CHEF ZEEY (Love in the Kitchen)
4
by @azizat
CHEF ZEEY
*Love In The Kitchen*
Topnotch season 4
©AzizatHamza2025
ArewaBooks @Azizat Hamza
4
ZEEY
"Sannu kin ji, Sannu Ziyadatu. Wannan jinya duk wata Allah ya kawo miki sauƙinsa"
Wani sharp zafi na ji a tsakiyar marata.
Na ɗan boƙare bayana kamar mai yin sujjada na tsaya a haka har sai da zafin ya sake ni sannan na gyara kwanciyata akan pillow ina cigaba da fitar da nishi.
Ya Allah! Duk macen da bata ciwon cikin period ko kuma zuwan period baya bata wahala to ta godewa Allah.
Tun da Magaribar jiya na ke jin cramps. Na sha pain reliever na ɗan samu relieve kaɗan na yi bacci ina addu'ar Allah ya taimakeni kada ciwon ya tashi min tsakar dare. Ai kuwa ƙarfe biyun dare na tashi da amai da gudawa. Sai da na amayar da komai na cikina amma still ban dena jin aman ba. Sau uku kenan ina sintirin banɗaki. A daren Kaka ta je ta ɗauko gas ta kawo na kunna mata dan bata iya kunnawa ba ta ɗaura min ruwan zafi. Ruwan zafin na ɗan sha kaɗan na sake watsa wasu maganin da ban san adadinsu ba a baki saboda na samu na ji relief da wuri. Ina da aiki gobe. Akwai kayan da aka kawo min zan yi video na yi tallensa sannan akwai matar da ta biya ni kuɗi 'yarta za ta yi aure tana so na je na koya mata yadda ake abincin gargajiya.
Ina kwance Kaka ta dinga matsa min marata da ruwan zafi har sai da ruwan ya yi sanyi.
Haka na dinga jujjuyawa ina nishi har Asuba kafin na ɗan samu relief har bacci ya ɗaukeni bayan na sake shan wasu pain relievers ɗin dan na amayar da wanda na sha.
Ban tashi ba sai ƙarfe tara na safe. Ƙarfe goma zan je gidan matar nan ga kuma na yiwa vendor ɗin da ta turo min garin kununta alƙawarin yau zan mata video na posting.
Ina tashi daga kan gadon idona ya kai kan stain ɗin dake bedsheet. Nan take raina ya sake ɓaci. On top kana fama da ciwon mara da ciwon kwankwaso haka za ka yi ta fama da matsalar stain.
Yaye zanin gadon na yi na ajiye gefe, idan na gama tsaftace kaina zan dawo ta kansa. Na buɗe akwatina na ɗau pad da pant na wuce banɗaki. Ina ciki Kaka ta ƙwanƙwasa min ta ajiye min ruwan zafi kusan cikin bokiti. Na ji daɗin ruwan dan duk da har yanzu ina jin ciwon ciki jikina ya ɗan warware sosai bayan na yi wanka da ruwa mai zafi.
Na fito looking clean and ready to face the day. Ina shiga ɗaki na ga Kaka ta riga ta shimfiɗa sabon bedsheet akan gadon ta ɗauke wanda ya yi staining ɗin.
Anya zan iya surviving a wani wajen idan babu Kaka?
Kaya na saka sannan na kira matar da zan je gidanta na ce ta yi haƙuri zan ɗan zo da latti ta expecting ɗina zuwa ƙarfe shaɗaya ba goma ba kamar yadda muka yi magana.
"Ziyadatu za ki ci ɗumame ne?" Kaka ta ƙwalo min kira
"a'a" na faɗa ina ɗan matsa marata
In dai ina period to ranaku ukun farko bana iya cin komai. Ko zan ci sai dai na forcing kaina na ci cokali biyu ko uku haka idan ba haka ba sai amai.
Kwalin garin kunun da aka aiko min na fito da shi na buɗe ina tunanin ya za a yi na yi videon. Dana gama ɗan joting abinda zan yi sai na fito da ringlight ɗina da ƙaramin tripod da kwalin garin kunun.
"Yanzu za ki yi musu bidiyon?"
"Yanzu zan yi, Kaka. Tun jiya ta ke ta min masifa wai ta aiko kaya ban mata video ba"
Roughly na faɗawa Kaka yadda zan yi and she was on board muka fara recording. Kusan shekara uku kenan ina food content ta riga ta gane yadda na ke abubuwana, duk da ma dai watanni shida da suka wuce ne na fara ɗaukan abin seriously har na sayi tripod. Ringlight kuwa dama Yaya Aminu ne ya siya min tun da jimawa.
Bana nuna fuskata shiyasa ɗaukan videon ya ke min sauƙi. Kaka ce ta yi kunun ni kawai ina saita mata yadda komai zai tafi ne. Muna cikin yi yaran gidanmu suka fara taruwa wai Anty Ziya ta fara bidiyo. Sun saba ganina ina yi fa amma kullum zan yi haka za ka ga suna shigowa gulmar abinda na ke yi.
"Wai ba za ku je Islamiyya bane kam!" Na korasu ganin sun fara distracting ɗina. Idan ina period ba ƙaramin masifa na ke ba. I guess gaskiyar Likitoci da suke cewa period yana sakawa mata mood swing.
Muna gama recording na zauna a tabarma a ƙofar ɗaki na fara editing videon while Kaka ta juyewa yaran kunun da muka yi ta ajiye min kaɗan in case zan sha.
Dana gama editing sai na shiga ɗaki na kulle na riƙe wayata na fara yin voiceover. Ba ni da microphone yanzu, da ina da wani wireless microphone amma ban san wa ya taka min transmitter ɗin ba ya zo ya dena yi.
Ina gama voiceover na ƙarisa editing ɗin na posting videon tareda tagging wacce ta aiko min kayan.
By the time na gama shiri na fito ƙarfe shaɗaya ta cika. Haka dai na fito da sauri na samu Keke na wuce gidan matar. I make sure na ɗauki extra pad dan baƙona ɗan iska ne, zai iya disgracing ɗina a ko'ina. Mata masu heavy bleeding suna fama...
***
Matsalar gida a GRA shine buga gate. Lokacin dana isa gidan sai dana yi ta faman buga gate kafin daga baya har na ji haushi zan tafi aka buɗe. Kuma fa na yita kiran matar tun kafin na iso amma bata ɗauka ba.
"Wa kike nema?" Wani yamutsatstsen tsoho ya tambayeni fiskarsa a ɗaure. Da alama shine Maigadi.
"Hajiya Maryam" "ta san da zuwana" na ƙara da haka dan kar ya ɗauka maula na zo yi gidan.
Wani kallon sama da ƙasa ya min kafin ya ce na shigo.
Kai Allah ya tsinewa Talauci. Yanzu dan zan shiga gida mai GATE shine ake min wannan walaƙancin...
"Ai mun yi ta jiranki. Kin san ni bana so ana wasa da lokaci" matar ta kalleni sannan ta ce "I DON'T LIKE IT"
"Dan Allah ki yi haƙuri, Hajiya. Wani uzuri ne ya riƙe ni" na faɗa a taƙaice saboda na san ni ce da laifi tunda dai ƙarfe goma na safe muka yi zan zo.
Kitchen ɗin gidan ta wuce da ni sannan ta ce bari ta kira min Hayfa, wato 'yarta da zan koyawa girki.
Na tsaya a kitchen ɗin na fara duba ledojin ingriedients ɗin da suka siyo dan na tura musu list last week.
Na fi minti ishirin ina tsaye kafin Hayfa ta fito sai wani tura baki ta ke irin an takurata ɗinnan.
Da headphone a kunnenta ta shigo kitchen ɗin ko magana bata min ba. Na yi ƙoƙarin gaisheta ma amma ko amsawa bata yi ba. Ta ja kujera ta zauna sai danna waya ta ke yi.
Ni dai biyana aka yi dan haka babu ruwana da attitude ɗinta. Zan yi abinda aka ce na yi ne na tafi.
Miyan kuka zamu fara yi amma ko kallo ban isheta ba, duk bayanin dana ke yi mata akan yadda ake miyar kuka ta yi yauƙi ta yi daɗi hankalinta na kan wayarta.
Sai da Hajiya Maryam ta shigo ta mata masifa ta karɓe wayan daga hannunta kafin ta taso daga kan kujeran ta tsaya kusa da ni. Daga masifar da Hajiyar ke yi na fahimci wanda Hayfan za ta aura a ƙasar waje yake da zama, kuma specifically zan koya mata abincinmu na gargajiya ne saboda yana so sosai. Da alama babban mutum za ta aura dan na ji Hajiyar na faɗin kada ta manta da mahimmancin wannan auren.
A yadda na ɗan fahimta, kamar yarinyar bata son auren. Ita kuma Hajiyar ta ɗauki maganar auren kamar ranta. Koma wanene za ta aura dai ban sani ba, dan basu faɗi sunansa ba.
Na dai fahimci wani abu kafin na tafi, wato suma mutanen gida mai GATE suna fama da tasu matsalar...
***
JAYKAY
Yau Sunday, yana gida tun safe babu inda ya je. Bayan ya karya keɓewa ya yi a ɗakinsa shi kaɗai kamar maye yana tunani. Wannan kaɗaicin shi ya ke tuna masa da abinda ya rasa lokacin da ya ajiye takardar aikinsa. Kafin ya dawo Nigeria bai san komai ba sai tuƙin jirgi. It's all he ever knows. It's all he ever wants.
Tun yana yaro yake son jirgi. Ko a toys ɗinsa jirgi ya fi so. Yana shekara takwas ya tabbatarwa iyayensa cewa Pilot ya ke son zama idan ya girma. Yana gama Secondary School Daddy ya tura shi Oxford Aviation Academy ya fara Pilots training a can. Yana samun Commercial Pilot License ɗinsa ya samu aiki da British Airways a matsayin First Officer. Shekara da shekaru yana aiki da su har ya excelling zuwa Senior First Officer. Lokacin da ya samu Airline Transport Pilot License (ATPL) ɗinsa kuma aka promoting ɗinsa zuwa Captain.
Shi Captain ne for good 5 years kafin wannan accident ɗin da ya faru shekaru uku da suka wuce wanda ya chanja komai na rayuwarsa.
Ranan Alhamis ne, ba zai taɓa mantawa ba. Yana iya tariyo abinda ya faru tiryan-tiryan kamar yau abun ke faruwa...
***
SHEKARA UKU DA SUKA WUCE
Captain Jalal Maiyaƙi yana shiga cockpit wajen zamansa a cikin jirgi ya fara yin system checkings na ƙarshe. Bayan ya gama duba komai tun daga flight plan, har zuwa adadin fuel levels da ake da shi. Sai ya fara addu'o'in da ya saba duk lokacin da zai tashi.
Wayarsa ce ta yi vibrating yai kamar ba zai duba ba sai kuma ya ciro wayar yana tunanin wataƙila Jamal ne ya ke son faɗa masa cewa ya isa Abuja lafiya.
Bai kamata ya duba wayarsa a wannan lokacin ba. Bai kamata ya amsa waya ba a irin wannan lokacin. Amma ganin sunan ɗan'uwansa ke kira sai ya ce bari kawai ya ɗauka ya faɗa masa zai kirashi idan suka sauka.
Lokacin da ya ɗau kiran maimakon muryan Jamal sai ya ji muryan wani yana faɗin "Hello, Hello, Allah yiwa mai wayan rasuwa. Muna hanyar Asibiti da sauran waɗanda suka yi hatsarin amma shi mai wayar ya cika ku samemu a Asibitin..."
"Captain" Copilot ɗinsa ya kira shi.
A birkice ya juyo ya kalleshi ƙwaƙwalwarsa bai gama processing abinda ake faɗa masa ba.
"Are you Okay?" Copilot ɗin ya tambaya.
Gyaɗa kai ya yi ya mayar da hankalinsa wajen jirgin yana kashe wayar tasa gaba ɗaya.
Hankalinsa rabuwa ya yi kashi-kashi. Waye ya kira shi da wayar Jamal? Wani irin prank zai masa da cewa wai mai wayar ya rasu. Ina Jamal ya ke?. Sun yi waya da Jamal jiya da daddare akan zai je Abuja gidan Uncle ɗinsu wajen matar da zai aura sati uku masu zuwa.
Har ya yi taxi a runway aka bashi clearance suka tashi hankalin Captain JK Maiyaƙi baya jikinsa. Tarin tambayoyine marasa amsa suka cika masa kwanya.
A haka dai ya cigaba da tuƙa jirgin har Allah ya kaisu lafiya. Sai dai saboda bashi da nitsuwar zuciya sai ya yi misjudging altitude ya sauka da sauri wanda hakan ya sa jirgin ya bugi ƙasa da ƙarfi har sai da tayoyin jirgin suka fashe. Fasinjojin jirgin suka ruɗe kowa ya fara ihu. Babu wanda ya ji ciwo amma kowa ya tsorata da fashewar tayar hatta sauran Crews ɗin dake cikin jirgin sun ɗan girgiza.
Emergency crew ne suka shigo da sauri aka fara duba mutane ana fito da su a hankali
"Are you okay, mate?" Copilot ɗinsa ya tambaya yana dafa kafaɗarsa.
Captain Jalal ya gyaɗa masa kai. Wayarsa ya ciro ya kunnata. Numbar Jamal ya sake kira amma sai ya jita a kashe. Nan fa hankalinsa ya sake tashi. Ya kira numbar Hajiyarsu amma ba a ɗauka ba. Numbar Uncle Idris ya kira ya kuwa ci sa'a aka ɗauka. Sunan Jamal ya fara ambata yana tambayar ko ya isa Abuja lafiya. Daskarewa ya yi a wajen lokacin da ƙanin mahaifinsu ke faɗin Allah ya yiwa Jamal rasuwa motarsa ta yi hatsari. Har Airline safety officers suka zo suka tafi da shi for questioning komai duhu ya ke gani.
Jamal ya rasu kaman yaya? Jamal fa, Jamal ƙaninsa, his best friend, his best buddy.
Tambayoyin da officers ɗin suka masa da kuma wayarsa da aka karɓa ne aka gano cewa already kafin a tashi maganar mutuwar ɗan'uwansa da aka masa ya taɓa shi. Nan take aka bashi temporary suspension for negligence.
Bayan ya gama serving suspension ɗinsa sai ya applying zai dawo tuƙi, amma Aviation Authorities suka hana shi dawowa saboda lokacin da aka masa Medical assessment an tabbatar yana fama da depression saboda rasuwar ɗan'uwansa kuma ya ƙi ya je ya yi therapy. Saboda mahimmancin Aviation Safety Laws sai aka ƙi mayar masa da license ɗinsa na tuƙin jirgi. Option ɗin aiki off-air suka bashi, suka ce ya koma ɓangaren Air Traffic control ko kuma Flight Instructor amma ya ƙi. Wannan ya sa shi rubuta resignation letter ya basu.
Shekara uku da suka wuce kenan da faruwar hakan. Bayan ya ajiye aikinsa ne ya dawo Nigeria saboda ya kula da Kamfanin da mahaifinsa da kuma ƙaninsa suka bari. It was not easy for him. Kula da kamfani, matsalar aurensa, surutun Hajiya, da kuma rayuwa da sanin cewa Jamal ya tafi kenan ba zai sake dawowa ba...