ƳAR KARUWA PART 1

ƳAR KARUWA Chapter 18

by @ayshadansabo

Arewabook@ayshadansabo

Paid book

***

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter18

Akan idanun Ammar Chiroma Mamie suka fito ita da Labibah,Labibah bata sauya shiga ba illa turban kaɗai data sauya amma waɗannan kayan dai da suka fidda surarta sune a jikinta.Mamie ce ta sauya shiga zuwa wata arebian gown mai mugun kyau,ta naɗe jikinta da veil mai kauri daya rufe jikinta sosai tare da haske farar fatarta kasantuwar kalar veil ɗin dark ash.Front seat Labibah ta buɗe ta shiga yayinda shi kuma A.Chiroma yayi saurin ficewa domin rufo gidan,koda ya dawo ya shiga motar baiyi gigin sake ɗaura idanunsa akan Labibah ba ya tashi motar suka fice daga gidan yana ayyana yadda zai ɓullowa Mamie ya yakice zancen wannan haɗin.

Sosai ya zaga dasu wuraren hutawa da ciye-ciye,lokacin yin lunch nayi suka isa wani ƙayataccen wajen cin abinci suka ci.Sunyi yawo sosai har Mamie na mamakin yadda Ammar ya jure baiyi ƙorafi ba ko ƙanƙani,Shi kuma ya jure ɗin ne kawai domin ya faranta zuciyar Mamie.

Sai misalin ƙarfe shida na yamma suka dawo gidan kowanne riƙe da manyan ledojin da suka yo shopping,domin sosai Labibah ta zage ta zaɓi abinda ranta keso time ɗin daya kaisu wani shopping mall dake kan hanyarsu ta dawowa gidansa.A gajiye suke sosai har shi kansa domin ya manta rabon da yayi yawo irin haka,kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya watsa ruwa tare da sauya kayan jikinsa.Bai sake gigin fita ko'ina ba yayi kwanciyarsa bisa sofa domin hutawa,wayansa ya janyo ya shiga neman layin Inna yana fata ya sameta domin kwanaki biyu kenan yana neman line ɗinta baya samu tunda suka tafi Saudi.Cikin sa a ringing biyu yayi ya ji ta ɗaga wayar ta doko masa sallama,amsa sallamar yayi yana ɗaurawa da faɗin,"Granny kodai za mu hanaki riƙe waya ne tunda bashi da amfani a wajenki?" Yadda yayi maganar cike da taɓara ya sanya Hajiya Inna sakin dariya kafin tace,"Haƙuri dai za ku cigaba dayi domin wallahi idan na aje wayar ne saina rasama ina take,ɗazunnan Takwara ta kirani itama ta gama ƙorafin cewa bata ga amfanin wayata ba,yanzu dai ya kake ya Mardiyyah da baƙuwar taka naji Muhammadu yace wai da Labibah suka taho ko?"Ammar ya saki ƙaramin tsaki yace cike da takaici,"Inna ina cikin ɓacin rai don Allah ki tayani addu'a Mamie ta fahimceni." Inna tace cikin sauri,"Baku daidaita kanku bane Ammaru? Har ina murna nace sai a haɗaku kai da ƴan ƙannenka a aurar daku,faɗa mini idan baka amshi zaɓin Mardiyyah ba wa kake dashi da za ka kawo mufa gaskiya mun gaji da ganinka babu aure Ammaru,don haka haƙuri kawai zakai ka amshi zaɓin...." Ammar ne ya katse Hajjah Inna ta hanyar faɗin,"Don Allah Inna kibar wannan maganar,indai matar aure ce zan fiddo ku sake bani lokaci amma da gaske bana son Labibah Inna." Hajiya Inna tace,"To yanzu me kake so ince?" Ammar yace cikin wani irin yanayi,"Addu'a Inna, addu'a za ki min kice Allah ya mallaka mini wacce zan nema aurenta kinji?" Cike da farin ciki Hajiya Inna tace,"Dama akwai wacce kake so ne Ammaru shine baka taɓa sanar mini ba?"Ammar Chiroma ya lumshe idanunsa tare da buɗesu yakai dubansa saitin da frame ɗin zanensa yake aje,cikin wani irin zuzzurfan sauti yace,"Inna ina dai addu'a Allah ya haɗani da ita tunda kun gaji dani kun ƙosa wata ta shigo cikin rayuwata,kiyi min addu'a Allah ya zaɓa mini mafi alkhairi kinji Granny? Hajiya Inna tace,"Naji Ammaruna,Allah ya haɗaka data gari,ita kuma Mardiyyah ka bita a hankali kaji ko?" Ammar ya jinjina kansa yace,"In Sha Allah Inna." Hajiya Inna tayi ƙasa da muryarta tace,"Ammaru dama ina so nayi maka wata tambaya." Ammar yace cikin ƙasaitacciyar muryarsa,"Ina jinki Hajiya Inna Allah yasa na sani." Hajiya Inna ta sake kwantar da murya tace,"Kasan wani Yaro Shureim ɗan wajen Farfesa Mansur Bichi (Professor) aminin Mahaifinka?"Ammar cike da ƙaguwa yace,"Na sanshi Inna me yafaru ne?" Hajiya tace cikin sauri,"Shi Muhammadu ya zaɓama Takwarata Ammaru,ina son sanin nagartarsa ne domin na tabbatar Hafsatu za ta amince dashi ne domin ta farantawa Mahaifinka rai,sabida Yarinyar zuciyarta na ga Aliyu Yaron Sanata Wase,kofa wata guda da fasa zancen aurensu ba a yi ba gashi Abbah ya kawo wannan yace wai Farfesa da kansa ya nemi alfarma aba shi Shureim ɗin dama yazo ya nemi ɗaya daga cikinsu,shine Abbanku ya sanar dashi cewa sai dai Hafsatu sabida Arfah an riga an amsa maganarta da ɗan gidan Alƙali,don Allah ka bincika mini kaji halayyar Yaron da nagartarsa duk da dai nasan Muhammadu bazai zaɓa mata abinda zai cutar da ita ba,amma wasu lokutan ku matasa kunfi sanin halayen ƴan uwanku wanda ba lallai ko Iyayensa susan wasu halayyar da yake gudanarwa a waje ba." Hajiya Inna ta dakata da kalamanta tana sauraron jin ta bakin Ammar Chiroma wanda tun fara maganarta ya tashi zaune bisa sofar yana saurarenta,da wani irin murya mai zurfi yace,"Ina jinki Inna cigaba da maganarki." Hajiya Inna cike da takaicin miskilancin Ammar Chiroma tace,"So nake ka sanar dani halayyarsa shin nutsatstse ne bashi da wani aibu ko kuwa irin sangartattun Yarannan ne da suka gama watsewarsu a turai Uban ke neman kai dashi shiyasa ya lallaɓo yana son a zaɓa masa nagartacciyar mace?" Sai da Ammar Chiroma ya ɗan cije baki tare da furzar da wani irin zazzafar numfashi kafin yace,"Inna na sanshi mutumin kirki ne bashi da wata damuwa indai Shureim Bichi ne,so baki da wani damuwa a kansa domin yana da riƙo da addini fiye da yadda kike tunani." Ya ƙare maganar murya can ƙasa yana sake jinjina dukkanin jawaban Hajiya Inna a cikin zuciyarsa.Cikin farin ciki ya jiyo Inna na faɗin,"Alhamdulillah! Hankalina har ya kwanta Ammaru,zan yi addu'a akan Hafsatu Allah ya bata dangana ya sanya mata soyayyarsa a cikin zuciyarta." Ammar ya kasa sake cewa komi hakan yasa ya sanya Hajiya Inna sake faɗin,"Hallo Ammaru kana jina kuwa?" Ammar ya ɗan rintse idanunsa yace cike da galabaita,"Ina jinki Inna yaushe ne su Arfah za su kammala karatun nasu?"Hajiya Inna tace,"Muhammadu za ka tambaya ko ita Arfan tunda ita Takwarata tace kota kira ku gaisa baka ma ɗaga wayarta,kuji tsoron Allah kaida Mardiyyah akan ƙin marainiyar Allah da kuke,Hafsatu bata da laifi domin dukkanin abinda ya faru tun daga kan auren Nuratu da Kabeeru ƙaddararsu ce wanda babu wanda ya isa ya canza komi,kaine Babbansu Ammar idan har baka jata a jiki taji cewa kai ɗin ɗan uwanta ne na jini da za ka maye musu gurbin Abbah a garesu a lokacin da ƙasa ya rufe idanunsa ba wa take dashi da zai jata a jiki?Ka daina biyewa ƙiyayyar da kuke wa Nuratu kaida Uwarka kuna nunawa halittar da bata ji ba bata gani ba rashin ƙauna don Allah." Hajiya Inna takai ƙarshen kalamanta tana jin zafin halin ko inkular da Ammar ke nunawa akan Jannat,domin tafi kowa sanin baya ƙaunar Yarinyar tun tana ƙaramarta.Cikin wani irin murya mai zurfi Ammar yace,"Inna kiyi haƙuri nifa ba ƙinta nake ba,kinfi kowa sanin ko Arfah bana janta a jiki,mubar maganar Yarannan Inna please!" Hajiya Inna tace a ƙufule,"An bar shi Ammar,yanzu yaushe Mardiyyah za su dawo ita da Amaryar taka?" Ai kawai sai Ammar ya kashe wayarsa yana sake jin wani irin ɓacin rai na lulluɓe zuciyarsa.Komawa yayi ya kwanta tare da lumshe idanunsa kansa na fara masa wani irin ciwo,ya ɗauki time mai tsawo a kwance idanunsa kuma a lumshe kafin ya buɗe idanunsa yana kallon time.Gani yayi lokacin sallar magriba ta kusa,ya tashi a nutse yana jin yadda ciwon kansa ke sake tsananta.Toilet ya nufa ya ɗauro alwala ya fito,ya nemi baƙin gilashinsa ya manna a idanunsa.Wayansa guda ya ɗauka tare da saka sauran a silent ya fito,babu motsin kowa a cikin falon hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi ma Ammar ba.Ya fice da sauri domin baya ma buƙatar su ga fitarsa,gidan Sheikh Irshad zai je wanda gidan ke can daga ƙasa kaɗan da jerin gidajen nasu.Tun jiya sukai waya dashi ya sanar dashi dawowarsa ƙasar domin yayi tafiya ne yaje can gida Kuwait duba Iyayensa,shiyasa yake son shiga su gaisa kafin ya sanya masa time ɗin da zasu cigaba da karatu.Duk a ranakun alhamis da juma'a Ammar Chiroma ke ɗaukar karatun manyan littafan addini a wajensa,a gidansu suke jam'in sallar magriba zuwa Isha'i bayan sun kammala ya kan matsama Ammar ɗin susha shayi irin nasu na labarawan Kuwait gabannin fara karatun.Sun shaƙu sosai da juna domin ya ɗauki Ammar Chiroma tamkar ɗan cikinsa ne domin shi Allah bai bashi haihuwar ɗa namiji ba,duka Yaransa uku mata ne ya aurar da biyu acan Kuwait sai autarsa Amal data rage mai shekaru sha bakwai yanzu haka tana level 2 ne a jami'ar ƙasar INSTANBUL tana karantar medicine.A ƙafa Ammar Chiroma ya dinga takawa cikin nutsuwarsa ta halitta,sosai yake motsa jikinsa ta hanyar tafiyar ƙafa idan zashi gidan Sheikh Irshad ɗin.Yana isa gidan ya samu ya fito domin gabatar da sallar magriba a wani waje na musamman daya ware a wajen gidansa ya maida shi tamkar ƙaramin masallaci,cikin fara'a ya tarbi Ammar suka rungume juna yana masa magana cikin harshen nasara domin Ammar kaɗan kaɗan yake koyan larabci a wajensa bai yi ƙwarewar da suke iya dogon magana da larabci ba.Tare suka gabatar da sallar magriba gabannin su zauna suna hirarsu Sheikh na bashi labarin yadda ya baro Iyayensa,Ammar ya sanar dashi cewa shima Mahaifiyarsa nanan ta kawo masa ziyara amma ya ɓoye masa maganar Labibah.Sai da aka sallaci Isha'i Sheikh Irshad ya jasu Jam'i sannan Ammar yayi sallama dashi yace zai koma gida,ga tsananin mamakin Ammar sai cewa Sheikh yayi ya jirayesa ya shiga ya sanar da Iyalinsa cewa zai je ya gaida Mahaifiyarsa.Ammar Chiroma ya amsa masa yana jin farin ciki sosai a cikin zuciyarsa game da yadda Shehin Mallamin ke tsananin ƙaunarsa,ba a jima ba sai gashi ya fito hannunsa riƙe da wata kyakykyawar kwanon Silva mai kyau irin wanda labarawa ke sha'awar zuba abinci a cikinsa.Da sauri Ammar Chiroma ya miƙa hannu ya amsa kwanon daga hannun Dattijon Mallamin wanda a girme ya girmi Abbah sosai,suka fara tafiya jere da juna suna tattauna muhimman al'amura a tsakaninsu.Time ɗin da suka ƙariso gidan sai Ammar Chiroma ya isa dashi wajen wani ƙayataccen rumfar hutawa dake daga ƙarshen harabar compound ɗin gidan,an zuba wasu irin kujerun kaba masu kyau a wajen tare da aje table a tsakiya.Lokuta da dama a ranakun weekend da baya fita ko'ina anan yake zama yana aikin zane-zanensa,sosai wajen ke da daɗin zama sabida shuke-shuken flowers masu ƙamshi dake zagaye da wajen suna bada iska mai matuƙar daɗin shaƙa.Sanar da Sheikh ɗin yayi cewa bari ya shiga ya sanar da Mamie cewa zai shigo ya gaidata,Shehin Malamin ya sanar dashi cewa babu komi hakan shine koyarwar addini dama.

"Mamie ga Sheikh Irshad nan ya zo domin ku gaisa." Cewar Ammar Chiroma lokacin daya shiga cikin falonsa ya tadda su Mamie zaune sun baje Pizza suna ci.Labibah sanye cikin wasu kayan bacci masu nuna jiki,kallo ɗaya yayi mata yayi saurin ɗauke kansa zuciyarsa na sake ɓaci.Mamie tace cikin fara'a,"Madallah amma ko ka kyauta da ka kawo mini shi har gida,shigo dashi mana ke Labibah jeki sanyo hijab don bai dace ya shigo ya ganki da wannan shigar ba ƙirji duk a waje." Labibah sai da ta saci duban fuskar Ammar Chiroma da yayi mugun haɗesa kafin ta kashe murya tace,"Okey Mamie kinsan ni bana son zama da kaya masu nauyi da dare komin sanyi." Ammar dai ficewa yayi yana jin tamkar zuciyarsa ta buga da tsanar Yarinyar da ƙyamatar ɗabi'unta.Yana gaba Sheikh na biye da bayansa suka shigo cikin falon,ya samu su Mamie sanye duk da hijaban da suke sallah.Da harshen turanci suka gaisa domin Mamie bata jin larabci sai kalmomi kaɗan kawai take tsinta,Labibah ma cikin harshen nasara ta gaida Shehin Malamin wanda yayi masifar yi mata kwarjini.Ya amsa ba tare da ya kalleta ba,idanunsa akan Ammar Chiroma da hankalinsa ke kan kiran Khairiyyah dake shigo masa yake baiwa Mamie labarin irin ƙwazo da ƙoƙarin da Ammar ke nunawa wajen ganin ya samu ilimin addini mai zurfi.Sheikh Irshad ya baiwa Ammar umurnin baiwa Mamie wannan kwanon da suka taho dashi,cike da Ladabi Ammar ya kai kwanon gaban Mamie ya aje yana faɗin,"Mamie gashi please kiyi masa godiya sosai Mallam yana ƙaunata matuƙa da gaske." Mamie cikin nuna farin cikin tayi masa godiya tare da tabbatar masa da cewa kafin ta bar ƙasar za ta je har gida ta duba Iyalansa,har Mallam ya tashi zai tafi Mamie ta tsaida shi tare da faɗi masa cewa tana son yin magana dashi.Ya koma ya zauna domin ya saurareta,hakan yasa ta maida dubanta kan Labibah tace,"Daughter ke da Ammar ku bamu wuri please." Ammar Chiroma shine ya fara tashi ya fice zuwa wajen rumfar hutawarsa,Labibah kuma ta nufi hanyar shiga ɗakunan baccinsu tana mai samun wuri ta laɓe daga jikin corridor ɗin ta yadda za ta saurari dukkanin kalaman da Mamie za su tattauna da Malamin wanda harshensa ya ji turanci sosai tamkar ma ba asalinsa balarabe bane.A hankali Mamie ta fayyace masa matsalar da take son fuskanta da Ammar Chiroma akan zaɓin matar aure data yi masa,ta bashi labarin cewa Yarinyar bata da wani matsala sai na rawar kai wanda kuma hakan bakomi bane domin da yawa ƴan matan yanzu haka suke shine zai saitata ta koma irin yadda yake so da zaran anyi auren.Ta cigaba da sanar da Shehin Mallamin irin yadda suka ɗauki tsawon lokaci suna bashi dama ya kawo zaɓinsa amma sai ya daina zuwa ƙasarsa ta haihuwa domin gujewa maganar aure,Mamie ta rufe maganar tana bayyana masa tsantsar damuwar da suke ciki akan ƙin yin auren Ammar Chiroma domin ita ta fara zargin kodai bashi da lafiya ne da sam baya jin feeling bare yayi tunanin aje Iyali.Shehin Mallamin ya tabbatar ma Mamie da cewa Ammar Chiroma lafiyarsa lau bashi tare da kowace irin matsala,sannan baya aikata fasiƙanci domin ya jima baiga matashin dake tashen samun kuɗi amma baya fallasar dasu wajen bibiyan ƴan mata ko saka kansa a harkar shaye-shayen zamani ba sai Ammar Chiroma.Ya sanar da Mamie cewa su godewa Allah domin Allah ya kintsa shi wanda ikonsa ne ba dabararsu bane,sannan ya kwantar mata da hankali wajen fahimtar da ita cewa shi aure addu'a ake dagewa dashi wajen neman zaɓin Allah bawai ta matsa cewa lallai sai ya auri zaɓinta ba,amma duk da hakan yayi mata alƙawarin cewa zai nunawa Ammar ɗin muhimmanci amsar zaɓin Iyaye da kuma yi musu biyayya akan duk abinda suka nuna suna so matuƙar bai saɓawa addini da shari'a ba.Mamie tayi masa godiya sosai tana sake jin ƙaunar Malamin sosai a cikin zuciyarta,har bakin kofar fita falon tayi masa rakiya tana sake zuba masa godiya.Ammar wanda tun fitowarsa suke waya da Khairiyyah sai yayi saurin tahowa domin ya hango fitowar Mallamin nasa,kashe wayar yayi bayan ya sanar da Khairiyyah cewa zai kirata zuwa anjima kafin ya kwanta su ƙarisa maganar da suka faro wanda akan zuwan da Mamien tayi da Labibah ce domin ita kanta Khairy bata ji daɗin hakan ba.Mamie ce ta sake yima Mallamin godiya kafin ta koma ciki su kuma suka isa can wajen Rumfar da Ammar ɗin ya taso,magana sukai na tsayin mintuna talatin Shehin Malamin na yiwa Ammar Chiroma nasiha akan cewa kada ya bijirewa zaɓin Mahaifiyarsa matuƙar yana neman albarka kuma bashi da zaɓin da zai gabatar mata na wacce shi yake so.Ya kawo masa misalai da dama akan fa'idar yiwa Iyaye biyayya musamman akan abinda ya shafi harkar aure,tabbas bazai taɓe ba matuƙar ya amshi zaɓin da kyakykyawar niyya.Ya rufe nasiharsa da bashi shawarar cewa ya baiwa Mahaifiyarsa haƙuri ya kuma sanar da ita cewa ya amshi zaɓinta,daga nan sai ya dage da addu'a yana neman zaɓin Allah shima zai taya shi.Tabbas idan har babu alkhairi cikin lamarin Allah bazai kunyatasu ba zai kawo sanadin da ita da Kanta Mamien za ta janye ƙudirinta,sosai Ammar Chiroma yaji jikinsa yayi sanyi ya kuma gamsu da dukkanin bayanan Mallam ɗin.Yayi masa godiya mai tarin yawa tare da bashi tabbacin cewa zaiyi amfani da shawarinsa,sukai sallama da juna Ammar ya taka masa har bakin ƙofar fita daga gidansa.Time ɗin daya juyo domin komawa ciki ji yayi ilahirin zuciya da gangar jikinsa na sake mutuwa,wani irin yanayi yake ji na dabaibaye zuciyarsa irin wanda bazai taɓa iya misaltawa ba......✍🏻