SAIFUDDEEN

Last free page.

by @hijjartabdoul06

********Babu kowa a office ɗin, domin yau weekend masu gadi kawai kuma ba su hana shi shiga ba, domin sun san ko shi ɗin waye. Kawai zallar annuri ne da murmushi ke fitowa a akan fuskarsa. Har ya samu nasarar buɗe office ɗin ganin ba'a sauya komai ba daga wancan da ya sani, key ɗin ne de da yake amfani da su wani lokacin idan kamar da weekend irin haka idan har wani abun ya kama ya zo office ɗin. A kan kujerarsa ya zauna, last paper kuma last file dake kan desk ɗin kawai ya ɗauka yana buɗewa. Page ɗin farko da ya gani baƙarmin girgiza shi abin ya yi ba. Kafin ya shiga buɗe saurin paper ɗin dake cikin file ɗin, information akan wani sabon company, ya jima da jin labarin Companyn. Domin su companyn za su nema ka su baka aiki sannan da kuɗin ka zaka yi aikin, ka kuma yi sighing contract ɗin iya adadin kuɗin da ka ke so, da zarar ka kammala aikin, muddin ya yi musu, za su baka kuɗi ninkin abinda ka buƙata, amma fa idan aikin be yi kyau ba. To basa asara, kuma ko naira ba za su baka ba na iya abinda ka yi asarar sannan su kwace kuɗin da suka baka. Ba kuma ace musu an fasa aiki sai de su , su ce sun fasa, domin za su cika tarar ɓata musu lokacin da ka yi. Komai na su a tsare yake, komai yana tare da hujja suna kuma da manyan lauyoyi da suka tsaya musu aiki da hujja da kuma doka. Domin abun yarjajjeniya ce, domin da baka amsa ba, ba zaka yi ba, ba kuma zaka fara ba, sannan ga komai na su nan a rubuce bisa tsari.

Juyi Sufyan ya yi akan kujerar cike da samun nasara ta farko yana mai ɗaukan numbern su da komai har email ɗin su. Kafin a hankali ya buɗe desktop computern sa, itama be sauya komai ba, wanda yake amfani da su ne.

Wani ɗan iskan murmushi ya yi mai sanyi sosai kafin ya sa Flash ya fara kwashe dukkan wasu kyakkyawan aiki da na sa masu kyau da muhimmanci. Ya rasa inda yaron yake samun wannan talent ɗin mai bala'in kyau haka? Shi kuma gashi nan ko oho ya kasa cigaba sai faɗuwa. To wai meke faruwa ne ma wai?

Amma ba komai yanzun zai yi kuɗin shima, duk da cewar ya ga akwai risky sosai ayin abinda yake shirin yi ɗin. Amma to ya zai yi? Safwan yake so ya kaudar daga gabansa ko zai samu ya shaƙi iska dakyau. Wani murmushin kawai ya yi yana ajje komai yarda ya gani sannan ya zare Flash ɗin sa yana mai sake duba file ɗin nan da kyau sannan ya sake yin murmushi ya fito. Har harabar wurin inda aka yi masu mararraba da na sa wurin. Daga saman wurin yaga yarda ya sa sunan Sufaina ɗoɗar da shi. Sai ya yi murmushi kawai yana girgiza kan sa. Dan wani irin haskowa ya yi kwana kusa za'a zo ana ruguje nan wurin ya siyar da shi.

Saƙo ya fara turawa companyn ta wani mail ɗin daban da yake wani aikin ba ainahin mako ɗin sa na office ba, kana ganin fuskarsa zaka ga zallar annurin dake fita a cikin ta, domin yasan tarar da za'a yiwa Safwan baƙaramin tara ba ce. Tara ce mai girma da sai ya siyar da wannan Lollipop abun nasa da ya sa. Idan ya yi hakan kuma ya tabbatar ya gama ruguza shi. Cikin sauƙi zai yi hakan batare da kowa ya zarge shi ba. Sannan shi kuma ya je ya maye gurbinsa ta hanyar copying ɗin idea ɗin sa da ya sata.

"Am so sorry my little brother, banda wani zaɓi bayan wannan".

Ya faɗa a fili yana wani irin abu da baki.

"Safwan Assiddeeq".

Ya faɗa yana sakin dariya shi kaɗai. Alamar daɗi kashe ni....

*********Farooq ne ya je gidan su Hafsah domin ya gaida Ummanta, ya jima be zo ba. Itama Hafsahn tunda aka yi auren sau biyu rak ta fito kawai, shi be san wanne yawon da ba wani abu ne muhimmi ba. Gidan su kuwa be bari ta je ba. Umma ta yi faɗan har ta gaji haka ita kan ta Hafsahn ta barshi kawai ta zuba masa ido, ita de tunda ya barta ta je na su gidan su, babu ruwanta balle ta yi masa shishshigi a dangin su, gidan su ne, ƴan uwan sa ne bata da ja akai sai abinda ya ce mata.

Umman na zaune ita sai su Jabir ɗin basu fita ba, ya yi sallama a ƙofar gidan, Jafar ɗin ya fita ya leƙa.

"Ya Farooq ka shigo mana".

"Umma tana nan?

"Ehh tana nan, bari na faɗa mata".

Ya faɗa yana juyawa, ba'a ɗauka wani dogon lokaci ba sai gashi nan ya dawo. Kan sa a ƙasa ya miƙawa Jafar ledan hannunsa sannan ya shige yana masa jagora.

"Farooq kai ne?

Ɗan murmushi ya yi yana sunkuyar da kan sa wai shi kunyar suruka. Ita Umma dariya kunyar nan take bata daga shi har Saif idan suna abin kunya ba su iya ba. Kawai kan ta ta girgiza suna gaisawa sosai da shi.

"Kuma ake ta hidima damu ko? Har yanzu bazaka dena bawa yaran nan kaya a kyauta ba idan suka zo siya ko?

"Kai Umma bakomai. Ai anzama ɗaya".

"Haka de ka ce".

Jabir yace, "Ɗazun nan Hameed ya bar nan".

"Me ya zo yi?

Jafar yace, "Baka sani ba?

Alamar ya yi da fuska irin me?

"Taab, Ya Farooq, Hameed ne yake san Nafisa, har Tahfiz ya shiga Asabar sa Lahadi saboda da ita".

Ɗan murmushi Farooq ya yi kawai dariya na so ta kama shi tunowa da Baba idan ya ji wannan labarin.

"Shi Hameed ɗin?

Ya faɗa sosai fuskar sa ke fitar da annurin dariya.

Umma tace, "Kai Shirmen yara kuma? Wanne bangani ba. Allah de ya kyauta".

"Ameen Umma".

Jabir ya faɗa.

Jafar yace, "To Umma Hameed de ya yi kamun fa Nafisa, ba kuma wanda za'a bawa sai shi".

"Ai daga kai har Hameed bansan wanda ya fi wani hankali ba".

Jabir yace, "Kai kuma sai ka koma san Hameedah ka ga sai ayi tuwo na mai na".

"Rufa min asiri, ina ni ina Baba? Ba zan iya ba".

Dariya Jafar ya yi sosai dan ba wanda be san halin Baba ba a unguwar ta su. Shigowar su Nafisan ce ita da Halisa yasa Farooq kallan Nafisan sai kuma dariya ta so ta kama shi amma de ya dake yana kallan su yadda suke gaida shi.

"Har antaso ?

Ya faɗa duk da ya san ba'a tashin ba dan nan Hameedah take yi.

"A'a Yaya Farooq kuɗin makaranta ne muka manta bamu kai ba".

Inda Nafisa ke cewa, "Umma wallahi yunuwa nake ji".

Jinjina kai kawai ya yi, ya tashi yana zaro dubu ɗaya ya bata.

Yace, "Gashi ku kai kuɗin makarantar toh".

Ya fice be jira godiyar su ba, suka haɗu da Baba ya juya zai tafi.

"Mtsww".

Ya ja tsaki. Farooq wucewa ya yi, ya ji. Halisa na cewa.

"Baba tunda yau Allah ya kawo ka. Baba ka taimaka ka bamu kuɗin Tahfiz da na islamiyya Wallahi yau koro mu aka yi aka ce ba za'a mana alfarma dan Allah Baba".

Tsak Farooq ya tsaya har ya ji ƙarshen zancen. Hakan na nufin Baba bama ya zuwa inda suke kenan ko me? Sai kuma ya ji Baban na cewa.

"Da ni nake biyan ku? Uwar ta biya maku mana, iskancin banza iskancin wofi. Banzo danna ɓata lokaci na ba. Ke Samira ki jawa ƴaƴanki kunne. Kar su sake tambayata wani abu. Da kuna so ai da kun bin inda nake kun kwashi arziki".

"Baba...

Kallan da Umma ta yiwa Jabir ne yasa shi yin shiru yana kumbura fuskarsa. Farooq be gama jin zancen Baban ya tafi kawai yana mamakin wanne al'amari ne wannan ɗin. Kai tsaye gidan su ya wuce tunda ya bar yaro a shagon na sa.

"Ya jikin Saif ɗin?

"Umma da sauƙi".

"Allah ya ƙara lafiya. Ko jikin nasa ne ya yi tsamari haka?

"Me ki ka gani?

Ya tambaya yana kallanta.

"Gani na yi duk ka yi wani iri da kai ai".

Ɗan murmushi ya yi yace.

"Umma, daga gidan su Hafsah nake".

"Me ya faru?

Ta tambaye shi tana kallansa. Iya abinda ya ji kawai ya sanar da ita tace.

"Ai tunda aka mayar da auren Babar Mubeena baya zuwa gidan, shi ya koma sabon gida. Sana'ar da take yi kuma duk bashi sun hanata kuɗin".

"Ba naga su Jabir na yin napep ba?

"Yarda na ji Hameed na cewa, jiya da suka ɗauko Baabar ta su daga gidan Mubeena sai suka tsaya suka siyawa su Halisa kayan shan ruwa suna ramuwar azumi, shine fa suka biyo su kawo kafin ba su fara sauketa ba. A ƙofar gidan ta ce su dena jin napep ko ta tsine musu".

"Ba zai iyu ace sun zo suna kashe kuɗin su akan wata banza ba da bata damu da su ba".

"Ka ji yarda aka yi".

"Amma bata kyauta ba".

Ɗan taɓe baki Umman ta yi kawai.

"Umman tausayi take bani wallahi Umma. To idan ba dama a raba auren mana....

"Ka so ma?

"Ba ruwan ka Umar, ka fita a harkar sun ɗin nan. Idan taimakon su zaka yi ka yi, iya gwargwadon ka, amma zancen su raba aure be ta so ba. Ba ruwan ka.....

Shide kam shiru amma yana tunanin Hafsah to ta san wannan zancen ko kuwa bata sani ba?

Shigowar Hameed ce yasa shi tunowa da zancen Jabir. Ehh dole ya dawo gida tunda Nafisa ta dawo. Ai da sai ya koma secondary school tunda ita ma bata kammala ba.

"Yaya ina kwana".

"Lafiya, kai ma koro ka aka yi?

Kai tsaye yace, "A'a break aka yi...

"Yaushe aka fara break a Tahfiz ana dawowa gida?

Shiru ya yi ya fara tsuke baki ya na jan sumar kan sa. Be je ga bashi amsa ba.

Farooq ya sake cewa, "Ina Hameedah kuma?

"Uhm...

Ya rasa abin cewa. Taɓe baki Farooq ya yi bece da shi komai ba.

Sai kuma yace, "Yaya dan Allah zan samu ɗan ɗari biyar a wurin ka?

"Umma ke ma ki ɗan ban ɗan ɗari biyar dan Allah".

Umma tace, "Me zaka yi da kuɗi har dubu ɗaya Hameed?

"Kai Umma turare zan siya".

"Turaren kuma har dubu ɗaya Hameed?

Turo baki ya yi yana zama a kusa da ita yana kallan Farooq da ke kallansa. Zai yi magana Baba ya shigo gidan da sallama.

Farooq yace, "Yanzu Baba ina ka je ka? Allah yasa ba kasuwa ka je ba. Tsakani da Allah ka ke wahalar da kan ka, kana zuwa kana yiwa mutane dako da mutuncin ma ka da kimar ka Baba?

Cewar Farooq ganin kaya a hannunsa.

Baban tsayawa ya yi kawai yana ganin Farooq ɗin yarda yake faɗa masa magana.

"Gaskiya Baba kawai ka dena".

"Kuma kasan ba lafiya ce ta ishe ka ba. Kawai dan ka ke ja min zagi a gari a wurin mutane".

Tsaki Baban ya ja ya je ya samu kusa da Hameed ya zauna yana ƙin zama a tabarmar da Umman ta shimfida masa, ya shiga baje kayan da ya siyo musu batare da ya kula da Farooq ba.

"Ungo nan, wannan naka ne".

Ya faɗa yana miƙawa Hameed wata shadda mai kyau blue. Ya ɗauko lace da doguwar riga ya miƙawa Umma. Hameed cike da farin ciki sau godiya yake yi masa.

"Wannan na Auta ne"

Ya sake ɗauko lace da Atampha ya bawa Umma yana cewa wannan nata ne. Sai cire nasa Farin yadi ya miƙawa Umma yana cewa nasa ne, sauran kuma ya fito da su Umman ta gani, lace ne da doguwar riga irin na Hameedah amma kalar ta banbanta, da shadda ash, da light blue. Ya mikawa Umma Light blue.

"Na Saif ne wannan, kai kuma idan ka ga dama ka ɗauka, idan baka gani ba, ka zubar su a shara dan uban ka".

Sosai suke yi masa godiya banda Farooq ya haɗe rai sosai yana so ya ji daga ina kuɗin ya fito.

"Wai dan Allah Baba...

"Farooqu kai ne ka haifeni? Ko nine na haife ka? Faɗa min na ji".

"Baba kawai bana so ka ke wahala ne ai".

Taɓe ta yi yace, "Bara na fara a gidan mai".

Ya kuma haɗe rai ba zaka taɓa cewa ba haka ba.

"Bara kuma Baba?

Suka haɗa baki wurin faɗa har Umman da ta kasa riƙe mamakinta.

"To ko zaku hanani ne?

"Amma bara Baba? Ba gwara dakon ba ma".

Hameed ya faɗa kamar ya saki kuka.

"To ko zaku hanani? Ba gashi na samu maku kuɗi ba har na siyo maku kayan sawa kuna darwaje haƙura kuna dariya".

"Ko sata na je na yi?

"To ni na gaji da zaman banzan nan da nake yi, banda aiki sai zaman kofar gida kowa ya zo wucewa ina amsawa masa gaisuwa ya mai karɓar gaisuwar makoki".

Ya faɗa yana sa takalaminsa ya fice ya bar su da mamaki. Wallahi Baba ya iya rikicin gangan, yanzu yaushe rabonsa da ya fita ɗin da? Wai ya gaji da zaman banza. Innalillah Baba idan ya ɓallo abu tamkar wanda ake bawa shawara. Ya iya tijara da dagiya akan abu.

*********Kawai kallan Saif Asma'u ke yi ko ƙiftawa, tana mamakin abinda zai sa shi ya bada rayuwarsa saboda ita. So take ta samar masa wani irin gurbi a cikin zuciyarta. Sai de ta rasa ina zata saka shi, ko da ta saka shi, bata san wanne matsayi zata bashi ba. Tabbas tana jinsa a ranta sosai tun sanda ta ganshi, tana tsananin tausayinsa, kuma duk marin da yake yi mata idan sun haɗu bata taɓa jin haushinsa ko zafin sa ba. Musamman da ta lura yana da shegen tsoro idan ya yi abu aka ce za'a rama. Ga dukkan mutumin da ya cece rayuwarka, ko da ace maƙiyane wallahi sai ka ji wani abu a ran ka game dashi, daga ranar kuma kun dena faɗa da gaba muddin aka ce hakan ta faru. Balle da ita da zata duka haɗuwar su nawa? Amma ya yi wannan kasadar ya jefa kan sa a cikin wannan haɗarin duk da kuwa baya da lafiya.A hankali ta lumshe idan ta, hawaye na zubo mata sosai tana mai saka hannunta a cikin sumar kan ta, gaba ɗaya ta rikice ta rasa ya zata yi da ran ta da kuma zuciyarta.

Dafa ta ta ji anyi hakan yasa ta juyowa ta zubawa Safwan ido, da ke tsaye a bayanta.

"Please kukan ya isa haka. Ina jin ba daɗi game da hakan ki yi haƙuri ki dena".

Shima kallansa kawai ta yi wasu sabbin hawaye na zubowa daga cikin idan ta. Ta kasa ce masa komai, balle ta buɗe baki ta yi masa magana dan bakin nata yayi nauyin da ba zata iya buɗe shi ba. A hankali ta shiga motsa bakin ta buɗe da niyyar yin magana kawai kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata mai tafe da sheshsheka gami ciwon yadda zata yi da kan ta.

Be yi tunanin komai ba, balle ya yi tunanin ya dace ko be da ce ba, kawai abinda ya sani baya son jin wannan kukan nata, kawai bata yi tsammani ba ta ji ta a cikin jikinsa gaba ɗayanta yana mai ɓoyeta a cikin faɗaɗɗe ƙirjinsa sai ta dawo wata ƴar ƙarama da ita a gabansa. Cike da dabara ya fara lallashinta yana shafa mata kai da har yanzu bata sa ɗankwalinta ba, balle kuma mayafi.

"Ki yi haƙuri".

Ya faɗa mata a cikin kunnenta. Bata da zaɓin da ya wuce ta yi kuka sosai domin ta ji sauƙin abinda ran ta ke yi mata tun a jiya da aka ce za'a hada ta da aure da Ya Abdul. Yadda bata san shi, shima haka be san ta, amma ba su da zaɓin da ya wuce su yi wa Baba biyayya a wuce wajen.

Kukan da take yi ne yasa Saif daga baccin da ya ɗan fara ya zubawa bayanta ido kawai yadda take kuka a jikin Safwan. Ɗan motsi ya yi zai tashi sai kuma ya yi saurin komawa ya kwanta.

"Yi haƙuri da zafi ko?

Ya ji wata yarinya ta faɗa. Juyowa ya yi kalli yarinyar dake kusa da shi ta riƙe hannunsa guda ɗaya.

"Thanks for saving her life".

Ɗan murmushi ya saki yana sake riƙe hannunsu.

"Sunana Asiya and you?

"Saif".

Ya faɗa mata a hankali.

"Saifullah?

Ta faɗa tana yatsine fuskarta kamar wanda bata san sunan. A hankali ya saki murmushi yace.

"Saifuddeen".

Gani ya yi ta darwaje baki tana sake matsowa kusa da shi sosai har ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan gadon da yake, ɗayan kuma tana ƙasa.

"Ka san me?

Ya girgiza mata kai. Sai tace.

"Before then, let's be friends, can you be my friend?

A hankali ya gyaɗa mata kai. Sai ta sake yin wani murmushin mai kyau.

Ta ware hannunsa, suka haɗa ƙaramin yatsansu suna juya shi kafin suka gaisa.

"Yesss, waya koya maka?

"You".

"Really?

Sai ya gyada mata kai kawai.

"To amma kaga ni yarinya ce am must 10, yau na cika 10 ɗin ma. Ka yarda ka zama ƙawana?

Murmushi ya yi mata jin wani zancen wai kawana. Sai kawai ya gyaɗa mata mai.

"Tohm, kasan meyasa na ji ba daɗi da ka ce sunanka Saifullah?

Ya girgiza mata kai.

"He's our bother ni da Ya Ma'u, amma he's never be nice to her, ka ga da shi da Anty that woman da ka shaƙe ta, da kuma Ya Laura, ba sa santa sosai, amma ka ga ni da Ya Abdul, da Ya Haydar Anty Fati muna san ta sosai".

"Kai ma kawai na ji ina saka cause you save her life".

Wani murmushin ya sake yi sosai yana cigaba da kallan yarinyar.

"Banda surutu ko?

"Banyi maka zance da yawa ba?

Dariya sosai ya ke so ya yi. Su wato dukan su ƴan gidan su haka suke shegen zancen da surutu.

"Baki da shi".

"Na gode Allah, kai kana da murmushi kana da dariya ba kamar wancan ba".

Ta faɗa tana nuna Safwan da sai yanzu ya sake ta yana zaunar da ita akan bench. Yana share mata hawaye..

"Da Ya Abdul ke tambayar waye kai ko? He isn't responds".

"Kawai ya yi wani shiru, ni bana san shi".

"Da ya sunansa?

"Safwan".

Ware ido ta yi tana cewa.

"Sunan Babana ne da shi".

Ta faɗa tana rufe bakinta sosai. Alamar ya haka?

Sai kuma tace, "ko da yake ai ba shi ne ba ko?

Sai ya gyaɗa mata kai kawai.

"To Alhamdulillah. Amma da ace kai ne mai sunana Babana da na kira ka da Daddy. Ina so nake kiran Babana da Daddy".

"Zaki iya ce masa, ai Babanki ne, you can him duk sunan da ki ke so".

"Idan yana raye ne kawai hakan zai faru, ba wanda zai sake replacing mahaifina bayan ya rasu, sai Baba. Shima sai da ya sha gwagwarmaya sosai kafin ya karbo ni. Baba ne kawai mutumin da zan iya kira da sunan Mahaifina".

Ta faɗa a hankali hawaye na zubo mata, tsananin tausayi yarinyar ta bashi tausayi sosai bakaɗan ba, sai ya ji kamar ya yi mata kuka. Dan abinda ciwo kuma da zafi kam babu ƙarya. Yarinya kamar wannan ace ta san rashin mahaifi? Ya Allah!. Shiyasa yake godiya ga Allah da girma da na sa iyaye suka kuma bashi tarbiyya gwargwadon iyawarsu. Wannan ma kaɗai wani abu ne.

"Ki masa addu'a uhm?

Ɗaga masa kai ta yi a hankali, yasa hannunta share mata hawaye.

"Ki dena kuka".

Ta sake gyaɗa masa kai.

Anan asibitin ya kwana, har dare Asma'un itama tana nan domin bata san abinda zata je ta tarar a gidan ba. Safwan ne kawai mai kwantar mata da hankali yayin da Saif kuma ya bala'in haɗe ran sa, dan be san ma ya kalleta, ko da kuwa sun haɗa ido bisa tsautsayi hararace zai zuba mata. Ga ƙawarsa Asiya da suka yi sabo sosai cikin lokaci kaɗan, Safwan ne ba su wani yin shiri dan shi be san yake yiwa yara dariya su rena shi. Anan Asibitin ya kwanta shi da Safwan kawai, dan ba'a kwana asibitin tunda ba'a wani buɗe shi ba kuma sannan aikin da ake yi a cikin da na zo ka tafi ne. Wanda za'a yi aikin da ya ke da buƙatar kwana kuma can asibitin suke tura su, su yi musu abinda ya ce.

Da safe sai ga Sufaina ta zo ita da Abbi da Mommy, Mommy banda faɗa ba abinda take yi akan meyasa zai yi kasa da rayuwarsa wurin cetar wata yarinya, sosai ta hau yi masa faɗa, shi de Abbi shiru kawai yana zubawa yaron nasa ido. Sai ga Sufyan shida Mubeena shima sun zo duba shi. Sufyan wani irin kallo yake yiwa Safwan na irin baka san abinda ke faruwa dan ka yi busy a tsakanin jiya zuwa yau. Kawai ya bashi hannu suna gaisawa fuskarsa da tsananin murmushi. Safwan be kawo komai a ran sa ba suka gaisa. Kafin ya shiga yiwa Saif ya jiki ya amsa masa cike da kulawa. Mubeena kam kawai lafiya yace da ita yana mai ignoring maganar da take yi masa.

"Wannan wurin ba asibiti ba ne ba amma ko?

Cewar Mommy. Safwan yace.

"Wurin da ake bada tallafin marasa lafiya ne, baku ga har sun fara zuwa ba".

"Kuma harda weekend?

Cewar Sufyan.

Safwan yace, "Ehh, saboda ai ba aiki bane na permanent, aiki na wani ɗan lokaci shine yasa kuma ga mutane".

"Naga angyara wurin ai".

Safwan yace, "Ehh ba".

Abbi yace, "Safwan ne ya siya, daman baka faɗa ba masa ba, ka kawo shi ya gani?

Abbi ya faɗa yana kallan Safwan. Sufyan danne wani mummunan abu ya yi da ya so ya bayyana a kan fuskarsa, amma duk da haka sai da zuciyarsa ta buga.

"Abbi ya za'a yi ya faɗa min, shima ya kai, ya zama mutum".

Mommy tace, "Sufyan Please kar ka fara, kar na ji kana yi wannan maganar. Ka yi masa uzuri dole zaka sani mana..kai ne babba fa".

"Mommy kenan ada nake Babban amma banda yanzu ai".

Safwan yace, "Ya Sufi ka yi haƙuri".

Kawai ya faɗa masa yana so a kau da maganar.

Saif yace, "Ni gaskiya gida zan je, na gaji da wannan zaman".

Ba wanda ya tanka shi. Mommy ta ce bari ta koma gida, suka tafi ita da su Sufaina da ta je makaranta, Abbi ne ya je ya dawo shi da Safwan. Suna fita ba jimawa sai ga Asma'u ta shigo, bayan ta kuma wani ɗan saurayine da ba zai wuce Safwan ɗin sa ba. Sai kuma Laurah da Saudah.

A hankali Asma'u ta matsa gefen sa, jikinta a matuƙar sanyaye.

"Na zo na yi maka kashedi, bansan ka ba. Baka sanni ba. Dan haka kowa ya yi rayuwarsa batare da ya shiga hurumin kowa ba. Wannan de ƴar uwata ce. Ko yanka ta na yi, baka da damar da zaka ce uffan".

"Abu na gaba babu kai, babu sake shiga sabgarta, tace bata san ka, a tsaya iya haka, mun yarda da bata san ka ba. Dan Allah ka gane ?

Gently Saif ya ɗago da ga shan tea ɗin da yake ya ware akan Saifullah.

Yace, "Idan kuma na ƙi fa?

"Akasin zama lafiyar ka da ƙarshen ka ne ya zo".

Ɗan gajeren murmushi Saif ya yi yana kallan Asma'u.

"Me ki ka kawo min, kin riƙe flask a hannu kin ƙi zuwa ki bani, haba My love".

Da wani saurin ta shiga girgiza kan ta ƙwalla na shirin fitowa daga idan ta.

"Wallahi Saifullah bansan shi ba, Allah kuwa, kawai haɗuwa muka yi yadda na faɗa maka, hasalima Wallahi fada muke yi Allah".

"Ni zaki yiwa ƙarya?

Ya faɗa yana yin kan ta zai zuba mata sai de kafin ya mareta shi nasa saukar marin ya isa gare shi.

"Whaat?

Saifullah ya faɗa cike da mamaki yana dafe kuncinsa. Dan baƙarya ya maru, tunda yake baya jin wani ya taɓa ɗaga hannunsa ya mare shi idan ba Babansa ba. Amma shine a yanzu wani can daban zai zo ya mare shi?

Asma'u sosai take kuka tana girgiza kan ta, ganin irin shegen kallan da Saif ke aikawa da Saifullah.

"Kai waye da zaka hana na dake ta? Ƙanwata ce...

"Ni kuma matar da zan aura ce".

Saukar kalmar a kunnen Asma'u ya sa ta saurin rintse ido sosai wasu sabbin ruwan hawayen sake zubowa a idan ta. Tana buɗe idan tana kallan Saif da ya ƙi ya kalleta ko wai zai ji tausayinta.

Amma ganin suna aikawa juna wasu mahaukatan kallan-kallo kamar za su kashe junansu yasa Asma'u matsawa a hankali.

Tace, "Dan Allah ka dena shiga sabgata. Ba ruwanka da ni. Bansanka ba, bansan daga ina ka fito ba. Ban kuma san ko kai ɗin waye ba, you are just my patient days ago da kuma jiya and then now, Dan Allah Rowdy Please".

Ta faɗa da matsanancin hawaye sosai na fita daga cikin idan ta, ta ƙarashe da haɗa hannunta biyu a gare shi.

"Ka fita a rayuwata...

"Asma'u".

Ya kira sunanta da wata irin muryar sa yasa ta saurin buɗe idan ta tana zuba masa ido.

"Daga sanda na haɗu da ke lokacin bugun da zuciyata ke min ya sauya. Har yau da na nake sake ganin ki, zuciya bata dena buga min dai-dai ba, shine zaki ce na fita daga rayuwar ki?

Ya faɗa yana daka mata matsananciyar tsawa sosai. Da sauri ya zubara ta yi baya tana mai toshe kunnenta.

"Kin zamo rayuwata, ba zan iya barinki. Ji na yi idan ki ka kubce min, duniyar zata juya min Cheeky, da ke nake kwana, nake tashi, dan meyasa zaki ce na rabu da ke?

Ya sake daka mata wata tsawar. Kafin ya wani janyota zuwa jikinsa da bala'in sauri yana kallan Saifullah da gabansa ke mugun faɗuwa sosai. Haɗa idan da suka yi yasa shi saurin runtse nasa domin ba zai juri ganin sa ba, wutar masifa ce ke tashi da ta bala'i a cikin su.

"Sanda wancan yarinyar ta ɗaura hannunta a kan fuskarta ta mareta dan kawai ta ƙi bata mota, jin zuciyata na yi tamkar zata fito, sannan wata daban can ta ce zata kashe ta?

"Idan ku da ku ke kiran kan ku, da ƴan uwanta baku tsaya mata ba. Ni da ba jininta ba. Daga rana irin ta yau, na yi alƙawarin hawaye ɗaya ba zata sake fitarwa ba muddin bana farin ciki ba ne. Zan zameta garkuwar da ku baku zame mata ba".

Ya faɗa yana sake matseta sosai a jikinsa. Wasu irin ruwan Hawaye ke fita daga idan Asma'u tana kallansa kawawai.

Sai ya yi shiru.

"Meye ma kace? Ko yanka ta ka yi meye ma?

Sai ya yi ɗan murmushi. Saifullah yace.

"To waj uban meye zaka yi idan an taɓa ɗin?

"Idan nace komai, ina nufin komai har kisa kai zan iya yi".

Ya faɗa yana saka idan sa a cikin na Saifullah da ya kasa hadiyar yawu. Matan kuwa haɗe jikin su suka yi domin idan sa kawai masifa ne, balle Saudah da ta sha shaƙa to yau tana magana ta tabbatar kasheta zai iya.

"Na sake ganin wanda ya taɓa ta, ko ya sa ta a kuka cikin ku. Wallahi wallahi wallahi sai ya yi nadamar rayuwarsa".

"Ke kuma...

Ya faɗa yana kallanta tare da kama kafaɗarta duka biyun girgizata.

"Idan ba zaki tsayawa ki ƙwace ƴan cin ki ba. Watarana zaki yi kukan da zaki zo kina danasani. Kada ki kuskura ki zamto mai haƙuri, domin ki ka zamto mai haƙuri kowa zai taka ki ne. Ki zamto mai juriya domin ki ji daɗin duniyarki. Ba'a ragawa mutumin da baya da mutunci".

"Kin ji ko baki ji ba?

Ya sake daka mata wata tsawar yana girgiza ta. Dum-dum zuciyarta ta yi wani kalar bugawa tana yin sototo tare da ja da baya tana kallansa, shi kuma ya sake rungume ta sosai a jikinsa yarda bazata ƙwacewa ba. Maganar ce ta zo mata a bazata, kuma da ƙarfi a cikin kunnenta, sannan ta shiga cikin ƙwaƙwalwarta ta yi mata girma ta hana mata tunanin akan zancensa. sannan ta danne mata zuciya. Ta kasa tantance inda maganar sa ta dosa.....