TURKEN GIDA.

Page 11

by @jamilaumarjanafty

TURKEN GIDA.

Wattpad:Jamilaumar315

Arewabooks:Jamilaumarjanafty

SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)

🅿️11

1994.

KATSINA. Ƙauyen Yashe dake ƙaramar Hukumar Kusada.

Hajiya Dubu na zaune a dandamalin ƙofar ɗakin ta, ta na ɓanɓaran masara. Masaran gonar Aminu ce an kawo ta gida yar sauran da ta rage ba ta bushe ba ne aka shanya bayan ta bushe shi ne take ɓanɓarewa.

  Daga ƙofar gida ta ji kamar hayaniya ba jimawa sai ga wani magidanci ya shigo riƙe da jaka a hannunsa bakinsa kamar gonar auduga saboda farin ciki.

"Hajiya Yaya Sule ne ya zo."

Haka ya faɗa. Itama sai ta washe baki lokaci ɗaya tana miƙewa kakkabe hannunta ta yi a jikin zanin jikinta kafin ta kalli yar yarinyar dake gefenta a zaune a rakuɓe wacce a shekaru iyakarta sha uku sannan ba za ta haura sha huɗu ba.

"Ke Asma'u kwashe mini masara ki kai cikin ɗakin can"

Haka ta faɗa kafin ta maida hankalinta ƙofar shigowa dai dai lokacin da aka yo sallama kamar wanda ya fara shigowa haka ya ke shima  sai dai a akwai bambamci shi daga ganin shigarsa za ka fahimci daga birni ya ke. Shadda ce mai duhuwa ya saka da takalminsa sahu ciki kansa da hula amman fuskarsa duk ta yi ƙura saboda kuran hanya tunda shekarun da yawa ba titina a lokacin kuma akuri kura ce za ka samu in ka sauka a bakin hanya ta shigo da kai cikin Ƙauyen.

"Maraba. Lale da zuwan Sule. Kai ne tafe."

Safiya ce domin lokacin ba zai gaza sha ɗaya da wani abu na safe ba. Kuma da karfi ta ke yi masa maraba da ya sa matan gidan da ƴa'ƴansu fitowa daga ɗakunan su. Har ƙasa ya duka ya na faɗin" Mun same ku lafiya Hajiya?

Da sauri ta ce"Haba dai. Tashi tashi maza Sule. Kai Sani shigar masa da jakarsa ciki ka yi masa shimfiɗa ka zauna anan ai sai ka ɓata jikinka"

  Sai da ya shiga ciki ƙaninsa Muhammad Sani ya yi masa shimfiɗa ya zauna sannan Hajiya Dubu ta shigo ita ma ta zauna a gefe suka gaisa. Sannan matar Sani ta shigo suka gaisa har yana karɓan yarinyar da ta ke goyo mardiya. Sannan yaran ma duk sun shigo sun gaishe shi ga su nan ɓutu ɓutu. Ba karatun boko suke yi ba saboda lokacin karatun bai yawaita har ƙauyuka ba sai dai  in namiji ne  a tura shi gona in mace ce kuma a yi musu aure masu rabo ne ma iyayensu kan tura su wani gari karatun allo.

  Matar Aminu ma ta zo ta gaishe shi kafin ka ce me an cika gabansa da ruwa da fura. Har da abinci ma tun da su ƙauye ba ruwansu da wani lokaci ko da yaushe ka zo suna da abinci sannan sun iya karrama baƙo. Baƙon ma irin Sule da ba ko yaushe ya ke zuwa ba sai in ya samu sarari. Yaran gidan sun zagaye shi sai da Hajiya ta fattatake su amma ba su tafi ba sai da ya buɗe jakarsa ya ɗauko alewan da ya siya musu na tsaraba ya ba ma Babban cikin su Nura ɗan wajen Sani ya ce ya je su raba sannan suka fita suna murna. Shima Sanin fitan ya yi ya ce zai gangara gona ya faɗa ma Yaya Aminu zuwan shi.

  "Ya wajen iyalan naka? Ina takwarata Dubu ina fatan duk kuna nan lafiya ko?

Hajiya Dubu ta faɗa tana gyara zama. Sai da ya kurɓi ruwa da cikin kwanon sha mai murfi da aka kawo masa sannan ya ce" Duk suna nan lafiya Hajiya. Rukayya da Maimuna duk suna gaishe ki. Takwaran ki kuma ta so ta biyo ni to sun fara zango karatun sakandiri na farko shi ya sa ban zo da ita ba. Sai dai ta yi jadadda mini saƙon gaisuwarta zuwa gare ki."

  Hajiya Duhu ta yi mirmishin farin ciki kafin ta ce" Duka ina amsawa. Allah sarki ashe takawara an sake zama ƴan makaranta. Ina jiranta in suka samu hutu."

"In sha Allahu."

Sun fara taɓa hira sama sama ta na faɗa mai gidan su Maimuna ma an yi rasuwa jiya ƙanin mahaifinta ya rasu sakamakon ba wayar hannu a lokacin sai dai a tada ɗan aike ya je ya faɗa. Daman tana shirin aika Sani ne sai kuma gashi ya zo.

"Allah Sarki. Allah ya jiƙansa. Daman tana ta zencen sa ashe jinya ba na tashi ba ne. Allah ya yi masa rahama."

Ta amsa da Amin Amin. Shi kuma ya ce zai je ya yi musu gaisuwa kafin ya tafi gobe in Allah ya kaimu.

"Gobe gobe nan za ka koma Sule?

Kai ya gyaɗa kafin ya ce"Saboda wajen aiki Hajiya. dama na ga kwana biyu ban leƙo ba shi ya sa na ce bari na zo na duba ku".

Ya faɗa lokaci ɗaya yana buɗe jakarsa ya fiddo da ledojin guda biyu duk ya tura gabanta ya na faɗin" Sabulai ne da sai siga Hajiya. A yi hakuri ba kamar yadda na saba zuwa ba ne. Tsakiyar wata ne ba a yi albashi ba."

Ta jawo ledojin gabanta ta na faɗin" An gode. Allah ya yi albarka Allah ya raya maka zuru'a. Allah ya ba ka masu jiƙan ka kamar yadda kake jin ƙanmu. Allah ya ba ka aljanna sanadin wannan zumuncin naka."

Yana ta amsa mata da Amin Amin cikin jin daɗi.

"Hasiya dai na can lafiya ko?

Hajiya Dubu ta gyara zama za  ta yi mgana kenan sai kawai ta ga inuwa daga saman kanta ta na ɗago kanta sai ta ga Asma'u tsaye ta na leƙen su. Shima Sulen sai ya kallo ƙofar ɗakin ya ga ana leƙe.

"Ke Asma'u zo nan.."

Sai ga ta ta shigo ta na laɓe laɓe hannunta  ta jawo ta zaunar da ita a gabanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ke kowa ya zo ya gaida babanku ke ba ki da hausan zuwa ki gaishe shi?

Sai ta kalle shi cikin yarinta kafin ta ce" Ina yini"

Cikin sanyin murya kamar za ta yi Sule ya yi mirmishi kafin ya ce"Ina kwana dai ko?

  Ya faɗa ya na kallonta. Hajiya Dubu ta taɓe baki kafin ta ce"Haka ta ke. Tunda Hasiyar ta kawo ta wajen wata ɗaya kenan ta kasa sakin jikinta. Ga yara ƴan'uwanta ta kasa sakin jiki a cikin su sai ƙulafacin uwa."

Sai ya kalli Hajiya Dubu kafin ya juya ya na kallon ƴar yarinyar cikin mamaki ya ce

" Ƴar waye wannan Hajiya?

"Yarinyar wajen Hasiya ce fa. Wacce ta haifa da marigayi Hashimu."

Cikin buɗe ido ya ce"Dama ba tana hannun dangin babanta ba ne?

Hajiya Dubu ta ce"Uhm' kafin ta cigaba da faɗin" To Hasiya da ƙulafaci mana. Wai can Asma'u ba sa'aninta ba ta jin daɗin zaman gidan. Bayan ta yi auren nan ta amso ta ta tafi da ita to ashe dai zama bai yi daɗi ba sai gashi ta dawo mini da ita wai ta zauna a hannuna."

"Me ya sa?.

Ya faɗa cikin mamaki Hajiya Dubu ta amsa shi da cewa" To ta dai ce min yaran mijinta na ta sun ƙi karɓan Asma'u sai megidan ya ce ta maida ta dangin ubanta. Su kuma kasan duk mata ne ƙannen Hashimu wata ma ƙanwarsa da yake can ƙauyen gaba damu ta so ɗaukan Asma'u Hasiya ta hana shi ne ta bar ta a wajena ni zan riƙeta in har Allah ya aramin rayuwar."

Sai ya jinjina kai kafin ya kira Asma'u da hannun alamun ta zo. Hajiya ta tura ta gabanshi. Riketa ya yi ya ɗora ta a saman cinyarta ya na faɗin" Me sunan ki?

"Asma'u."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce"Ma'u ce"  Sai ya ƙara kallonta kafin ya ce" Za ki bi ni can birni kano? Akwai abokan wasa kamar ki Rahilatu da Sadiya. "

Sai ta kalle shi kamar yadda Hajiya Dubu ke kallon shi sai Asma'u ta kalle shi kafin ta kalli Hajiya ita kuma sai ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba ruwana. Kawun ki ne in  za ki bishi shike nan nima na huta.".

Sai ta ɗaga masa kai alamun za ta bishi. Sai ya dawo da kallonsa kan Hajiya ya na faɗin" Hajiya zan ta fi da Asma'u na je na haɗa ta da su Sadiya na sakata a makaranta. Ba zan bari a kaita ƙauye a gurgurta mata rayuwa ba"

"Allah ya ba ka lada Sule. Daman Hasiya burinta Asma'u ta samu rayuwa mai inganci. Allah ya taya ka riƙo"

Ya amsa mata da Amin Amin sai ta ce to Asma'u ta tashi ta haɗo kayanta a wanke saboda gobe Sule zai wuce zai tafi da ita. Sai ta fice tana murna. Hajiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ja'ira itama tana son bin ka ashe."

  Sun cigaba da hira har aka kira sallah ya yi alwala ya fita masallaci domin ya yi salla bayan ya idar ya daɗe a waje yana gaisuwa da mutane da aka kwana biyu ba a haɗu ba. Ya na wajen Aminu da babban ɗansa Muntari da Sani suka dawo daga gona rumgume ɗan uwansa Aminu ya yi yana murna da ganinsa Muntari ya duƙa har ƙasa yana faɗin.

"Sannu da zuwa Baba Sule."

Kansa ya shafa kafin ya ta da shi tsaye yana faɗin" Muntari ka ƙi zuwa dai na saka ka a makaranta tare da su Hamza ko? Ka gwammace ka yi ta zuwa gona da babanka ko?

Kansa na ƙasa ya na shafa ƙeya ya ce" Zan zo Baba in sha Allahu."

  Sani ne faɗin ai yana yin makaranta gwammati na cikin garin kusada. Sai Sule ya ce hakan da na kyau in ya gama ya zo ya same shi a kano domin ya nema masa ta gaba da sakandiri saboda ilimi na da amfani sun ga misali a kan shi da ilimin da ya yi ya zama abin ya zama yanzu.

Cikin gida suka shiga gabaɗayansu kamar yadda suka saba in dai Sule ya zo a ɗakin Hajiya Dubu suke haɗuwa su ci abinci. To yau ma haka suka yi bayan sun gama cin abinci suka sake fita suka raka shi gidan su Maimuna ya yi gaisuwa da alƙwarin in ya koma ita za ta zo in sha Allahu.

Ranar dai ya yini cikin ƴan'uwansa har dare suna tare  Hajiya ta faɗa musu zai tafi da Asma'u Aminu ya ce gwara haka ƙila za ta fi sakin jiki sannan can za ta yi karatu nan kuwa sai dai ta ta ƙara tasawa a yi mata aure.

  A tsohon ɗakin su na zaure ya kwana gidan da ya ke ginin mutanen da ne na ƙasa ne da yaɓe. Da safe bayan sun karya ya yi wanka ya yi shirin tafiya  kuɗi ya ba ma Hajiya Duhu ta yi ta saka albarka Asma'u an haɗa mata kayanta a kullen ɗan kwalli itama ta ci gayunta da takalminta ɗan madina da hijabinta da ya yi mata yawa.

Lokacin da Sule da Hajiya Dube suke sallama ya ce mata" Hajiya don Allah ki bari na zo na ɗauke ki in na gama gina gidana ki koma can da zama."

Hajiya Dubu ta ce"To Sule in na bika su na nan ai sai su ce na fi sonka ne ko?

Su Sani na wajen su ka saka dariya domin su san ba ta son barin garin kwata kwata.

  Aminu ne ya ce" Hajiya da mu da Yaya Sule duk ɗaya ne. Mu ma za mu so ki samu rayuwa mai inganci da jin daɗi kafin wa'adi ya yi. Mu kuma ki bar mu anan mu ai ba yara ba ne muna da iyalai da yara. sai mu riƙa zuwa muna duba ki in sha Allahu."

  Ba ta dai ce komai ba sai ta wani rausayar da kanta alamun ba ta amince ba shi kuma Sule ya shuru ne ya dai gama gina gidan na shi tabbas sai ya ɗauke Hajiya zuwa Kano domin itama ta samu chanjin rayuwa.

Har ƙofar gida Hajiya ta raka shi da zugan yara duk ya sallamesu da kuɗi sulalla ya ce su je raba a tsakaninsu Muntari ne ya ɗaukan masa jaka yana gaba tare da Asma'u shi kuma ya na baya tare da ƴan'uwansa suna tattauna mganar gonar shi da ake noma masa tana hannunsu ne tun da sune suke cikin garin.

Sune har zuwa in da ya samu akori kuran da zai ɗauke su zuwa babban hanya da za su samu motar kusada daga can su hau ta zuwa garin Kano.

*****

KANO. Fagge.

Ba zan manta ranar da Alhajinmu ya zo da Ma'u gidanmu ba. A wata ranar lahadi ne da yamma domin sanda suka iso ba ma gida muna isalamiya ni da Rahilaa mun dawo makaranta ne muka ga wata baƙuwar yarinya mai kallon mutane da idanuwanta a tsaye a cikin ɗakin mu.

A lokacin Yaya Aina ce kawai ta yi aure. Amman su Yaya Murja sune ƴan mata a lokacin ita da Yaya Balki tun da ba su da tsareyan haihuwa. Ita Yaya Murja ta na ajin kusa da ƙarshe a babban sakandiri ita kuma Yaya Balki tana ajin farko. Ni da Rahila ne muke tasawa a lokacin sai Amina da ke bin bayan mu a lokacin da Datti da ya ke namiji.

  Lokacin da na shiga ɗakin mu na ga baƙuwa. Kallon juna muka yi cikin ido tun a wannan lokacin Ma'u ba ta kwanta mini arai ba idanuwanta kir suke a kan mutane. Rahila ce ta tsaya ta na tambayanta ita wacece, ni ina ko hijabin isalamiyata ban cire ba na fita tsakar gidaa in da Gwaggo da ke shanya kaya a igiya sai Mama dake cikin ƙaramin madafin da ke tsakar gida suna kuma hira jefi jefi da juna.

" Gwaggo Alhajimu ya dawo ne?

Na faɗa ina kallonta. Ba ita ta bani amsa ba Mama ce ta amsa min da E. Lokacin muna gidan Haya ne kafin mu koma gidanmu na Ɗorayi Alhajimu ba shi da bangare sai dai yana zama a ɗakin duk wacce ke da girki ne.

  Ina so na tambayi wace ce na gani amman na kasa na wuce zuwa ƙofar ɗakin Mama na tsinkayi muryan Rahila ta na faɗin" La Gwagggo wannan wace ce? Alhajimu ya zo da ita daga Yashe?

Ta faɗa bakinta kamar kunne saboda na juya na kalleta. Sai na ji raina ya ɓaci ganinta rike da hannun yarinyar da na ji Gwaggo na faɗin" E sunanta Asma'u. Yarinyar Baabarku Hasiya ce. Anjuma dai Alhaji zai yi muku bayani sosai."

  "Asma'u"

Na maimaita sunan a ƙasan raina. Kai na kauda ganin Rahila na tsallen murna to miye abin murna. Tana da ni to kuma miye na jin daɗi domin an kawo wata. Duk da akiyasin shekaru ba za mu girmi Asma'u ba tabbas sai dai mu zo tsara. Ni da Rahila tare iyayenmu suka yi goyon cikin mu kwana arba'in ne cif a tsakaninmu.

Lokacin da su Yaya Murja suka yo sallama suka shigo gidan suma da Kayan islamiyansu ni kuma na yi sallama a ɗakin Mama Alhajinmu ya amsa sannan na shiga. Sannu da zuwa na yi masa ya amsa ya na kishiɗen kan kujera ganina ya sa ya ɗan miƙe zaune ya na faɗin" Dubu. An dawo?

Na amsa ina gurfanawa a gabansa.

"Alhajinmu ina tsaraba ta? Ko Hajiya ba ta baka wani abu ka kawo mini ba?

Abin da na fara faɗi kenan kuma kamar ba haka ya dace na ce ba. Ƙila ya dace na ce ne" Alhajinmu wace ce ka zo da ita? Amman ban ce ba. Shi kuma bai damu ba yana yar dariya ya ce"Tsaraban ki ta gyaɗa ta nan. Sai da Hajiya ta jadadda mini ke kaɗai ce mai gyaɗar nan."

  Ina jin haka na washe baki na zauna ina tambayan ya ya baro su Baba Aminu ya amsa da duk suna gaishe mu.

"Alhajinmu yaushe to mu za mu ce?

Saboda ina son garin Yashe ina jin daɗi in na je garin Hajiya ta na ji dani saboda sunanta aka sakamin shi ya sa ma Alhajinmu da su Gwaggo ke kirana Dubu. Sauran ƴan uwana kuma Sadiya.

  "Sai kun samu hutun makaranta. Tun ga ma Asma'u in za ta je ganin gida ke da Rahila za ku riƙa rakata."

  Kallonsa na yi kamar zan yi mgana sai na fasa. Sai kawai na bige da faɗin" Yaushe Hajiya za ta dawo gidanmu da zama?

Alhajinmu ya muskuta kafin ya ce"Sai na gama ginin gidana Dubu. Akwai ɗakin Hajiya sai na ɗauko ta zauna damu? Hakan ya yi ko?

Sai na gyaɗa masa kai ina mirmishi. Labarin makaranta ya tambayeni na gyara zama ina bashi labari sai da aka kira sallar mangariba sannan hiran mu ta katse.

  Kowa ya yi alwala domin gabatar da Sallah. Alhajinmu shi da Yaya Abubakar da Yaya Auwal sai Datti suka tafi masallaci Yaya Hamza baya nan ya na Niger can ya ke karatun babban sakandirinsa. Shi Yaya Abubakar je ka ka dawo ya ke yi anan cikin garin kano.

  Ina zaune a gefe ina ganin yadda ƴan gidanmu ke kara kaina akan Asma'u da Yaya Murja ta fara laƙaba mata sunan Ma'u da ya kashe Asma'un ma gabaɗaya. Kowa na rawan jikin tambayata abin da take so ta ci Rahila har tana ɗaukan kayanta ta na saka shi cikin jakar kayan mu na sawa tun da kayanmu na waje ɗaya ne. Ni dai ko magana ta fatar baki ba ta haɗa mu ba kusa da ita ma ban je ba. Har da Gwaggo da Mama a masu kai da kawo akan Ma'u.

Sai da aka yi isha'i su Alhajinmu suka dawo. Kowa ya ci tuwon da Mama ta yi amman ban da ni ba kuma ba na jin yunwa ba ne ina ji amman Rahila ce ta baƙan ta mini rai.

  "Mama ki haɗa mana Tuwon mu tare da Ma'u ko Sadiya?

Tsabar haushi sai kawai na ce"Ni ban ci.".

Saboda na ga daga zuwan yarinya amman Rahila ta fifita ta sama da ni kawai sai na ce na ƙoshi.

Gwaggo ta kalle ni kafin ta ce"Me kika ci?

Sai na rausayar da kai kafin na ce"Bakomai."

Sanin halina na tsirfa wani lokacin sai Mama tace a rabu dani.

Ranar na sha mamaki domin Ma'u kasa cin tuwo ta yi tana ta jagwalgwalawa har su Alhajinmu suka shigo a ka shimfiɗa babban tabarma a tsakar gida ana zazzaune ana cin tuwo ni kuma ina daga gefe ina kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.

"Bakuwar nan fa kamar ba ta cin Tuwo"

Yaya Abubakar ya faɗa duk sai suka kalleta. Haka ne ko ba ta ci sai wasa take yi da shi a hannunta.

"Ko ba ta cin Tuwo ne Alhaji?

Cewar Gwaggo. Mama ke ce tambayan Ma'u ko ba ta cin tuwo dai dai lokacin da Alhajinmu ya ce"Anya. Ban sani ba. Asma'u a siyo miki wani abun ne?

Sai ta kalle shi amman ba ta yi mgana ba.

"Za ki sha shayi?

Yaya Abubakar ya faɗa sai ta kalle shi sannan ta ɗaga kai alamun eh. Na sandare a zaune lokacin da Alhajinmu ya ciro kuɗi daga aljihunsa ya ce Yaya Abubakar ya je ya haɗo kayan haɗa shayi a haɗa ma Asma'u tunda ba ta cin tuwo. Da fitansa da sauri da tashin da Rahila ta yi ta ce bari ta sa ruwan zafi sai Mama ta ce akwai ma a saman tukunya a madafi.

A daran nan dai Ma'u shayi ta sha da buredinta. Ahalin har Alhajinmu tuwo ya ci. Gabaɗaya hankalin yan gidanmu na kanta kamar sun ga wata sabuwar hallitta. Ina ji Alhajinmu na kora bayanin wace ce Ma'u a garemu gabaɗaya.

"Ɗiyar ƙanwata ce Hasiya. Mahaifinta ya rasu ɗan nan garin Yashe ne. Ta dawo hannun Hajiya da zama shi ne da na je na ganta na taho da ita za ta zauna da mu har abada."

"Allah ya taya mu riƙo Alhaji."

Gwaggo da Mama har suna haɗa baki wajen faɗa.

"ƴar uwan ku ce Ina fata za ku kalleta a matsayin jini ɗaya."

Yaya Abubakar ya amsa da in sha Allahu.

  Yaya Murja ta yi karaf ta ce"Muna son ta Alhaji. Ga ƙawa ma na yi mata Rahila."

A lokacin ƙankance ido na yi ganin ta haɗa hannun Rahila da Ma'u waje ɗaya. Saboda sun zauna daman a kusa da juna ne. Ita kuma Rahila sai mirmishi take yi a yayin da Ma'u ke kallon kowa da idanuwanta. Tun kafin zuwan Ma'u daman ni da Yaya Murja ba ma zama a waje ɗaya saboda ta na da faɗa ni kuna ina da baki ta bakin ta ta ce ba ni da kunya manya na mgana ina saka musu baki.

"Har da Dubu ma. Saboda na ga za su yi tsara ya sa na samu karfin gwiwan ɗauko Asma'u."

Alhajinmu ya faɗa sannan idanuwansa suka fara laluɓena sai ya ganni a can baya ina zaune.

"Dubu..'

   

Ya kirani kamar yadda ya saba kirana sai na amsa. Sai ya ya fito ni da hannu na taso na zo gaban shi.

"Dubu ba ki ga yar'uwan ki Asma'u ba ne?

Na juya muka kalli juna ni da ita sai na kauda kaina kafin na ce" Na ganta."

Ya na mirmishi kafin ya ce"To ga ta nan ke da Rahila na bar ma Amanan Asma'u. Ku yi ƙawa da ita kun ji ko?

Ni dai kai na ɗaga Rahila  ce ta amsa har ta na cewa" Alhajinmu a saka ta a makarantar mu don Allah"

Sai kawai na ji Alhaji na faɗin "In sha Allahu tun da daman Hajiya ta ce ta gama firamari sai na saka ta a tare daku har islamiya ma"

Sai kawai Rahila  ta rumgume Ma'u tana murna.

A lokacin Yaya Abubakar ya kalleni ya ga na haɗe rai sai kawai ya kalli Ma'u yana faɗin" In Sadiya ta yi miki wani abu kar ki raga mata ki rama kin ji ko?

Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya yana nuna ni. Ana ta dariya har Alhajinmu. Amman ni ban yi dariya saboda ni ban ɗau abin da wasa ba. Mun ƙara kallon juna ni da Ma'u na wani lokaci sannan kowa ya ɗauke kansa.

Yaya Murja har tana faɗin" Wallahi kuwa. In Sadiya ta ga sakenta ai ta shiga uku."

Mutane biyu da suka fara bin bayan Ma'u tun kafin tafiya ta yi nisa. Suna faɗa mata abu mara kyau game dani.

  A wajen kwanciya ma na ga abu. Mu uku muke kwana a karamar katifa a ƙasa ni da Rahila da Amina. Amman sai Rahila ta jajibo mana Ma'u ban iya shuru ba sai da na ce" Rahila a ina za ta kwanta? Ko ke za ki kwana a ƙasa ki bar mata wajen ki?

Daga mgana sai aka ga laifina. Kawai sai Yaya Murja ta fara zagina su suna babban gado ita da Yaya Balki. Gwaggo sai da ta shigo ta raba faɗan da har Yaya Murja ta ce Ma'u ta dawo gadon su ta bar mun katifar sai Gwaggo ta ce Amina ta koma wajen su Yaya Murja mu kuma mu kwanta mu uku ban ji daɗin hukunci Gwaggo ba amman ba ni da mafita ni ta kafafunsu na kwanta Rahila na bari da kwanciya filo ɗaya da Ma'u.

  Tun daga wannan ranar Ma'u ta zama yar gida ko na ce tafi ma wasu yan gidan sakewa tun da tama da masu tsaya mata. Da ya ke Rahila tafi mu girman jiki ni kuna siririya ce ina da tsawo ba can can ba amman yanayin fasalin jikin mu ɗaya da Ma'u. Mama ta saka na tsinta kayana na ba ma Ma'u saboda sune za su yi mata kafin Alhajimu ya siya mata wasu kayan saboda wanda ta zo da su duk sun yage an zubar. Sannan Yaya Murja ta yi mata tsifa suka rakata gidan kitso.

Komai fa nuna mata suke yi ga shi ba ta cin Tuwo sai dai in tuwon shinkafa ne miyar ganye. Ba ta cin dambu ba ta shan fate tsirfa dai kala kala kuma an ɗaure mata gindi. Duk ranar da aka yi ɗaya daga cikin su sai dai a siya mata wani abun ko kuma a dafa mata wani abun ta ci ita yar gata.

Islamiyarmu aka fara saka ta. Sai da aka yi albashi Alhajinmu ya saka ta a makarantar mu ta Goverment Girls Junior Secondary School Diso. Kuma abin mamaki da irin sunan da muke amfani da shi. ASMA'U SULAIMAN YASHE. lokacin da Yaya Abubakar ya kai ta makaranta za a saka sunan Babanta mahaifi sai ta kalli Yaya Abubakar ta na faɗin"Ba sunan Alhajinmu za a saka mini ba?

Shi kuma Yaya Abubakar bai yi shawara da kowa ba ya sanya mata sunan Alhajinmu wanda dashi ta ke alfahari har gobe kuma har abada.

  Sai da ya dawo gida ya faɗa Alhajinmu kuma bai ce don menene ba. Ba aji ɗaya aka sanya mu ba mu muna A ita kuma ta na B. Anan ne ta haɗu da Shema'u da daman halinsu yazo ɗaya. Rahila ce ke wani rawan jiki akan Ma'u amman ni sai na iya kirga ma maganarmu yadda ba ta mini mgana nima ba na yi mata kowa harkan gabansa kawai ya ke yi. Tun kafin kowa ya lura ni na fara lura da makircin Ma'u saboda ni ke kula da duka motsinta a gaban mutane saliha ce sai a makaranta in ka ganta tare da ƙawarta ba ka ce ita ce ba. Ban taɓa nuna ta a makaranta na ce ƴar uwata ba ce saboda ni ba ni ma da ƙawaye Rahila ce kaɗai na ke tare da ita. Amman ita Rahila mai jama'a ce kowa nata ne ni kuma ko ana son ƙawancen dani ba na ba da fuska ki gaji da naci ki haƙura ba islamiyan ba bakon ba.

  Sai ya zamanto komai za a yi mana a gida guda uku ne tare da Ma'u. Ta zama yar gaban goshin Yaya Abubakaar shi ke koya mata karatu baya shigowa hannun rabbana sai ya yo mata tsaraba. Sannan Yaya Murja yadda take ƙaunar Ma'u ko ni yar uwanta ba ta sona haka. Alhajinmu ma gata yake nuna mata shi da su Gwaggo. Tun ina mamaki har na daina na sadakar da Ma'u ta samu tasiri mai yawa a zukatan yan gidanmu.

Baaba Hasiya ta zo ta duba Ma'u bayan ta yi wattani huɗu a tare da mu. Lokacin tun ba mu gama zama cikakkun mata ba na ji Baaba na yi ma ƴarta huɗuba da cewa" Kin samu rayuwa mai inganci Asma'u. Ki kwantar da kanki ki yi ma Yaya Sule da Gwaggo biyayya domin ita ce matar Fari. Wancan Rukayyar ba ta gabana. Sannan ki samu cikin yaran nan na Yaya Sule  Maza wani ya yaba dake sai ki yi auran ki kin ji ko?

  Ina laɓe ina jin su kuma ba niyyata na yi laɓe ba na zo shiga ɗakin ne na ji suna mgana na tsaya. Ban ankaraa ba sai ga sun fito. Baaba Hasiya daman in dai ta zo a ɗakin Gwaggo ta ke sauka ba ta sauka a ɗakin Mama na taɓa jin tana faɗa ma Alhajinmu a wani zuwa da ta taɓa yi wai Mama mai farar ƙafa ce tun da ya aure ta al'amarinsa ya ja baya tun da ga Lokacin na san ba ta ƙaunar Mama kuma mun taɓa zuwa Yashe a ɗakin Hajiya ta yi ma Mama rashin kunya har Hajiya Dubu na yi mata faɗa ina ƙarama a lokacin amman na ƙasa mantawa da abin.

"Ke lafiya? Ko laɓe kike yi mana"

Baaba ta katse ni tana hararata. Sai na kalleta kafin na kalli Ma'u sai kawai na ga ta yi mini wani kallo kafin ta ce" Daman Baaba ba ta sona. tun da na zo gidan nan."

Sai kawai na saki baki ina kallon Ma'u Baaba kuma ta fara tafa hannu ta na faɗin" To ai sai ta kore ki. Shegiya mai mugun hali to Asma'u zama daram in ji mai naguda."

  Maganarta ya jawo hankalin su Mama da Gwaggo Ranar Lahadi kowa na gida.

Baaba sai ta fara kuka tana faɗin labe ta kama ni ina yi musu ta na fitowa ta ganni shine ta fara min faɗa na yi mata rashin kunya har ina zagin Ma'u ina cewa ta zo cin arziƙi ba gidan ubanta ba ne"

  Ban mantawa maganar har sai da ta kai kunnen Alhajinmu. Yaya Murja har ta na marina saboda ta dunguremin kai na ce Allah ya isa ta mare ni. Yaya Abubakar ya saka ni kneel down ban ji ba ban gani ba. Ni kuma ban ƙaryata su ba amman na yi ma Ma'u wani kallo ganin tana yi mini dariya. Alhajinmu ya yi min faɗa fata fata abin da bai taɓa yi min ba yana ƙara jadadda mini Asma'u ba bare ba ce ƴ'a take kamar kowa.

  Ina ji ina gani Ma'u ta zo gidanmu tana mini iko. Sai ta takale ni da faɗa ni kuma ban gane makircinta ba sai na tanka ta shikenan in aka zo jin ba'asi sai ta marairaice ta fara kuka tana faɗin na ce mata in ta gaji ta koma gidan ubanta kafin Ma'u ta rufe shekara a gidanmu har gwammatina a wajen Alhaji ta hambarar da shi da makircinta kowa ba ya faɗin abu mai kyau akaina ko abu ya haɗamu sai ace Ma'u ce mai gaskiya ni ce mara gaskiya.

Har Rahila ce mini ta ke yi" Don Allah Sadiya ki daina takurama Ma'u a cikin gidan nan. Ban ga abun da ta tare ki miki ba."

Itama goyon bayan Ma'un take yi kenan daga lokacin na fahimci gwara na miƙe na kwaci kaina domin ba ni da mai goyon bayana ko Mama ce na je na faɗa mata sai ta ce ni ce ba ni da gaskiya ba mai cewa a tsaya a bincika. Mutum ɗaya ne bai taɓa goyin bayan Ma'u ba shi ne Yaya Hamza lokacin da ya dawo hutu mun taɓa wani dambe da Ma'u akan ina zaune a ƙofar ɗakin mu ina gyaran jakar makaranta ita kuma ta fito wanka. Ga hanya na bata amman da ya ke makira ce sai da ta ga ba kowa a tsakar gidan sai ta takani za ta wuce ni kuma na miƙe na jawota ta baya wajen ta tsaya sai kafartaa ta turguɗe sai ga ta a ƙasa amman yarinyar nan sai ta fasa ihu ana taruwa ta ce ni na saka mata kafa ta faɗi.

Lokacin an saka ranar auran Yaya Murja ita ta saka mini hannu Yaya Hamza ya tsawatar   ashe ya na daga can ƙofar ɗakinsu ya na ganin abin da faruwa.

  "Yaya Hamza Sadiya ta ɗora ma  Ma'u karan tsana tun daga ranar da Alhajinmu ya kawo ta gidan nan saboda ta ganta ba ta son tashin hankali."

  Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce"Ita ta ce miki ta tsane ta? Ya za a yi ta tsane ta sai dai in akwai abin da take yi mata ne wanda ba ta so."

Yaya Murja za ta yi mgana ya ɗaga mata hannu kafin ya ce"Ki daina ɗaukan bangare ɗaya a matsayinki na babba ki zama adala. Ina  can daga ƙofar ɗaki na ga abin da ya faru. Ke ce ba ki da gaskiya ta ba ki hanya amman saboda tonon faɗa kika takata ta miƙe ta jawo ki sai aka yi rashin sa'a kafarki ta turguɗe kika faɗi ko ba haka aka yi ba?

Ya faɗa ya na tsare ta da ido. Duk rashin kunyarta sai ta sadda kai ƙasa ta kasa mgana shi Yaya Hamza akwai tsare gida ba irin Yaya Abubakar ba ne shi kamar wani mace yake jin kansa.

Kai tsaye ya ce Ma'u sai ta bani hakuri dolenta kuma ta bani a kausashe ya kalleta kafin ya ce" Kar ƙi kara takalanta. Ni na san Sadiya ba ta faɗa ba a taɓa ta ba. Ku zauna lafiya da junan ku.'

  Sai ta gyaɗa kai. Ni kuma sai ya riƙe hannuna zuwa ɗakinsa yana lallashina. Tun daman akwai fahimtar juna a tsakanimu. Ina kuka ina faɗa masa makircin Ma'u sai abin ma ya bashi dariya cikin dariyan ya ce" To ke ma ki riƙa ramawa mana. Ki daina bari ta na samun galaba a kan ki."

Shi mamaki ya ke yi ƴar Ma'u ta iya makirci tunda ya ganin ma idanuwansa.

  Zaman Yaya Hamza a gida sai na samu lafiyan Ma'u. Tsoron shi take ji ko maganarsa ta ji yanzu za ta shiga taitayinta. In ya na waje ba ta iya wani motsin kirki har sai ya gama hutun shi ya koma tun kuma daga lokacin nima na gane in ta yi mini abu na rama kafin ta kai ga  haɗa min makircin ni

Na haɗa mata amman ba ya tasiri tun da ni daman na yi ƙaurin suna sai ya kasance Ma'u ta riƙa cin nasara akaina ko a makaranta in na ganta tare da ƙawayenta suna nuna ni suna dariya barin ma wannan shegiyar ƙawar tata mai kama da biri Shema'u na tsane ta har acikin raina.

  Mun je Yashe sau ɗaya bayan zuwan Ma'u gidanmu. Mun yi sati ɗaya har gidan Babanta mun je sai na ƙara raina mata kamar ma ba sa son ta. Domin ba a wani tarbe mu ba shi ya sa ita kanta ba ta zauna ba. Sai da muka dawo kano sai ita da Rahila suka shirya suka tafi kura in da Baaba ke aure ni kuma na ce ba zan je ba. Daga kuma lokacin in faɗa ya haɗa mu da Ma'u sai na yi mata gori da cewa in ta ji na dame ta

Za ta iya komawa gidan tsoho a ƙauye nan dai gidan Ubana ne kuma ba ta isa ta hanani sakewa ba saboda na daina tsoro ko a gaban waye za ta kai ni ta fahimci makircinta ba ya yi mini aiki sai ta koma itama ramawa. Na samu sauƙi Yaya Murja ta yi aure a shekaran 1996. Yaya Balki kuma ba ta kai Yaya Murja zafi ba.

  

Sai da bikin Yaya Murja sannan na fahimci Ma'u ta ɗau huɗubar Baaba saboda Yaya Hamza ya dawo gida ya gama babban sakandiri shi da Yaya Abubakar duk suna gida jarabarwarsu ba ta yi kyau ba sai sun sake yi. A lokacin na fahimci in dai ta gan shi yanzu za ta fara gyare gyare lokacin muna Ajin biyun ƙaramar sakandiri ne amma har Ma'u ta san ta yi ma namiji karairaiya.

Abin da na fahimta kamar tunaninta na kan Yaya Hamza shi kuma Yaya Abubakar tunaninsa na kan Ma'u ni ce na fara lura da ita da kuma abin da ke faruwa saboda ni ce daman idona ke kan duka motsinta.

  Shi Yaya Hamza bai ma san ta na yi ba. Namiji ne mai tsare gida ba ya ɗaukan reni ba shi kuma da yawan sakewa mutane shi kuma Yaya Abubakar yana da sanyi ga arhan dariya shi fa kowa na magana dashi ga surutu ba kamar Yaya Hamza ba. Ga aji ga tsare gida mgana ɗaya bayan ɗaya cikin wayewa shi ya sa na ke ƙaunar Yaya Hamza na kuma saka acikin tunanin irin mijin da zan aura mai hali irin na Yaya Hamza ne sannan na ji a raina ba zan iya auran mai hali irin na Yaya Abubakar ba. Shi daman Yaya Auwal da shi da babu a gidan duk ɗaya. Sai a yi abu goma bai sani ba yana da ƙokari ko yau she yana ɗaki yana karatu in ba na boko ba na arabi. Kuma shi yana da ƙyaluwa ba kasafai ya ke saka baki a wasu abubuwan ba. Shi sai a shekaran ma ya zana jarabawar shiga babban sakandiri.

Janafty