7
KURURUWA A KUNNEN KURMA 🥀 🥀
A 2025NOVEL
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
Wattpad:@ Ummu-Ameer
Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa
From d experience writer of:
Zaytoonah
Abarwa rai
Gudun wuce sa'a
Kibiyar so
Kulsum
Bahiyya
Nuudarr
& Now Kururuwa a kunnen kurma
Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏
Nagode sosai en uwa, Allah ya saka da alheri ya kuma bada lada.
FREE PAGE 7
Da ace Safnah ta nemi rabuwa da shi ne akan gazawarsa ga abinda tayi masa umarni surely he would have been angry with himself and zai ji kunyar kiran kansa da suna namiji, But tuna cewa she choose someone else wanda kallo ɗaya Yayi masa ya fahimci cewa bai fishi da komai ba fa ce tarin dukiya kawai da yake da ita hakan sai yasa yaji cewa he has no pain or regret at all about ending their relationship with her. Kuma shi ɗin ya ɗaukarwa kansa alƙawari har abada ya baiwa Safnah baya kenan har ba duniya.
Ya jima a tsaye yana mai jin baƙin ciki da raɗadi sosai a ransa marar misaltuwa, at the end kawai ya kama hanya da ƙyar ya koma gida, ya na zuwa yayi alwalar magarib ya wuce masallaci bai dawo ba sai kusan 10pm,Bilal has been calling him domin ya ji yanda suka ƙare but he has no courage to pick the call domin bai san ma ta yanda zai fara masa bayani ba, that's why kawai ya sharesa ya samu masallaci yayi zaman sa yayi ta tilawar alƙur'ani da nufin samun sanyin wutar da ke ci a cikin ƙoƙon zuciyar sa,yana nan har sai da yaji cewa ya samu nutsuwar rai sosai sannan daga ƙarshe ya yi addu'ar Allah ya ba shi haƙuri da juriya akan wannan abun da ya faru tsakanin shi da Safnah yasa kuma ya zama shi ne mafi alheri a tsakanin su.
🪐🪐🪐
Ina shiga gida da gudu na faɗa jikin mama ina mai jin zuciyata sakayau bata da sauran wata damuwa......
"Oh! Farin ciki bisa farin ciki ni Shafa'atu, Safnah mi kuma muka samu haka?"
Janye jikina nayi ina dariya nace.
"Mama shikenan yau na jefar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda, Ni da Xunnurain yau munyi hannun riga Mama"
Dariya ce itama ta suɓuce mata ta na mai faɗin.
"To daman ai Xunnurain tsaga da faɗi yayi, amma kuma yanzu da kika fahimtar da shi cewa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa ai sai ya ba kansa lafiya...."
Kiran wayata da Naseer yayi shi ya katse mana hanzari, cikin azama nayi picking.
"Ki fita waje ki karɓo saƙo"
Daga haka ya tsinke wayar, kallo na mama tayi tace.
"Tsayin me kike to? Yi maza kada ya gaji da jira ya tafiyar sa dan Allah"
Da sauri na mayarda veil ɗina a kafaɗa na fita, zaune mutumin yake a mota sai da ya ga na fito sannan ya buɗe motar ya fito tare da durƙusawa har ƙasa ya gaishe ni cike da girmamawa wanda ni abin ma dariya ya bani.
Bayan mun gama gaisawa ya tashi ya buɗe Booth ɗin motar ya ciro min wata madaidaiciyar Ghana must go ya bani wadda na ɗauke ta da ƙyar domin ta ɗan yi nauyi.
Ina shiga na wuce har bedroom ɗin Mama wanda a lokacin har ta wuce ta ɗoro alwalar magariba.
A hankali na zuge zip ɗin jakar wadda idanuwan Mama ke kai tamkar za su faɗo ƙasa, ganin ɗaurin damman kuɗaɗe da yawa yasa ta saurin waigawa ko ina ta dudduba, da sauri ta janyo sallaya ta lulluɓa sannan ta sake komawa ta janyo duvet da bedsheets ta tuttula da kyau ta ɓatar da kamannin jakar ya koma tamkar kayan wanki ne ta ke haɗawa.
Ganin nayi sototo ina kallon ta yasa ta ɗan harare ni sannan ta ce.
"Ke sam baki da wayau wallahi wani lokaci, Alhaji na gidan nan, sannan uwa uba Deen, ki bari sai sun fice... Ke bari sai kowa ya shige kwana sannan muzo mu ƙirga su mu gani"
Murmushi nayi nace.
"Haka ne fa Mama, bari na je na yi sallah na dawo to"
Daga haka na je na gabatar da Sallar magrib, sannan na koma parlorn Baba na kwashe kayan da na kaiwa su Naseer abinci, na dawo na zauna muka shiga chart da rabin rai na har aka kira Isha, daga nan na tashi nayi sallah, bayan na kambala na je domin yi wa Baba sai da safe, a nan na tarar da Deen, Baba da kuma Sa'adu wanda da alama yanxu ya iso.
Dukkan su babu wanda yace min uffan nima haka, sai ma wani ƙara haɗe fuskanta da nayi domin kada wani yaron ya kawo min wasa, gefe na samu na tsugunna na ce.
"Baba ina wuni"
Ɗagowa yayi ya kalle ni sannan ya amsa da
"Lafiya Lau Safnah, baƙon ya tafi ko? Ina fata komai lafiya?"
Cikin jin daɗin kalamansa na ce.
"Komai lafiya ƙalau Baba, Allah ya tashe mu lafiya"
Kallo na yayi for some seconds sai kuma ya juya suma ya kalle su sannan ya ce.
"Sa'adu! Ba yanxu ka iso ba? Miyasa banga kunyi magana da juna ba? Ko akwai wata matsala ne?"
Girgiza kai Sa'adu yayi sannan ya ce.
"Alaji wallahi ba wata matsala, kawai dai kasan halin ta, yanzu mutum zai yi mata magana sai kaga ta fassara ta zuwa wani abu na daban"
Harararsa na fara yi sannan na kalli Baba na ce.
"Ƙarya ya ke Baba, kawai na lura tunda aka tsayar da magana ta da Naseer shi kenan su ka daina shiga sabga ta"
Gyaɗa kansa yayi sannan ya dubi Deen ya ce.
"Shamsuddeen Miyasa kuke yi mata haka? Kun manta cewa komai na Allah ne, duk yanda kuke son Usman tunda Allah ya rubuto ba mijin ta ba ne ai sai kuyi haƙuri,ku tayata murna sannan ku yi mata fatan alheri"
Gyaɗa kansa Deen yayi sannan ya ce.
"Ayi haƙuri Alaji in sha Allah komai ya wuce"
Cikin jin daɗi Baba ya ce.
"Ba komai, Safnah kina iya tafiya"
Daga haka na juya na fice su kuma suka ci gaba da abinda suke yi na lissafin kuɗin kasuwa da suka taso.
Bayan na koma na yi duk abinda zanyi sai kuma na zauna muka ci gaba da chart ni da Naseer wanda ni yanxu bani ma da lokacin kowa a social media baki ɗayanta sai na sa.
Ina nan har sai da bacci ya fara ɗauka ta can sama sama naji Mama na tashi na, haka na miƙe muka je ɗakinta da giyar bacci a ido na, muna shiga ta dannawa ƙofar key ta jani sai gaban jakar kuɗin, hannu na ta kama tana rawa dani cikin nishaɗi tana zuba mini kirari da faɗin.
"Da ka haifi Governor gwanda ka haifi matar Governor, ɗaya-ɗaya tamkar da dubu Safnah ta, nikam haihuwarki ta mini rana babu abinda zance da ubangiji sai godiya..."
Ni dai babu abinda nike sai bin tulin kuɗaɗen da kallo, ƙarshe na kalleta na ce.
"Da kika ƙirga nawane kika gani hala Mama?
Zaunawa tayi ƙasa daɓas! Sannan ta ce.
" Ana zancen bindiga wane ƙyastu, ai kuɗin nan ba zai ƙirgu ba Safnah am! Wallahi dukiya ce mai tarin yawa "
Cikin farin ciki na ce.
" Daman Naseer ya ce min za'a yi buki wanda ya amsa sunan sa buki Mama, so yake duniya ta amsa ta kuma shaida da auren sa ta ko wane ɓangare "
Jinjina kai tayi ta ce.
" Tabbas kuwa maganar sa dutse, ba shi kaɗai ba Safnah, ko ni nan sai na yi bukin da ya amsa sunansa buki, sai na yi yanda raina ya ke so da kuɗi, kema kuma ki samu ƙawayenki ɗiyan manyan masu kuɗin nan kuma kada su wuce shida highest bakwai, bukin en gayu za'ayi, ga shi Allah ma yasa ba nan za'a yi bukin ba kinga mun huta dole sai wanda muke so ya zo zai zo "
" To ni Mama ai kinsan bani da wasu ƙawaye ɗiyan hamshaƙai wannan sai su Aydah, sai dai idan su zan yi wa magana kinga su duk yawanci ma ƙawayen su ba su cika zama nan ƙasar ba sai ɗaɗɗaya musamman Xuhrah"
Washe baki tayi tana faɗin.
"Yauwa! Shi kenan ma haka za ayi, ta shi kije ki kwanta gobe da wuri zamu fita zuwa gidan Hajiya binta idan Allah ya kaimu"
🪐🪐🪐
Kayan kitchen na ji da gani Mama ta zage ta sayamin tare da taimakon Hajiya Binta babbar ƙawarta kuma er uwar ta guda da ta ke da ita a garin Gusau, ta yi siyayyar kayan souveniers tayi ɗinkuna kala da kala, komai ta gama shirya shi, hatta mutanen da ta gayyata waɗan da zasu je Sokoto duk itace tayi musu ɗinki sannan ta ba su kuɗin motar da za su hawo su zo Sokoton.
Tun daren jiya Sa'adu ya tafi tare da Bus ɗin da ta kwashi kayanmu, Wanda mu kuma yau ne ni da Mama Deen ya ɗauke mu a motar sa muka tafi.
Muna isa direct muka wuce part ɗin mu da ke cikin gidan Daddy wanda yayi sa na musamman da sunan Babanmu. Duk muka zo a nan muke sauka.
Bayan mun sauka bai fi 20mnt ba sai ga shi duk mutanen gidan sun zo wurin yi mana barka da zuwa.
Muna haɗa Ido da Aydah ta sakar min murmushi sannan ta zo a hankali ta rungume ni tana faɗin.
"Welcome Sis"
Breaking hug ɗin nayi na kalleta ina murmushi na ce.
"Thanks Aydah"
Hannun ta ta ɗora a fuskata tana shafawa tace.
"Kalli yanda fuskar Amaryar mu ke sheƙi masha Allah! You look beautiful and you change also"
Dariya muka saka a tare sannan na ce.
"Naseer ask for my permission cewa zuwa 5pm zai zo muje pre-weeding pix, what did you suggest? hope zaku rakani ke da Xuhra?"
Faɗaɗa murmushin ta tayi tace.
"Why not Amaryar Naseer? Zamu rakaki mana, ai from now on kece the Sarauniya and we are the Maids, duk abinda kika ce ayi shi za'a yi"
Jin kalar feedback ɗinta sai ya ƙara min ƙwarin guiwa na ce.
"Thank you Aydah. And again, kin san cewa bani da friends a nan, dan Allah ina neman alfarma da ku yi inviting friends naku a samu a yi bikin ya tafi yanda ake so"
Hannunta ta sanya cikin nawa ta matse kaɗan sannan ta ce.
"Safnah, ke fa er uwarmu ce and you have no one here to be with you idan ba mu ba, so karki wani damu komai za'a yi yanda kike so in sha Allah, zamu gayyato friends ɗin mu za'a yi komai a tsari"
"Thank you so much Aydah, shiyasa ko da yaushe ni ke alfahari da ku"
"Ahh, karki wani damu, Allah yasa ayi lafiya a watse lafiya"
Murmushi na yi na ce.
"Amin, wai ni kam ina Xuhra ne?"
Ɗan Jim! tayi alamar tunani sannan tace
"Xuhra ta je ta ajiye ƙawarta Shakirat Azeez a Airport"
"Shakirat Azeez ƙawarta ta Lagos da sukayi karatu tare ko?"
Gyaɗa Kanta tayi sannan ta ce.
"Yeah! Ta zo ne domin yin wani aiki sai jiya ta samu ta kambala, shi ne taje tayi dropping na ta, but in sha Allah nasan yanzu tana hanyar dawowa, kawai kije ki shirya nima zanje nayi shaf-shaf kafin ta iso"
Daga haka ta wuce gida domin shiryawa, nima na shige banɗaki na na fara yin wanka sannan na fito nayi sallar Asr na shirya, ko ta kan abincinda aka ajiyemin ban bi ba domin a 'yan kwanakin nan ma ni kwata-kwata na daina jin yunwa.
Daga ni sai wayata na fito kamar yanda Naseer ɗin ya umurce ni domin yace komai an tanadar min.
Sai kusan 5:30pm muka fito bayan mun gama zaman jiran Xuhra shiru bata dawo ba.
A main gate muka tarar da mutumin da Naseer ya aiko ya ɗauke mu tun around 5pm,muna batun shiga motar sai ga motar Xuhra ta danno ta shigo bayan Mai gadi ya buɗe mata ƙofa.
Tsaye muka yi ni da Aydah muna kallon ta har ta gama daidaita parking ta fito. Da murmushinta ta iso har inda muke ta bani side hug tana faɗin.
"Welcome our beautiful bride"
Murmushin na mayar mata nima nace.
"Thank you Sis, and you are welcome too"
Daga haka ta juya da nufin shigewa gida sai dai tuni Aydah ta katse mata da hanzari ta ce.
"Tun ɗazu fa ke muke jira"
waigowa Xuhra tayi ta kalleta ta ce.
"Na me fa?"
"Zamu raka Safnah ita da Naseer za su ɗauka hotunan bukin su..."
Girgiza kai tayi sannan ta ce.
"Count me out please"
Wani kallo Aydah ta aika mata sannan ta ce.
"And why? Xuhra you know it cewa Safnah ba ta da wasu ƙawayen a nan garin idan ba mu ba, dan Allah ki daure kiyi haƙuri mu kasance tare da ita a bukin nan please...."
Cikin cool voice ɗinta na rashin son hayaniya ta ce.
"Aydah kinga bukin ya zo ne banyi participating ba? Excuse me please"
Daga haka ta Juya tayi tafiyar ta ko sake kallon in da muke tsaye batayi ba. Ni, Xuhra, Aydah babu wanda ya baiwa wani shekara a tsakanin mu duk en kai muke, tun muna ƙanana mun riga mun sa ba da halinta shiyasa abin baya damun mu, but a gaskiya yau abinda tayimin ba ƙaramin ƙona mini zuciya yayi ba....
Hannuna Aydah ta ja tare da buga tsaki ta ce.
"Yi banza da ita, daman na kawo a raina sai ta bamu matsala sai gashi kuwa bata shanye raɗa ba, idan ba ta je ba sai me zai faru! Mtsw. Zo muje gidan su babbar ƙawata Zeeyat Mahmoud ta rakamu"
Ban iya furta komai ba, haka na bi ta muka shige motar ni da ita. Muna tafiya tana mishi kwatance har muka isa gidan su ƙawar ta ta er gayu da ita, bayan mun gaisa da Mummyn su ne ta yi mata bayani muka fito ya ɗaukemu sai studion da Naseer ya ke zaune yana zaman jiran mu.
Muna haɗa ido ya sakar min lallausan Murmushin sa ni kuma sai na shiga ba shi haƙuri akan ɓata mi shi lokaci da mukayi but ko kaɗan bai nuna wata damuwa ba, da wasa da dariya suka gaisa da Aydah sannan daga baya ya kira wata matashiyar mata taxo ya ce mu shiga ciki ta shirya ni.
Wai bahaushe yace yabon gwani ya zama dole! Haƙiƙa dalili na na yin wannan furucin shi ne, duk wanda ya kalle ni a yanda matar nan ta tsantsara min make-up abinda ake kira make-up, sai kasan cewa tabbas ita ɗin gwana ce a cikin gwanaye,da kanta ta zaɓa min kalar kaya ta farko na saka sannan ta ɗaura min dankwali na musamman, ko ni da na kalli kai na sai da naji har cikin rai na cewa na ƙayatu, murmushi fal fuskata na kalle ta na ce.
"Thank you"
Murmushi tayi min ta ce.
"your welcome Ma"
Yanda na ke santin kai na haka su Aydah su ma suka shiga santi suna masu tayani farin ciki. Bayan ta gama shiryani shi ma sai ga shi ya shigo cikin shiga irin ta alfarma and kayansa saka thesame color da nawa.
Ɗakin da ake ɗaukar hoton muka shiga camera man ɗin ya shiga snapping na mu, haka mukayita canja kaya har sau bakwai, a na takwas ne Aydah ta ce ya kamata mu haƙura hakanan domin Daddy sai kiran wayoyin mu yake.
Sai da tayimin magana ne sannan na duba time ashe har 11pm ta gota ba mu da labari, cikin tashin hankali muka nemi izinin tafiya gida ba shiri yasa mutumin da ya kawo mu ɗazu ya ɗaukemu zuwa gida.
Muna shiga a gate ɗin farko ya zube mu yayi tafiyar sa , ni da Aydah kuma sai addu'a muke domin a lokacin har 12am ta buga, muna shiga gate na biyu muka cimma Yah Umar tare da Yah Abdul a tsaye jikin motar sa wadda ko daidaita mata parking bai gama yi ba, Yah Umar ɗin na latsa waya shi kuma Yah Abdul yana magana a waya.
Kallon sa Aydah tayi jiki a sanyaye ta ce.
"Yah Umar good Evening"
Duk da cewa dare ne, hakan bai hana shi ƙare mana kallo ba tun daga sama har ƙasa sanadiyyar hasken bolb ɗin da ya gauraye ko ina na gidan tamkar hasken rana.
"Daga ina kuke?"
Mitsi-mitsi nayi da ido yayin da zuciya ta ta shiga bugawa da ƙarfi....
"I said from where are you?"
Murya na ɓari Aydah ta ce.
"Da... Man.. Daman na rakata ne wurin mijin ta"
Kallona ya sake yi sannan ya ce.
"Wurin mijin ta? Daman an ɗaura auren ne bamu sani ba?"
Da sauri na girgiza kai na ce.
"A'a daman hotunan bukin ne muka yo..."
"OK! Da izinin waye kenan kukaje ɗin?"
Aydah ta ce.
"Gaskiya ba da izinin kowa ba Yah Umar but please we are sorry"
Nodding ɗin kansa yayi sannan ya ce.
"Kada hakan ta sa ke faruwa, shirin aure ba hauka ba ne"
Jin wannan maganar yasa mu saurin shigewa gida da gudu muna mai yi mai godiya, Yah Umar ba shi da daɗin sha'ani mutum ne mai tsattsauran ra'ayi amma fa mu a namu tunanin.
Cikin kwanaki uku hotunan mu da katin auren mu suka bazu ko ina a social media,hakan yasa muka zo on top of the table ta kowane ɓangare domin a ko ina labarin mu a ke,ga shi mun yi matching sosai mun dace da juna. Ganin yanda ake tattauna zance na ba ƙaramin jindaɗi ya saka ni ba tare da ɗaukar manyan burika a rai na waɗanda ni ke fatan cikar su watan wata rana musamman idan na wayi gari na buɗi ido a cikin gidana a matsayin matar Naseer Sani Wurno.
🪐🪐🪐
Zaune yake a office ɗinsa da ke shagon su na Wali's furniture yana duba new design da Siddeeq ke nuna masa waɗanda za'a ƙera musu cikin kwanakin nan......
Da wani ɓacin rai Kanoma ya banko door ɗin ta sa ya shigo kai tsaye ya na mai jefa masa wayarsa murya cike da baƙin ciki ya ce.
"Usman duba wannan abun ka gani, hope ba brain ɗina ce ke neman taɓuwa ba!"
Kallo ɗaya yayiwa pictures ɗin ya kawarda kai gefe cikin ko in kula ya ce.
"Brain ɗinka is functioning well Bilal, ba gizau ba ne Safnah ce"
Cikin shock ya ce.
"You mean that you know about it?"
Kallon sa yayi da kyau sannan ya ce.
"Yeah I know....."
Wata irin cakuma Bilal ya kai masa kamar wani zautacce yana faɗin.
"Wai Usman ko ka zare ne? Matar da zaka aura ce fa a nan ake shirin ɗaura mata aure gobe..."
Miƙewa yayi tsaye sannan ya saka hannayensa ya zare hannuwan Kanoma daga kan shoulders ɗinsa yana facing ɗinsa da kyau calmly ya ce.
"She choose him Bilal, ta faɗamin cewa na je na nemi wata ita ba zata aure ni ba, so I have no choice rather than na manta da ita...."
"And kuma kake rayuwa babu alamar wata damuwa a tare da kai?...." daga haka sai kuma ya girgiza kansa ya ce "You are the most Craziest, Mad and a stupid friend I ever have in my life Usman" Calmly ya sake kiran sunan abokin nasa ya ce.
"Bilal! cool down please! tabbas na so Safnah so babba wanda ban san ma da me zan iya misalta shi ba, but she chooses to ended our relationship because of him, I have nothing to do because babu dole a soyayya. Bilal! haƙiƙa don mun rabu da Safnah ba zan ce maka rayuwa ta tazo ƙarshe ba, but zan ɗauki dogon lokaci abin na damun zuxiyata because she betrayed me and break my trust.... "
Cikin tsananin ɓacin rai Bilal ya ce.
" Ƙyale ta! Munafuka azzaluma... "
Da sauri Xunnurain ya ɗaga masa hannu alamar ya yi shiru sannan ya girgiza kai ya ce.
" Bilal kada ka yi haka, ni wallahi na yafe mata bana jin haushin ta ko kaɗan, kada ka manta muma muna yayyu muna da kuma ƙanne kamar ta, kawai mu yi mata fatan alheri....."
Kafin ya iyar da rufe bakin sa, kwatsam ya tafi luu! Zai zube zuwa ƙasa, cikin sauri Bilal da Siddeeq wanda zuciyar sa ke wani irin azalzala tun ɗaxu suna rige rige wurin tare sa domin hana sa kaiwa, sai dai ina! Bakin alƙalami ya riga da ya bushe domin tuni yakai ƙasa wanwar babu ɗigon numfashi a tare da shi..........
OUM AMEER