Ɗan Jim yayi yana mai nazari na en wasu seconds sannan daga baya yayi murmushin ya ce.

"Mi zai hana Deen yin na'am da kai bayan ita wadda ta zaɓe ka tayi na'am da kai, karka ji komai kar ka ji haufi you are highly welcome to our family, Allah ya sanya alheri da albarka a cikin rayuwar aurenku"

Cikin jin daɗi Naseer ya amsa da Amin. Daga nan Deen ya miƙe yana faɗin.

"Alhaji yana kasuwa but in sha Allah yanxu zan kira sa zai dawo"

Daga haka ya fice yana mai kiran Baba a wayar sa.

Ni kuma na jima sosai ina shirya wanda na ɓata lokaci wurin neman kayan da suka cancanta har sai da Mama ta shigo ta taimakamin.

Bayan na gama na je da sallama ta na shiga.

Kallona yayi from head to toe ya ce.

"Amaryar Naseer ta fara ƙyallin Amarci... Kaima Jabir Kaga hakan ko?"

Ya ƙarashe maganar yana mai kallon Abokin sa wanda ni shine farkon haɗuwa ta da shi.

Murmushi Wanda ya kira da Jabir yayi sannan ya bude bakin sa ya ce.

"Amarya kam tayi masha Allah! Allah ya nuna mana lokaci lafiya. Wato aboki na kasan irin kamun da kayi shiyasa ka nace cikin azama aka shirya komai domin kada kayi sake ayi maka sakkiya"

Cikin dariyar nan tasa mai kashe ni ya ci gaba da kallo na ya ce.

"Safnah is different Jabir"

A duk lokacin da naji ya furta wannan kalmar a gare ni ba ƙaramin farin ciki ta ke sanya ni ba.

Zaunawa nayi muka gaisa da su sannan daga baya na ba su wuri domin su ci abinci, but ko da na dawo ruwa kawai na tarar sun sha, wanda hakan bai min daɗi ba......

"Ya naga kamar kin ɓata rai Safnah ta?"

Ɗagowa nayi na kallesa na ce.

"Why would I burn my face bayan na sha wahala na yi maka girki amma baka ci ba"

Murmushi yayi ya ce.

"Da gaske ke kika dafa?"

Ganin na yi masa nodding ɗin kai na yasa shi sake sakin murmushi ya ce.

"To ɗauki plate ki zuba min kaɗan, amma ka da ki zubawa Jabir domin ba zai ci girkin ki ba sai kinje gidana"

Plate ɗin na ɗauka na zuba masa, wanda a gabana yayi 3 spoon ya ajiye ya ce min shima ba yanzu zai mori girkin ba sai bayan auren mu.

Ta shi na yi na je na kira masa Mama suka gaisa da ita, bayan sun gaisa ta shige gida ne Jabir shima ya tashi ya bamu wuri mu ka kasance mu biyu.

Kallona yayi ya ce.

"Safnah ki dawo ta nan a kusa dani ki zauna"

Ta shi nayi na koma gefen sa kamar yanda ya ce na zauna zuciya ta na wani irin bugawa ina ji wani sabon yanayi yana daɗa ninkuwa a zuciya ta.

Shiru ne ya ratsa tsakanin mu wanda kowa da abinda yake saƙawa a ransa.

Can bayan wa su mintuna ya ce.

"Safnah Hayatudden"

Ɗagowa nayi na kalle sa tare da amsa masa ina mai yin murmushi.

"Kada ki damu, kuɗi ko nawa ne ko sun kai adadin nawa kada ki ji komai ki tambaye ni, gaskiya is a slap on my face ace wai matar Naseer guda an ɗauki set ɗin akwati ɗaya jal an kai mata...."

"Kayi haƙuri, komai kake so ka yi zaka iya idan mun yi auren"

Gyaɗa kansa yayi yace.

"Hakane. To yanxu duk abinda kike buƙata ki faɗamin ko nawa kike so tun daga yanzu har lokacin bukin.... Ko da yake bari na baki kawai sai ki ajiye ba sai an tsaya wani lissafi ba"

Cikin jindaɗi na ce.

"Na gode sosai, Allah ya saka da alheri"

"Amin. Abu na gaba, na yanke a Sokoto zamu fara zama domin hankalin ki da na en uwanki ya ƙara kwantawa, sai dai bayan mun gama zaman da zamuyi ban sani ba tsakanin Kaduna, Abuja, Lagos ina kike so ki zauna?"

Cikin farin ciki na ce.

"Abuja ni ke so"

Gyaɗa kansa yayi ya ce.

"OK, an gama matar Naseer.."

Haka muka yi ta fira har sai da kiran Deen ya shigo wayata, bayan na ɗauka ya ce min ga shi sun zo tare da Baba.

Fita nayi na shigo da Baba, Naseer na ganin sa yayi saurin saukowa ƙasa ya zube ya shiga gaishe sa cikin mutuntawa wanda na ji daɗin hakan a raina ba kaɗan ba.

Bayan sun gama gaisawa baba ya shiga yi mana addu'a daga ƙarshe ya ta shi ya shige ciki. Ƙarfe biyar da rabi ya ta shi za su tafi na rakosa har ƙofar gida.... Turus nayi ganin Xunnurain a tsaye,wani murmushin dole na ƙaƙabo na ɗora akan fuskata gudun kada Naseer ɗin ya fahimci wani abu.

  Xunnurain......

Satin su ɗaya a Jigawa suka dawo, tunda ya dawo ya fita zancen Safnah, kullum Bilal cikin tambayar sa yake abinda yake damun sa amma bai taɓa buɗe baki yayi masa magana ba, sai jiya da ya nuna masa matuƙar ɓacin rai sannan ya buɗe baki ya gaya masa duk abunda ya faru.

Cike da zallar Mamaki kanoma ya shiga kallon sa, bayan ya gama ƙare masa kallo ne ya jinjina kai yace.

"Wai miyasa kai kullum miskilancin ka ƙara yin gaba yake? Tunda har kaji ta ce tana so kuyi aure da wuri haka something is wrong..."

Girgiza kansa yayi ya ce.

"Ta shirya wulaƙantani ne kawai Bilal.."

"Ni kuma what I think is that, ƙila akwai matsalar da ta ke damunta har ta saka take neman auren ku da wuri"

"Wace kalar matsala kenan Kanoma? Ciki tayi tana so ta shigar min da shi gidana ko kuma wani take so ta aura daban...."

Da sauri kanoma ya girgiza kansa ya ce.

"Allah ma ya kare, kafi kowa Sanin Safnah da kuma kalar tarbiyar gidan su ba zata aika ta maka hakaba, sannan kai kanka ka sa ni duk tsawon shekarun nan da kuka share bata taɓa attempting yin wani saurayi ba kai ɗin dai kai ne, saboda haka ni shawara ta a nan shi ne, tun da har abin ya zo a haka ka tura su Alhaji kamar yanda ta ce a dawo da auren naku baya, in ya so sai ka shiga gidana tunda ni ko budurwar banda ita, kuma ka kwantar da hankalin ka in sha Allah abun da za'a yi hidimar nan har a ƙare ba zai gagara ba, Allah ba zai bari muji kunya ba...... "

Da sauri Xunnurain ya girgiza kansa yace.

" Ba zai yi yu ba kan... "

" Hey! I know you with your stubbornness kada ka ce zaka yi min gardama a nan, just do what i said, idan kuma ba haka ba wallahi kaji na rantse maka da Allah daga na bar nan zanje na shaidawa Hajiya duk abinda ake ciki...."

Da sauri ya ce

" Shike nan naji "

He has no choice rather than yayi accepting maganar aminin nasa, idan ba haka ba, duk ya bari zancen nan ya kai kunnen Hajiya Sa'a akwai matsala domin ba za'a kwana ba sai ta lulluɓa ta je gidan,kuma a yanda yaga Safnah naji da ruwan rashin kunya idan har hajiya taje gidan su abin zai yi wani iri, sannan idan ta dawo duk wasu dangi da maƙota, da wanda zancen ya shafa da wanda bai shafa ba duk sai ta bi su ta faɗa musu, shiyasa ya ƙwammace ya ɗauki zancen kanoman kawai.....

Kallon sa Kanoma yayi da kyau ya ce.

" Ba zancen kaji ba, ka shirya gobe idan Allah ya kaimu kaje ku sasanta kanku daga nan sai ayi abinda ya dace, ba girman ku ba ne aikata irin wannan domin ku yanxu iyayene a soyayya kun girmi yin faɗa.... "

Ɗan guntun tsaki ya na mai squizing face ya ce.

" Malam maganar ka ta fiye yawa, please naji ka barni dan Allah "

Harararsa Kanoma yayi ya ce.

" Ka ga irin kalar tsiyar ta ka, shiyasa na ke so ayi auren nan da kai da Safnah domin ita kaɗai ce macenda zata iya zama da kai da irin kalar rayuwar ka. Usman please.... Ko da kaje dan Allah ka da ka biye ta kasan mata sai a hankali, dole tayi fushi tsawon wata ɗaya ka share ta saboda haka ka bata haƙuri kuma kace zaka yi duk abinda take so... "

Duk zubar nan da Kanoma ke yi idanun Xunnurain a rufe suke, kuma ba don wai yana bacci ba, duk abinda yake faɗa yana sauraren sa tsabar miskilanci ne kawai. Daga ƙarshe ma miƙewa yayi kawai yayi tafiyar sa gida.

Washe gari sai da ya je Wali's furnitures ya wuni, daga ƙarshe ya baro siddeeq ya dawo gida ya shirya bayan ya dawo masallacin Asr ya nufi gidan su Safnah cikin karsashin sa na nufin yunƙurin daidaita komai a tsakanin su,sai dai kash! Ganin wasu jibga jibgan motoci guda biyu a ƙofar gidan su sai ya karye masa zuciya, maimakon ya kira wayar ta gefe ya samu ya tsaya wani jikin gini yana mai bin motocin da kallo, bai fi minti ashirin da tsayuwa ba sai ga ta ta fito tare da wani mutum mai sanye da manyan kaya wanda kallo ɗaya yayi masa ya fahimci mai kuɗi ne na ƙarshe musamman yanayin kayan jikin sa.

Suna haɗa ido yaji wani irin muguwar faɗuwar gaba.

Sai dai lokaci ɗaya ya da ke tare da jingina jikin sa jikin gini ya harɗe hannayensa yana kallon su.

Ni kuma gabana sai faɗuwa ya ke ina addu'a a raina cewa 'Allah yasa kada Xunnurain ya zo nan ya kofsa min'

  Tsaye yayi kawai yana bin mu da ido wanda shi Naseer ma na fahimci bai lura da shi ba, ko bayan ya zauna a mota mun kai mintuna sha biyar muna gama sannan daga baya na yi musu sallama suka wuce, sai da suka ɓacewa ganina sannan na tako na zo na tsaya a gaban sa a wulaƙalance na buɗe baki da nufin yi masa tijara sai dai da sauri ya ɗagamin hannu, with so much heart broken ya ce.

"I understand Safnah! Wannan shi ne dalilin ki na duk wulaƙancin da kike min right?"

Taɓe baki nayi na ce.

"Ai na ɗauka zaka je gabansa ne ka tsaya ka tuhume sa"

Girgiza kai yayi yace.

"kinfi kowa sa ni Usman will never do that, but abu ɗaya nike so ki tuna Safnah; shekara huɗu na kwashe ina bautawa soyayyarki, ka da ki yarda wani ƙyalƙyali ya raba ni da ke don Allah, so ɗaya ni ke miki, ban taɓa son wata mace ba sai ke...."

Harararsa nayi na ce.

"Yanxu sai ka je ka fara, ni ma ai ban taɓa son wani ba sai kai daga baya kuma na je na fara wanda a yanzu auren mu saura kwanaki ne suka rage, ni da na daina ganinka na ɗauka ma ka haƙura ashe don rashin zuciya sai da ka dawo"

Cike da ɓacin rai ya ce.

"Ƙarya kike Safnah! Usman ne ni, ma'abocin haske biyu, ko don albarkacin mai sunan ubangiji na ba zai bari na wulakanta ba, nafi ƙarfin ki ce min bani da zuciya kin fi kowa sanin hakan, abinda yasa na dawo na ɗauka cewa gonar tawa ce har yanzu shiyasa na dawo, ashe ban san cewa ita gonar an sallamawa wani na ba kuma, but daga yau ki ɗauka cewa Xunnurain ya mutu har abada ba zai dawo ba... "

Gyaɗa kai na nayi na ce.

"That's very good of you, ina maka fatan alheri"

Har na juya sai naji ya kira sunana, ba tare da na waigo ba na tsaya turus alamar ina sauraren sa.

Wani kalar murmushi ya saki mai ciwo sannan yace.

"ki dai bi a hankali domin ba dukkan ƙyalli ba ne ya ke zama Zinari"

Wata dariya na saki mai sauti sannan na juyo na kalle sa na ce.

"Idan kuma ana a tsakiyar gonar ta, duk wani ƙyalli da zaka gani tabbas Zinarin ne ba bu wani haufi"

"Fatan nasara Safnah Hayatudden"

"kai ma haka, Usman Shaheed"

Har na juya ya sake kiran sunana a karo na biyu.

Waigowa na yi kacokam na zo na tsaya a gabansa ina mai sakin wani murmushi na ce.

"Lafiya Malam Xunnurain? Ko so ka ke tunda zaka mutu kayi min kallon ƙarshe yanda hoton fuskata ba zai ɓace maka ba?"

Wani irin zafi ne da raɗaɗi yaji sun ziyarci zuciyar sa a lokaci ɗaya,

Wani karyayyen kallo  ya bini da shi har sai da na tsora ta na ja baya

Murya a raunane ya ce.

" Kin illata zuciya ta da guba mafi muni Safnah, ba zan yi fatan sharri a gareki ba, domin nima ina da ƙanne mata da yawa kamar ke, ki je Allah yasa hakan shi ne mafi alheri a tsakanin mu"

Murguɗa masa baki nayi sannan na yi shigewata gida.

 

 

              OUM AMEER