37
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
*AMATURRAHAMAN*
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
💞💞💞💞💞💞💞💞
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*BOOK 1*
*PAGE 37*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Fuska a cunkushe ta ƙarasa ɗakin Momynta ta sameta itama fuska ba walwala, zama tayi tana ɗora kanta saman kafaɗar Momyn tace. "Wallahi Momy in na bari Aunty Zaheera ta samu Yaya Zayyad ban haifu a cikin ki ba, ai wallahi in dai ban same shi ba to ba shegiyar data isa ta same shi a cikin gidan nan bare har tazo tana hura mana hanci. Momy wai Kinga rashin mutuncin data min yanzu kuwa!".
"Kin ga ki rabu da ita zamuyi lokacinta, yanzu Dadynku ne ya kira yace ki shirya kije ki gaishe da waɗan can mutanen suna sashen Hajiya Iya." Momyn ta faɗa tamkar ta fashe da kuka tsabar haushi.
"Momy ni dai ba zanje ba, ai naga sanda suka shigo nayi wucewa ta." Cewar Anisa tana gyara kwanciyarta.
"Kinga maza tashi ki shirya muje tare ai shi yaƙi ɗan zamba ne, kuma sannan kin san halin Dadynku sarai dai ba sai an tuna maki ba." Momy ta faɗa tana janye jikinta ta miƙe. Tashi Anisa tayi ba don taso ba tana ƙun-ƙuni ta shiga ɗakinta ta sako hijabi akan doguwar rigar English wears ɗin dake jikinta suka wuce ita da Momy data haɗa abin motsa baki a ƙaton tire aka rufe da farin ƙyalle ta bawa Anisa ta riƙe tana tura baki suka wuce.
Sun same su sunci sun sha suna ta hira da Hajiya Iya Sarkin zance, zama suka yi suka shiga gaisawa fuskar Momy cike da fara'a kai ba zaka taɓa cewa bata son haɗin ba. Suna haka Dady ya shigo da sallama ya zauna shima aka shiga gaisawa, ya mai jiki Alhaji Abba gana ya masa ya amsa masa da "Alhamdulillah."
Hira suka ci gaba dayi irin ta aminai, tayin zuwa sashin su Momy ta yiwa Hajiya Shuwa. Ba musu kuwa suka bita ita da ƴanmatanta guda biyu, Anisa ma binsu tayi don ta tsani irin kallon da Abdulmajid yake binta da shi. Suna fita maimakon sashin su sai ta waske ta nufi sashin Ammah, lura da hakan da Momy tayi ne yasa tace ma Anisan "Ga ƴan'uwanki nan ku tafi tare mana." Ta ƙare maganar tana murmushi n yaƙe gudun kar Hajiya Shuwan ta zargi wani abu.
Safah data lura da yanda Anisa take wani shan ƙanshi tace "A'a Momy taje kawai." Dama ba wani son zuwan nasu take ba sai kawai ta kaɗa kai tayi gaba abinta. Murmushin yaƙen itama Hajiya Shuwan tayi suka wuce.
A can ɓangaren Baba Alhaji kuwa Alhaji Abba gana ne ya sako maganar ɗaurin auren, yace ko za'a ɗaga ne har Baba Alhajin ya ƙara war-warewa.
"Ai jiki yayi sauƙi Alhamdulillah, nan da sati ɗaya kawai sai a ɗaura a wuce wurin kawai." Cewar Baba Alhaji. Wani irin daɗi ne ya mamaye zuciyar Abdulmajid yaji tamkar ya taka rawa don murna.
Basu bar gidan ba sai da aka tabbatar da maganar ɗaurin auren ranar Asabar.
*Muzaffar.....*
A ɓangaren Muzaffar kuwa tunda suka dawo daga duba Baba Alhaji ayyuka suka masa yawa, wani case ne mai sarƙaƙiya yake gudanarwa a Kotu wanda yake da matuƙar saka masa zafin kai. Hakan ne yasa ya tattara gaba ɗaya hankalinsa don ganin ya kamo bakin zaren sarƙaƙiyar dake damfare a cikin case ɗin. Wannan ne dalilin ne ya hana shi komawa Matazu domin duba jikin Amaturrahaman.
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
A can Matazu kuwa Amaturrahaman ta zama Boss a gidansu dama umguwarsu gaba ɗaya, domin kuwa yanzu kowa mugun tsoronta yake ji ba wanda ke shiga gonarta koda wasa. Wanda yayi kuskuren hakan kuwa koda a cikin rashin sani ne ya san abinda zai biyo baya domin bata yafiya ana mata zata yi hukunci.
Wannan jajircewar da tayi ta tsaya wa kanta yasa masu shirin haiƙewa rayuwarta don ganin yanzu ita kaɗi ce babu masifaffiyar Yayarta suka maida mugun yawunsu a kanta, domin kuwa kowa ya samu labarin irin ta'asar da karen Labor ke yiwa mutane dasu Labor ɗin kansu.
Ta kai ta kawo yanzu Amaturrahaman ta saba da karen sosai saboda kyautata masa da take yi, tana bashi umurni yake bi babu gardama don haka rayuwarta take gudanarwa hankalinta kwance ba tare da fargabar suwa zasu kawo mata hari ba.
Taso ta haɗu da Gaddafi domin huce haushinta a kansa, sai dai su Labor sun bincika duk wani wuri da ake ganin Gaddafi amma ba'a same shi ba. A ƙarshe dai sun zo mata da labarin cewa Mahaifinsa ya fitar da shi ƙasar waje Karatu. Wani miskilin murmushi ne ta suɓuce mata lokacin data samu labarin.
Ta tabbatar da manufa Alhaji Tanimu ya tura Gaddafi wata ƙasar amma ba komai duk ma inda ya shiga zai dawo komin daɗewa, itama kuma bata manta bashin gaba bare ɗaukar fansa. Da wannan tunanin ta ture babin Gaddafi kamar yanda ta manta da Doctor Farhan taci gaba da rubuta jarabawarta da ita kawai take so ta kammala domin fara karatunta wanda ta canza ƙuduri daga abinda tayi niyar karantawa a farko saboda wani dalili nata na kanta.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Kamar yanda Hajiya Ruƙayya ta tsarawa Salim ya fara bin tsarin kamar yanda take so domin kuwa ya rage yawon da yake yi yanzu yana kwana a gida, sannan kullum da safe yana shiga ɓangaren Baba Alhaji ya gaishe su shida Hajiya Iya wacce mamaki yasa ta kasa shiru sai da ta magantu. "Ikon Allah! Salim yau kaine a natse haka kazo gaishemu da safiyar Allah?." Ta ƙare maganar da tsananin mamaki don rabonta da taga Salim a cikin natsuwarsa haka har ya kwana a gida da safe yazo gaishe su har ta manta ranar.
"Nine mana Hajiya Iya Allah ne ya kawo min shiriya na gane gaskiya." Salim ya faɗa yana wani sunkuyar da kai kamar mutumin kirkin da gaske.
"Masha Allah, ai haka muke son ganinka dama Salim sai kaci gaba kamar yanda ka fara domin rayuwarka tayi kyau." Baba Alhaji dake kishingiɗe saman shimfiɗarsa ya faɗa.
"In sha Allah Baba zan ci gaba da kasancewa haka ko don in samu soyayyarka nima." Salim ya faɗa yana jin zuciyarsa na masa zafi akan yanda Baba Alhajin ya fifita wan can guy ɗin fiye da kowa a cikin family ɗin gaba ɗaya. Murmushi Baba Alhaji yayi saboda ya jima da sanin cewa da yawa daga cikin yaran jikokin nasa suna ganin cewa yafi son Zayyad da fifita shi a cikin su.
Eh ƙwarai hakane soyayyar da suke yiwa Zayyad ta da bance a cikin yaran gidan saboda kasancewarsa jika na farko da suka samu, sannan kuma yaron yana da shiga rai tun yana jariri. Ɗaya girma kuma nagartattun halayensa su suke ƙara saka soyayyarsa a zukatan mutane. Amma duk da haka suna ƙoƙarin ganin sun haɗa kan ahalinsu da nuna musu su ɗin abu ɗaya ne a wurinsu.
Sai dai Hajiya Ruƙayya a kullum tana rusa wannan ginin da suke yi ta hanyar horar da zuciyar yaranta a kan ƙiyayyar ƴan'uwansu musanman shi Zayyad daya tsonewa mutane da dama ido, a kullum nuna musu take su ɗin abokan gabarsu ne waɗanda suka tare musu samun ci gabansu musamman Zayyad da Allah ya ɗaukaka a cikinsu ta hanyar bashi arziƙin daya zo ya zarta na Mahaifinsu da suke tutiya dashi.
Abu na biyu Allah ya yi shi kamilin mutum nutsatstse mai matuƙar kamewa sannan mai tausayin na ƙasa da shi mai kyauta da karamci, sai dai baya ɗaukar raini. Waɗannan halaye nasa na kyautatawa shike ƙara janyo masa farin jinin al'umma a duk inda yaje ya mu'amalancesu. Sannan kuma Allah ya masa albarkar hannu ta yanda duk abinda ya kasa da sunan sayarwa sai dai kuɗinsa, yanzu bai daɗe da buɗe Companynsa na sarrafa abinci ba amma a ƙanƙanen lokaci Companyn ya sanu ya kuma karɓu ga al'umma saboda ingancin kayan da yake fitarwa da kuma sauƙinsa.
Yanzu babu inda ba'a kaiwa kaya daga Companyn a faɗin jahohin Nigeria, sannan ba ƙananan kuɗaɗe Companyn ke kawo wa ba, banda ma sauran shares da yake dasu a wasu kamfanonin musamman na Mahaifinsa da ya kusa mamaye wa saboda duk kamfani zaka samu yana da 50 ko 70% na hannu jari. Ga kuma gidan gonarsa dake fitar da manyan kuɗaɗe da albarkatun gona da kuma dabbobi. Duka wannan ɗaukakar da Allah ya masa itace ta tsonewa mutane ido ta haifar masa da tarin maƙiya duk da irin kyautatawar da yake yiwa kowa dai-dai gwargwado duk da ma shi aikinsa yafi bawa mahimmanci baya zama ya sadaukar da lokacinsa da lafiyarsa da basirarsa wurin bawa ƙasarsa kariya, dukiyar tasa ma wasu ya ɗora suke kula masa da ita.
Wasu daga ciki suna hannu ɗan'uwansa wasu kuma Mahaifinsa ne ke kulawa dasu, yayinda wasun kuma aka ɗora amintattu mutane suke gudanarwa.
Ajiyar zuciya Baba Alhaji ya sauke lokacin daya gama tunaninsa yayi murmushi ya dubi Salim yace "Ni dama ban taɓa ƙinka ba Salim kai ɗin jikana ne ina jin ka a zuciyata tamkar yanda nake jin kowa daga cikin Jikokina. Abinda nake so ka fahimta shine ba'a taɓa ƙin mutum sai dai a ƙyamaci halinsa, nima halayenka mara kyau su nake ƙyamata kuma ina maka addu'a kullum akan Allah ya shirye ka ka gane gaskiya, Alhamdulillah kuma ka gane yanzu komai ya wuce." Ya ƙare maganar cike da tausasawa a gare shi, sai dai hakan ko kaɗan bai yi tasiri ba a zuciyar Salim domin ɗaukar hakan yake a matsayin daɗin baki Baba Alhajin ke masa saboda ya riga yayi nisa a wannan tunanin da kuma turbar da Mahaifiyarsa ta ɗora shi a kai. A zahiri kuwa murmushi yayi ya masa godiya ya miƙe ya fice yayinda Hajiya Iya ke binsa da kallon mamaki don ita dai ganin abin take yi kamar a mafarki.
"Anya yaron nan shine kuwa?." Ta faɗa still dai tana mamakin abin, domin abin ayi mamakin ne.
"Shine mana, fatana dai shine Allah yasa da gaske yake ya gane gaskiyar, sannan ina fatan Allah ya haɗa kawunansu ya kaɗe fitina. Zanyi farin ciki idan naga kan iyalina a haɗe sun zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, zan kasance a cikin farin ciki koda ace bana raye a wannan duniyar wannan shine fatana da burina a duniya!". Ya ƙare maganar rauni na cika zuciyarsa saboda ganin duk yanda yaso hakan bai samu ba, duk da dai ya samu nasara ta farko ta hanyar haɗe kaf zuri'arsa suke rayuwa a cikin gida ɗaya ba tare da sun rarrabu ba.
"In sha Allah burinka zai cika Alhaji." Hajiya Iya ta faɗa cikin son kwantar masa da hankali saboda jikin nasa har yanzu ba wai yayi ƙalau bane, Alhamdulillah dai yana samun sauƙi.
Salim kuwa yana fita tsaki ya saka ya nufi ɓangaren mahaifinsa dake cikin gininsu, shima gaisuwar yaje ya masa tamkar yanda yayi wa su Baba Alhaji. A ɓangarensa ma yaji daɗin ganin Salim ɗin a natse don haka yayi masa nasiha sosai kafin ya sallame shi. Wurin Mahaifiyarsa ya koma wacce ke jiransa don sanin yanda abubuwa suka gudana, da wannan damar ta zaman gida da Salim keyi tayi amfani ta riƙa bashi ruwan rubutun da Malam na kan buzu ya bada a bashi domin ya daina abinda yake ita kuma ta mallake shi ya zamana cewar duk abinda ta saka shi shi zai yi.
Ana samun ci gaba tunda yanzu baya fita yawon banzan, sai dai abinda bata sani ba shine in ya shige ɗakinsa ya kulle ba abinda baya sha na kayan mayensa. Sai dai ya rage sosai kuma cikin tsari yake shan domin sai da dare idan zai kwanta. Masu aikin ɓangarenta kuwa da take tura masa domin yi masa hidima yanzu dasu yake mua'amalarsa ba tare da saninta ba.
___________&
Ba ƙaramin rikici aka kwasa tsakanin Hajiya Sha'awanatu da Dady ba lokacin daya sanar da ita taci gaba da shiri nan da sati ɗaya za'a ɗaura auren Anisa. Sosai ta saka masa daru akan bata amince ba saboda Anisa bata so, wanketa tas yayi ya kuma mata rantsuwar zai iya sakinta idan ta kawo masa wargi a kan maganar auren nan.
Dole taja bakinta tayi shiru saboda bai taɓa furta mata haka ba tunda suka yi aure tsawon shekara ashirin da wani abu, sannan kuma gaskiya na ƙaramin son Mijinta take yi ba, bata buƙatar abinda zai taba igiyar aurenta don haka tabi shawarar aminiyarta da tace ta lallaɓa Anisa ayi auren daga baya zasu san yanda suka yi suka kashe auren ba tare da an zarge su ba.
Duk da bata so hakan ba amma haka ta haƙura ta lallaɓa Anisar wacce tayi ta botsarewa akan bata so sai da tace zata barta da Dadyn nasu san nan ta haƙura zuciyarta tamkar zata fashe.......