FreeArewaPen original
ƳAR KARUWA PART 1
- 1views
- 25chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Am so proud to be a hausa writer.
Sample · ƳAR KARUWA Chapter 1
*ƳAR KARUWA* Arewabooks@ayshadansabo Paid book ©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻 Chapter 1 Dukkanin yabo da kuma godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin sammai da ƙassai,wanda ya bani ikon fara wannan rubutu mai suna a sama.Ina roƙo Ubangiji ya bani ikon rubuta daidai ya kuma yafe kura-kuran da za su samu a cikin labarin.Sannan ina kira ga makaranta labarin ƳAR KARUWA da su sani cewa labarin dukkaninsa ƙirƙirarran labari ne mallakar marubuciyar,don haka duk wacce ko wanda labarin yayi kamanceceniya da rayuwarta ko nasa to arashi aka samu.Har ila yau kuma ina sake kira da babbar murya cewa,a guji sarrafa ko juya mini wannan labari ta wani salo na daban ko karanta shi a kowani kafar sadarwa ba tare da izini na ba.Ina fata kuma makaranta za su amshi wannan labari tare da yin tururuwa wajen mallakarsa ta hanyar saka kuɗi su saya domin jin cikakken saƙon da ya ƙunsa,daga ƙarshe ina ma dukkanin masoyana fatan alkhairy a ko'ina suke a faɗin duniya,kuma ina alfahari daku da irin ƙaunar da kuke nuna wa rubutuna. **********"Jannat kiyi haƙuri ki rungumi wannan al'amari daya faru a matsayin ƙaddara wanda ya riga fata,Allah bai yi nufin ke da shi za ku zama ma'aurata bane,ki gane cewa komi muƙaddari ne daga Allah kin ji ko?" Kyakykyawar farar tsohuwar mai kimanin shekaru sittin da bakwai a duniya take furta waɗannan kalaman hannunta riƙe dana kyakykyawar budurwar dake kwance a jikinta tana kuka sosai cikin ƙaramin sauti.Budurwar wacce kalar fatarta ya kasance wankan tarwaɗa tana da matuƙar kyawu da zubin halitta,a shekaru ba za ta haura shekaru sha takwas a duniya ba,ta sake shigewa cikin jikin tsohuwar tana cigaba da kukanta silently,cikin muryar kukan kuma take faɗin, "Na amshi ƙaddarata Inna,wallahi na amsa da hannu bibiyu,ina kuka ne na tausayin kaina da irin baƙin fentin da ke bibiyar rayuwata yana rusa dukkanin farin cikina,ina kuka ne na baƙin cikin kasancewar Ummu a matsayin wacce ta kawoni duniya In...." Kukan da ya sake cin ƙarfinta ne ya hanata ƙarisa kalamanta,ta sake shigewa cikin jikin tsohuwar tana jin yadda jiki da zuciyarta ke sake ɗaukar rawa.Ganin hakan ya sanya tsohuwar sake rungumarta sosai a cikin jikinta ta shiga shafa bayanta a hankali alamun rarrashi,sai dai kafin ta sake buɗe baki tayi magana suka jiyo sallama daga can cikin falon Innar.Tsohuwar ta ɗaga murya ta amsa sallamar tare da zarcewa da faɗin, "Shigo Muhammadu gamu nan a cikin ɗakin baccina." Ba a rufa mintuna biyu ba sai ga muryar wanda ta kira da Muhammadun na sake doka sallama daga bakin ƙofar shigowa bedroom ɗin,Hajiya Inna ta amsa masa sallamar tare da bashi izinin shigowa.Cikin nutsuwa ya sanyo kansa cikin ɗakin idanunsa na sauka akan Jannat da har lokacin ke naɗe a cikin jikin Innar tana kuka silently,Hajiya Inna ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan ingarman magidancin ɗan ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.