9
by @nanadiso10
ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TARA
Da zarar As'ad Babangida ya iso fadar mai martaba, sai aka fara masa kirari kamar yadda aka saba a gidan sarauta
A hankali ya shiga cikin gidan sarautar, yana kallon ko'ina da idanuwansa. Yau shekara ɗaya da rabi kenan rabon da ya taka wannan gida. Gidan da ya tsana fiye da komai da ba don iyayensa na ciki ba, da ko kusa ba zai sake taka shi ba.
Tun da ya kammala karatu, As'ad ya yanke shawarar komawa birnin tarayya, gidan mahaifinsa. Hajja, matar sarki ta biyu, tana zama a can tare da 'ya'yanta guda biyar Mamy Shamsiyya (ta farko), As'ad, Kanwarsa Zaitu (wacce ke zaune a London), Abba, da Fiddausi (ƙarama kuma fitinanniya). Sauran yaran kuwa na sauran matan sarki ne.
As'ad ya kasance mutum mai ra'ayin kansa wanda baya sha'awar rayuwar sarauta, shiyasa ya fi zama nesa da gidan mai martaba.
Tunda As'ad ya iso harabar fadar mai martaba, ake masa kirari da girmamawa, ana aika masa gaisuwa daga kowanne bangare. Mai sanarwa na fada ya ɗaga murya cikin izza "Gaisuwa ta musamman ga ɗan gidan sarauta, As'ad Babangida! Ɗa na biyu ga mai martaba, jikan sarki, hamshakin mai arziki da ƙasar ke alfahari da shi! Allah ya ƙara girma da ɗaukaka!"
Fadawa suka gyara zane suna kallon yadda As'ad ke takawa cikin natsuwa da girmamawa, ya na kara kusa da zauren sarki. Cikin fadar kuwa, an riga an sanar da mai martaba cewa As'ad ya iso. Sarki ya ɗaga hannu cikin jin daɗi, yana murmushi irin na mai alfarma.
A hankali, As'ad ya shiga cikin zauren fada. Ya tsaya ya sunkuyar da kai cikin ladabi, sannan ya yi gaisuwar sarauta
"Ranka ya daɗe, Allah ya ja zamanin sarki."
Sarki ya amsa da murmushi mai cike da kulawa
"As'ad, maraba da kai. Allah ya ƙara maka nasara da albarka."
As'ad ya samu wuri ya zauna a gefen sarki cikin natsuwa, yana kallon fadawa da 'yan uwa na gidan sarauta. Yana lura da yadda gidan ya sake samun kwarjini fiye da yadda ya barshi. Shekara ɗaya da rabi kenan bai taka fadar ba. Shi kam ba don mahaifinsa da mahaifiyarsa Hajja suna nan ba, da bai kara zuwa ba.
Sarki ya yi gyaran murya, ya kalli As'ad da kulawa, sannan ya ce
"As'ad, ɗana mai albarka. Yanzu haka ne? Sai ni na je inda kake saboda wata dabi'a ta ƙin sarauta? Ko in mutu ma baka da ikon zuwa ka ga iyayenka da yan uwanka? Kuɗi ba komai ba ne, As'ad. Ina gaya maka, duk arzikin da kake tunanin ka tara, a nan gidan sarauta ne tushen komai."
Ya ɗan numfasa kafin ya ci gaba da magana cikin natsuwa
"Kai fa ɗan gidan sarauta ne. Meye na gujewa gidan sarauta? Ban ce kada ka je Abuja ba, amma fa dole ka rike martabar gidan nan. Na aura maka mace sau uku, duk ka sake su. Me yasa baka son ƙara aure ne? Ka duba ‘yan uwanka, dukkansu suna da gida, suna da zuri'a sama da ɗaya. Wannan magana da nake maka ba shawara ba ce, umarni ne. Ƴar gidan Fulani, Maryam, itace nake so ka je ka gani. Wannan magana ta gama karewa."
As'ad ya sunkuyar da kansa cikin jin nauyi, sannan ya ce cikin ladabi
"To ranka ya daɗe, za a yi yadda kake so."
Sarki ya yi murmushi cikin farin ciki, yana jin daɗin yadda As'ad ya amsa. Ya ɗaga hannunsa yana addu'ar samun albarka a kan ɗansa.
"Allah ya sanya alkhairi. Ka je ka shirya, za a kawo Maryam nan fada gobe, domin ka ganta da idanunka."
Cikin girmamawa, As'ad ya durƙusa gaban mai martaba sannan ya ce da ladabi
"Allah ya taimake, a yi haƙuri, zanje inshaa Allahu."
Wannan ɗabi'ar tasa ce ta ladabi da girmamawa bai taɓa yin gardama ko musanta umarnin mai martaba ba, duk da rashin sha'awarsa ga rayuwar sarauta. Har lokacin da ya auri Ayshatu ma, shi ne ya bashi izini, kuma ya amince. Haka kuma sauran matan da ya aura duk da shi ne ya nemi izini kuma aka amince masa.
Cike da farin ciki, mai martaba ya amsa da murmushi mai cike da annuri
"Allah ya yi maka albarka, na baka izinin tafiya."
Da girmamawa As'ad ya miƙe, ya fice daga fadar mai martaba yana yi wa sarki addu'ar albarka da tsawon rai. Cikin zuciyarsa, yana jin daɗin yadda aka yi komai cikin sauƙi da girmamawa, duk da yana matuƙar guje wa irin waɗannan taruka na gidan sarauta.
As'ad na shiga bangaren mahaifiyarsa, wanda yake da kyau da tsari irin na gidan sarauta, sai ya tarar da kaninsa Abba yana cin abinci. Da ganin shi, Abba ya ajiye kwanon abincin ya miƙe tsaye, yana durƙusawa cikin girmamawa:
"Yaya barka da zuwa."
As'ad ya amsa da fara'a, yana ɗagowa da shi tare da ɗan runguma. Yana tambayar lafiyar gida da aiki. Abba ya amsa cikin ladabi, sannan suka zauna cikin tsari irin na gidan sarauta.
Bayan sun ɗan yi hira, Abba ya fara magana cikin natsuwa
"Yaya, da zaka yarda na nufi gidan Fiddausi, wallahi wannan fitsarar nata ta yi yawa. Anty Aysha ma ta kira ni, ta ba ni labarin yadda abin ya faru."
As'ad ya ɗan murmusa, yana jin mamakin yadda Aysha ta kira Abba
"Ka kwantar da hankalinka, Abba. Na riga na yi maganinta."
Kafin su cigaba da magana, Hajja ta sauko daga bene cikin hanzari, tana dubansu da fuskar rashin jin daɗi
"Abba! As'ad! Kuna tattauna Fiddausi kamar ba ku san darajar 'yar uwarku ba? Kun ga ai sai ku haɗu ku yi mana duka tare, ko? Abba, ka kiyaye ni akan Fiddausi. Ni na haife ku, ba ku kuka haife ni ba! Kun damarmun yarinya da maganganunku!"
Ta ɗan ja numfashi, sannan ta cigaba da fada cikin takaici
"Yanzu har Fiddausi zata je gidan As'ad sai matarsa ta ba da izini kafin ta ga ɗan uwanta? Yaushe kuka fara ba wa matanku wannan ƙarfi fiye da 'yan uwanku da kuke ciki ɗaya?"
Abba ya sunkuyar da kai cikin kunya, yana sauraron mamarsu. As'ad kuwa ya yi shiru, yana kallon yadda Hajja ke nuna damuwarta da ƙarfi
Cikin zafin rai, Hajja ta yi magana cikin ƙarfin murya
"Wallahi bazan taɓa yarda da wannan ba! Ayshatu ba ta da wannan ikon! Na gaya muku, dukanku!"
Cikin girmamawa, As'ad ya tsugunna har ƙasa ya gaisheta
"Hajja,Za'a kiyayye inshaa Allahu. ?"
Ta amsa tana tambayar yadda su Nawal suke.
"Alhamdulillah, suna Dubai, Hajja. Ta yi musu fatan dawowa lafiya."
Hajja ta yi gyaran murya, tana magana cikin nuna damuwa
"Maganar Fiddausi nake so mu yi. Daman taje kun ci mata mutunci kai da matarka. Duk lokacin da yarinya ta fara kuka game da mijinta, yakamata ku saurareta. Kuna ganin kamar Fiddausi ba ta da kunya, amma ai mace mai rauni ce. Kun san mahaifinku da girmama al'adar gida. Ni kuma bazan zuba ido rayuwar 'yata ta lalace ba. Kun sha gayamata mijinta yana biya mata buƙata, amma kullum cikin rashin kunya da fitsara take. To tayaya zata girmama namiji mara kuzari agado? Bata faɗa mini ba, sai yanzu da take cewa har magani aka nema babu ci gaba. Kuma duk kwayar da ya sha, ba tashi yake yi ba, sai jiri da kwanciya har asuba! Yaya aure zai yiwu haka?"
As'ad ya sunkuyar da kansa cikin ladabi
"Hajja, ki yi haƙuri, Fiddausi ce dai. Mun yi magana da mijinta, ba haka ya sanar da ni ba, shi ya sa na yanke hukunci. Amma duk yadda mai martaba ya faɗa, haka za mu yi. Allah ya zaɓa musu abin da yafi alkhairi."
Hajja tace
"Munif yana son Fiddausi sosai, bana tunanin zai iya sanar da kai matsalar. Amma ku tsaya mata! Ni shekaruna sun ja, ku zaku tsaya kamar iyayenta."
Abba yace
"Inshaa Allahu, Hajja, za mu gyara."
Hajja ta yi ɗan nishi kadan
"Maganar diyar Maryama fa? Ka amince?"
As'ad ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce
"Zabinku shine alkhairi, kamar yadda mahaifina ya umurce ni. Inshaa Allahu, da daddare zan je na ganta."
Sai Hajja ta ɗaga murya cikin takaici
"As'ad! Wannan biyayyar taka tana cutar da kai! Yanzu Haneefa zaka aura? Yarinyar da kowa yasan rashin tarbiyanta, kuma kasan mahaifiyarta makiyata ce! Wallahi tun da mahaifinka ya gaya min sai na ji bata kwanta mun ba! Ina roƙonka ka canja wannan shawarar."
Har sai da Abba ya sa baki
"Dan Allah, yaya, kada ka aureta. Haneefa fa? Haba yaya, auren nan da manufa!"
Hajja ta kara nuna damuwarta
"Biyayyarka ta yi yawa, As'ad. Yarinyar da aurenta fiye da biyar, duk ta kasa riƙe ɗaya. Na ƙarshe ma, sata tayi masa ya rabu da ita. Dan Allah, ka kiyaye."
As'ad ya girgiza kai cikin ladabi
"Hajja, ki yi mun addu'a. Bazan iya tsallake umarninsa ba."
"To Allah ya duba mu, ya yi muku albarka."
Bayan ya fita, Abba ya kalli Hajja cikin mamaki
"Hajja, anya ba asiri aka yi wa yaya ba? Wannan biyayya fa ta yi yawa!"
Hajja ta yi dariya
"Abba, mahaifinku ne yayi masa amma dai."
Abba ya ɗan nuna damuwa
"A'a Hajja, kar ki sani, dan Allah."
Ta yi shiru na ɗan lokaci tana nazari. Abba kuwa ya kalle ta yana mai nuna damuwa
"Hajja, wallahi abin da yaya yake yi yana bani mamaki. Wannan biyayyar kamar ba ta al'ada bace. Ko dai akwai wani abu a ƙasa ne?"
Hajja ta ja numfashi, ta dube shi da ido cikin natsuwa
"Abba, mahaifinku ne ya yi masa wannan Tun yana ƙarami, ya horar da shi da biyayya da ladabi. Babu wani sihiri ko asiri a cikin wannan lamari. Amma gaskiya ni kaina ina tsoron irin wannan biyayyar, musamman yadda yake tafiya akan batun Haneefa."
Abba ya girgiza kai cikin takaici
"Hajja, idan aka ce mutum ya yi biyayya, ai yana da hankali. Amma wannan kamar an mamaye tunanin sa ne. Haneefa fa? Duk gidan sarauta sun san halinta. Ina roƙon Allah kada wannan aure ya zama matsala."
Hajja ta ɗan yi dariya mai raɗaɗi
"Abba, mahaifinku ya yi imani da soyayyar danginsa da haɗin kai.
******
A cikin falon Maryama, Haneefa na zaune tana daddanna waya yayin da mahaifiyarta ta fito daga ɗaki tana kallonta da wani irin yanayi na tsananin takaici. Ta daka mata tsawa
"Dan ubanki! Haneefa, haka zaki fita da wannan shigar? Nayi miki dinki gashi can, show me your body! Ki saka shi ki cika. Ki yi dam! Ki ɗakko brazier guda uku ki haɗa. Wannan wandon da na siyo miki na cikon hips ki saka, ki ɗauki jan jambakinki ki sa. Wannan kwalliyar da na karɓo miki daga wancan mai gyaran fuska, ki yi amfani da ita. Kuma idan kina magana, kina narkewa, nagaya miki!"
Ta ja numfashi tana gyara gyalen da ke kafadarta
"Matarsa fa yar gayu ce sosai, kuma kyakkyawa ce duk da baƙaramin jiki gareta ba. Da kadan zata girmeki, amma fa dirine da ita! Kina jin ni kuwa? Ki tashi kiyi maza! Yanzu zakiga As'ad."
Haneefa ta gyara zaman rigar da ta saka, tana murmushi mai ɗauke da son zuciya.
"To Fulany," ta fada tana barin falon cikin jin daɗi. Zuciyarta fes, tana tunanin yadda zata burge As'ad. Tuni tunaninta ya tafi ga yadda zata sa shi ya kafe mata ido, yana ganin ita ce mace ta daban da babu kamarta.
Ta dauki wandon da aka kawo mata, ta saka brazier guda uku kamar yadda aka umurta, sannan ta yi make-up mai tsauri, tana mai danna jan jambaki sosai. Ta kalli kanta a madubi, ta gyara gashinta da wani irin salo na matan zamani.
"Yau fa sai As'ad ya san ni ce matar da ta dace da shi," ta fada a hankali tana murmushi mai dauke da kulle-kullen cin nasara.
A cikin zuciyarta, ta yi alkawarin cewa komai zai yiwu domin ta samu matsayin matar As'ad, ko da kuwa ta nemi taimakon Fulany don ganin burinta ya cika. Duk da cewa zuciyarta ta san cewa As'ad mutum ne mai tsari da kamala, hakan ba zai hana ta amfani da duk wani salo don ja hankalinsa ba.
Ta ɗauki wayarta, ta danna kira
"Mama, na shirya! Yanzu zan fito."
Fulany ta yi murmushi daga nesa tana jin sautin muryar 'yarta
"To haka nake so! Yi hakan da kyau ki ga yadda zai zuba miki ido."
Maryama ta fito daga ɗakinta tana tafiya da sauri zuwa falon inda ta tarar da Haneefa tana kammala kwalliya. Ta daka mata tsawa da murya mai ƙarfi
"Au Haneefa! Maza zo nan! Sarki ya sanar da cewa yana gidan yanzu, yana jiranki. Ga direba can, ki hanzarta ki tafi!"
Ta gabatar da wata ƙaramar kwalba na turare mai ƙamshi mai ƙarfi
"Karɓi wannan turaren. Gab da zaki shiga gidan sarauta, ki gogashi a wuyanki da kunnuwanki. Wannan garin kuma ki watsa shi a kafar hagu. Wannan abu sirri ne, na tabbatar da cewa zai ja hankalin As'ad."
Ta tsayar da Haneefa ta kalli ta cikin ido
"Haneefa, komai rintsi, kada ki soma magana da kowa sai As'ad. Koda suna gaishe ki, ki yi kamar ba ki ji ba. Kin ji ni? Kada ki ɓatamun aiki!"
Haneefa ta gyara tsayuwarta, tana gyada kai
"Na ji mama. Zan yi yadda kika ce."
Maryama ta yi ɗan murmushi mai ɗauke da nasara
"Kin ga yan uwanki suna kokari, amma ke kadai na yarda da ke. Ki kula sosai, kada ki yi wani abu da zai bata mana suna. IAs'ad yana da rauni akan mace mai kyau da nutsuwa. Ki nuna masa cewa ke ce zaɓin da ya dace."
Nana hadiza
***