ƳAR KARUWA PART 1

ƳAR KARUWA Chapter 15

by @ayshadansabo

Arewabook@ayshadansabo

Paid book

***

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 15

SATURDAY

Tun safe Jannat ta gaza samun nutsuwar zuciya domin gabaki ɗaya zuciyarta cike take da taraddadi da damuwa akan baƙon da za ta yi a yau ɗin,domin ko a ɗazu da Abbah ya kirata suyi sallama sabida yau ne za su tashi zuwa Umrah shi da Inna saida ya sake jaddada mata cewa ta amshi baƙonsa da hannu bibiyu.Babu abinda ke sake ɗaga mata hankali irin yadda Abban yaƙi sanar da ita waye baƙon? Hakan na matuƙar ɗaga hankalinta sosan gaske.

Yanzu haka wanka ta fito amma ta gaza shiryawa sabida yadda gabaki ɗaya take jin zuciyarta a hargitse ga ƙirjinta sai faman sauya bugu yake,Feenah bata nan taje ɗakko Arfah a train station wacce ta kusa sauka.Sosai suka sha aikin girka abinci dasu snacks da abubuwan sha da za su tarbi baƙon dashi ita da Feenah,jiki a mace ta yunƙura ta isa wajen kayanta ta fiddo wani rantsatstsan lace mara nauyi wanda Ummu ce ta aiko musu shi su uku ita da Feenah da kuma Arfah.Kowa kalan nasa daban ne sabida kowanne sai da ya faɗi choice ɗinsa sannan Ummun ta ware musu don a cikin kayan sayarwanta ta zabar musu,kalar na Jannat blue black ne da akai ma ado da pich and silver colour.

Ɗinkin straight gown aka mata wanda yayi bala'in zama a jikinta time ɗin data saka rigar,sosai ya dace da tsayi da baiwar cikar halittar da Allah yayi mata baiwarsa.Komi ya fito tamkar yayi magana,back and front duka sun fito da kansu matuƙa da gaske.Bata yi gigin shafa komi a saman face ɗinta ba asalin natural beauty dinta kawai ke haskawa,turarenta mai sanyi da daɗi ta saka kaɗan domin kayan kansu ƙamshi na musamman suke fiddawa kasantuwar duk kayan da za su shiryasu cikin drawer sai sun tabbatar ya turaru a kabbasa da turarukan kaya tukunna.Koda ta isa gaban standing mirrow ɗin dake ɗakin Feenah daga sama har ƙasa ta kalli kanta tana mamakin yadda kaya ke amsarta,tasha ji Inna na faɗin cewa wai karuwar jiki gareta irin wanda duk kayan data raɓa ko ƙananu ko manyan kaya sai sun amsheta.Kaɗan ta saka baƙin kwalli a idanunta ganin yadda sukai firgai-firgai sabida fargabar data sanya a ranta tun ranar da sukai waya da Abbah,sosai fuskarta ya sake haskawa domin kwallin data saka kaɗai ya ƙara fiddo kyawun idanunta masu wani irin walainiya tamkar tana tawa ruwan hawaye a cikinsu.Tana ɗaura ɗankwalin kayan Feenah suka shigo,ta gane hakan ne ta hanyar jiyo rakaɗin Arfah da Momy ta fito tarba.Ta saki kyakykyawar murmushinta da kumatunta suka loɓa farin cikin zuwan Arfah na sake mamaye zuciyarta,kafin tayi wani motsi Arfah ta runtumo zuwa cikin ɗakin tana faɗin,"Sis i miss u." Jannat ta ruga suka rungume juna tana faɗin,"Miss u too my Sis, where is my Manar meyasa Anty Khairy bata haɗoku tare ba?"Arfah ta bankawa Jannat harara kafin tace,"U are not serious Jannat,ina ni ina tahowa da Manar ta addabeni." Dariya Jannat da Feenah suka kwashe dashi kafin Jannat tace,"Kedai wallahi baki son hidimar Yara naga yadda za ki yi idan kuka haifi naku da Habibin naki." Arfah ta saki dariya tana faɗin,"Ai namu da Habibi kika ce Jannat,yanzu dai me aka tanadar mini,kuma wannan wankan duk na murnar tahowata ne?" Feenah ce tayi saurin faɗin,"Ina fa Arfah,baƙo za mu yi ne ina ga duk inda yake ma zuwa yanzu ya kusa ƙarisowa." Cike da mamaki Arfah ta kama baki tace,"Haba! Da gaske Jannat munyi kamu ne?"Harara Jannat ta aika musu su duka kafin ta narke murya tace,"Arfah wallahi shekaranjiya Abbah ya kirani yace wai na shirya zan yi baƙo kuma yaƙi sanar dani ko wane ne." Arfah take sai maganar da sukai da Mamie ya faɗo mata arai,cikin sauri ta furta,"Oh! My god,Allah yasa dai ba speaker Attah bane Abbah ya amince masa yazo ku gana." A rikice Jannat ta dubi Arfah tace,"Waye kuma speaker Attah Arfah?" Yadda Jannat tayi maganar a rikice ya baiwa Arfah dariya,ta saki dariya kaɗan kafin tace,"Hon.Attah dai da kika sani a Jos kakakin majilisar jiharmu na plateau." Ai sai hankalin Jannat ya sake tashi,cikin rawar murya tace,"Na shiga uku Arfah ina zan kai wannan Dattijon banzan,to waima ni a ina ya ganni bare har yace yana sona?" Dukkansu tausayi Jannat ta basu sai dai kafin wani yayi magana a cikinsu kira ya shigo cikin wayar Jannat ɗin,ganin baƙin lambobi ya sanya tayi receiving tare da saka wayar a speaker. "Assalamu alaikum!" Wani irin sassanyar murya ya doki kunnuwarsu time ɗin da yake furta kalmar sallamar.Sai suka kalli juna su duka Arfah tayi ma Jannat sign da ido alamun ta amsa shi,Jannat ta shagwaɓe face tace,"Waalaikumussalam." Daga ɓangarensa sai yace,"Gani a wajen gate Hafsatt a taimaka azo a shigo dani please!" Jannat tayi ƙarfin halin faɗin,"Okay yanzu In Sha Allah." Daga haka ta kashe wayar ta zubawa su Feenah idanu waɗanda ke yi mata dariya ganin yadda tayi da fuska.Arfah ce tayi saurin faɗin,"Sis wannan muryar bata wancan Dattijon bace wallahi,wannan daga ji ɗanyen jini ne kuma mai class ke kinji yadda ya kirayi sunanki ne?Oya jeki shigo dashi ni bara na ɗan watsa ruwa na ci abinci don a gajiya nake gaskiya." Tana kai ƙarshen kalamanta ta fara rage kayan jikinta ita kuma Feenah ta dubi Jannat dako motsi batai ba tace,"Wai miye haka Jannat mutum na jira kin wani shagwaɓe mana face ba za ki je ki kai shi sitting room ɗin bane?" Jannat ta sake kwaɓe face tace,"Ki taimaka ki je ki masa jagora Feenah wallahi zuciyata bugu take bazan iya ba please!" Harara Feenah ta watsa mata kafin tace,"Muje na rakaki dai amma wallahi bazan je ni kaɗai ba haka kawai." Jannat ta jinjina kanta tace,"Na daiji muje ɗin to." Tayi maganar tana janyo dogon hijab ɗinta har ƙasa ta maka,duk yadda Feenah tayi akan ta saka mayafine ƙi tayi.Hakanan suka fice domin yi masa iso zuwa sitting room,a falo suka tadda Momy da Mamah a zaune tana koya mata homework."Momy ya iso za mu shigo dashi zuwa sitting room." Feenah ta faɗi hakan yayinda Jannat tayi gaba ƙirjinta na cigaba da bugawa da ƙarfin gaske.A dawo lafiya Momy tayi musu Feenah ta fito suka jera da Jannat zuwa bakin gate,tuni an buɗe masa gate driver ya shigo da jibgegiyar motar da suka taho da ita amma iyakarsu bakin gate basu ƙariso da motar zuwa parking space ba.

Tun daga nesa Shureim Mansur Bichi ya hango santaleliyar budurwar data sace zuciyarsa tun a ganin farko daya yiwa hotonta a wayar Mahifinsa Prof.Mansur Bichi,ya kafeta da ido har suka ƙariso wajen motarsa ya kasa ɗauke ganinsa a kanta.Sallama Feenah ta doka daga ɓangaren driver seat,take glashin ɓangaren back seat ya sauka tabbacin gogan na hakimce a back seat kenan.Jannat dake tsaye daga gefe ne idanunta suka fara sauka akan kyakykyawan farin fuskarsa ma'abociya kyawu da kwarjini,tayi saurin yin ƙasa da kanta sakamakon yadda taga ya zube idanunsa a kanta baya ko ƙiftawa."Ranka shi daɗe barka da isowa,bismillah muje ko?" Feenah ta faɗi hakan time ɗin da Ingarman matashin ya samu nasarar fitowa daga cikin motar ya tsaya akan ƙafafunsa,dogo ne kyakykyawan gaske ma'abocin yawan murmushi da cikar zati.Yana sanye cikin wasu ubansun riga da wando na wani haɗaɗɗen yadi ɗan gaske,kallo ɗaya zakai wa ɗinkin da kuma yadin kasan cewa bada ƙananun kuɗi aka mallakesu ba.Idanunsa zube akan Jannat wacce tunda tayi masa duba ɗaya bata sake ba ya zubesu kafin ya furta,"Alright thank u Sis." Daga haka Feenah tayi gaba yana biye da bayanta yayinda ita kuma Jannat ke bin bayansu daga ƙarshe,a haka suka isa ƙayataccen sitting room ɗin da suke sauƙe baƙi inda suka kammala shirya duk wani abu da zasu tarbesa dashi bisa table dake tsakiyar ɗakin.Kujerar 2 seater dake facing ƙofar shigowa ɗakin ya samu ya zauna,gabaki ɗaya ƙamshin ɗakin ya haɗe da ƙamshin turarensa mai wani irin mugun daɗi.Akan Idanunsa Jannat ta sanyo kanta cikin ɗakin bayan tayi ƴar siririyar sallama,Feenah ce ta amsa sallamar tare da nufan hanyar fita tana faɗin,"A huta lafiya ranka ya daɗe sai na shigo mu sake gaisawa a nutse ko?" Kai S.M Bichi ya jinjina kafin yace,"Okay Sis thank u a gaida mutanen gidan please." Feenah ta fice tana bashi tabbacin cewa za su ji.Ya sake maido dubansa kan Jannat data kai zaune cikin one seater dake facing ɗinsa kanta a ƙasa tana wasa da hannun hijab ɗinta ta ciki,sai dai a jikinta kawai take jin tasirin idanunsa dake kaikawo a kanta bugun zuciyarta na sake hautsinewa.Cikin sassanyar muryarta mai zaƙi da laushin amo ta furta,"Ina yini,da fatan ka iso lafiya?" Shureim Bichi ya saki wani lallausar murmushi daɗin muryarta na sake kashe zuciyarsa,cikin nasa daddaɗan muryar ya amsa da cewa,"Lafiya lau ƴan Mata hope na sameku lafiya?" Jannat tamkar ta saki ihu haka taji sabida yadda ƙirjinta ke cigaba da tsananta bugu,cike da ƙarfin hali ta furta,"Lafiya lau Alhamdulillah!" Shiru ne ya ratsa ɗakin na wasu seconds kafin shi ya katse shirun ta hanyar kiran sunanta,"Hafsatt." Yadda yake furta sunan ba ƙaramin dukan zuciyarta yake ba,hakan ya sanya ta ɗago manyan idanunta ta sauke a kansa tana faɗin,"Na'am." Wani irin smile daya sakin mata shi ya sanya tayi saurin maida kanta ƙasa tana ji tamkar ta tashi ta fice daga ɗakin domin ta fahimci ya faye kallo da yawa."Sunana Shureim Bichi Babban Ɗa a wajen Prof.Mansur Bichi kuma Amini a wajen Abbanku Hafsatt." Ya dakata da kalamansa yana kallon yadda Jannat ta ɗago da sauri ta dubesa tana mamakin dama wai ɗan gidan Abbah Prof ne aminin Abbanta baƙon? Basu taɓa ganin Shureim ɗin ido da ido ba suna dai jin sunansa abakin Abbah time to time,cikin son ɓoye mamakinta tayi ƙasa da kanta tana faɗin,"Allah sarki yasu Abbah Prof ɗin,dafatan suna lafiya?" Shureim yace,"Lafiya Lau Jannat." Shiru ya ɗan sake ratsawa a tsakaninsu kafin Shureim Bichi ya buɗe baki ya sanar da Hafsat Kabeer Chiroma cewa soyayya ya kawosa zuwa gareta kuma da aure,ya sanar da ita cewa Abbansa shine ya nemi Alhaji Muhammad Chiroma da ya bashi dama yazo ya nemi auren ɗaya daga cikinsu domin su ƙara danƙon zumunci.Take sai Abban ya sanar da Prof ɗin cewa Shureim yazo ya nemi auren Jannat,amma yana roƙon a bata lokaci zuwa ta gama exam hankalinta ya sake dawowa jikinta ta kuma sake samun nutsuwar zuciya game da rabuwarsu da Aliyu wanda Abban keda tabbacin zuciyarta na matuƙar ƙaunarsa.Sai dai daga randa Hon.Attah yazo masa da batun yana son Jannat sai yaji hankalinsa ya tashi,hakan ya sanya ya kira Prof ya sanar dashi cewa Shureim zai iya zuwa a kowani lokaci su gana da Jannat ɗin.Idan har zukatansu sun haɗu da juna immediately after sun ƙare exam sai ayi maganar sanya lokaci,wannan dalilin shine yasa Shureim Bichi yin gaggawar zuwa domin tunda Abbansa ya nuna masa hoton Hafsat ɗin ya ji tayi masa zuciyarsa kuma ta kamu da soyayyarta.Dukkanin wannan bayanan Shureim yayi wa Hafsat su ne cikin taushi da nutsuwar muryar,ya rufe maganar da faɗin,"Hafsat ina sonki,tabbas zuciyata ta kamu da ƙaunarki don haka ina roƙon ki bani dama mu fahimci juna please!" Hafsat ta ɗago idanunta da sukai masifar laushi ta dubesa zuciyarta na sake shiga cikin tarin ruɗani mai yawan gaske,da wani irin sanyin murya tace,"Am sorry Yaya Shureim bazan iya ba." Shureim ya zuba mata idanunsa zuciyarsa na shiga cikin wani irin tashin hankali,domin a yanzu ne da ya ganta a zahiri ya tabbatar da cewa itace irin macen daya jima yana mafarkin mallaka.Da wani irin amon murya yace,"Please Hafsat kiyi haƙuri ki buɗe mini ƙofa koda kaɗan ne domin na jaraba luck ɗina,bance ki amince dani cikin gaggawa ba nidai burina kawai ki bani dama na nuna miki tawa kalar soyayyar kinji ko?" Kai kawai Jannat ta iya gyaɗa masa domin bata so suyi ta jayayya musamman yadda ya sanar da ita cewa Abbanta shiya tallatata zuwa ga Mahaifinsa a matsayin ita ya zaɓama Shureim ɗin yazo ya nemi soyayyarta,wasu haɗaɗɗun hawaye suka cika idanunta amma tayi gaggawar maidasu ta tashi a nutse ta isa wajen table ɗin da suka shirya abinci da snacks na alfarma ta fara zuba masa.Duk abinda take yi idanunsa na kanta yana sake yaba nutsuwarta da kamewarta,sosai zuciyarsa ke sake shiga cikin ɗokin son ta kasance mallakinsa a cikin suturar aure.Plate ɗin dake ɗauke da Mandi rice with chicken da salad a gefe ta fara kawowa ta aje masa daga gefe domin yana zaune a cikin 2 seater ne,time ɗin data aje plate ɗin ne wani irin sassanyar ƙamshinta ya doki hancinsa har baisan time ɗin da idanunsa suka lumshe ba.Koda ya buɗe idanunsa sai ya saukesu akan bayanta lokacin data juya domin ɗakko bowl ɗin data zuba masa snacks dangin su samosa da meat pie,ya haɗiye wani miyau mai kauri sakamakon yadda surarta ya bayyana masa.Jannat cike da ƙarfin hali ta juyo ta kawo masa bowl ɗin snacks ɗin haɗe da ruwa da lemuka ta aje tana jin tasirin Idanunsa na mamayeta,tana ajewa ta juya domin barin ɗakin tana faɗin,"Yaya Shureim bari na shiga ciki na dawo don Allah kaci abincin please!" Tana kammala faɗin hakan ta fice da sauri tamkar za ta ci ta baki sabida yadda ta ƙosa tayi nesa dashi kota samu ta shaƙi iskar da babu wannan fitinannan ƙamshin nasa a ciki,shi kuwa bayanta yabi da kallo yana ji tamkar ya tashi ya maidota cikin ɗakin sabida ko kaɗan idanunsa basu gaji da ganin kyakkyawar fuskarta ba.

"Princess wannan irin Babban kamu haka? Gaskiya guy ɗin ya haɗu over kuma za ku dace da juna." Feenah ce ta faɗi hakan time ɗin da Jannat ta shigo cikin ɗakin nasu fuskarta a kwaɓe tamkar za ta saki kuka.Harara Jannat ta dalla mata tana aje ganinta akan Arfah dake cin Apple tace,"Kina da damuwa Feenah wato ke har dacewarmu kike hangowa baki tausayin zuciyata ko?" Arfah ce ta kwashe dariya tana faɗin,"Su tausayin zuciya anji jiki,wai waye ne baƙon Pretty wanda haɗuwarsa ya tashi kan Feenah haka?"Jannat ta zauna kusa da Arfah tana sauke numfashi tace,"Yaya Shureim ne Babban Yaron Abbah Prof Arfah,ni bansan shi ba kin sani,muna dai jin Abbah na zancansa amma bansan ko ke kin taɓa ganinsa ba." Arfah ta saki murmushi tace,"Wai kina nufin S.M Bichi Abbah ke nufin ya zaɓa miki dama?" A rikice Jannat ta dubi Arfah dake sake kasheta da smile tace,"Dama kinsan batun Arfah,amma meyasa baki faɗi min ba?" Arfah tace cikin sauri,"No! Jannat bansan komi ba,Mamie ce ke gaya mini wai Abbah yace yayi miki miji,itama ta ji hakan ne a ranar da Hon.Attah yaje gida ya samesa da batun wai yana sonki kuma da aure,but nayi matuƙar farin ciki domin guy ɗin ya haɗu over kuma wallahi an shaidesa yana da nutsuwa sosai,na taɓa ganin pics ɗinsa a wayar Khaleel domin abokin Ameeru ne cousine ɗin Khaleel tare sukai degree ɗinsu a Malaysia,kuma abokin Yaya Ammar ne duk da cewa yanzu nasan abotan tayi rauni kasancewar sunyi nesa da juna,please Jannat accept him matuƙar yana ƙaunarki na tabbatar ba za kiyi danasanin bashi zuciyarki ba." Arfah ta ƙare maganar cikin kwantar da murya alamun rarrashi ga Jannat ɗin,wacce gabaki ɗaya zuciyarta ba a nutse take ba ta rasa yadda za ta fassara yanayin da take ji a cikin zuciyarta.Cike da raunin murya tace,"Why Arfah,meyasa kuke faɗin hakan alhali kunsan an yiwa zuciyata illa?" Wannan karon Feenah ce ta amsa zancen tace,"Sanin anyi mata illar yasa muke so kiyi amfani da damar da Allah ya sake baki ta hanyar jeho miki wanda yafi Aliyu komi,domin wannan guy ɗin ko shakka babu yafi Aliyu Wase komi ciki har da nutsuwa da aji,don haka kiyi haƙuri ki bashi dama kiga da wani kalar soyayya yazo,musamman daya kasance Abbah ne da kansa ya bashi damar zuwa gareki so accept him Jannat In Sha Allah ba za kiyi danasani ba."Jannat ta share hawayen tausayin kanta da suka zubo mata domin jinsu kawai take,amma zuciyarta na faɗi mata cewa Shima tafiya zaiyi da zaran yasan ita ɗin ɗiyar wace ce.Cikin low voice ta furta,"Bani da zaɓin daya wuce na Abbah duk duniya,idan har shi ya zaɓa mini zan amshesa Feenah just pray for me Allah ya cire mini soyayyar Aliyu daga cikin zuciyata." Jannat ta ƙare maganar tana mai kwantar da kanta a kafaɗun Arfah ta saki wani kuka mai cin rai.Dukkaninsu tausayin Jannat ɗin ya sake mamaye zukatansu,suka haɗu suka dinga rarrashinta har ta tsaida kukan tana faman sauke ajiyar zuciya.Ganin ta shafe fiye da mintuna talatin da barowarta sitting room ɗin yasa Feenah kama hannunta tana faɗin,"Tashi muje Jannat nasan yanzu ya kammala,Arfah muje mu gaisa sai mu dawo mu sake barinsa tare da gimbiyar ko?" Arfah ta tashi tana ɗaukar veil ta yafa a saman doguwar rigar dake jikinta na material mara nauyi,ta zura flat shoe ɗinta suka fice domin zuwa su gaisa da S.M Bichi wanda Arfah ke son itama ta gansa a zahirinsa ba irin ganin data yi masa a pics ba......✍🏻