13
by @nanadiso10
ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA UKU
Adaren nan Abba gaba ɗaya bai kwanta ba. Bakaramun hankalinsa tashi yayi ba, domin tunanin abin da ya faru yana ta faman yi masa yawo a zuciya. Bai taɓa tsammanin za ta aikata irin wannan abu ba. A zahiri, bai iya ganewa ba ko da mafarki ne ko gaske. Ya daɗe yana tunani kafin ya miƙe ya watsa ruwa, sannan ya koma kan dadduma ya ɗora sallah, yana neman nutsuwa da natsuwa a cikin zuciyarsa.
Mumy ce ta taso daga ɗaki, tana lura da yanayin Abba. Ta san cewa lallai wannan lamari ya dame shi sosai. Ta zauna kusa da shi, cikin tausayi da natsuwa ta fara magana, "Dan Allah Abba, kayi haƙuri. Ai bata taɓa aikata haka ba, wannan ne na farko. Kasani, yaran yanzu, ba za ka iya musu ba. Kawaye ne ke jan su da waɗannan abubuwa. Ka yafe mata, dan Allah."
Abba bai ce komai ba, kawai sai ya cigaba da addu'o'insa cikin natsuwa. Bayan ya gama, ya kalli Mumy da kyau, yana jin nauyin maganar da take yi. Zuciyarsa na bugawa, yana ji kamar zuciyarsa ta tsinke saboda takaici da kuma tunanin yadda tarbiyyar 'yarsa ta fara ɓaci.
Mumy ta sake cewa, "Dan Allah, Abba, kayi haƙuri. Ni kaina na yi mamaki, amma ka ba ta dama ta gyara kuskurenta. Ka san yaran yanzu, sukan yi kuskure amma kuma suna buƙatar shiriya."
Abba ya ɗan numfasa, ya na jin baƙin cikin abinda ya faru, amma kuma yana jin maganar Mumy tana yi masa tasiri. Sai dai zuciyarsa tana ƙunci. Yana tunani, "Ina nayi kuskure ne wajen tarbiyyarta? Me yasa ta aikata haka?"
**
Washegarin ranar, da safe, jikina har yanzu yana ciwo, musamman ma ciwon kai da ya tashi tun da asuba. Na san na yi laifi, shi yasa tun ƙarfe huɗu ban sake yin bacci ba. Na shiga gyaran gida duk da cewa kwayar da Fareed ya zubamun a lemo bata gama sakina ba, ga gajiya da ciwon jiki. Duk da haka, na tattara ƙarfin guiwa na gyara ko'ina, na wanke bandakuna, sannan na ɗora abin kari. Ganin ƙarfe shida na safe ya kusa, sai na nufi ɗakin yaa Billy don tambayarta abin da zan dafa mata.
A lokacin ne na ji dariyarta, tana kyalkyala cikin jin daɗi. Cikin mamaki, na tsaya na saurari maganar da take yi. "Oga, wai wace kwaya ce yarinyar nan tasha? Ka san ko daga hannunta bata yi ba. Ni fa ban taɓa shan irinsu ba, yau na sha wata sabuwa. Gaba ɗaya ta kasa ɗaukata, baccin ma ban yi ba."
Na ji zuciyata na tsinkewa. Na furta cikin tsoro, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un." Na dafa kirjina, ina tunani, "Kenan da gaske shaye-shaye take yi? Ko kuwa wani abu daban ne?" Amma ba wannan ne kawai ya fi tayar min da hankali ba, sai dai maganar da ta sake yi.
"Ai na gaya maka, wallahi sai na lalata rayuwar Ramlah. Soyayyar da mahaifina ya nuna kanta fiye da ni, sai ta zama masa ajalinsa. Ina so ka bani kwayar da zan dinga zuba mata cikin abin shanta. Lokaci kaɗan, shaye-shaye zai kama jikinta. Duk gidan nan, ni tafi yarda da ni. Nifa na fi kowa nuna mata kulawa. Kai dai kawai ka kawo. Ko Mumy bata isa ta nuna mata irin kaunar da nake nuna mata ba."
Gaba ɗaya jikina ya mutu, hawaye na zuba a fuskata. Na koma kitchen cikin sauri, na fashe da kuka. "Wannan wace irin ƙaddara ce? Yaya billy ce ke shirya wannan mugun nufin akaina? Na yi zaton itace mafi ƙauna a gare ni a gidan nan!"
Cikin wannan halin ne, Mumy ta shigo kitchen ɗin, ta ga ni ina goge hawaye. Ta ce cikin kulawa, "Yar albarka, har kin tashi? Na san ba halinki ba ne wannan. Kidaina damuwa da faɗan Abba, kinji? Ai inda kikaje ba wani abu ba ne. Haka yan gayu sukeyi. Kin san Abba bai waye ba. Ni da kin gaya min ai da sai na ce kije gidan Abbas ki kwana. Kema yakamata ki zama yar gayu ai."
Na rasa abin cewa, zuciyata na ƙara tsananin raɗaɗi. "Shin Mumy bata fahimci cewa da gaske Fatima tana nufin cutar da ni bane? Ko kuwa itama tana cikin wannan haɗin bakin?"
A cikin wannan tunanin, na san cewa ba zan iya dogara da kowa ba yanzu. Dole ne in nemi mafita kaina, kafin lamarin ya wuce gona da iri. "Amma ta yaya zan yi? Kuma wa zan nema ya taimakeni?"
Mumy ta gyara murya, tana dubana cikin yanayi na nuna kulawa.
"Kinga kawarki Fatima, tana son ki zama yar gayu. Bakya ganin yayarki ai? Macce sai da gayu. Mazan ma sun fi son yaran da idonsu suka buɗe."
Sai na ji wani irin karsashi ya shige ni, zuciyata tana raya cewa gaskiya Mumy ta faɗa. Tunda a makaranta ma haka suke cemin, wai ni marar wayewa ce. Na ji kamar idan na bi shawarar Fatima, zan zama kamar sauran 'yan mata. A hankali na ji kwarin gwiwa ya fara shigata.
Mumy kuwa, tana hawa sama sai ta faɗawa Abba, "Abban Ramlah, ni dai ina da shawara. Yarinyar nan kadaina bata kuɗin kashewa kwata-kwata. Ya zama na ƙanƙane mata, ta ji daɗin wahala, shi zai sa ta ƙara nutsuwa."
Abba ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan yace, "Ai tun da, daman ina tunanin haka."
Na je gaishe shi, bai amsa ba, duk da yadda na riƙa ba shi haƙuri. Na ji zuciyata ta tsinke, duk da haka sai da na fito muka tafi makaranta da Malam Idi.
A makaranta, na yi niyya ba zan kula Fatima ba kwata-kwata. Amma sai ga ta tazo tana bani haƙuri, abin mamaki kuwa sai na ji na yarda da ita. "Ai Mumy ta ce min Fatima masoyiyata ce, tana so in zama cikakkiyar yar gayu," na raya a zuciyata, duk da cewa na san halayyarta ba ta da kyau.
Yinin ranar, sai tiktok kawai take yi a wayarta. Lokacin da aka fita break, sai na fara jin cewa hakan ma yana da kyau, duk da farko ban kula ba. Sai da aka tashi sannan ta sake bani haƙuri, na kalleta cikin rashin gamsuwa nace
"Kinsan masifar da kika janyo min gida kuwa?"
Ta fashe da dariya, tana cewa, "Au, har yanzu ba a daina miki faɗa ba? Lallai!" Na tsaya ina kallonta da mamaki, sai ta ce
"Gobe idan na zo, zamuje gidan malami. A rufe bakin iyayenki baki, su daina ce miki komai akan duk abin da kike yi. Ki huta da wannan faɗan!"
Na ji kamar an tsikare ni, zuciyata ta tsinke da tsoro. Fatima ta shige mota ta bar makaranta, ni kuma na zauna a bakin hanya ina mamakin maganar da ta faɗa. "Gidan malami? Rufe bakin iyaye? Wannan wani irin shiri ne haka?"
*******
Kafin ya ce komai, Haneefa ta kai hannunta ta shafi sumar kansa da laushi. Wani irin raɗaɗi da nishadi suka haɗu suka mamaye shi. Jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya. Idanunsa suka fara lumshewa tamkar yana jin daɗin abin da take yi.
Ta sunkuya a kan kunnensa, tana saukar masa da numfashi mai dumi.
"As’ad... Na san ba ka saba da wannan ba."
Sai ya ji zuciyarsa na rauni, jikinsa na narkewa, tamkar wani abu yana tasiri cikin zuciyarsa.
Haneefa ta ɗora kanta a ƙirjinsa, tana wasa da wuyan rigarsa.
"Kada ka kore ni, ranka ya daɗe... Na jima ina mafarkin wannan daren."
Maimakon ya yi magana, sai kawai ya lumshe ido, numfashinsa na fita a hankali.
Haneefa ta lura cewa tasirin maganin ya fara aiki. Ta yi murmushi mai cike da nasara, sannan ta ɗaga fuskarsa a hankali.
"Ranka ya daɗe, ina son ka..." Ta furta a hankali, tana shafa gefen fuskarsa.
As’ad ya yi ƙoƙarin faɗar wani abu, amma muryarsa ta yi rauni sosai. "Haneefa... ki... ki barni..."
Sai ta ɗaura yatsunta a leɓensa. "Shiii... Kada ka ce komai. Ni zan kula da kai."
Ta dinga murza hannunta akan ƙirjinsa, tana shafawa cikin salo na bariki. Jikinsa ya fara rawar sanyi, idanunsa sun sauya daga tsayayyen mutum zuwa tamkar wani marar ikon tsayayya.
Ta ɗaura kansa a cinyarta, tana murza gashinsa, sannan ta rafka masa wata dariya mai kashe zuciya.
"Ka bar komai a hannuna, mijina."
Kafin ya ce komai, sai ta yi wani irin motsin birgewa, ta ɗora hannunta a gadon bayan wuyansa, tana murzawa cikin sanyi.
As’ad ya runtse ido, yana jin tamkar wani zararre. Kowane motsinta yana narkar da jikinsa.
Kowane motsin Haneefa na narkar da shi. Yana jin tamkar an daure masa tunani, duk wata tsayayyar zuciya ta gushe. Yana jin tamkar bawan da aka rufe a keji.
Ta yi murmushi mai cike da mugunta, sannan ta kai bakinta kusa da kunnensa.
"Zan kasance da kai duk daren nan. Ko da ace ka kore ni, ba zan tafi ba."
Ta kai hannunta ta ɗan murza gemunsa, sannan ta sunkuya tana raɗa a kunnensa.
"Kai ne jarumi na... Yau zan nuna maka banbancin matan gida da 'yan bariki."
Kafin ya ankara, sai ta dinga girgiza jikinta a hankali kamar mai raɗaɗin zumudi, tana kwantar da kanta a ƙirjinsa. Numfashinsa ya yi nauyi, yana jin tamkar zuciyarsa zata tarwatse.
As’ad ya kasa magana, yana jin zuciyarsa na kuna da sha’awa marar misaltuwa. Sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa na ƙoƙarin bijirewa, amma yana jin raunin da ya gagara tsayayya. A wannan lokacin, Haneefa ta rungume shi sosai, tana lallaɓa shi kamar jariri.
Bayan ɗan lokaci, ya yi ƙoƙarin janye jikinsa, amma ta sake manne masa. Sai kawai ya daina ƙoƙarin tsayayya, yana jin wani irin yanayi na murmurɗiyar zuciya.
"Ni naki ne... Haneefa..." Ya furta cikin rauni, tamkar wanda aka kwashewa tunani.
Haneefa ta yi murmushi mai cike da farin ciki, ta dora kanta a ƙirjinsa, tana jin cewa burinta na fara cika.
Nana hadiza
***