SAIFUDDEEN

8

by @hijjartabdoul06

******Sai Magriba sannan ya koma gida da sauran ruwan da ya yi ta siya da zarar ya ƙare. Saura befi uku ba ya rage masa. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya shigo cikin unguwar ta su. Ruwa kawai ya ɗebo a fanfon ƙofar gida ya yi wanka a gurguje yana sauya kaya zuwa na shan iska. Ya tafi masallaci yana dawowa ya jefa ɗan wake ya ci abinsa, ya zo zai sha ruwa kawai ya tuno da ita. 'fulaamin' ya faɗa a ran sa yana sakin murmushi tare da girgiza kan sa. Yana gama ci ya wanke kwanon da ya ɓata duka kafin ya karkaɗe shimfidarsa ya fice daga gidan.

Be taɓa zama a majalisar yan unguwar ta su ba sai yau. Daga ka sha kwanar layin na su a wurin mai shayi da biredi ake zama. Kullum de yana ganin su idan ya dawo daga unguwar su Farooq, ya tsaya su gaisa. Ba ƙaramin burge shi suka yi ba dan ba gulmar mata balle kuma gulmar ƴan unguwa sai musu da ake taftakawa tsakanin ƴan ball. Ba su da zance sai na ball. Kuma sai dare ake zama a wurin domin shine kowa yake available sai su kai har ƙarfe ɗaya a wurin. Shi de Saif banda dariya ba abinda yake yi, shi ba kallan ball ba, shi ba buga ball ba. Dan haka ne san komai ba a harkar sai de kawai ya kalle su ya yi dariya abinsa. Duk wanda ya siya indomien ce ko shayin ana yi masa Bismillah yace A'a ya ƙoshi. Sosai suka ɗebe masa kewa kafin Malam ya zo siyawa ɗan sa ɗan yaye bread ya gan shi.

"Saif kar ka ce min kai ma ka fara zaman ɓata wannan lokacin anan wurin".

Nan fa samarin wurin suka fara yiwa Malam a'a Malam muma fa da aikinmu.

Suka faɗa masa kkwa da abinda yake faɗa sai de cike da girmamawa ake zancen dan sun saba da sosai da shi, Malam ba ruwan sa shima ya faɗa ne dan ya ji abinda za su ce.

"Ai gaskiya na faɗa, ba ku da aiki sai musu akan abinda be taka kara ya karya ba. Kuma duk akan wata ball. Indai ball ce tunda na dena kowa ma zai dena".

Dariya suka sa sosai. Kafin ya tafi ya bar su.

"Sunanka Saif ne?

Cewar mai shayin yana zama a kusa da shi. Gyaɗa masa kai Saif ya yi.

"Ni kuma Adams".

"Ohh!

Saif ɗin yi murmushi cike da rashin sabo. Ya jima sosai a wurin har ya fara jin bacci kafin ya tashi ya yi musu sallama ya koma gida. Ko da ya za zo kwanciya sai da ya tuno da Fulaamin. Ya yi dariya kawai yana tashi ya yi sallahr wutri ya kwanta.

Washegari dake ya samu aikin ɗaukan siminti sai be yi talla ba, har Magriba suna aikin sai dare sannan ya dawo. Sai ya mayar da kan sa busy, shine wannan shine wannan baya wannan baya wannan, ga wani irin sabo da suka yi da samarin unguwar. Hakan yasa shi saro rake yake siyarwa. Ba ƙaramin jin daɗin hakan suka yi ba. Suna shan take shan tafka musu, shi da Adams suyi musu dariya. Wani sa'in Saleem har nan ɗin yake zuwa ganin Saif ɗin ya dawo unguwar ta shi dagaske ya kaurace musu. Kuma daman yace musu ya fara siyar da rake da daddare. Sosai ya ke maida kan sa busy dan kada ma ya je gidan su. Idan Abbi ne zai bishi har inda yake ya gaida shi. Haka ma Mommy zai je office ɗin ta a ranar da ya san ta fita aiki ya gaida ta. Tun tana masa faɗa har ta gaji ta haƙura ganin faɗan da take yi masa ne yake sa shi sake nesan ta kan sa da shi. Har aka cimma wata uku be sake taka inda gidan su yake ba.

*******A ɓangaren Safwan kuwa da Sufyan abin sai de ace Allah ya kyauta. Dan abubuwa da yawa sun haɗe sun caɓe musu. Abu kaɗan Safwan ya yi za su yi faɗa da Sufyan, kwata-kwata Sufyan haushi Safwan yake ji musamman da ya zamana yanzu yana samun kuɗi sosai. A cikin lokaci ƙanƙani har ya sauya wurin sa suna ya sa Lollipop ya ji kuma ƙishin-ƙishin ɗin zai koma Kaduna ko Abuja da zama domin gina kasuwancinsa. Abin ba ƙaramin ƙuna masa rai ya ke ba. Sosai yake nuna baƙin cikin sa a fili yana tambayar kan sa taya za'a ce hakan ta faru? Hakan ya sa shi hasala sosai yana neman sa da faɗa, dan duk sanda suka yi faɗa shi ake bawa Gaskiya shi kuma Safwan a bashi rashin gaskiya. So yake kawai a ƙwace wannan wurin da aka raba musu a haɗa masa, idan ba'a haɗa masa an bashi ba kuma kawai a hade shi kamar shi da. Ta hanyar taƙalar shi suna faɗa ne kawai yake ganin Abbi zai yi hakan..sai de har yanzu Abbin be yi ba, amma ya tabbatar da zai yi ɗin. Shi yasa a yanzu yake kam shirya masa wani abu. Abun da zai sa Abbin dole sai ya ƙwace duk wani abu da ya bashi. Domin ya ji labarin kwangilar da Abbi ya ɗauka ta kula da marasa lafiyan ido da Cancer da kuma ciwon ƙoda da hanta kyauta na tsawon shekara ɗaya, wanda a da na wata uku ko biyu zuwa ɗaya ake yi. Duk na yarda aka sa, shi ake ɗaurawa akai, ba kuma sa cike iya adadin watanni yake cewa a an rufe, kuma ya ji labarin Safwan Abbi ya bawa. Yayin da za'a samu kuɗi bana uban wasa ba. Ada idan irin haka ta faru shi ake bawa, amma yanzu aka bawa Safwan? Sosai abin yake sosa masa tun ranar da ya ji labarin an bashi ɗin. Hakan yasa shi ɗamarar sake riƙe damtse sosai ganin cewar ya kawar da shi kawai a huta.

Yayin da shi kuma Safwan kwata-kwata be san yawan wannan faɗan da suke yi da shi, wallahi ya yi bala'in gajiya, zai iya bar masa komai domin ya samu salama da hutun wannan abun, amma sai de ya rasa gane kan matsalar inda Sufyan ɗin ta dosa. Sufyan faɗan da rashin haƙuri, shi kuma zuciya da gardama. Idan ya ɓullo ta nan sai ya ɓullo masa ta nan. Ya rasa gane kan komai da komai. Ga de kuɗi suna shigo masa bayan aikin da ya haɗu yake yi da Company wurin uku suna biyan sa, sannan ya zuba share ɗin sa a ciki. Zai yi musu aiki, su biya shi, sannan ga kuɗin share ɗin sa dake tare da su. Gashi da wayon iya aiki da dabara. Baya abu shi kadai sai ya tambayi shawarar Saif da Abbi....

*******Yau ta kama juma'a duk ranar juma'a kuma baya zuwa ko ina, domin wanki yake yi, ya kimtsa gidan sa, idan ya gama da wuri ya yi shirin masallaci ya tafi banki, ya je ya kai kuɗin sa daga can ya wuce. To yau ɗin ma de ya yi ɗan gyaran gyaran sa, sai de fa ya tashi da zazzabi mai tsanani zafi a jikin sa, ga ciwon kai dake addabar sa sosai, amma duk da haka sai da ya shirya abinsa tsaf sai ƙamshin turarensa yake yi yana baza ƙamshi ya rufe gidan sa ya fita. Yana fita yaga Sufaina da Safwan a bakin layin su, suna neman gidan sa.

"Liliiiii".

Ya faɗa da ƙarfi yana yin wajen su. A tare suka sakar masa harara kafin Sufaina ta juya zata shige mota, haka ma shima Safwan ɗin. Murmushi ya yi mai tattare da nunawa cewa fushi suke da shi kenan.

"Lollipop am sorry ki yi haƙuri".

Ya faɗa a hankali yana mai kama kunnen sa.

"Iya ita kawai zaka bawa haƙurin?

"Kana da matsala Lili".

"Haka ma zaka ce?

"To na ji yi haƙuri".

Sufaina tace,"Wallahi Ya Saif abinda ka ke baka kyautawa. Yaushe rabon ka da mu? Yaushe rabon da ka zo inda muke? When last na ganka? Har na manta ya kalar ta ke".

Dariya sosai zai yi sai kuma ya yi saurin gimtsewa a hankali ya ƙara sa ya bata side hug yana furta.

"Am so sorry Lollipop ki yi haƙuri".

Turo baki ta yi gaba kafin a hankali itama ta ɗan bashi side hug ɗin ya saki murmushi mai sanyi yana kalln Safwan.

"Jikin ka zafi sosai Lili".

Jinjina mata kai kawai ya yi yace.

"Asibiti zan je".

Safwan yace,"zan haƙura kawai, idan ka shiga mota muka tafi inda zaka je sannan na kai ka asibitn".

"Ohhh!

"Yes!

Ya faɗa masa yana ɗage masa gira. Ba yarda ya iya ya shiga gaba, Sufaina ta shiga baya, sai ta dawo tsakiya. Bayan ya sanar da shi inda zai je.

Sufaina tace, "Problems everywhere a gida da baka nan".

Juyowa ya yi ya kalleta as in what happened?

Safwan ya ce, "Uhmm".

Sai ya yi shiru kafin yace, "Ya Saif, abubuwan dake faruwa bansan ta ina suke ɓullowa ba. But the best solution shine zan bar gidan kawai. Na koma Abuja ko Kaduna da zama. Na gaji ba zan iya ba. Shine Babba, shike yin ba daidai ba, amma ake ganin laifina, from the beginning shine ya fara abinda be dace ba a rayuwar sa. Laifina ne dan zuciya ta bata san shi?

"And that wicked bitch wife of his, bata da aiki sai aikena, saboda kawai she's pregnant? Dan uwarta akan ta a ka fara samun ciki or what? Mommy idan ban je ba baga yarda take min ba, har fushi ta yi da ni".

"Haka mutanen dake zama da surukai a gida suke yi ne ko me? Ko kuma ta mu surukar ce haka? Duk ranar da aka ce yau Mommy bata gidan nan ta fita aiki baka ga yarda take mulka all maids dake gidan ba. Meyasa? Akan me?

"Jiya kuma tace da Sufaina wai zata ɓarar mata da ciki a gaban Yaa Sufi, baka ga marin da ya mata ba. Yadda ake san a kan shi aka fara haihuwa da samun ciki, ƴan wahala kawai".

Ya yi shiru yana ɗan huci ganin sun tsaya a danja. Ya rufe idan sa kawai yana jan tsaki, da ɗan sosa kan sa.

"Zan sha ruwa".

Cewar Sufaina tana nuna pure water. Zuge glass Saif ya yi ya miƙa ashrin aka basu biyu. Kawai ya yi murmushi yana mika mata guda ɗaya, a tsayin wata ukun da aka yi be taɓa manta ta ba, duk sanda zai sha ruwa ko yaga wani ya sha sai tuno da ita ya kuma yi murmushi. Be taɓa cin karo da yarinya ƴar renin hankali irin wannan yarinyar ba. Amma tana da sauƙin sosai ba kamar Ma'u mai majina ba. Mai shegen surutu da gardama.

Ganin sun fara tafiya ya Saif kallan Safwan uffan be ce da shi ba. Sai ran sa da har yanzun yake a bace.

"To ni de ba Mubeena ba ne, ba kuma Sufyan ba ne. Idan zaka saki rai ka saka, idan ba haka ba kuma zan iya fitar maka a mota. Banga dalilin da zaka ɗauko kana haɗe min fuska ba".

"Ya Saif ba zaka taɓa ganewa ba, ko da an yi maka bayani".

"Uhm".

"Bari na kai ka Asibitin da na ce maka Abbu ya siya. Na sa sunanka a jiki".

"Ni me yasa ba'a sa sunana ba?

"Rashin jin ki zai barki a sa ne? Shegiyar uwar kishin tsiya".

Zumɓura baki ta yi tana gunguni. Shi Saif ya san ba sunan sa aka sa ba dan Safwan din yana sanar da shi kome ake ciki. Kawai dan ya tsokane ta ne.

"The Triple S kuma?

Ta faɗa a fili tana kallan Safwan da ya sa kan sa a cikin asibitin. An gyara asibitin sosai fiye da yadda yake a baya. Sai de iya ɓarin da suke aikin iya nan aka sake gyarawa sosai.

"Kaii amma ya yi kyau".

Ta faɗa tana fitowa veil ɗin ta na kuncewa akan ta. Ƙanan kalabanta suka zubo. Ranƙwashi Safwan ya sakar mata..

"Bana san rashin hankali".

"Gaskiya Lili ka dena taɓa ni".

Ta faɗa tana turo baki, Saif ne ya je ya rungume ta yace.

"Rabu da shi".

A tsakiya suka sa ta Safwan na hararanta ita kuma tana zungura baki. Mutane sosai suka tarar a reception ɗin wasu ma bakyan gani. Tsabar yarda ciwo ya yi musu yawa abin ba'a cewa komai, idan Allah ya barka da lafiyar ba ƙaramin rahama ba ne.

San sannu suke yi musu har Safwan ya musu jagora zuwa office ɗin Ma'u. Ta gama duba wata mai ciwon ƙoda kenan tana haɗa file nata ta miƙa. Ya yi sallama ya shigo.

"Har na manta yaushe rabon na gan ka".

Ta faɗa masa tana muna masa wurin zama. Zare glass ɗin ta ta yi a hankali tana sauke ajiyar zuciya. Na alamar gajiya.

"To gashi yau na zo. Aiki ne ya riƙe ni".

"Oh!

"To ya ka ke?

"Alhamdulillah,y aikin?

"Da godiya".

"Yau ɗin ma Yayana na kawo ki duba, baya da lafiya shine na kawo shi ki duba min shi dan Allah".

"Amma ki bi min shi a hankali fa".

"Kar ka damu in sha Allah. Amma shi da ba ƙaramin yaro ba?

Murmushi ya yi kawai ya tashi ya buɗe musu.

"Ya Saif ku shigo".

Sufaina ta fara shigowa sannan shi, Safwan ya tashi ya bashi kujera, sam bata gan shi ba, shima haka be ganta ba saboda jirin dake nema ya kwashe shi.

Sai da ta ɗago lokacin shima ya ɗago kawai ta sauke shi a akan sa shima ya kalle ta.

"Rowdy!

"Cheeky?

Suka faɗa a tare. Kafin ta kalli Safwan sai ta kalle shi. Sannan ta kalli Sufaina dake zauna a gefen shi, ita Khan Sufaina tana ta kallan ta kamar wanda ta samu TV. Eh tabbas sai yanzu taga kamar, ashe Safwan da shi yake kama shiyasa har yau ta kasa ganewa sa saninin inda ta san Safwan. Ashe mai irin wannan fuskar ce suke shigen kama. Ƙanin ya fi Yayan hankali da nutsuwa sosai. Dole yace a lallabashi mana.

"Wai wannan abar ce zata duba ni?

Saif ya faɗa yana kallan Asma'u dake cigaba da file.

"Da wata da ka gani ne bayan ni?

Ta bashi amsa tana ɗagowa ta zuba masa harara.

"Wa ki ke harara?

"Wanda yaga na harare shi".

"Ni fa Safwan ka ɗauke ni anan, dan wannan abar ba zata dubani ba".

"Wacece abar?

"Ga ki nan a zaune a wurin".

Be jira amsar ta ba ya yi saurin tashi zai fita, jiri ya kwashe shi sosai, zai faɗi Safwan ya yi saurin taro shi shida Sufaina dake kusa da shi, ita kan ta Asma'un tashi tsaye ta yi jin yarda zuciyar ta ta yi wani irin bugawa lokaci kaɗan ganin zai faɗi.

"Ni ku sake ni".

Ba su kula shi suka ajje shi a gadon da ake duba marasa lafiya.

"Sannu kawai suke jera masa".

Sosai kan sa ke masa ciwo mai tsanani kawai dauriyace yake yi dan jinyar ta cinye shi sosai.

"Gaskiya ba zaki yi min allura ba".

Ya faɗa yana ganin zata zuƙi jinin shi. Jijiyar shi ta ɗaure ta ɗiba jinin nasa ga Safwan ya wani danne shi. Ganin dagaske yake bazai yadda ta duba shi ba.

Da kan ta ta je ta yi test ɗin ta dawo tana kallan masa faɗan yadda malaria ta yi kama shi. Bata yi aune ba kawai ta ji saukar mari a fuskar ta, kamar de yarda ya saba marin ta.

"Uban wa ki ke yiwa faɗan nan?

Kawai tsayawa ta yi tana kallansa. Kafin ta bawa Safwan tace ya siyo Maganin nan a wajen pharmacy dan asibitin ba babu pharmacy, ita kuma Sufaina ta aiketa ta karbo mata drip idan ta fita ta tambaya, sannan ta dawo da kallanta ga Saif dake cewa.

"Kawai zaki sani a gaba kina min faɗa? Kuma allurar da ki ke haɗawa ki san wanda zaki yi wa amma ba de ni ba....

Saukar allurar da ya ji a bayan sa ya sa shi yin shiru yana daga kwance. Ta caka masa tana mai mugun haɗe ran ta sosai. Kuma ta je ya zauna.

"Wayyo Allah na zata kashe ni".

"Innalillah wa'inna ilahirin raji'un Babaaaa".

Ya faɗa da ɗan ƙarfin. Ɗagowa ta yi ta kalle shi.

Tace, "Za'a ji ka, aji namiji na kukan allura".

Toshe bakin ya yi da hannu yana bala'in ƙwalalo ido.

"Dan girman Allah ki zo ki cire min".

"Ba ni ka rena ba? Har ka ke marina ko?

"Na dena renaki, na dena ba zan sake ba".

"Daga yau ya sunana".

"Ma'u Majina".

"What?

Ta faɗa cike da mamakin inda ya san sunan. Sai kuma ya yi saurin cewa.

"A'a sunan ki Asma'u".

"Asma'u kai tsaye?

"Anty Asma'u dan Allah ki yi haƙuri".

Sai da ta tabbatar ya ladabtu Sannan ta zo ta zare masa allurar.

"Allah ya isa, muguwa azzaluma kawai".

Ya faɗa yana zabga mata harara da ƙwalalwalan idan sa.

"Daga baya kenan".

Lokacin Sufaina ta shigo tana miƙa mata abubuwan drip ɗin. Kama hannunsa ta yi da ƙarfi zata sa masa carnular ya sa shi fara ƙoƙarin ƙwacewa, mistakenly carnularn ta cake ta, da sauri ta yar tana ganin jinin da ya fara ɗan yi saboda kartar da ta yi. Har cikin ƙasan zuciyar sa sai da ya ji wani abu ya danne masa ƙahon zuciya, saboda ciwon da ta ji. Hakan yasa shi cikin saurin ya wani kamo hannun na ta kawai yana sa auduga ya danne wurin. Sai kuma ya hau ya yi mata masifa, kamar zai ari baki. Duk abinda yake kuma kan sa masifar ciwo yake masa tamkar ya rabe biyu haka yake ji, ga tsananin jiri da ya ke kwasar shi. Amma a haka yake mata faɗa tamkar wanda ita ce ta sa ta ji ciwon. Ba shin ne ya ji mata ba. Yayin da ita kuma kawai kallan sa take yi tana jin wani irin a game da shi.

Kamar wanda ya tuna da wani abu, sai kuma ya tsaya yana kallanta shima.

"Ba kai ne ka ji min ciwon ba, kuma ka zo ka ke min faɗa".

Haushi ne ya kama shi, ganin ma yarda ya kula da ita ɗin, kawai ya yi saurin zama yana dafe kan sa. A hankali Sufaina ta matsa kusa da shi tana dafa shi. Kafin Ma'u ta ƙara ta fara sa masa wata carnularn.

"Shuuuuuu".

Kamar wanda ya zata zare masa rai, ganin irin rakin da yake yi yasa Sufaina kawai rungume shi tana kawar masa da kan gefe. Ita Asma'u abin ma bala'in dariya ya bata, in her entire life bata taɓa ganin mutum kuma babba Kuma namiji yana tsoron allura ba. Sai yau da Allah ya haɗa ta da wannan mutumin, gashi de he's so stubborn amma akwai raki da tsoro.

Murmushi ne ya suɓuce mata bata shirya ba, kafin ta yi saurin gyara fuskarta ta sa masa drip ɗin shi kuma ya yi bacci a jikin Sufaina. Ita ce ta taimaka ta ta kwantar shi sannan ta kira Safwan ya taho masa da abinci.

********Buɗe idan sa ya yi yana jin kan sa na ɗan sakawa sai de har yanzu jikin da zafi sosai. Tana zaune tana ta aikin duba patient cike da sakin fuska sai murmushi take yiwa yaron dake ɗauke da ciwon ƙona, wanda za'a fara yi masa wankin ƙoda. Abin har abin tausayi ma. Amma a haka take ƙarfafa masa gwiwar kada fa ya damu, ba wani abu ne ba. Tunda gashi kyauta za'a yi masa. Kuma ina sha Allah za'a dace. Ya dena damuwa, ƙilan ma ya sani ko ya warke gaba ɗaya?

Da wannan ne ta samu damar ɗaurawa yaron kyakkyawan murmushi a fuskar sa, yayin da ita kuma take murmushin tausayinsu. Daga nan ya fi sai wannan ya zo. Ta duba mutane sun kai goma duka masu ɗauke da lalura daban-daban, wanda kasan wani ma kawai ikon Allah ne ke sawa yana rayuwa. Ga talauci ga rashin wadataccen abinci sannan ga lalura mafi muni. Allah kenan, me yi yarda ya so a sanda ya so.

"Ya Allah!

Ya ji ta faɗa tana yin miƙa. Kafin a hankali ta tashi tsaye sai kuma a ka kira ta a waya, da murmushi ta ɗaga tana amsawa.

"Baba ina yini, ya aiki".

Baya jin abinda ake faɗa amma ya ji tace.

"Baba zan ci. In sha Allah ka cewa Mama zan dawo bada jimawa ba. Ina Ya Abdul ɗin? Ya zo?

Ta faɗa cike da excitement.

"Baba da mota na fito ba sai ya zo ya ɗauke ni ba. In sha Allah da wuri zan dawo".

Daga haka ya suka yi sallama tana murmushi kafin ta tashi ta je ta wanke hannunta sannan ta zo ta fara shan alawa.

"Ke! Zo ki cire min wannan abun".

Ya faɗa yana turo baki, kallan ruwan ta yi tace.

"Ka bari ya ƙare ya kusan ƙarewa".

"Fitsari da kashi nake ji ko zaki kai ni na yi da drip ɗin?

Dafe kai ta yi kawai tana girgiza kan ta. Ko kunyar ta be ji ba, wai fitsar gatsal da kashi ko sakayawa ai sai ya yi ko a matsayin ta na macen da besani ba. Ai akwai kunya. Ta sowa ta yi cire masa har wani su cije baki. Kamar ta ta dake shi ma ta ji tsabar takaici. Yayin da ya ɗan kalli hannunta yaga ciwon dake wurin kamar ma bata ji ciwon ba dan dama ƴar karcewa ce ta yi.

"Aka ce bakya ji".

"Ka ce me?

"Ba sai kin ji ba uwar gulma".

Taɓe baki ta yi ta rabu da shi kawai. Harya tashi ya yi saurin komawa ya zauna yana dafe kan sa. Matsowa ta yi kusa da shi tana yi masa sannu. Aka turo ƙofar tare da yin sallama Abbi ne sai su Safwan da'alama daga masallaci suke.

Yana ganin Abbi ya wani narke yana sakin kuka cike da tsantsan Shagwaɓa da sakalci, da saurin Abbin ya je ya rungume ɗan sa,shi kuma Saif ya yi bala'in shigewa cikin jikin sa yana sakin ajiyar zuciya. Cike da so sosai Abbi ya shiga shafa kan sa, sai ka ce irin uwa da ɗan ta ɗin nan da ta yi shekara bata gan shi ba, haka Saif ya duƙunƙune a jikin Abbi.

"Yana da buƙatar ya ci abinci".

"Ga abincin da Safwan ya kawo masa".

Ta faɗa, ta faɗa tana sake bashi. Da kan sa Abbi ya bashi abincin ya ci sosai, kafin ya sake komawa bacci batare da ya yi sallahn ba. Sai can zuwa yamma sannan ya tashi lokacin ita ta tafi sai Safwan kawai da Abbi. Tare da su Abbi ya tafi gida domin ya warware shi kaɗai a gida waye zai wani kula da shi....