AMATURRAHAMAN

33

by @oumfatima33

💞💞💞💞💞💞💞💞

*AMATURRAHAMAN*

_*By*_

*_OUM FATIMA_*

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

💞💞💞💞💞💞💞💞

_*DASHEN🌲ALLAH*_

_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_

_*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_

*BOOK 1*

*PAGE 33*

_*بسم الله الر حمن الر حيم*_

"Ba wani wanda zai taimakeni ne wai don Allah!." Amaturrahaman ta faɗa cikin tashin hankali tana ɗaga murya. A hankali mutane suka riƙa zame wa kowa ya kama gabansa yana faɗar abinda yaga dama game da lamarin.

Wani irin matsanancin kuka ne ya ƙwacewa Amaturrahaman ta shiga rusa shi da ƙarfi tamkar ranta zai fita, kuka take tana surutai da neman ɗauki a taimaketa ta kai ƴar'uwarta asibiti kar ta rasata. "Don Allah na roƙeku wani ya taimaka min mu kaita asibiti kar na rasata itama, rayuwata bata da amfani idan bata tare da ni, ita kaɗai gareni don Allah!". Ta ƙare maganar muryarta na siƙewa tsabar yanda take kuka da neman taimako.

Amma saboda tsabar rashin tausayi da bushewar zuciya irin na al'ummarmu a yanzu kowa sai dai ya bita da ido suna faɗar magana mara daɗi a kanta. Suna sukarta da cewar garin yawon iskancinta ta janyo abinda yafi ƙarfin kanta, yanzu ga abinda ya faru nan dan haka ba wanda zai taɓata suje su san yanda zasuyi ita da ƙanwarta mai azabar girman kai.

So take ta rungumeta tayi mukan a jikinta anma ba damar hakan saboda babu inda bai ƙone ba a jikinta, koda Amaturrahaman taga ba mai ƙoƙarin taimakonta a wurin sai ta miƙe tana layi domin neman abin hawan da zai kai su asibiti. Sai dai tana miƙewa jiri ya kwasheta ta zube ƙasa a sume.

A kuma dai-dai lokacin ne motar Muzaffar da shigowarsa kenan zaije gidan gonar Yayansa domin duba lissafin ƙarshen shekara da aka haɗa kasancewar shine lauyan yayan nasa kuma shike kula da duk wani Kasuwancinsa na nan Nigeria, so yake ya ganta shi yasa kai tsaye ya nufi hanyar gidansu da niyar idan ya ganta sai yaje gidan gonar yayi abinda ya kawo shi garin. Sai dai yana tsaya a ƙofar gidan ganin taron mutane an zagaye Amah data faɗi yasa shi fitowa da sauri ya nufi wurin yana tambayar abinda ke faruwa.

Yana isa wurin yaci karo da Amaturrahaman ta suma sai kuma wata daya gani a babbake shimfiɗe saman tabarmar kaba kusa da Amaturrahaman ɗin.

"Subhanallah! Wai mike faruwa a nan?." Ya tambaya cikin tashin hankali yana kallon mutanen dake wurin.

Ganin da aka masa tsaf dashi da kuma irin motar daya zo da ita yasa aka shiga zayyane masa abinda ya faru. Cikin kaɗuwar da yayi jin wai Ya Nafi Amaturrahaman ce wanna ta zama haka yace.

"Kuma shine ba wanda yayi ƙoƙarin kaisu asibiti kuka zagaye su kuna kallonsu saboda rashin imani!". Ya faɗa a fusace yana ƙarewa mutanen wurin kallo kafin ya nufi motarsa ya ɗauko robar ruwa ya dawo ya yayyafawa Amaturrahaman saman fuskarta.

A firgice ta farka tana ƙwala kiran sunan Ya Nafi "Relax, ki natsu kinji ko, yanzu zamu kaita asibiti zata samu lafiya in sha Allah." Muzaffar ya faɗa yana riƙo hannun Amaturrahaman dake ƙoƙarin zubawa da gudu.

"Yauwa gatanan mu kaita asibiti, don Allah ka taimake ni mu kaita asibiti kar in rasata!". Tayi maganar cikin zautuwa tana riƙo hannunsa ba tare da damuwa da hakan ba saboda a rikice take bata cikin hayyacinta.

"Wani ya kama min mana mu sakata a mota!." Ya faɗa cikin daka tsawa. Cikin borin kunya wasu daga cikin mutanen wurin suka kama tabarmar aka sakata a bayan motar, gefen mai zaman banza ya buɗewa Amaturrahaman ta shiga ya zagaya da sauri ya shiga mazaunin direba yaja motar da matsiyacin gudu suka fice daga layin.

Kai tsaye babban asibitin dake cikin Matazu ya nufa dasu duk da yaso wucewa Katsina dasu saboda yanda abin ya munana, amma ya yanke shawarar fara kaisu na kusa domin a rage mata raɗaɗin da take ji ko yaya ne. Ƙure gudun motarsa yayi wanda cikin ƙanƙanin lokaci suka isa Asibitin inda aka amsheta aka shiga da ita. Kai kawo kawai suke yi a gaban ɗakin da ake dubata yayinda Amaturrahaman ke ribzar kuka na fitar hayyaci wanda ko sautinsa ba'a ji.

Muzaffar dake cikin tashin hankali shima ba irin rarrashin da bai yi mata ba amma bata ko iya kallonsa ba. Sai da likitoci suka kwashe tsawon awanni kafin lokacin su fara fitowa. A sukwane suka nufi likitan daya fara fitowa don jin halin da take ciki.

"Muje Office muyi magana." Ya faɗa yana yin gaba sauran likitocin na mara masa baya, su Amaturrahaman ma bayansu suka bi.

Sai da suka gama tattaunawa a tsakaninsu sannan aka buƙaci ganin Muzaffar, duk yanda yaso Amaturrahaman ta jira shi a waje ƙiyawa tayi, dole ya rabu da ita suka shiga tare. Bayani babban likita ya fara musu kamar haka.

"A gaskiya ƙunar tayi mata illah sosai saboda babu inda bai ƙone ba a jikinta, gaba ɗaya naman jiƙanta ya ƙone don da kansa ma zuba yake. A matsayinmu na likitoci munyi iya abinda zamu iya sauran kuma mun barwa Allah. Sai dai kuma zaku iya fitar da ita waje akwai ƙasashen da suka ƙware sosai a wannan aikin, so idan kuna buƙata zaku iya fitar da ita amma kafin nan zamu yi muku transfer zuwa Asibitin babbar riga domin a bata kulawar da ta dace." Ya ƙare maganar yana kallon Muzaffar.

"Doctor don Allah kuyi mata duk abinda ya dace zamu biya ko nawa ake buƙata, nidai ta samu lafiya kawai nake so!." Amaturrahaman ta faɗa cikin kuka wanda sai a lokacin wasu kyikitocin suka lura da ita saboda a bayan Muzaffar ta laɓe.

Cikin sauri Muzaffar ya amshe zancen da cewa " Eh doctor zamu iya fitar da ita, sai a bincika mana asibitin daya dace mu kaita."

"Ok ba matsala za'a bincika." Doctor ya faɗa yana miƙawa Muzaffar bill's ɗin da zai je yayi settiling, amsa yayi ba musu yaje ya biya tarin kuɗaɗen da aka rubuta ba tare da jin ko ɗar akan hakan ba. Amaturrahaman kuwa na tsaye a wurin daya barta yace ta jira shi yana zuwa.

A nan ya sameta zaune tayi tagumi abin tausayi, gaba ɗaya farin hijabin uniform ɗin nata ya ɓaci da jirwayen hawaye da abin baƙin kwalli da take sakawa idanunta. "Ki tashi in kaiki gida ki canza kaya kici wani abu sai in dawo dake." Muzaffar ya faɗa mata cikin tausasawa.

"A'a ba zan iya tafiya ba, ina son ganinta ne." Ta faɗa da shaƙaƙƙiyar muryarta wacce da ƙyar take fita. Lallaɓata ya shiga yi amma ta ƙiya saboda dama can tana da taurin kai. Izinin likitocin ya nema akan su barta ta ganta hankalinta ya kwanta.

Izini aka basu suka shiga ɗakin har tana tuntuɓe, a kwance ta hango Ya Nafinta wacce aka naɗe jikinta gaba ɗaya da bandage har fuskarta. Wasu sabbin hawayen ne suka sauko mata yayinda take tsinewa duk wani mai saka hannu a cikin saka ƴar'uwarta a wannan bala'in. Take kuma cin alwashin ɗaiɗaita rayuwar kosu waye koda kuwa ace duka duniya gatansu ce.

Kusa da kanta ta matsa tayi mata addu'oi sosai tana nema mata sauƙin raɗaɗin da tasan ya addabeta har a cikin barcin da aka sakata yi. Da ƙyar Muzaffar ya lallaɓata suka wuce da nufin zai maido ta idan ta kintsa taci wani abin.

A ƙofar gidan yayi parking ta fita jiki ba ƙwari, take away ɗin daya biya ya sayo mata ya miƙa mata sannan ya ɗauki ɗayar wayarsa ya miƙa mata yace "Idan kin gama sai ki kirani." Ya faɗa yana nuna mata number da zata kira.

Kai kawai ta ɗaga masa ta shige zauren gidan da take jin tamkar ta zuba fetur ta kunna wuta ta babbaka uban kowa tsabar yanda take jin tsanar mutanen gidan gaba ɗaya. Kamar yanda suka saba zama a ƙasan bishiya da sunan yin hira wacce rabi gulma da zagin mutane ne.

Yanzu ma a nan ta same su wanda tana shiga gaba ɗaya suka zuba mata ido suna jiran jin abinda zata faɗa, Aunty Rakiya ce ta miƙe tsaye ta nufota ta buɗe baki zata yi magana. Wani mugun kallo mai cike da tsana, mai bayyana gargaɗi Amaturrahaman ta watsa mata wanda yasa ta kasa yin maganar da tayi niya na tambayar jikin Ya Nafin ta koma cikin sanyin jiki.

Wucewa tayi ta nufi ƙofarsu inda ƴan zaman inuwar suka kwashe da dariya suna cewa Aunty Rakiya "Maganin mai shishi-shigin tsiya kenan."

"Eh nayi shish-shigin, ai Allah yaga zuciyata ina da niyar taimakon yaran nan ƙarfina aka fi aka rabani dasu." Aunty Rakiya ta faɗa muryarta na bayyana gaskiyarta.

"Munafurcin banza." cewar Babar Salaha. Bata ƙara kulata ba ta kwashe kayanta ta shige ɓangarenta ta barsu a nan suna abinda suka fi ƙwarewa.

Amaturrahaman kuwa tana shiga uniform ɗin ta fara cirewa ta ɗibi ruwa ta shiga wanka, alwala tayi bayan ta gama ta fito gaba ɗaya. Ko ta kan man shafawa bata biba ta zaro doguwar riga ta zura ta saka hijabi ta tada sallah. Sosai tayiwa Ya Nafi addu'a bayan ta kammala sallar tana zubar da hawaye. A hankali ta kai kallonta inda ta aje laidar take away ɗin data shigo da ita. Gaba ɗaya ji tayi bata son cin abincin amma haka ta daure saboda alƙawarin da tayiwa Muzaffar akan zataci, kuma sannan a karan kanta tana da buƙatar samun ƙwarin jiki domin kulawa da ƴar'uwarta wanda hakan ba zai samu ba sai taci abincin.

Cikin sanyi ta miƙe ta ɗauko laidar ta dawo ta zauna ta shiga buɗewa, lafiyayyar fried rice ce da taji kayan lambu sai dunƙulen naman kaza a sama. Ba dan tana jin daɗin abincin ba ta samu ta kai loma biyar da ƙyar ta ture shi hawaye na zubo mata tunawa da tayi Yaya Nafi na yawan sayo musu irin wannan suci tare tana ta surutu da santi, ita kuma Amaturrahaman na mata murmushi.

Wayar daya bata ta kalla a inda ta ajeta, ɗaukota tayi ta saka kiran number daya nuna mata ta kira. Bugu biyu ya ɗauka da sallama yana tambayarta ko ta gama yana jiranta.

"Ina fitowa yanzu." Ta faɗa cikin sanyin muryarta, tashi tayi ta gyara hijabin dake jikinta ta fice a gidan bayan ta kulle ɗakin nasu ta kuma kulle ƙofar gidan. A ƙofar gida ta same shi ya faka motarsa inda ya aje ɗazu, lokacin data wuce majalissar su Kawu Isa tana jin su suna cewa "Itama karuwar ɓoyen ta fara bayyana nata iskanci, tunda ɗayar bata da amfani yanzu."

"Idan ma ta tsira ko? Ai wannan yarinyar bana jin zata tashi gaskiya saboda ba kaɗan ba wutar ta cinyeta." Malam Mamuda makwafcinsu ya faɗa. Wani irin tuƙuƙin ciwo take ji yana ƙoƙarin toshe mata numfashi amma ta daure ta haɗiye shi ta isa motar don yanzu ba lokacin kula abinda mutane zasu faɗa bane.

Kallonta yake cike da tausayawa yayinda zuciyarsa ke narkewa da shauƙin ƙaunarta, tausayinta mai tsanani ke ƙara rugur-guza zuciyarsa a duk sanda ya kalleta. Duka ma yarinyar guda nawa take amma ta haɗu da wannan ƙaddarar, tayi ƙankanta sosai ba zata iya ɗauka ba ita kaɗai. Shi yasa ya yanke cewa idan ya mayar da ita yanzu zai koma Katsina ya sanar da Ammah abinda ke faruwa yasan zata taimaka sosai akan al'amurin.

"Kinci abincin kuwa?." Muzaffar yayi mata tambayar cike da kulawa. Kai ta ɗaga masa a hankali tana janye idanunta da suka jeme sukayi jawur saboda kukan da taci.

"Muje ko." Ya faɗa yana buɗe mata gefensa. Shiga tayi ta zauna da kyau sannan ta janyo murfin ta rufe, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki ya tada Motar suka wuce.

Sai da ya rakata har ƙofar ɗakin sannan ya e mata. "Ki jirani yanzu zan koma gida in sanar da Ammah abinda ke faruwa, amma kafin nan ya kamata a samu wanda zai tayaki zama kafin in dawo mu wuce Katsinar gaba ɗaya kafin lokacin fitar da ita yayi."

Karon farko data ɗago ta zuba masa ido tana girmama karamcinsa a gare ta, duk da dai ta kasa sake jiki dashi har yanzu don ita gaba ɗaya mutanen duniya tsoro suke bata, ba wanda ta yarda da shi.

"Na gode sosai da taimakon da kayi min, amma bana buƙatar kowa da zai tayani kula da ƴar'uwata saboda bamu da kowa ni kaɗai gareta, nima kuma ita kaɗai gareni. Zan kuma iya kula da ita har ƙarshen numfashina maganar fitar da ita kuma idan an samu asibin da za'a kaita ni zan biya ko nawa ake buƙata." Ta ƙare maganar a nutse kuma cikin sanyi.

Mamakin yanda take yin magana ya kama Muzaffar musanman ma da yaji tace zata biya ko nawa ake buƙata domin kulawa da yayarta, to suda basu da kowa mai kula dasu a ina zata samu maƙudan kuɗaɗen da za'a buƙata? Haka yayi ta waɗannan wasi-wasin. Haɗiye komai yayi ya kalleta yace ki kula sosai zan yi magana da Doctor kafin in wuce zan kuma dawo a kan lokaci domin mayar da ita Katsinan." Yana gama faɗa ya wuce ya nufi Ofishin likita yayi masa bayanin cewa zai je ya dawo amma don Allah yana so a samu mai kula da yaran saboda yanzu yamma tayi sosai kafin ya isa gida dare yayi ba zai yiwu ya dawo yau ba. Kuma sai gobe ne za'a mayar da ita Katsinan......