ƳAR KARUWA Chapter 20
Arewabook@ayshadansabo
Paid book
***
©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
Chapter 20
Idanun Ammar Chiroma a lumshe suke maganar da Mamien tayi kuma baisa ya buɗe idanun ba illa ma sake lumshesu da yayi,baya son ganin kowa a gabansa a halin da yake ciki a yanzu.Sai dai yafi kawo sanin Mamie ba za ta taɓa barinsa ba har sai ya sanar da ita damuwarsa,cikin wani irin low voice yace,"Mamie head ɗina." Mamie ta sauke numfashi tace,"But Ammar yaushe ka fara irin wannan ciwon kan mai galabaitarwa haka? Sanar dani inda kake aje magunguna na ɗakko maka na ciwon kan please." Da hannu yayi mata nuni da side drawer ɗin bed ɗinsa.Mamie ta miƙe ta isa bakin side drawer ɗin ta buɗe,magunguna ne a ciki burjik irinsu tsadaddun paracetamol da duk wasu emergency drugs daya dace mutum ya riƙa ajewa a gida sabida tsaro da kuma dare. Sachet ɗin paracetamol ta ɗakko ta rufe drawer ɗin ta nufi saman dressing mirrow ɗin data hango goran table water ta ɗakko,zama tayi daga bakin bed ɗin bayan ta aje goran ruwan a jikinta.Hannu ta miƙa ta riƙo na Ammar Chiroma wanda idanunsa ke a rufe har lokacin,cikin kulawa tace,"Tashi kasha maganin kafin na haɗa maka tea ɗin tunda ga komi can Labibah ta haɗo ruwan zafin kawai za a zuba." Bai musa ba ya tashi zaune tare da buɗe manyan idanunsa da ciwon kai yasa suka shige ciki ya sauke akan Mamie, itama nata idanun a kansa suke hakan yasa hankalinta sake tashi sakamakon ganin yadda idanunsa sukai jajir.Maganin ta ɓalla ta bashi tare da kafa masa goran ruwan a baki,amsa yayi ya kurɓi ruwan tare da afa maganin ya maida idanunsa ya lumshe.Cikin zuzzufar muryarsa ya furta,"Mamie please ki daina turota tana shigo min ɗaki,baki ga irin shigar dake jikinta bane Mamie?Hakan bai dace ba don Allah Mamie ta daina shigo min ɗaki." Mamie ta dubesa tare da jinjina kanta tace,"Ashe dai lafiyarka ƙalau tunda kana jin feeling,aina ɗauka baka da lafiya shiyasa kake gujema zancen aure,karka damu ba za ta sake shigo maka ɗaki da kayan bacci a jikinta ba,yanzu dai bari na haɗa maka tea ɗin kasha." Ammar ya buɗe Idanunsa da ƙyar ya zubesu akan Mamie kafin ya girgiza kansa yace,"Mamie bazan sha komi ba am okey please." Mamie sai ta koma ta gyara zamanta daga bakin bed ɗin idanunta na sauka akan ƙaramin frame ɗin dake ɗauke da zanen halittar dake jigatar da zuciyar Ammar Chiroma,da wani irin sauri ta miƙe ta ɗakko frame ɗin tana kafe zanen da ido amma ta kasa tantance ko fuskar wace ce ya zana.Dubansa tayi taga yadda ya ɗauke kansa tare da komawa ya kwanta,ta buɗe baki cikin kaushin murya tace,"Ammar wannan zanen wace fuska ce wannan? Dama soyayya kake da wata? Ƴar gidan uban wace ce daka kasa bayyana mana ita kake kauce ma maganar aure sabida ita?" Ammar da kansa ke sake masa ciwo sakamakon ɗaga muryar da Mamie keyi a kansa sai yayi gaggawar buɗe idanunsa dake sake birkicewa da wani yanayi mai zafi yace,"Mamie ta mutu,just pray for me Allah ya bani dangana." Yadda yayi maganar cikin wani irin karyayyen sauti ba ƙaramin dukan zuciyar Mamie yayi ba,ta dubesa da sauri tausayinsa na lulluɓe zuciyarta.Da wani irin murya mai cike da rarrashi da nuna tsantsar kulawa tace,"Allah sarki Ammar dama a dalilin hakan kake gujema zancen aure? A ina kuka haɗu kuma yaushe ta rasun?" Ammar da ko kaɗan baiso maganar tayi tsayi sai yace a gajarce,"Five years kenan Mamie,ƴar Nigeria ce hakan shine dalilin da yasa zuwa 9ja ya fita a kaina."Mamie cike da tsantsar mamaki ta sake cewa,"But meyasa baka taɓa bayyanawa kowa hakan ba?" A gajiye Ammar Chiroma yace,"I don't know Mamie,but abinda na sani shine bazan taɓa son wata ƙwayar halitta sama da yadda nake son Angel ba Mamie,I luv her so very much ta yadda har bansan yadda zan iya misaltawa ba,kamarta nake fata Allah ya haɗani da ita shiyasa na kasa duban kowace mace da sunan soyayya." Duk wannan maganar Ammar yayi ne cikin wani irin sanyin muryar fuskarsa na haskawa da tsantsar damuwar da Mamie bata taɓa gani ba.Takai hannu ta riƙo nasa tana murzawa a hankali,cikin rarrashi tace,"Za ka so wata Ammar,tabbas za ka so Labibah ka kuma ƙaunaceta domin itama mace ce har mace,kayi haƙuri ka fidda wannan ɗin daga cikin zuciyarka tunda bata a raye Ammar,please ka taimakeni ka maye gurbinta da Labibah ka ji Ammarun Mamie?" Mamie ta ƙare maganar cike da magiya tana sake murza yatsun Ammar Chiroma wanda ke ji tamkar wani fami Mamie take yiwa zuciyarsa mai zafin gaske.Baisan mai zai sake cewa Mamie ta fahimci yadda irin ƙarfin soyayyar da yake wa zanen halittar dake aje a jikinta ba,hakan ya sanya ya zame hannunsa tare da komawa ya kwanta ya sake maida idanunsa ya lumshesu yana fata Mamie ta barshi haka karta sake cewa komi.Kamar ko ta karanci zuciyarsa sai bata sake cewa komi ɗin ba illa ɗaga frame ɗin data yi daga jikinta ta kafe zanen da ido,duk iya yadda taso ta fahimci ko zanen wace ce kasawa tayi,domin wani irin zane ne yayi a disashe amma kuma yana ɗaukar idanu alamun dama can haka ake da buƙatar zanen ya fita bawai don ba a ƙware bane wajen yinsa.Maida frame ɗin tayi ta aje tana jin tausayin tilon ɗan nata na ratsa zuciyarta,bata taɓa kawowa zuciyarta cewa Ammar ya taɓa son wata mace bane da har ƙarfin soyayyar da yake mata zai hanashi kula wasu matan alhali yace ƙasama ya rufe idanunta.Zuciyarta ne ta kira sunan Kabeer Chiroma da ƙarfin gaske,take tarihin soyayyarsa da Nuratu da irin zazzafar ƙaunar da ya gwada mata suka haska a cikin kwanyarta."Meyasa Ammar Chiroma yayi gadon abubuwa da yawa na ƙanin Mahaifinsa?" Ta tambayi kanta tana jin zuciyarta na amsawa da wani irin zazzafar yanayi domin kuwa bata so ta tuna baya ko ƙanƙani.A hankali ta miƙe tare da matsawa wajen da Ammar Chiroma ya aje kansa ta duƙa ta sumbaci kyakykyawar fuskarsa da idanunsa ke lumshe har lokacin,cikin wani irin soft voice ta furta,"Ammar Allah zai yaye maka soyayyar matacciya ya maye gurbinta da rayayyiyar dake ƙaunarka In Sha Allah,Allah ya baka lafiya ni zan tafi na kwanta kuma indai shigowar Labibah ɗakinka ne baka so ba za ta sake ba."Tana kaiwa ƙarshen kalaman ta juya ta fito daga ɗakin tana jin zuciyarta na sake cika da tausayinsa,domin sai a yanzu da ta gano cewa ciwon rashin da yayi na abar ƙaunarsa da yace bata a raye zafin dafinsa ne ya hanashi sake kula kowace mace da sunan soyayya.Idan har hakan ne ya zama dole ayi gaggawar ɗaura masa aure da Labibah,domin ta hakan ne kawai zaifi saurin warkewa daga wancan ciwon ya amshi Labibah har ma ya sanyata a cikin zuciyarsa.Da wannan tunanin Mamie ta ƙarisa zuwa room ɗinsu,tana shiga ta tadda Labibah tayi ɗai-ɗai a saman bed suna yin vedio call da wani saurayinta Sadeeq.Sosai ran Mamie ya ɓaci domin karo na biyu kenan data kamata tana waya da Samari alhali kuma ta nuna cewa Ammar shine ta zaɓa ya zama abokin rayuwarta,cike da ɓacin rai Mamie ta wuce zuwa toilet domin wanko bakinta ta fito.Koda ta fito Labibah bata gama wayar ba,hakan ya sanya Mamie nufan wajen makunnin fitullun ɗakin ta kashe duka ta bar guda kaɗai mai duhun haske.Take Labibah ta shiga cikin ɓacin rai domin a ganinta ƙarshen wulaƙanci ne Mamie tayi mata,hakan yasa ta yanke vedio call ɗin ta dubi Mamie data hawo saman bed ɗin domin kwanciya tace,"Mamie meyasa kika kashe fitullun vedio call fa nake amsawa kuma kinsan yafi daɗi kayi cikin haske Mamie." Cike da ɓacin rai Mamie tace,"Sabida banga amfanin ga wanda kike so da aure amma ki cigaba da biyewa sakarkaru ba,Ammar ya amince ya amsheki a matsayin zaɓin dana yi masa don haka idan har kika cigaba da kula wasu samarin har ya gano hakan tabbas za a sama damuwa Labibah don haka ki nutsu kisan yadda za ki jawo hankalinsa ki fitar da soyayyar wacce tayi karan tsaye a cikin zuciyarsa bawai ki dinga biyewa shashashun da ba aurenki suke da niyyar yi ba." Da tsananin mamaki Labibah ta dubi Mamie cikin ƙaramin hasken daya haska face ɗin Mamien tace,"Mamie me kike nufi? Kina nufin dama Ammar wata yake so shiyasa yake ta yarfani haka?" Mamie ta kwashe yadda suka yi da Ammar Chiroma ta sanar da Labibah,ta ƙare maganar da faɗin,"Yaƙi faɗi mini ƴar wace ce a Nigeria kuma a ina ma suka haɗu,hoton fuskarta nanan ya zana ya kafe a saman side drawer ɗinsa Labibah,tabbas ba ƙaramin so yayi mata ba amma abin yazo da sauƙi tunda ta riga da tabar duniyar baki ɗaya don haka cire ragowar soyayyarta a cikin zuciyarsa abu ne mai sauƙi matuƙar za ki kwantar dakai ki zama mace mai nutsuwa da kamewa koda a gaban idanunsa kaɗai ne." Labibah cike da gamsuwa ta jinjina kanta tace,"An gama Mamie,zanyi iya yina har saina cire soyayyarta a cikin zuciyarsa." Suka cigaba da tattaunawa akan batun Mamien na sanar da ita hanyoyin da za ta bi domin ta samu gurbi a cikin zuciyar Ammar Chiroma.
A ɓangaren Ammar kuwa Mamie na fita daga cikin ɗakin ya yunƙura ya tashi zaune,cikin cije baki ya sakko daga bed ɗin ya nufi ƙofar ɗakinsa ya murza key.Toilet ya nufa direct ya wanko bakinsa tare da ɗaura alwala ya fito,shafa'i da wuturi da baiyi ba ya gabatar.Koda ya idar hannu ya ɗaga yayi addu'a sosai,ya shafa addu'ar tare da miƙewa tsaye yana jin ciwon kan bai sakesa ba.Bisa bed ɗin ya koma bayan ya kashe wutan ɗakin sai bed side lamp kaɗai daya kunna,wayarsa ya ɗauka ya kalli time daya buga ƙarfe sha ɗaya har da mintuna talatin na dare agogon can.Ɓangaren contact ɗinsa ya buɗe ya lalubo lambar wayar da koda wasa bai taɓa yunƙurin kira ba tsayin shekaru biyar da yayi saving ɗinsa a cikin wayarsa,zuwa yanzu ma bashi da tabbacin cewa tana amfani da line ɗin ko bata yi.Ya zuba ma lambobin idanu kai kace ƙidayensu yake,cikin wani irin zazzafar yanayi ya aje wayar tare da miƙa hannu ya ɗakko zanen da baya gajiya da rungumarsa duk dare.Sosai ya zuba ma zanen idanunsa ilahirin zuciya da gangar jikinsa na sake amsawa da wani zazzafan yanayi," Mamie ta mutu ."Kalaman suka dawo masa tamkar a yanzu ya furtasu ga Mamien.Ya rumgume frame ɗin tsam a ƙirjinsa idanunsa na cika da ruwan hawayen da duk ƙarfin zuciyarsa baya hanasu zuba indai akan ƙaunarta ne,sosai yaji ƙirjinsa yayi nauyi tsananin damuwa da bege na sake lulluɓe zuciyarsa."Meyasa za kai mata ƙaryar ta mutu?"Wani sashi na zuciyarsa ya tuhumesa,sai ya lumshesu idanunsa zuciyarsa na sake tuhumarsa da cewa idan kuma Allah ya ɗauki ranta da gasken fa?Cikin sauri ya buɗe idanunsa da suka sake hargitsewa ya zubesu akan zanen fuskarta yana jin wani tashi hankali na sake mamaye zuciyarsa,"No please! Allah karka jarabeni da hakan." Ya furta can ƙasa-ƙasa yana sake manne hoton a saman ƙirjinsa.Kwanciya yayi sosai zuwa rigingine ya kai hannu ya dafe frame ɗin a saman ƙirjinsa,babu abinda ke sake ɗaga hankalinsa irin auren Labibah daya amince dashi alhali yana da tabbacin ba za ta taɓa samun soyayyarsa ba matuƙar wannan halittar dake azabtar da zuciyarsa na cigaba da existing a doron ƙasa.Ya shiga cikin mawuyacin yanayin da bazai misaltu ba a cikin wannan daren yana fata bacci ya ɗaukesa,hakan bai samu ba sai da taimakon sallar dare daya tashi yayi ya kuma yi karatun Qur'ani gabannin ya samu baccin ya ɗaukesa.
**********
KADUNA,NIGERIA.
2:35am
Jannat ce zaune a saman sallaya tana cigaba da zabga addu'a bayan ta idar da nafilfilinta data gabatar,ta ɗaga manyan idanunta ta kai dubanta saman bed ɗinsu inda Feenah ke kwance tana baccinta sadidan kasancewar tana period ne shiyasa bata tada ita ba.A hankali ta fara jin ciwon mara na mintsininta wanda tun jiya da rana ta fara jin alamunsa,hankalinta ne yayi mummunar tashi sabida irin wahalar da take sha duk idan za ta yi period.Karatun Qur'ani tayi sosai kafin ta miƙe a nutse ta kashe hasken bed side lamp data kunna,ta koma ta kwanta tana addu'ar Allah ya taƙaita Mata wahala a wannan karon.
*********
Ta kusa makara sallar asuba domin ta farka ne daga bacci taji ana sallame sallah a masallacin dake manne da jikin gidan Daddy,tayi saurin sauka daga bed ɗin bayan ta karanto addu'ar tashi daga bacci ta nufi toilet.Alwala ta ɗauro ta gabatar da sallar asuba,tana gama yin azkar ta koma ta kwanta tana mamakin yadda Feenah ko motsawa bata yi ba baccinta kawai take cike da nutsuwa.Wayarta dake gefen pillow ne ya bada sautin wani zuu alamun shigowar saƙo,sai ta miƙa hannu ta ɗakko wayar bacci na sake cika idanunta.Text message ne daga Shureim Bichi wanda duk safiyar duniya baya gajiya da turo mata sanyayan kalamai masu taushi da narkar da zuciya,ta buɗe saƙon ta karanta tare da taɓe baki.Aje wayar tayi ta koma ta kwanta zuciyarta na tuno mata da wayar da suka yi a daren jiya,irin kalaman da yake gaya mata na yadda zuciyarsa ta kamu da soyayyarta abin har mamaki yake bata.Sai dai ta kasa sakin jiki dashi ta bashi time ɗinta kamar yadda yake da buƙata,domin ko waya ya kira sai ta ga dama take picking call ɗin.Idan ma ta amsa ɗin bata iya cewa komi daga eh sai a'a ne kawai,hakan ba ƙaramin raunata zuciyar S.M Bichi yake ba domin shi da gaske yake ƙaunarta ya riga ya gama mamaye zuciyarsa bashi da burin da ya wuce ya mallaketa nan kurkusa.Sai ya kirata sau biyar a yini amma zai yi wahala ta ɗaga wayarsa sau biyu,bai taɓa bayyana mata damuwarsa ba domin lallaɓata yake ta ƙaunacesa don radin kanta bada tursasawa ba.Ta maida idanunta ta lumshe ba tare da tunanin maida masa reply ba,don hakan ma bai taɓa faruwa ba domin zuciyarta kullum na sanar da ita cewa ta gama soyayya tunda har ta rasa Aliyu Wase cikin rayuwarta.Kallon Feenah kawai take idan tana mata tsiyar cewa za ta kuma son wani namiji a rayuwarta kwatankwacin yadda taso Aliyu,tana ganin cewa har abada hakan ba zai faru ba domin shi ɗin a kansa ta fara ɗanɗana zaƙin soyayya,sannan a kansa tasan yadda ɗacin rabuwa da abinda kake so yake.Don haka bata jin cewa akwai wani ƙwayar halitta a cikin rijalu da za ta kuma so irin yadda taso Aliyu ta ƙaunacesa,shiyasa duk wani kalamai da rawar ƙafar da S.M Bichi ke gwada mata suka kasa yin tasiri a cikin zuciyarta.Ta amince ta cigaba da sauraransa ne albarkacin Abbah da Ummu wacce ta kirata ta bata shawarar cewa ta amshi Shureim ɗin a matsayin zaɓin Abbah da take da tabbacin cewa ba za ta taɓa yin danasanin hakan ba,sannan ta sanar da ita cewa ta manta da Aliyu Wase ta ɗauka cewa ƙaddara ce kawai ta haɗa zukatansu ba don su mallaki juna ba.
Jannat ta sauke ajiyar zuciya tare da muskutawa ta gyara kwanciyarta baccin da suka cika idanunta na rinjayarsu,bada jimawa ba baccin yayi awon gaba da ita.Bata farka ba sai misalin ƙarfe tara na safe,Allah yaso bata da class ɗin safe yau da tabbas sai tayi late kafin ta gama shiri har ta shiga skull ɗin.Toilet ta nufa kai tsaye domin yin wanka da brush,ta ɗauki dogon lokaci domin wankanta akwai daɗewa sabida yadda take ɓata lokaci wajen ƙalailaitar salle lafiyayyar fatarta.Tana fitowa daga toilet ɗin ɗaure da babban towel Feenah na shigowa cikin ɗakin,suka haɗa idanu tare da sakarwa juna murmushi Feenah ta riga faɗin,"Morning Mrs S.M Bichi an gama baccin an tashi kenan?Ai tun 8am dana tashi naso in tadaki sai na tuna kince yau sai 12 kuke da class." Jannat ta aikawa Feenah harara tace,"Besty bana son wannan sunan fa." Feenah tace cike da tsokana,"Aiko dole kiso tunda dai kin amincewa Abbah kin amshi zaɓinsa to ba time kawai za mu jira ba?" Jannat ta ɓata face zuciyarta na motsawa da wani yanayi,ta buɗe baki cike da shagwaɓa tace,"To ai saiki jira time ɗin yayi,yaushe za ki wuce skull ɗin yau?" Feenah ta dubi time tace,"Nan da one hour." Jannat ta jinjina kanta tace,"Ai ina ga tare za mu wuce saina zauna wajensu Aysha kafin time ɗin lacture ɗinmu yayi,Dr.Gumel garemu yau ɗin ji nake kamar ma na share kar na je sabida na fara jin ciwon mara Feenah." Feenah ta waro idanu waje tace,"Aiko ki gaggauta shan magani nifa har fargaba nake ji idan naji kince kin fara jin ciwon mara,kiyi maza kisha maganinnan na Islamic da Momy ta amso miki wancan karon dama yace da kin fara jin alamun zuwansa za ki fara sha." Jannat ta yamutsa fuska tace,"Zan sha Feenah ai ya zama dole ma nasha duk rashin daɗinsa hakanan zan daure,yanzu dai barni na shirya nayi breakfast tukunna." Tana gama faɗin hakan ta janyo lotion ɗinta daya dace da brown skin ɗinta mai haske ta fara murzawa,product ɗin ba ƙaramin amsarta yayi ba shiyasa duk tsadar set ɗin bata damuwa dashi ta sake sayensa tunda dai Allah ya riga ya hore abin sayen.Feenah da dama wayarta ta shigo ta ɗauka sai ta nufi saman sofa ta ɗauki wayar tana faɗin,"Sai kin fito Besty ni nayi nan." Daga haka ta fice daga ɗakin tabar Jannat na cigaba da shafa manta,koda ta kammala ta saka turaren jiki sai ta nufi wajen kayanta domin ɗakko rigar da za ta saka tayi shirin shiga skull ɗin gaba ɗaya..........✍🏻