ƳAR KARUWA Chapter 1
*ƳAR KARUWA* Arewabooks@ayshadansabo
Paid book
©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
Chapter 1
Dukkanin yabo da kuma godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin sammai da ƙassai,wanda ya bani ikon fara wannan rubutu mai suna a sama.Ina roƙo Ubangiji ya bani ikon rubuta daidai ya kuma yafe kura-kuran da za su samu a cikin labarin.Sannan ina kira ga makaranta labarin ƳAR KARUWA da su sani cewa labarin dukkaninsa ƙirƙirarran labari ne mallakar marubuciyar,don haka duk wacce ko wanda labarin yayi kamanceceniya da rayuwarta ko nasa to arashi aka samu.Har ila yau kuma ina sake kira da babbar murya cewa,a guji sarrafa ko juya mini wannan labari ta wani salo na daban ko karanta shi a kowani kafar sadarwa ba tare da izini na ba.Ina fata kuma makaranta za su amshi wannan labari tare da yin tururuwa wajen mallakarsa ta hanyar saka kuɗi su saya domin jin cikakken saƙon da ya ƙunsa,daga ƙarshe ina ma dukkanin masoyana fatan alkhairy a ko'ina suke a faɗin duniya,kuma ina alfahari daku da irin ƙaunar da kuke nuna wa rubutuna.
**********
"Jannat kiyi haƙuri ki rungumi wannan al'amari daya faru a matsayin ƙaddara wanda ya riga fata,Allah bai yi nufin ke da shi za ku zama ma'aurata bane,ki gane cewa komi muƙaddari ne daga Allah kin ji ko?" Kyakykyawar farar tsohuwar mai kimanin shekaru sittin da bakwai a duniya take furta waɗannan kalaman hannunta riƙe dana kyakykyawar budurwar dake kwance a jikinta tana kuka sosai cikin ƙaramin sauti.
Budurwar wacce kalar fatarta ya kasance wankan tarwaɗa tana da matuƙar kyawu da zubin halitta,a shekaru ba za ta haura shekaru sha takwas a duniya ba,ta sake shigewa cikin jikin tsohuwar tana cigaba da kukanta silently,cikin muryar kukan kuma take faɗin, "Na amshi ƙaddarata Inna,wallahi na amsa da hannu bibiyu,ina kuka ne na tausayin kaina da irin baƙin fentin da ke bibiyar rayuwata yana rusa dukkanin farin cikina,ina kuka ne na baƙin cikin kasancewar Ummu a matsayin wacce ta kawoni duniya In...." Kukan da ya sake cin ƙarfinta ne ya hanata ƙarisa kalamanta,ta sake shigewa cikin jikin tsohuwar tana jin yadda jiki da zuciyarta ke sake ɗaukar rawa.Ganin hakan ya sanya tsohuwar sake rungumarta sosai a cikin jikinta ta shiga shafa bayanta a hankali alamun rarrashi,sai dai kafin ta sake buɗe baki tayi magana suka jiyo sallama daga can cikin falon Innar.Tsohuwar ta ɗaga murya ta amsa sallamar tare da zarcewa da faɗin, "Shigo Muhammadu gamu nan a cikin ɗakin baccina." Ba a rufa mintuna biyu ba sai ga muryar wanda ta kira da Muhammadun na sake doka sallama daga bakin ƙofar shigowa bedroom ɗin,Hajiya Inna ta amsa masa sallamar tare da bashi izinin shigowa.Cikin nutsuwa ya sanyo kansa cikin ɗakin idanunsa na sauka akan Jannat da har lokacin ke naɗe a cikin jikin Innar tana kuka silently,Hajiya Inna ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan ingarman magidancin ɗan nata mai shekaru hamsin a duniya,kyakykyawan Dattijo ne na gaske,baƙi mai ɗauke da wani irin kwarjini da cikar da haiba a saman fuskarsa.Sosai ya ɗebo kamannin Inna a saman fuskarsa ta yadda a kallo ɗaya za ka yi musu shi da ita kasan cewa ita da shi Uwa da Ɗa ne,a hankali ya ke takawa har zuwa bakin bed ɗin da Innar ke zaune yana faɗin, "Subhanallah! Mamana har yanzu dai kukan yaƙi ƙarewa ne? Meyasa ba za ki yi haƙuri ki rungumi duk abinda ya faru a matsayin ƙaddara ba? Maza tashi ki sanar dani miye damuwar a halin yanzu kin ji ko?" Ya ƙare maganar yana kaiwa zaune kusa da Innar.Jannat jin muryarsa kaɗai ya sake karya zuciyarta,ta saki wani marayan kuka tana tashi daga jikin Inna ta ɗaga manyan idanunta dake zubda da ruwan hawaye ta sauke a kansa.Ganin yadda ya kafeta da ido ya sanya tayi saurin isa zuwa garesa tare da faɗawa jikinsa tana sake sakin kuka mai cin rai,shi kuma sai ya yi saurin rungumarta yana faɗin, "It's okey my daughter,kiyi haƙuri ki daure ki amshi komi a matsayin ƙaddara wanda ya riga fata,Allah bai yi nufin wani al'amari zai ƙullu a tsakaninki ke da shi bane kin ji ko?" Jannat ta gyaɗa kanta dake kwance bisa kafaɗunsa ba tare da ta iya cewa komi ba.
Ya miƙa hannu a nutse ya ɗago face ɗinta tare da fara share mata ruwan hawayen da suka kasa tsaya mata, "Kin ci abinci?" Ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta yana jin tarin ƙauna da tausayinta na sake yiwa zuciyarsa yawa.Hajiya Inna ita ce ta bashi amsar tambayar da cewa, "Ina fa taci abinci,yanzu dai nake ta faman na samu tayi shiruma mu fita ta ci abincin sai ta sha magani,sabida likita ya ce kada ayi wasa da shan maganinta akan lokaci." Ta ƙare maganar fuskarta na sake bayyana tsantsar damuwar dake cikin zuciyarta. "Mamana tashi mu je side ɗina muci abincin tare nima banyi dinner ba,akwai nama da fura ai za ki ci ko?" Ya jefawa Jannat tambayar yana ɗagota zaune sosai tare da kafeta da kaifafan idanunsa.A hankali ta buɗe baki ta ce, "Abbah bana jin cin komi ne bakina ma ɗaci yake mini." Abban ya miƙe yana sake duban yadda duk ta rame cikin kwanaki bakwai kacal da fasa maganar aurenta da Aliyu ɗin.Cikin muryar rarrashi ya ce, "Daurewa za ki yi daughter kici ko ba yawa ne,oya sakko ki saka hijab mu je idan kin gama sai na maidoki wajen innarki,Inna bani magungunan nata ta sha a can ɗin." Ya ƙare maganar yana maida dubansa kan Inna da itama nata idanun ke kansa tana sake jin alfahari da shi a cikin zuciyarta.Soyayyar da yake gwadawa Jannat da yadda ya riƙe amanar maraicinta na faranta ranta a duk kwanan duniya,sosai take ji a jikinta cewa ko bayan ranta Abban ba zai taɓa barin jinin ɗan uwansa ta wulaƙanta a doran ƙasa ba.Ta miƙe a nutse ta ɗakko masa ledar magungunan dake aje saman drawer ɗin jikin gadonta ta miƙa masa,ya amsa yana duban Hafsatu da ta nufi wajen sofar dake ɗakin Innar ta ɗauki hijab ta saka. "Ki daure Hafsatu ki sha koda furar ce idan abincin yaƙi ciwuwa miki kin ji ko? Allah zai baki dangana ya kuma kawo miki mafi alkhairyn da za a ɗaura dashi In Sha Allah!" Cewar Hajiya Inna idanunta akan Hafsatu da ta nufi wajen da Abban ke tsaye yana jiranta.Ya riƙo hannunta ya sanya cikin nasa time ɗin da ta gyaɗawa Inna kai alamun ta amsa maganarta,sai Innar ta saki murmushi ta ce, "Sai kun dawo kada dai kace za ka barta wajen makirar matarka don ba kulawa da ita za ta yi ba." Abban ya dubi Innar fuskarsa na haskawa da wani yanayi ya ce, "Zan maidota Inna karki damu." Daga haka suka fice daga cikin ɗakin yana riƙe da hannun Jannat,ɗaya hannunsa kuma riƙe da ledar magungunanta.Tafe suke yana faman sake rarrashinta da bata baki har suka fito zuwa asalin compound ɗin ƙaton gidan nasa da ya gaji da tsaruwa,ko'ina hasken fararen fitullu ne tarwai kamar rana ba dare ba.Suka cigaba da takawa sannu a hankali har suka isa ga ƙofar isa falonsa ta baya,ya sanya key ya buɗe ƙofar suka sanya kansu cikin rantsatstsen falonsa dake downstairs ɗin domin ginin ɓangarensa bene ne.Idanun Hafsatu suka fara sauka akan Hajiya Mardiyyah da ke kame cikin kujerar 2 seater na rantsatstsun Turkish chairs da sukai ma falon ƙawanya,ta ci ado cikin wata haɗaɗɗiyar riga da wando na bacci masu santsi da ɗaukar idanu.Sai dai daga samansu ta ɗaura wata kimono data rufe shigar sai daga gaba ne kawai take a buɗe ta yadda ake iya hango shigar da ke ciki ɗin,ɗagowa Hajiya Mardiyyah tayi cike da zumuɗi domin amsa sallamar mijin nata da take dakon shigowarsa.Idanunta suka sauka a kansu su biyu shi da halittar da take jin tsanarta fiye da komi a duniya,nan da nan annurin dake saman fuskarta ta ɓace ɓat! Tayi saurin ɗauke dubanta daga garesu ta mayar kan makeken smartTV ɗin dake kunne yana aiki.Abba hannunsa har lokacin riƙe dana Jannat suka fara takawa zuwa cikin falon bayan ya jiyo yadda Mamien ta amsa sallamar tasa a ciki-ciki,bai nuna ya fahimci canjin da ya gani a saman fuskarta ba don kawai ta gansa tare da ƴarsa ya nufi bakin 3 seater ɗin dake daura da inda take zaune ya zaunar da Hafsatu yana faɗin, "Yauwa daughter zauna,jirani na shiga ɗaki na fito sai mu nufi dining ko kuma ma wife a sakko min da abinci daga saman dining zuwa nan tsakiyar falo please!" Ya ƙare maganar idanunsa akan Hajiya Mardiyyah da ta ɗago tana dubansa da wani irin kallo,ya sake tamke fuskarsa babu alamun wasa ya kuma faɗin, "Ki ɗakko ruwa mara sanyi daughter za ta sha magani dashi." Daga haka ya juya ya nufi stairs ɗin da zai sada shi da ɗakin barcinsa dake sama cikin nutsatstsen takunsa mai cike da aji da ginshira.Mami Hajiya Mardiyyah sai ta haɗiyi wani miyau mai kauri tana rakashi da idanunta har ya ɓacewa ganinta,a hankali ta maido dubanta kan Hafsatu da kanta ke ƙasa tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa."Mami ina yini." Tayi saurin furta gaisuwar a ɗarare domin tafi kowa sanin cewa Mami bata yinta ko kaɗan a gidan,hasalima tayi mata wata iriyar mugunyar tsanar da ko kaɗan bata ƙaunar ma suyi inuwa ɗaya da Mamin.Mamin bata amsa gaisuwar tata ba illa wani mugun tsaki da ta saki kafin ta kaurara harshenta tana faɗin, "Uban me ya hanaki zama acan sashin kici abincin har sai kin biyoshi nan ɗin? Wai shin a kanki aka fara sanya ranar aure a kuma rusashi da za ki addabi kanki ki addabi wasu ki hana kowa sukuni da koke-koke? Indai sanya ranar aure a fasa ne yanzu kika fara gani matuƙar Nuratu ce ta kawoki duniya domin babu macen arziƙi kuma ƴar gidan mutunci da za ta so jininta ya gauraya dana ƳAR KARUWA irinki,Karuwar ma shahararriyar da ta kewaye dukkanin ƙasashen duniya wajen yawon bariki,don haka idan ma za ki naɗa gammon ɗaukar duk wani tozarci da gori gwara ki naɗa ki daina tashin hankalin mijina yana lalacewa a kanki wajen rarrashi,da kin ɗauka cewa kasancewarki nutsatstsiya wacce ta ƙware a iyayi da gwalli na munafurcin da kika tsotsa a jikin KARUWAR UWARKI shi zai sanya ko wani namiji ya raɓeki Iyayensa su amince da ke? To ina so ki rubuta ki aje cewa duk wani namijin da Iyayensa suka san zafi da ciwonsa ba za su taɓa so ya raɓeki ba domin ke ɗin jinin tsiyace,ƳAR KARU....." Kalamanta suka maƙale a lokacin da Alhaji Muhammad Mansur Chiroma ke sakkowa daga stairs ɗin benan.Ta yi wuf ta wuce zuwa ɓangaren dining ɗin ba tare da ta san cewa kalamanta na ƙarshe da suka maƙale a kunnuwarsa taso ƙarisa su ba.Cikin tsananin ɓacin rai ya ja ƙaramin ƙwafa tare da ƙoƙarin haɗiye fushinsa,domin ko kaɗan bayi ƙaunar wannan baƙin halin da rashin ƙaunar da Mardiyyah ke gwadawa Marainiyar Allah.Koda ya ƙarisa sakkowa ya nufi wajen da Jannat ke zaune ya samu tana kuka ne sosai cikin ƙaramin sautin da sai wanda ya matso kusa da ita zai iya jiyo sautin fitarsa,ya sanya hannuwansa duka biyu ya rungumota zuwa jikinsa yana faɗin, "It's okey Mamana,kiyi haƙuri komi mai wucewa ne kinji ko? Bana so ki aje komi a cikin zuciyarki domin babu abinda ke dauwama,kuma ko wani bawa da irin tasa kalar ƙaddarar don haka ina so ki zama mai ƙarfin zuciya kinji ko?" Cikin rishin kuka Hafsatu ta jinjina masa kanta tana ƙoƙarin haɗiye sabon kukan da ya taho mata.Hannunta Abban ke murzawa alamun rarrashi yana sake bata baki har Mami ta fara kawo warmers ɗin abincin tana jeresu daga ƙasan tsakiyar lallausar carfet ɗin bayan ta shinfiɗa ledar cin abinci a sama,bai ko kalli inda take ba ya cigaba da rarrashin Hafsatu har ya samu ta tsaida kukan baki ɗaya.Suka sauka zuwa ƙasan carfet ɗin yana riƙe da hannunta,daidai kuma lokacin Mami ta aje haɗaɗɗen jug ɗin da ta juye lafiyayyiyar damammiyar furar da ya shigo dashi daga inda ya saba siyowa.Ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Mamin kafin ya buɗe baki a dake ya ce, "Oya zuba min abincin sai ki juye gasasshen naman can a plate,ki ɗibi naki ki bamu waje domin bana buƙatar damuwa zan lallashi ɗiyata ta ci abinci tunda ke har yau baki da zuciyar imani da tausayin jin ƙan maraya Mardiyyah." Kalamansa suka dira a kunnuwar Mami tare da kaɗa zuciyarta suna sake haifar mata da jin zazzafar tsanar Jannat a cikin jininta,ba tun yau ya saɓa yaɓa mata zafafan kalamai akan rashin ƙaunar da take gwadawa Hafsatun ba,amma sai ta ji na yau ɗin yayi mata ciwo matuƙa.Cikin wani irin karyayyen sauti ta dubesa tana faɗin, "Abban Arfah ni ce yau kake kira da mara imani?" Cike da sake kausasa murya ya ce, "Na faɗa ɗin,ke ɗin mara imani ce Mardiyyah domin ban taɓa cin karo da macen da bata jin tausayin maraya irinki ba,ina sane da dukkanin rashin imanin da kika gwadawa Mamana akan wasu dalilanki marasa tushe bare makama,akan dalilan da ko yau naso cika burina zan auro in shigo da ita cikin gidana ko kina so ko ba kya so,don haka ki bi a sannu ki kuma kiyayeni kin ji na gaya miki domin duk wanda ya nemi cutar da Mamana a gidannan to wallahi mun dinga sanya ƙafar wando ɗaya dashi kenan,oya maza ki kammala aikinki ki bamu wuri." Ya ƙare maganar daidai time ɗin da wayarsa ta fara tsuwwa,hakan ya sanya Mami bata samu damar cewa komi ba illa cika umurninsa ta fara zuba lafiyayyar brown spaghetti da ya ji veggies da tsokar naman kaza.Daga gefe guda ta zuba haɗin salad da yaji kayan haɗi har da yankakkun green apples a ciki,ta tura zuwa gabansa tana sake ɗaukar wani plate ɗin ta juye gashin naman da ke turiri yana fidda wani azababban ƙamshin spices.Aroma ɗin naman kawai ya tashi kanta har ta ji miyanta na tsinkewa,hakan ya sanya ta rage kaɗan wanda za ta ci bata juye duka ba kamar dai yadda ya ce ɗin.A fusace ta miƙe ɗauke da foil paper ɗin da aka naɗe naman ta nufi hanyar shigewa ɓangarenta ta cikin falon,har lokacin Abban waya yake cikin harshen nasara da yake ɗan surkawa da yaren hausa kaɗan-kaɗan.
Jannat ce ta raka Mamin da ido tana sake jin zuciyarta na karyewa,tsoron Mamin da shakkarta kullum kwanan duniya sake ƙaruwa suke a cikin zuciyarta.Tana tsananin son taga Mamin ta daina hantararta da kuma nuna mata tsana amma hakan ya ci tura,kullum tamkar ana ƙarawa wutan fetur ne akan irin tsanar da Mamin ke gwada mata duk kwanan duniya.Maganar Abba ne ya maido da ita hayyacinta time ɗin da ya kammala wayar ya furta, "Bismillah daughter maza ɗauki spoon mu ci abinci kinga ba mai nauyi bane ga kuma salad da kike so a ciki ko?" Hafsatu sai ta kasa yi masa musu domin har cikin zuciyarta take jin ƙaunarsa da kuma alfaharin yadda ya riƙeta tamkar ɗiyar cikinsa.Tunda ta taso tayi wayau shi take kallo a matsayin mahaifin da ya kawota duniya har zuwa time ɗin da ta gane cewa Ubanta rasuwa yayi shi Abban Arfah Yayan Abbanta ne amma ba shine ya haifeta ba,wanda a ranar tayi kuka mai yawa amma kuma sai sam bata ji maraicin rashin Uba ba domin duk wani gata da kulawa haɗi da ƙauna da soyayyar da ke tsakanin Uba da Ƴarsa Abba ya gama gwada mata har ma fiye da yadda idan nata Abban na raye zai gwada mata ɗin.Ta ɗauki spoon a sanyaye ta ɗebo lomar abincin ta kai bakinta,suka haɗa idanu da Abban ya sakar mata kyakykyawar murmushi tare da jinjina mata kansa alamun hakan yake so........✍🏻