YAR HANNU A LAGOS

CHAPTER 1

by @oumyasmeen

Lagos agege

wata uwar miƙa tayi ta saki wata uwar hamma, kamshin gasassun kaji ne yayi mata sallama a kofufin hancinta, da sauri ta sauko kan gadon tuni zulfa'u ta nannaɗe ledar naman ta tace "wallahi Allah halee ba zaki ci ba, ga hanya nan kema fita ki samu naki rabon...,

haɗe rai tayi ta ɗauki wayar ta keypad ta soma dannawa, tace"kinsan ni ba matsiyaciya bace...,

dariya zulfa'u ta sheƙe da ita, cikin rainin hankali tace "au Allah, ai bani da labari...,

dama yaushe zaki samu labari kina can ana kwakular'gindin ki, ta fada tana watsa mata harara

dariya ta kuma sheƙewa da ita tace" kina baƙin ciki ne da irin baiwar da Ubangiji yayi mun ke baki da ita...?,

God forbid wallahi, gwara na mutu banci ba banza karuwa,

Owo dai, wata ta samu a yaba,

tashi tsaye tayi ta jujjuya tace "kalleni da kyau ba abin da Ubangiji be min ba, alhmdullahi na godewa Allah ina neman halilina, kema ina me nusar dake tun kafin duniya tayi miki juyin waina ki tuba,

banza tayi mata kanta ba ɗankwali ta fita, kalaba ce a kan ta ta zubo har gadon bayanta masha Allah, kallo ɗaya zakai wa, halee kasan anyi ubangiji yayi halitta, jingina tayi a bango ta dafe mararta da ta kulle, da alama baƙonta na kan hanya, dogon tsaki taja lokacin da tayi ido huɗu da Monica da Samuel, yana zura mata hannu a riga yana murzar nonuwanta, bakin su hade kamar zasu hadiye juna, ita kuwa hannunta na wandonsa sai aikatashi take,

tsaki ta ja kai Allah ya kawo musu ɗauki su bar gidan nan, kullum ƙazantar gidan ƙaruwa take, tun bata fahimci wacce irin rayuwa ce wannan harta gane, daga karuwai sai yan madigo ne a gidan....

iya kuɗin ki iya shagalin ki, ashe zancan zuci da take ya fito fili, haɗe rai tayi ta nufi dakin ummanta, kamar dai ko da yaushe tana zaune tana karatu, ɗurkusawa tayi tace "umma ina kwana...,

ɗago da kanta tayi tace"halimatu badai yanzu kika tashi ba....?,

ɗan ya mutsa innocent baby face ɗin ta tayi tace "eh amma nayi sallah....,

ai daman tun da naga kin tafi ɗakin zulfa'u, to nasan bacci kika koma, Allah ya shirye ki..

zama tayi tace "umma ba wani abu ne... wallahi yunwa nake ji..?,

ajiyar zuciya ta sauke tace "to haleematou wallahi babu amma Allah zai kawo, tace Allah yasa.