ƳAR KARUWA Chapter 10
*ƳAR KARUWA* Arewabook@ayshadanaabo
Paid book
©️ Aysha Dansabo Lemu ✍🏻
Free pages
Chapter 10
A rikice Hajiya Inna da Tabawa dake zaune suna hira suka ɗago kansu tare da sauke ganinsu akan Jannat data shigo kamar an jefota,Hajiya Inna tace,"Subhanallahi! Lafiya Hafsatu,me yafaru?" Jannat ta nufi wajen Inna tare da zubewa a jikinta tana sake sakin kuka cikin ƙaramin sauti,cikin muryar kukan take faɗin,"Aliyu ne Inna,yace ba zai iya rabuwa dani ba" Hajiya Inna ta saki salati tana faɗin,"Dama shine baƙon da aka ce kinyi ɗazu? Dolensa ko ya rabu dake tunda ba tare kuka zo duniya ba,wato ya dawo garin ne ya maido miki da hannun agogo baya muna murna kin fara samun nutsuwa? Oh! Ni Hafsatu." Hajiya Inna tayi maganar tana sake rungume Jannat a cikin jikinta yayin da Tabawa itama ta shiga rarrashin Hafsat tana bata baki akan cewa tayi haƙuri karta maido da hannun agogo baya.Da ƙyar suka samu Jannat tayi shiru sai faman sauke ajiyar zuciya take a hankali,Hajiya Inna ta cigaba da shafa bayanta tana sake bata shawara akan tayi haƙuri tayi yaƙi da zuciyarta ta cire soyayyar Aliyu daga cikinta."Hafsatu ƙiyayyar Uwar miji masiface koda ace baki da tabon da za ta yaƙeki da shi,don haka kiyi haƙuri domin daga Sanata har Hajiya Salmah sun fice daga kaina tunda suka nuna mana su ƙananun mutane ne." Hajiya Inna ta ƙare maganar tana jin zafi da ciwon yadda Iyayen Aliyu suka iya rufe ido suka faɗi maganganu tare da rusa ranar auren da aka saka a tsakaninsu bayan har an kawo kayan al'ada,Allah yaso ba a yi azarɓabin raba kayan ba aka jinkirta sai gashi komi ya watse abin tamkar sihiri ko waɗanda aka tunzuro suyi rashin arziƙi."Inna ba kuka nake yi na cewa wai nima bazan iya haƙura dashi ba,ina kuka ne na tausayin yadda Aliyu ya dawo Inna,yana sona,wallahi Aliyu yana mini soyayyar da bazan iya misaltawa ba amma haƙuri zaiyi domin nima bana ji a yanzu zan iya aurensa koda da goyan bayan Iyayensa ne,shi ma kuma kuyi masa addu'ar Allah ya cire masa soyayyata Inna please!" Hafsatu ta ƙare maganar cike da magiya wasu hawaye masu zafi na sulmiyowa daga cikin idanunta.Ta tashi da ƙyar ta nufi ɗakinta bayan Inna sun gama rarrashinta da bata baki,sun kuma tabbatar mata da cewa za su taya Aliyu da addu'a domin tabbas suma shaida ne yana ƙaunarta kuma bashi da laifi akan dukkanin abinda ya faru sai ma cutar dashi da aka yi wajen rabashi da abinda zuciyarsa ke so.
*******
Daga ɓangaren Abbah kuwa bayan fitar Jannat bai bar Aliyu ya tafi ba sai da ya sake yi masa nasihu masu ratsa jiki,jinsa kawai Aliyu ya dinga yi amma tun fitar Jannat daga ɗakin ya daina gane komi illa wani irin ciwon kai da jiri da yake ji.A haka yayi ma Abbah sallama,Abban bai barsa ba saida ya rakashi har wajen mota.Aliyu yaso matuƙa ya roƙi Abbah akan ya bashi damar sake ganin Jannat kafin ya tafi,amma sai Abban yayi masa wani irin kwarjini da ya kasa furta masa komi.Abbah yayi masa fatan alkhairi tare da sake jaddada roƙonsa ga Aliyu akan ya haƙura da Jannat ya barta ta fuskanci karatunta,domin babu amfanin ya cigaba da bibiyarta alhali Iyayensa sunce sun zaɓa masa ƴar uwarsa a matsayin wacce suke so yayi rayuwar aure da ita.Haka Aliyu ya ja motarsa ya bar gidan yana ji tamkar zuciyarsa za ta kama da wuta tsabagen yadda take masa wani irin zafi da raɗaɗi,sosai yake jin wani irin motsin son Jannat da zazzafar ƙaunar da yake mata na sake motsa zuciyarsa da tsananin ƙarfi.Shiyasa koda ya fito daga street ɗinsu ya hau kan kwalta a maimakon ya ɗauki hanyar gida sai ya ɗauki na hotel,domin baya buƙatar zuwa gida a wannan yanayin da yake ciki hasalima babu wanda yasan da isowarsa garin na Jos sai driver ɗinsu daya kai masa mota airport.Shima kuma ya gargaɗesa akan cewa kada ya sake ya sanar da kowa ya shigo garin,shiyasa hankalinsa kwance ya nufi hotel ɗin da ya tabbatar zai samu nutsuwa a cikinsa kafin zuwa dare ya isa gida ya fuskanci Mum ɗinsa domin sanar da ita cewa bazai taɓa auren Surayyah a matsayin macen da suka zaɓa masa ba,koda kuwa duniya ne za su haɗu domin ganin hakan ya faru.
********
"Abban Arfah lafiya naga kamar ranka a ɓace yake?" Hajiya Mardiyyah ce ta jefawa Abbah tambayar tana mai zama kusa dashi har jikinsu na gugar juna.Abbah ya kai hannu ya ɗauki cup ɗin sassanyar lemun red grapes ya kai bakinsa yayi siffing a hankali,aje cup ɗin yayi yana ɗaura manyan idanunsa akan Mamie yace,"Mardiyyah Yaron nan ne Aliyu ya zo wajen Mamana yana son maido mana da hannun agogo baya alhali ita tana iyakan bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta manta dashi,duk da cewa nasan zuciyarta tana gareshi domin da gaske soyayyar Jannat yayi ma zuciyar Aliyu muguwar kamu,so amma ya zamuyi haƙuri da junansu shine mafi alkhairy domin bazan taɓa lamuntar cin mutunci da tozarci ba,da ƙyar na rarrashesa ya bar gidannan bayan nayi masa rakiya har wajen motarsa na kuma sake roƙonsa akan ya daina bibiyarta,shiyasa gara ta zo ta koma skull a gobe kowa ma ya huta." Ya ƙarisa kalamansa yana kallon yadda Mamie ta wani taɓe baki kafin tace,"Allah sarki,to shi banda abinsa ba sai yayi haƙuri ya amshi zaɓin da sukai masa ba,nacin na mine ne?" Abbah ya jinjina kansa yace,"Hmm! Mardiyyah kenan,kina matuƙar bani mamaki akan yadda kike nunawa akan Mamana,ke ko jin nauyi da kunyar idanuna bakya yi kike nuna zallar ƙiyayyarki ga jinin Kabeeru Mardiyyah? Kabeeru fa ya ƙaunaceki tare da baki girmanki har ya koma zuwa ga Allah bai taɓa yi miki wani abu na rashin kyautatawa ba,Kabeeru yaso Ammar har fiye da soyayyar da nake gwada masa,sannan karki manta dukkanin wannan daular da muke ciki ta sanadin arziƙinsa dana gada ne Allah ya cigaba da sanyawa dukiyar albarka,ina ce ko domin hakan yaci ace kin ƙaunaci jininsa kin haɗa da naki tare da bata dukkanin kulawar da za ki baiwa su Arfah koma fiye dasu,sai gashi kin gaza yin hakan sabida wani dalili naki na ƙiyayyar wacce bata sanma kina yi ba,idan ma tasani ɗin bakya gabanta Mardiyyah domin tayi miki nisa."Ya kai ƙarshen kalamansa wani irin makirin murmushi na haskawa a saman fuskarsa ganin yadda fuskar Mamie tayi kicin-kicin tamkar za ta ɗaɗe da kuka.Cikin wani irin murya tace,"Bazan iya ba Abbansu,kome za ka ce bazan taɓa ƙaunar duk wani abu da zai fito daga tsatson Nuratu ba,don haka kadaina ma ci mini fuska domin hakan yana sake ninka ƙiyayyarsu a cikin zuciyata ne." Ta ƙare maganar tana tashi fuu ta bar masa falon.Abbah ya saki wani ƙayataccen murmushi yana jinjina kansa,cup ɗin lemunsa ya sake ɗauka yayi siffing tare da aje cup ɗin ya lalubi wayarsa domin saka kiran layin Ammar Chiroma wanda ya kirasa ɗazu bai samu damar amsa call ɗin nasa ba.Bugu biyu Ammar ɗin ya ɗaga kiran Abban,hakan ya sanya Abbah kishingiɗa a jikin seatern tare da saka wayar a speaker time ɗin da daddaɗan muryar Arch.Ammar Chiroma ya doki kunnuwarsa lokacin da ya furta,"Abbah ina yini dafatan duk kuna lafiya?" Abbah yace kai tsaye,"Lafiya Lau Ammar ya ayyuka da rashin samun isasshen lokaci?" Ammar ya amsa kai tsaye da faɗin,"Alhamdulillah Abbah,rashin lokaci kam akwaisa sosai sai a ranakun weekend muke samun hutu." Abbah murmushi yayi sosai yana hasko yadda tilon ɗan nasa ke fiddo kalaman nasa,yace cike da tsokana,"To Ammarun Inna yaushe za ka taho musha bikinka da zaɓin Mamien taka?"Ammar kawai sai ya katse kiran ya kira vedio call domin yana buƙatar su ga juna shi da Abban.Abbah ya saki murmushi time ɗin da vid call ɗin ya shigo,yayi receiving call ɗin kyakykyawar fuskar Ammar Chiroma na haskawa bisa allon screen ɗin wayar."Abbah please ka tayani sanar da Mamie cewa bamu dace da juna ba,I don't know yadda zanyi ta fahimci cewa bana son wannan haɗin please Abbah."Cewar Ammar wannan miskilalliyar fuskar tasa na sake tsumewa tamkar hadari.Abbah ya saki murmushi mai faɗi kafin ya furta,"Au baku dace da juna bane Ammar,aina ɗauka kaine da kanka kaga Yarinyar kace ka yaba?" Ammar tamkar ya saki ihu haka yake ji,da ƙyar ya iya buɗe baki yace da Abbah,"Abbah ni babu ruwana ita ce dai suka shirya hakan ita da Anty Barirah, Please Abb...." Abbah ne yayi saurin katse Ammar ta hanyar faɗin,"Kaga Ammar,ni babu ruwana da shiga shirginka da Mamienka domin kafi kowa biyewa shirmenta,abinda nake so kawai dakai shine idan baka son Yarinyar to kayi ƙoƙarin kawo mini naka zaɓin,ni kuma zan shige maka gaba domin ganin ka auri wacce zuciyarka keso matuƙar akwai ilimi da tarbiyyah ta addini a tattare da Yarinyar,ni kaina na gaji da zamanka babu aure Ammar,yanzu fa gasu Mamana shirin zana jarabarwar ƙarshe suke a jami'a kuma da zaran sun kammala nace su fiddo miji aure zanyi musu,sai kaine kana namiji shekaru talatin da biyar amma ace ka kasa fiddo macen aure ai wannan abin kunya ne Ammar,duk da cewa komi yana da lokaci amma ya dace ace zuwa yanzu kayi hoɓɓasa sai kaga Allah ya shige maka gaba,kayi ƙoƙarin fiddo zaɓinka idan ba haka ba dole ka amshi zaɓin Mamienka koda baku dace da juna ba." Yadda Abban yayi maganar in a serious manner ya sanya hankalin Ammar tashi sosai,ya rasa abin cewa sai fuskarsa daya sake tsukewa yana jin tarin rashin nutsuwa da zancen Labibah.Sun jima suna magana da Abban akan aikinsa da irin buɗi da ɗaukakan da yake sake samu a duk kwanan duniya,domin a yanzu ne yake tashen samu sabida tsabar ƙwarewarsa wajen iya zanawa da fidda taswirar gina-gine na zamani da ake yi a ciki da wajen ƙasar INSTANBUL ɗin,a matsayinsa na wanda ya karanci Architecture yayi digirinsa na farko dana biyu duk akan harkar zane.Zamantowarsa Professional a harkar wanda Ubangiji ya zuba masa fikrah da baiwa ya sanya ɗaya daga cikin manyan kamfanin dake amsar kwangilar ginin gidaje da ma'aikatu a ƙasar INSTANBUL ta ɗaukeshi aiki,suka bashi matsayi mai girman gaske domin kaf cikin masu musu zanen gidaje da fidda taswirarsu babu mai kwanya da baiwar da Architect Ammar Chiroma ke dashi.Sannan a gefe guda yana amsar kwangilar zane daga sauran manyan kamfanin dake harkar real estate,shiyasa cikin shekaru biyar zuwa shida yayi wani Shura a ciki da wajen ƙasar sabida baiwarsa da kuma ƙwarewarsa a harkar zanen gidaje da manyan estate da ma'aikatu.Sosai Abban ke alfahari da ɗan nasa wanda Allah yayi masa baiwar fikra bata wasa ba,shiyasa bashi da buri a yanzu da ya wuce Arch.Ammar Chiroma ya samu nagartacciyar mace amatsayin abokiyar rayuwarsa domin ya mori ƙuruciyarsa cikin aminci.Ya aje wayarsa bayan sunyi sallama da A.Chiroma,wani irin ajiyar zuciya Abban ya sauke yana tuna batun da suka tattauna da amininsa Prof.Mansur Bichi akan Hafsat Kabeer Chiroma,wacce yake da tabbacin zuciyarta ba a nutse take a halin yanzu ba.Bai sake neman Mamie ba kamar yadda itama tunda ta fice bata sake shigowa ba,yana nan zaune yana duba wasu muhimman saƙwanni a cikin laptop ɗinsa har aka kirayi sallar la'asar hakan ya sanya shi rufe kwanfutar ya fice zuwa masallacin dake wajen gidan domin bin jam'i.
*********
A ɓangaren Hafsat Kabeer Chiroma kuwa ta jima tana a kwance bisa sofar dake ɗakinta bayan kammala cin abincinta tana kokawa da zuciyarta akan tsananin tausayin halin data ga Aliyu Wase a ciki,domin ba ƙaramin rama da fita hayyacinsa taga yayi cikin kwanaki Goma da rusa zancen aurensu da akai ba.Da ƙyar ta yunƙura ta tashi time ɗin aka kirayi sallar la'asar ta faɗa toilet domin ɗaura alwala,koda ta fito direct wajen sallaya ta nufa ta tada Sallah.Bayan ta idar ta jima a zaune tana yi musu addu'a ita da shi akan Allah ya tausaya musu ya cire musu soyayyar junansu ya kuma musanya musu da mafi alkhairin abokanan rayuwa,ta zarce da karanto dukkanin azkar ɗin data saba yi na maraice kafin ta shafa addu'ar ta miƙe domin cire hijab ɗin jikinta tana ji zuciya da hankalinta gabaki ɗaya sun tafi akan son komawarta Kd cikin gaggawa.......✍🏻