07
by @nanadiso10
ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA BAKWAI
Gaba ɗaya zuciyar Ayshatu cike take da rudani da rashin kwanciyar hankali. Duk da cewa tafiyar za ta ba su damar yawon ƙasashe masu kyau, bata jin daɗin barin Habibie a baya. Kishinta yana ratsa jijiyoyin jikinta kamar wutar lantarki mai ƙarfi domin ita ba ta jin za ta iya yin nesa da shi ko da na ɗan lokaci ne.
A wannan karon, sai ta lura Habibie yana da wasu abubuwa masu matuƙar muhimmanci da ke gabansa abubuwan da suka fi tafiya a wurinsa. Wannan ne ya saka mata wata irin fargaba da ba ta taɓa ji ba a baya. Kullum bayan tafiyarsa, sai wani labari ya riske ta ko dai an daura masa aure, ko kuma an tsayar masa da wata magana. Saboda haka, wannan karon zuciyarta tana kukan shiru tana tsoron sake kasancewa a sahun baya a rayuwarsa.
Amma duk da haka, tana da tabbacin babu wata mace da ta ɗauki gurbi a zuciyarsa irin nata. Saboda haka, kafin tafiyarsu, tana ƙoƙarin bar masa wani ƙamshi wani salo na musamman da zai kasance masa kamar alamar tunawa. Wani abu da duk lokacin da ya ɗan lumshe ido, ya tuna da ita da kyanta, da lafuzanta masu taushi, da ƙaunar da ta dora masa.
An gama tattara kayayyaki tun kafin ƙarfe biyu, direbobi biyu na jiran su a gaban ƙofar manyan motocin da za su wuce su kai su filin jirgi. Komai yana tafiya bisa tsari, kamar yadda ya dace da mutanen da ke rayuwa cikin jin daɗi da martaba.
Karfe biyu da rabi da mintuna arba’in da ɗaya kenan a agogon tagwayenta na Cartier, lokacin da kira ya shigo Habibie ne. Muryarsa mai laushi da nutsuwa ta cika kunnen ta da wani salo da ke sanya mata kuzari ko da ta gaji. Ya shaida mata cewa jirginsu zai tashi da misalin ƙarfe huɗu. Wannan ya sa ta hanzarta komawa dakinta domin gyara jikinta.
Ba ta ɗauki lokaci ba wajen zabar Arabian abaya mai ɗinki irin na Al-Zahra Collections abaya mai dinki irin na Amirat mai launin ja da yadin siliki wanda ya rufe jikinta cikin salo da ladabi. Ta rataya ɗan kunne na Van Cleef & Arpels, sannan ta fesa turaren ta na Oud Royal daga kasa har sama turaren da ke saka kowane numfashi ya kasance kamar wata zallar saƙo na ƙauna.
Gaban madubi ta tsaya tana duba kanta. Fuskar ta cike da annuri, ba saɓani da fatar ta mai santsi. Daga nan ta ɗauki handbag ɗinta na Chanel sannan ta rufe dakin da natsuwa, ta nufi babban bangarensa.
Da ta shiga babban falonsa wanda aka yi wa ado ba ta same shi ba. Ta wuce cikin nutsuwa zuwa ɗakinsa, tana bubbuga ƙofar da taushi sannan ta shiga. Ta saki sallama cikin ladabi yayin da idanunta suka sauka a kansa yana waya, fuskar sa cike da annuri da murmushi. Ba sai an gaya mata ba, ta san da Hajja ce mahaifiyarsa yake waya, domin ita kaɗai ce ke da ikon motsa masa zuciya da dariya haka.
Tsit... lokaci kamar ya tsaya. Wani irin salo na ƙauna da cikar burin zuciya ya lullube Ayshatu, tana kallon Habibie da wani irin shauƙi da ko cikin mafarki ba ta taɓa tunanin za ta iya ji ba. Tana ƙarasowa, ƙamshin turarenta mai kyau na Oud Royal yana gauraye da dumin sutturar ta, Arabian abaya mai ɗinke na sarauta da launin zinariya wanda ke zubewa a jikinta kamar ruwa a kan yashi mai laushi.
Ba tare da wata faɗa ko wani bayani ba, ta faɗa masa jiki. Rungumar da ta fi kowacce magana da kalma, tana nemansa kamar wacce aka ƙwacewa iska. Sai da ya gama sallama da mahaifiyarsa cikin ladabi da annuri, sannan ya ɗauki lokaci yana kallonta idanuwanta cike da hawaye masu nauyin ƙauna.
"Please, Habibie... bana son yin wannan tafiyar... ba tare da kai ba." Ta furta cikin wata irin raɗa mai ƙayatarwa.
Wani murmushi mai ɗauke da jin daɗi da mamakin zurfin soyayyarta ya bayyana a fuskarsa, yana jawo gefen kuncinta da yatsansa mai sanyi da tsabta. Kafin ya kai ga amsa, sai ta kai bakinta cikin nasa ta masa wata mahaukaciyar sumba mai cike da tsananin daɗi da buƙata. Jikinsa ya birkice. Numfashinsa ya ƙara nauyi. Idanunsa suka lumshe da tsantsar jin daɗi.
Yana ƙoƙarin daidaita kansa ne ya kalli Rolex ɗin hannunsa. Mintuna uku suka rage kafin jirgi ya tashi. Yayi ƙoƙarin zare kansa daga cikin wannan narkakkiyar soyayyar, yana ce mata da murya mai cike da kwantar da hankali
"Ki sani Ayshatu, ko cikin aljihun zuciyata zan tafi da ke."
Sai ya kama hannunta, sannan ya ce
"Mu tafi. Zan rakaki filin jirgi da kaina."
Ta zube masa murmushi mai cike da cin nasara da jin ƙauna. Ita dai ta san ta karɓe dukkan tunaninsa. A motar suka wuce motar da aka zana tana masa addu’ar samun lafiya da kariya daga sharri.
Yayin da suke yin sallama a Airport ɗin, Ayshatu ta jinkirta da gangan tana kallon yadda iska ke kaɗawa a rigarsa mai alamar Zegna. Ta kama hannunsa a karo na ƙarshe, ta fesa masa ƙamshinta, sannan da murya mai raɗa ta furta
"Kada ka bar kowa ya raba ni da kai, Habibie... Allah ya tsare ka."
Daga nan ta juya cikin tafiya mai cike da izza da tausayi, zuciyarta cike da fatan cewa ƙaunarta za ta kafa sansani a zuciyarsa har abada.
Ko da ya koma gida, ya yi gaggawar shiga cikin babban ɗakinsa mai ƙamshi da kwanciyar hankali. Wanka yayi da sabulun Arabian oud mai ɗaukar hankali, sannan ya saka riga da wando na tsadaddan yadi kaya masu launin zinariya da shudi, haɗe da takalmansa na Ferragamo. Tufafin da suka haɗu da halittarsa suka ƙara fito da cikakken surarsa ta namiji wanda ya saba da alfarma.
Yayin da ya fito daga ƙaton falonsa, ya tsaya gaban layin motocinsa – G-Wagon, Maybach da kuma Lamborghini mai launin zinariya. Idanunsa suka sauka a kan wata mace dake tsaye a gefe, cikin shigar abaya mai sheƙi, gefenta kuma na ɗauke da ƙaramin bag.
Bilkisu ce.
Zuciyarta ta soma harbawa da ƙarfi, kamar zata fito waje. Ta tsare shi da ido, kamar wacce take so ya karanta tunaninta. Murmushi ya kwanta a fuskarta, amma zuciyarta na tsaka da tafasa da addu'a "Ya Allah, ka sa ya ce yana sona... Ya aure ni... Wallahi da na more mijin kirki."
Kamar wanda ya karanta zuciyarta ne, Habibie ya ce da wata murya mai sanyi da izza
"Muje ko?"
Wani sanyi ya ratsa Bilkisu. Zuciyarta ta kada kamar gangar sarauta. Ta ce cikin fara'a
"Tohm, Dady."
Ta ɗauka motar da za su shiga ɗaya ce. Sai dai sai ta ga shi ya nufi wata daga cikin tsadaddun motarsa Range Rover mai sunan sa a lambar ita kuma direban gida ya buɗe mata wata daban.
Murmushinta ya ɗan dushe, amma har yanzu zuciyarta cike take da fatan alheri. Ta ɗora hannunta kan ƙirjinta, tana lumshe ido tana cewa a hankali
"Ko da ba a tare ba yanzu… in Allah ya yarda, zan kasance matar gidan nan."
*******
A cikin kwanaki biyu da suka gabata, gaba ɗaya na fara lura da sauyin jikina. Kibar da na tara ta ragu sosai, jikina ya fara komawa yadda yake da. Allah ne masani burina kawai shi ne in ga ni na zama cikakkiya, kamar yadda sauran 'yan ajinmu suke.
Amma fa fargaba nake sosai, domin bayanan da nake karantawa game da illar magungunan ƙara kiba na sa ni jin tsoro har cikin ƙashi.
Yau Juma’a ce ranar karshe ta jarabawarmu. Ni dai, Ramlah, nasan ban shirya sosai ba. Ayyuka sun yi mun yawa, har ba zan iya cewa na tsunduma cikin karatu yadda ya kamata ba.
Da na ga har ƙarfe shida na safe ne, sai na sa gaggawa. Na shiga kitchen da sauri, na dafa chips da kwai, na zuba a food flask dina. Na rantse ba zan yi girki da Momy ba yau. Jiya ma ta gayyato kawayenta, ni kuma ta tura ni na dafawa musu mandi da kaza da salad amma fa, wallahi, sai da ta rabar musu abinci. Na bar gurin cikin ɓacin rai, sai lemo da biscuits kawai na ci. Ina cewa zan yi magana, sai ta watsa mun banzan amsa
"Rashin kunya za ki yi mun ne, Ramlah?"
Abu kafan ya rage, sai na ga zata kai ta hada ni da Abba. Na yi shiru, na janye na bar wajen. Ko gyara gidan banyi ba –yau ta san yadda aikin gida yake.
Murmushi ne kawai ya subuce mun yayin da na ɗauki kaya kala ɗaya, na sanya a cikin jakar makaranta na fita.
A filin gidan na tarar da Abba yana lazumi. Na gaidashi cikin ladabi, sannan na shaida masa
"Abba, yau zamuyi practical a makaranta, za mu gama 6. Malam Idi ne zai zo ya ɗauke ni."
Ya ɗago kansa, ya kalleni da kulawa, sannan ya yi mun addu’a da fatan alheri. Sai ya ƙara mun kuɗin makaranta.
A mota nake cewa da Malam Idi:
"Anjima, dan Allah zaka kaini gidan Mama. Bata jin daɗi. Amma don Allah, kada ka faɗawa kowa."
Ya saki dariya yana cewa
"Haba, kar ki damu, babu wanda zai ji."
Gimbiya Momy bata farka daga baccin hutunta ba sai bayan ƙarfe takwas na safe. A hankali ta miƙe daga gadonta, tana lumshe ido kamar wadda ta yi dare tana faman tunani ko gajiya.
A lokacin Abba ma ya tashi, ya kammala shiri yana fatan fita da wuri, sai dai da ya sauko falo, abu na farko da ya lura da shi shine babu breakfast a kan dining table. Ya tsaya cak, ya ɗan yatsina fuska yana kallon tagar kitchen.
Momy tana zaune a kan kujera tana gyara zaninta, sai ta ce da shi cikin murmushin rainin hankali
"To, Ramlah batayi bani ba??
Idanun Abba suka ciko da mamaki da ɗan ɓacin rai, ya ce cikin murya mai ɗan ƙarfi
"Ramlah ke da hakkin dafa min abinci yanzu? Ita matar gidan ce? Ko ita kike so ta rika rikewa alhakin aikin da ba nata bane?"
Maganar ta yi mata zafi. Bata ce komai ba, sai kawai ta miƙe cikin fushi, ta shige bandaki da hanzari. Brush kawai tayi sannan ta fito, ta sakko ƙasa. Da ta sauka, ta tarar da gidan kamar yadda aka bar shi babu gyara, babu motsi, babu tsafta, komai a hargitse.
Wani irin takaici ya tsaya mata a kirji. Ta cika da bacin rai
"Wallahi zan dawo na sameta! Karfe goma sha biyu zamu fita! Wannan shegiyar yarinyar da ke tazamemun karfen kafa, sai na yi maganinta, ni ba zan ƙyale ta ba!"
Ta gama masifar ne tana shirin kai abincin karin kumallo wa Abba. Sai dai duk yadda ta ƙoƙarta, ta kasa nutsuwa. Kitchen ɗin da kanta ta buɗe shi sai da ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta na suya kamar ana hura mata wuta.
"Yau zan karɓi baƙi. Bilkisu ma zata dawo. Gidan haka? Kitchen haka? Allah Ka sani, ba zan iya haka kullum ba."
Tana kallon komai a cikin gidan, sai da ta ɗan zauna a jikin bango ba saboda gajiya ba, sai don damuwar da ta yi nauyi a jikinta.
Sai ta ɗauki waya cikin takaici, ta kira wata lamba.
"Kawata , dan Allah ki zo nan gida anjima... akwai maganar gaggawa."
"Lafiya dai, zainab?" muryar ta fito da damuwa.
"Wallahi sai na ci uban Ramlah! Yarinyar nan ta isheni! Wallahi na gaji da ita!"
Momy kuwa, da ta kai wa Abba abinci ɗakinsa, sai ta shigo da sallama da kissa, tana ɗauke da fuskar fara’a kamar wadda ba ta da wata damuwa.
Ta ajiye flask ɗin a gabansa, tana haɗa masa shayi da kulawa, sannan ta ce da sassanyar murya
"Ka yi hakuri Abban Ramlah. Auta ce da kanta ta ce min zata dafa maka kosai da kunu da safe, tunda ta ga kana so."
Ta ɗan lumshe ido sannan ta ci gaba da magana
"Ina jin ko yau ta makara ne daga bacci, shiyasa bata samu tayi maka ba. Allah ya huci zuciyarka, ayi hakuri."
Ta ƙarasa haɗa masa shayin tana kallonsa da tausayi.
"Auta ai tana ƙoƙari. Allah dai ya albarkace ta, ya kare min ita."
Daga ƙarshe sai ta ƙarasa da fatan
"Allah yasa taci wani abu kafin ta fita, kada ta tafi da yunwa."
Abba dai ya zauna yana sauraren ta ba tare da ya ce uffan ba. Sai kawai ya ɗauki shayin ya ɗan kurɓa.
Nana hadiza
***