Ajnabiyya page 1
AJNABIYA...
NA
*HAJJA CE* 👈
Arewabook@Hajja22522
Wattpad@Hajjac
Facebook@Hajjace
Bismillahir rahamanur Raheem...
Dukka wannan labarin na rubuta shine dan tunatarwa. Banyi dan rayuwar wata ko wani ba, idan har kinga abu yazo da yanayin rayuwarki/ka. Nayi shine bisa experience bawai na sanki ba ne ko na sanka. Alƙalami ne ya biyo ta kan irin halin. Fatan zaku biyo labarin dan muje meke cikin AJNABIYA
Page 1
Ɗaura gwiwoyi Ameerah tayi a gefen tabarma tana kallon tukunyar miyar kukar da ke ta dafa kanta akan ƙaramin murhu. Wutar tana ci a hankali tana ta fitar da hayaƙi. Yayin da gefe guda kuma hayaƙin yana ta bugar cikin idanunta da hancinta, idanunta sunyi jawur sai zubar da hawaye suke yi. Sai dai amma ba hayakin ne ya yi sanadin fitowar ƙwallar da ke shirin zubo mata ba, zuciyarta ce ta cika da burin da take jin kamar mafarki ne kawai. A fuskar Ameerah babu wata damuwa da za ta kai irin wadda take ji a yau. Duk da ƙananan shekarunta, ta rigada ta fahimci cewa ba kowa ne yake da zabin yadda rayuwarsa zata kasance ba. Ita dai ta san cewa ta fito ne daga gida irin wanda ta ke ganin bai dace da ita ba, gidan da ko ruwa na shan safe sai an jira a ɗebo daga rijiyar unguwar. Amma Allah ya rufa musu asiri, ya sanya kullum suna da abin da za su ci ko da kuwa ba mai ɗanɗano bane ba. Ko kuma ba mai fentin sha’awa bane a idanuwa da zaka kalla kaji daɗi. Ameerah tana kallon miyar zuciyarta na yawo a cikin mafarkin da ta jima tana ɓoyewa a cikin ranta.
"Da ace ina gidan masu kuɗi…" Ta furta a hankali kamar wani yaro da yake ba da labarin yadda aljanna ta ke.
"Da yanzu abinci kawai za a kawo min a farantai masu kyau da ɗaukar idanuwa. A gefe kuma naman kaji ko na zabi ne da lemo mai sanyi ko madara mai rai da lafiya. Ko ruwa mai sanyi da zan sha ba tare da na debo a cikin rijiyar da dubban mutane ke dabdala a gabanta ba." Tana magana idonta ya sauka kan tuwon da ke gefe da alama yana shirin dahuwa ne. Ta runtse ido hawaye na gudu saman kumatunta har ya zubo saboda baƙin ciki.
"Amma me yasa zama burin mai kuÉ—i yake da daÉ—i kamar haka?" Ta sake tambayar kanta tana yin shiru tamkar mai jira a bata amsa.
"Me yasa ba a bani zabin ina zan fito nayi rayuwa ba?" Ameerah ta faɗa tana ɗaga idanunta sama tana kallon sararin samaniya ta hanyar hujin ramin da ke jikin rufin zannuwar da ta ke karkashi a zaune. A can wani jinjirin wata ya fara leƙowa ta kura masa ido tamkar shi ta ke jira ya bata amsar tambayoyinta.
"Allah ka san abinda ke zuciyata." Ta furta da murya kamar mai roƙo.
"Ka bani dama na ɗan ɗanɗana rayuwar da zuciyata ke mafarkin kasancewa a ciki ko da sau ɗaya ne. Ka bani dama in san yadda ake tashi da safe abinci ya riga ya shiryu. Nama da lemo ya kasance gaba na ina tunanin inci ko ince a canzo min da farfesun kifi, ba wai mafarki ba." Ƙamshin kamun da tuwon ya fara shine ya dawo da ita daga addu'ar samawa zuciyarta abinda take so tayi. Ta daure zuciyarta ta janye tukunyar ta fara juyewa a cikin robobi. Amma dai zuciyarta ta riga ta cika da ƙamshin burin da ba da ruwan miyar kuka za ta iya wanke shi ba.
Ranar bata da bambanci da sauran ranakun da Ameerah ta keyi tun lokacin da ta fara mallakar hankalinta. Sai dai fa zuciyar Ameerah da ayau take da nauyi fiye da kullum, ji ta keyi tamkar ta ɓarar da tuwon ƙasa yabi ƙasa ko za'a samu a sauya musu cimarsu koda kuwa ta yau ɗin ce kawai. Bayan ta gama juye tuwon, ta shimfiɗa farar leda a tsakiyar ɗaki mai haske mara fenti, sannan ta ajiye roba ɗaya a can gefe na Maman ta. Ta juye nata cikin ƙaramin kwano ta tsuguna kamar yadda ta saba, amma hannunta ya tsaya a tsakiyar iska saboda karta dinga shaƙar ƙamshin miyar tana jiyo warin daddawa. Miyar kukar kuwa tana ta zuba hayaki, amma bata jin yunwa saboda mafarkin da ya tayi ya cika mata zuciya. Kallon tuwon kawai take yi kamar wacca aka ce tayi bankwana da duk wani burinki cin cikakken abinci mai daɗi.
Na da nan kuwa zuciyarta ta koma gidan da ta ke mafarki, gidan da duk abinci ana kawo shi ne a cikin ƙawatattun kuloli masu ɗumi da tashin kai, wanda a cikin su akwai kamar su gurasar milk bread da butter a gefe. Ko nama a cikin kwano mai murfi ga kuma kayan marmari da ledojin kayan sha masu sanyi da ƙamshin daɗi a cikin gidan da idan da ita ce a cikinsa tabbas tana zauna ne a cikin babban ɗaki tana kallo a plasma screen tana cin abinci ba tare da an kira ta ana cewa.
"Me yasa baki ƙarasa shanya kayan nan ba?" ko kuma ace,
"Tashi ki je ki ɗebo ruwa, sai kin ɗebo za'a ɗora girki." Dariya ce ta zo mata, amma daga cikin idanunta hawaye ne a cike. Ita kanta ta san mafarkin nata kamar mai taɓin hankali ne, amma me ya fi ƙarya daɗi? Duk da haka rayuwar da take ciki ma ba ita ce mafarkin kowanne ɗan Adam ba. Tana cikin wannan tunanin ne Maman su ta fito daga wani ɗakin dake ciki tana sanye da riga da skirt da aka wanke har sun yayyage tana ɗauke da littafin Yassin a hannunta take cewa.
"Ameerah ki zo ki kaiwa Baba abincin shi kin san baya son jinkiri." Ameerah ta tashi da sauri ta share hawayenta da yatsanta, ta ɗauki kwanon tuwon ta fita. Amma a zuciyarta wani sabon ƙuduri ne ya fara girma na ƙudurin fita daga rayuwar da take ciki ta nemo burinta ko da kuwa zai ɗauki shekaru da hawaye a idanunta. Tana so ta canza tarihi, bata so a ce a haka tarihinta zai kasance har gaban abadah.
Ameerah tana fitowa taga hasken wutar nepa a gidajen dake zagaye dasu ya cika mata ido, nan da nan taji wani abu ya daki zuciyarta tunawa da tayi tun last month da suka kasa biyan kuɗi ƴan wutar suka hau suka yanke musu ita tun daga ranar basu sake ganin nepa a cikin gidan su ba. Da wani irin yanayi tabar unguwar ta nufi wajan da Babansu yake gudanar da sana'arsa. Bata jima ba ta juyo. Tana hanyar dawowa unguwar daga kaiwa Baba abinci, ta samu wani yaro ɗan unguwar yana ta zagaye a ƙofar gidan su. Tana hango shi ta ce da zuciyarta,
"Wannan fa? Wa yake nema ko yayi ɓatan hanya ne?" Sai dai kafin ta buɗe baki ya taho wajanta da murmushi akan fuskarsa yana cewa.
"Ke ce Ameerah?" Ta É—aga masa kai alamar eh cikin mamaki.
“Malamin makarantar ku ne yace ki je gobe da wuri. Wata mata daga NGO ta zo suna ɗaukar daliban da suka fi ƙoƙari don basu wata scholarship. Malam yace ke ce ta biyu a aji." Sai da kalmomin suka gama ratsawa kunnuwanta sannan suka fara shiga cikin zuciyarta kamar ruwan sama kafin cike da mamaki tace.
"Ni? Ni Ameeran ce wata dama zata same ni? Ahhh! Scholarship kuma?" Tayi shiru hawaye na yawo cikin idanunta. Ta kasa amsa sai da ta ga yaron ya fara ja da baya kafin ya ce,
"Ki yi haƙuri idan na ɓata miki rai."
"Gobe da wuri zan je." Haka kawai ta furta da wani irin ƙarfin zuciya da bata saba da shi ba.
Da kyar taja ƙafarta ta shiga gida tana tajin zuciyarta na yi mata wani irin nauyi. A daren ranar sam Ameerah bata iya bacci ba. Tana kwance a ƙasa, kanta a jikin ƙaramin matashin kai wanda aka yi da tsohuwar riga tana kallon sama. Idonta yana hangen sama kamar tana ƙoƙarin ganin gobe da idanun ta.
"Ko dai wannan ce damar da nake ta jira ne? Ko ita ce hanyar da zata fitar da ni daga cikin ƙuncin nan?" Ta lumshe ido ta fara hasashen kanta cikin makaranta mai kyau da tsafta, tana sake hangota sanye da kaya masu sheƙi da walwali. Hangota ta keyi tana zaune cikin aji mai sanyi da AC tana rubutu cikin sabon littafi da sabon biro, tana jin malami yana faɗar sunanta cikin girmamawa, lallashi da kuma kulawa. Sai dai a zahiri wani ƙaramin tunani ya datse mata mafarkin nata.
"Ko zan samu kayan da zan saka gobe?" Cikin sauri Ameerah ta tashi ta nufi gefen kwalayen da suke a jere cikin É—akin ta fara bincika kayan tana ware kayan da za ta iya fita dasu gaban mutane. Da kyar ta samo atamfa É—aya mai launin shuÉ—i da rawaya da ta fi duka kayan mutunci da hankali duk kuwa da rigar kayan sai da tayi mata É—in kin zare da allura. Amma bata damu ba saboda su É—in ne masu mutunci a ciki. Abin da ya fi damunta shi ne damar da ke gabanta.
Washegari tun kafin kiran asubahi Ameerah ta farka ta wanke fuskarta ta sa tufafin da ta tanada. Hijabi ta saka tayi sallah sannan tayi addu'a ta miƙe. Sai da tayi shara ta wanke kwanukan da suka ɓata daren jiya, sannan ta sake wanke ƙafafunta ta shiga ɗaki. Sai da ta ɗan jira lokacin da zata iya fitowa ya yi sannan ta ɗaura hijab daidai gwargwado a jikinta. Duk da yunwar da ke damunta, bata tsaya neman abinci ba, zuciyarta cike take da burin sauyi a cikin rayuwarta. Mama ta yiwa sallama bayan ta sanar da ita cewa a makaranta ake kiranta. Ta fito daga ƙofar gidan su tana tafiya da ƙafafunta marasa takalma masu kyau, dan a fuska idan ka ganta ba zaka ce itace mai wannan takalmin a ƙafa ba. Sai dai ita Ameerah ma cikin zuciyarta tana tafiya ne da takalman alfahari ne ba wai wanda ake gani a zahirance ba. Tana ji a jikinta cewa rayuwa zata canza mata. Jin daɗi zai wanzu, walwala da nishaɗi zasu saukar mata. Ko dai yau, ko ta cikin wannan damar domin tana ji a jikinta cewa ita ɗin wata abace a cikin al'ummarta.
A ƙafarta ta ke duka wannan tafiyar duk da uban nisa dake da inda tabaro zuwa inda zata je. Toh ya zatayi idan bata taho da ƙafarta ba? Wa ta ajiye da zai kawo ta? Naira nawa gareta da zata share mata wannan wahalar da tayi dan a kawota a sauƙaƙe? Sisi bata da dashi, haka ma iyayenta babu wanda ya bata bare ta sa ran zata riƙe koda naira biyar ne. Yanayin da rana ta fara hango hasken safiya, gari ya haskaka mutane suna ta hada-hadar su. Ameerah ta isa makaranta cikin gajiyayyen takunta, amma zuciyarta cike ta ke da kuzari da ƙuduri mai girman gaake. Makarantar bata cika sosai ba, saboda yawancin yara basu fara shigowa ba. Ta samu waje ta zauna a ƙarƙashin ɗanyer bishiyar da ke bakin harabar makarantar ta riƙe jaka tana sauraren bugun zuciyarta. Can kuwa sai ga Malam Sa'idu, wato malamin lissafi ya fito daga ofishin malamai domin ya hango ta. Nan da nan ya nufe ta da murmushi a fuskarsa yana cewa.
"Ameerah yau kam Allah na tare da ke. Na ga sunan ki cikin jerin waÉ—anda za a yiwa jarrabawa, idan har kika ci wata kungiya za ta É—auke ki gaba É—aya karatu har iya inda kike so...." Ameerah ta runtse ido hawaye na tsiyaya a hankali daga gefen fuskarta. Bata ce uffan ba sai zuciyarta da taji tana ta tsalle. Malam Sa'id ya ce,
"Kada kiyi kuka Ameerah. Ki tsaya da ƙarfinki wata rana za ki tuna yau ne ranar da rayuwarki ta fara canzawa." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da abinda ya gaya mata, kafin ta fara waige-waige ko zata hango sauran abokanta da a koda yaushe suna tare. Bata tsaya biya musu ba saboda ta ƙagu ne a lokacin da ta fito daga gida, burinta kawai ta ganta cikin makaranta wanda hakan ne ya faru. Bata kai ga juyawa ɗaya ɓarin ba, malam Sa'id na barin wajan ta hango mutanan nata, cikin sauri ta saki murmushi tamkar ba itace ke zubar da hawaye ba. Tashi tayi ta nufi wajan su.
"Munje gida Mama tace kin taho." Yaseer ya faÉ—a yana kafeta da idanuwa. Ameerah ta É—an yi murmushi kawai tana janyo hannun Meenal. Sai da suka samu waje suka zauna kafin tace.
"Na kasa zaman gidan ne, kuma bansan kuma anje an sanar daku irin kiran da ake yi min ba shi yasa na kasa biya ku gabaki É—aya zuciya ta tayo nan." A nan Ameerah ta ke sanar dasu yadda malam Sa'id ya gaya mata.....
Hmmmmm Ameerah rai da buri, shin wane irin gida Ameerah ke burin ace ita ɗin ƴar nan ce? Masu karatu kuna hasaso mata kalarsa?😂