ƳAR KARUWA PART 1

ƳAR KARUWAR Chapter 6

by @ayshadansabo

*ƳAR KARUWA* Arewabook@ayshadanaabo

Paid book

©️ Aysha Dansabo Lemu ✍🏻

Free pages

Chapter 6

Gaida Hajiya Inna Mamie tayi Hajiyar ta amsa babu yabo babu fallasa tana sauke ganinta akan Labibah wacce taci ado cikin wasu matsatstsun riga da skat na atamfa da sukai masifar fidda surarta,babu mayafi a jikinta domin yafa shi ba cimarta bane tafi ganewa fita a haka gayarta tsabagen gogewa a boko da kuma buɗewar idanu irin na ƴan matan garin Jos.Muryar Labiban ce ya doki kunnuwar su Inna time ɗin da take gaida Hajiya Inna,Hajiya Inna ta amsa da fara'a tana faɗin,"Ya wajen Barirar,dafatan duk suna lafiya ita da Mahaifin naki?" Labibah tace a gajarce,"Lafiya lau Hajiya." Jannat ta dubi Mamie tace,"Mamie ina yini,Anty Labibah barka da zuwa."Daga Mamien har Labibah wani irin kallo suka watsawa Jannat ɗin kafin Mamie ta amsa da cewa,"Lafiya lau."Jiki a mace Jannat ta tashi domin isa kitchen ta kawo ruwa da lemu.Kamar jira Mamie take ta bar wajen ta gyara zamanta tana duban Hajiya Inna dake ta faman mamakin yadda Labibah kullum tarbiyyarta take sake lalacewa,cike da karsashi Mamie ke faɗin,"Hajiya Labibah itace za ta zama surukar tamu,sun daidaita kansu ita Ammar kinga Allah ya amshi addu'armu bana dai za a yi shagalin bikin mutumin naki." Galala Hajiya Inna tayi tana sake ƙure ganinta akan Labibah dake sakin wani makirin murmushi,cike da tsantsar damuwa Inna tace,"Toh! Shi kuma ita tayi masa kodai haɗinku ne kawai ke da aminiyar taki?" Hajiya Mardiyyah ta tsuke face tace,"Kusan hakan ne Inna sai kuma aka yi sa a ya amince domin Labibah ta mallaki duk wani abu da zai nema a ɗiya mace." Hajiya Inna ta jinjina kanta tace,"Ba shakka to Allah ya tabbatar da alkhairi yayi masa zaɓi mafi alkhairi." Kafin Mamie ta amsa Jannat ta ratso cikin falon hannunta ɗauke da tray data ɗauro table wata da lemuka masu sanyi matsakaici,kusa da Labibah ta isa ta aje tray ɗin tana faɗin,"Bismillah." Daga Labibah har Mamie suka sake watsa mata wani kallo kafin Labibah tace,"Thank u."Miƙewa Mamie tayi tana duban Hajiya Inna tace,"Ameen Hajiya,za mu wuce ina son na je gidan ƙawata Hajiya Habibah ne saina dawo." Labibah itama miƙewa tayi tana ɓalle bakin jaka ta zaro kuɗi dubu biyar sabbin ƴan dubu ta isa wajen Inna ta aje kuɗin tana faɗin,"Hajiya Inna gashi a sai goro babu yawa." Hajiya ta dubi kuɗin tace,"To Madallah Allah yayi albarka ki gaida Barirar." Daga haka sukai sallama da Inna suka fice.Hajiya ta kama haɓa bayan fitarsu tace,"Ikon Allah,shi kuma Ammar wannan fitsararriyar Yarinyar yaga cewar ta dace da rayuwarsa duk son iyayin nasa na banza ne ashe." Dariya ne ya kama Jannat ta dubi Inna tace,"Hajjaju me kuma yafaru ne?" Hajiya Inna tace,"Komai ma ya faru Takwara,wai wannan Yarinyar Labibah itace Mardiyyah za ta haɗasu aure da Yayanku Ammaru ke kinga haɗin yayi?" Jannat cike da mamaki ta dubi Inna tace,"Yaya Ammar fa? Anty Labibah zai aura?" Hajiya ta saki tsaki tace,"Kema dai kya gani,sam wannan haɗi bai yi ba amma za mu zuba ido mu gani har zuwa ya dawo." Jannat ta ɗan girgiza kanta tace,"To kila tayi masa ne Inna tunda tana da kyau kuma ƴar gayuce,any way mudai dama mun ƙosa yayi aure musha biki." Harara Hajiya Inna ta aika mata tana faɗin,"In Sha Allah ko zaiyi bada wannan Yarinyar Labibah ba domin haka kawai ban yaba da tarbiyarta ba, sannan Hajiya Barirah da kike gani bata da kirki na tabbatar suna da manufarsu nayin hakan ita Mardiyyah sakarya ce sai abinda Barirah ta shirya mata take bi,gaba ɗaya ta gama ɓata Mardiyyah da miyagun halaye irin nata,nidai kullum fatana kada Allah ya baiwa kowace mace galaba akan zuriyata,Allah ya kare min Muhammadu daga kaidinsu dana sauran mata." Hajiya Inna ta ƙare maganar cike da damuwa domin gabaki ɗaya halayyar Mamie na bata tsoro,domin kullum lamuranta na rashin kirki sake gaba suke.Murya a sanyaye Jannat tace,"Ameen Inna,Allah ya kyauta." Daga haka suka kama wani hirar kafin Jannat ta miƙe ta isa ɗakinta domin kwanciya ta huta before la'asar.Can ta hango wayarta data kashe yashe bisa bed ɗinta,koda ta kunna wayar saƙwanni ne sukai ta shigowa duk daga lambar da Aliyu ya kirata dashi ne.Blocking lambar ta fara yi kafin ta goge duka saƙwannin ba tare da ta buɗe ko guda ɗaya ba,duk da cewa haka zuciyarta ke ruwaita mata akan ta karanta koda guda ɗaya ne amma bata bi shawarar zuciyartata ba ta gogesu duka.Tana shirin aje wayar kiran Feenah ya shigo mata,jiki a sanyaye ta ɗaga call ɗin suka jima suna magana kafin suyi sallama da juna Jannat ta sanar da ita cewa ta gaida mata da Mummy tana nan isowa zuwa jibi.Tana aje wayar ta zame ta kwanta tare da lumshe idanunta hoton fuskar Ummu na cika idanunta,ta sake rintse idanunta tana son koya ne taji tsanar Ummu a cikin zuciyarta amma ta kasa.Tana sonta sosai kamar yadda itama Ummun ke ƙaunarta,sai dai ta sani ba za su taɓa zama inuwa ɗaya da Ummu su nunawa junansu ƙaunar da suke wa juna ta Uwa da Ƴa ba domin halayya da ɗabi'unsu sunyi hannun riga da juna.Hasalima tasha ayyanawa a cikin zuciyarta cewa ina ma ɗan adam an bashi zaɓin da zai iya sauya Iyaye,da tabbas sai ta canza Ummu a matsayin Uwa ta maye gurbinta da mace mai kamun kai mara aikata saɓon Ubangijin.Wasu irin hawaye masu zafi suka shiga sulmiyowa suna biyo fuskarta,zuciyarta ta sake matsewa da wani irin yanayi mai wuyar fassara.Kira da ya shigo cikin wayarta ya sanya ta buɗe idanunta tare da kai hannu ta janyo wayartata,sunan wacce ta gani bisa allon screen ɗin ne ya sanyata saurin tashi ta zauna dingir a saman bed ɗin zuciyarta na sake ɗaukar rawa.Kiran ne ya yanke wani ya sake shigowa amma vedio call ne wannan karan,hakan ya sanya Jannat ta tsuke fuskarta tana receiving call ɗin ba tare da ta iya ɗaga idanunta ta dubi fuskar wayar da zuwa lokacin kyakykyawar fuskar farar matar ya gama cika allon screen ɗin."Angel." Sassanyar muryar Ummu ya doki kunnuwar Jannat,hakan ya sanya ta rintse idanunta tasirin sunan da take kiranta dashi na ratsa kowani kafar sadarwa na jikinta.Bata amsa ba kamar yadda bata kalli fuskar wayarba sai ma idanunta data sake lumshewa hawaye suka cigaba da wanke fuskarta,a karo na biyu Ummu da hankalinta ya gama tashi da ganin halin da Jannat ke ciki ta sake kiran sunanta,"My Angel." Jannat sai ta buɗe idanunta tare da kallon fuskar wayarta,idanunta suka sauka akan kyakykyawar halittar dake sanye cikin wasu riga da ya wando da suka kama jikinta,fuskarta yasha make-up tamkar wata sweet sixteen bamai shekaru arba'in da biyu a duniya ba,sosai tayi mugun kyau musamman hujin hancinta dake haskawa da ƙyallin barimar gwal da aka maƙala masa.Wani irin abu mai nauyi ne ya danne zuciyar Jannat time ɗin data kalli gefen Ummu ta fahimci cewa a wajen wani hutawa Ummun take,wacce ta zaɓi zama a jihar Lagos ɗin da ta zaɓesa ya zama garin sheƙe ayarta da more rayuwarta irin yadda take so."Ummu ina yini." Jannat ta fisgo kalaman gaisuwar suka fito da ƙyar kuma cikin raunin murya.Ummun ta sake zubawa kyakykyawar fuskar tilon ƴarta idanu,wacce babu inda ta barota a kammannu sai hasken fata data fi Jannat ɗin.Cikin low voice tace,"Daughter meyasa kike kuka?Nice baki son gani ko?" Jannat tayi saurin girgiza kanta tace,"Ummu ni ba haka bane,kawai kin kira ne a time ɗin da bana jin daɗi." Kai tsaye Ummu tace,"Meya sameki?Ko duk akan batun fasa maganar aurenki da ɗan gidan Sanata Mukhtar Wase ne? Ina da labarin komi domin Inna da kanta ta kirani ta sanar dani time ɗin da aka kaiki asibiti,why Jannat? Meyasa ba za ki haƙura dashi ba ki jira dubunsa da za su kawo kansu zuwa gareki ba? Karki taɓa damuwa don an fasa aurenki dashi,domin ni farin ciki nayi da jin hakan don ina da tabbacin da anyi auren zai kasance mutum biyu za ki yi mu'amalar aure dasu,ina nufin Uban da kuma ɗan domin babu yadda za a yi Sanata Mukhtar ya ɗaura idanunsa a kanki ya iya barinma tilon ɗansa ba tare da shegiyar kwaɗayinsa ta biyo ta kanki ba,ance Hajiya Salma ce ta hana auren sabida tace ni Karuwace ɗanta ba zai raɓi jinina ba Ko?Bata san cewa nima ba zan so ƴata ta haɗa jini da ƙazantaccen mijinta bunsuru mara aji ba,domin duk ƙazantata Sanata ya ninkani sau dubu don haka karki taɓa damuwa don kin rabu da Aliyu domin ni da Ubansa duk kanwar jace,ke harma da Uwar tasa kuma ta jira shigowata garin Jos sai na bata mamaki."Yadda Ummu ta ƙare maganar cike da cin alawashi ne yayi masifar sake hargitse kwanyar Jannat,ta ɗago a rikice idanunta na sake tsiyayar da hawaye tace,"Ummu dama kinsansu ne?" Ummu ta sakar mata kyakykyawar murmushi tace,"Hafsatu ke Yarinya ce,ni dai abinda nake so dake kawai ki cire soyayyarsa a cikin zuciyarki,kiyi haƙuri Jannat nasan kina nan kina jin zafin cewa zunubaina ne suka fara bibiyarki Ko? Idan har ƙaddara ta iya zaɓa mini miji irin Mahaifinki a baya,to ina so ki sanya a cikin zuciyarki cewa kema za ki samu mijin da ya zarce Aliyu Wase a komi da komi."Har Ummu ta dasa aya Jannat ta kasa tsaida ruwan hawayen dake kwaranya daga cikin idanunta,kamar yadda har lokacin jawaban Ummu na farko basu daina dukan zuciyarta suna hargitsa kwanyarta ba.Ta kasa cewa komi har Ummu ta cigaba da rarrashinta da kalamai na nuna ƙauna da kwantar hankali,daga ƙarshe Ummun tace,"Ina nan zuwa Jos ɗin nan da wata guda ko sama da hakan,yaushe za ki wuce skull ɗin Inna tace kina nan a Jos ko?" Jannat ta jinjina kai kafin tayi magana a raunace tace,"Jibi Abbah yace Ummu." Kissing ɗinta Ummu tayi tace,"I luv u daughter,karki damu Ummu za ta gyaru ta zama irin yadda kike so just pray for me kinji ko?"Jannat ta jinjina kanta tana jiyo sautin wani kiss ɗin da Ummu ta sake jefo mata kafin tayi cutting call ɗin.Ta maida idanunta ta lumshe tana jin wani abu na gudu a cikin jinin jikinta,kalaman Ummu suka sake yin tsawa a cikin kanta lokacin da take faɗin, " Meyasa ba za ki haƙura dashi ba ki jira dubunsa da za su kawo kansu zuwa gareki ba?Ina da tabbacin da anyi auren zai kasance mutum biyu za ki yi mu'amalar aure dasu wato Uban da kuma Ɗan domin babu yadda za a yi Sanata Mukhtar Wase ya ɗaura idanunsa a kanki ya iya barinma tilon ɗansa ba tare da shegiyar kwaɗayinsa ya biyo ta kanki ba." Waɗannan kalaman na Ummun sune suka dawo cikin kwanyarta suna sake hargitsa dukkanin tunaninta."Ummu me hakan ke nufi kenan?" Jannat tayi tambayar a bayyane tana sake jin wani irin yanayi na kassara zuciyarta."Kar dai ace Sanata Mukhtar shima manemin mata ne?" Ta sake jefawa kanta tambayar tana jin tausayin Aliyu Masary na jiƙa zuciyarta."Shikenan Baby dukkaninmu ashe ƙaddararmu iri ɗaya ce." Hafsatu ta sake furta kalaman a bayyane tana jin tarin tausayin kanta na sake mamaye zuciyarta.Duk yadda taso baccin da ta shigo yi ya ɗauketa ta kasa,sai kawai ta janyo wayarta ta kunna data ta hau online.Messages ne suka dinga shigowa rabinsu duk daga group na skull ne,sai na friends ɗinta Aysha da Muffy da suke mata complain akan tayi ta dawo an yiyyi test's sosai amma sun samu sunyi mata guda biyu ɗaya ne kawai tayi missing shima kuma course ɗin mutuminta Dr.Gumel ne suna da tabbacin bata da damuwa.Aysha ce tayi mata waɗannan bayanan,hakan ya sanya ta aika mata emoji na harara domin ta tsani ta tuna cewa Dr.Gumel ya bala'in matowa a kanta, amma ita tsanarsa take ji domin Dattijo ne irin mara kamun kannan.........✍🏻

Ina muku albishir da cewa part 1 gabaki ɗayansa zai muku a kyauta ne,da zaran mun kammala za mu ɗaura part 2 wanda shine za ku saka kuɗi kusha karatu.