ƳAR KARUWA Chapter 24
Arewabook@ayshadansabo
Paid book
***
©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻
Chapter 24
Koda suka isa Abuja Arfah da driver ɗin Anty Khairy ne suka zo suka ɗauketa a train station ɗin,suna tafe a cikin motar Arfah da Jannat na hirarsu cike da murnar ganin juna kai kace sun shekara ne basu ga juna ba.Koda suka isa gidan Anty Khairy dake Apo a guje Jannat ta fice daga cikin motar lokacin da driver ya gama yin parking,sosai ta ƙosa ta sanya Yayar tasu a cikin idanunta domin sunyi missing ganin juna matuƙa.Tun daga downstairs ta fara ƙwallawa Anty Khairy kira,sai gata ta fito daga ɓangaren kitchen dake nan downstairs ɗin tana faɗin,"Oyoyo da mutanan KD,Jannat we miss u." Tayi maganar tana warewa Jannat hannuwanta fuskarta ɗauke da maɗaukakin murmushi.Da sassarfa Jannat ta isa gareta suka rungume juna Jannat na faɗin,"Anty Khairy i miss u too,where is my luv?" Khairiyyah ta saki murmushi tana sakin Jannat daga rungumar juna da sukai tace,"Mannar tayi bacci yau daru take ji sosai." Jannat ta narke face tace,"Ayyah!Lafiyarta lau dai ko?" Anty Khairy ta saki kyakykyawar murmushi tana faɗin,"Karki damu lafiyarta lau rigima ce kawai." Kafin Jannat tace komi Arfah ta shigo cikin falon riƙe da bag ɗin Jannat driver na biye da ita da luggage ɗin,daga bakin ƙofar shigowa falon ya aje luggage ɗin yana gaida Anty Khairy.Ta amsa da kulawa tana yi masa masa sannu,da kanta ta janyo luggage ɗin Jannat zuwa ciki tana faɗin,"Ya kika baro su Anty Rahman Jannat?" Jannat tace,"Lafiya lau Anty suna gaidaku duka,ita ma bikin cousine ɗinta za su yi shiyasa bamu taho tare da Feenah ba." Anty Khairy ta jinjina kanta tana nufan hanyar corridor ɗin da zai sadata da ɗakunan baccin biyu dake downstairs tace,"Allah sarki haka Arfah tace,Allah ya sanya alkhairy ya nuna mana ranar naku kuma,ki taho ki watsa ruwa kafin ki huta kici abinci karki biyewa surutun Arfah." Dariya Jannat ta saki tana rufawa Anty Khairy baya zuwa room ɗin da Arfah ke amfani dashi a gidan.
Arfan ce ta biyo bayansu riƙe da jakan hannu na Jannat tana faɗin,"Anty Khairy wato karta biye mini sabida ga aku sarkin taɗi ko?" Anty Khairy ta harareta tace,"Aikin ma fi aku surutu shiyasa ba za ki yi shiri da big Bro ba,ke taɗi shi miskilanci kinga akwai prob kenan." Arfah ta taɓe baki tace,"To ni dama ina ruwana dashi tunda baya yina baya janmu a jiki daga ni har Jannat da take miskila itama irinsa,ni wallahi Yaya Ammar miskilancinsa haushi yake bani Anty Khairy,kowa skull za ki ji yana faɗin suna good time da Brothers ɗinsu amma mu ban damu ni har mantawa nake ina da Yaya Namiji ma." Dariya sosai Anty Khairy tayi kafin tace,"Sorry Autan Mamie don shi ɗin ba mazaunin ƙasar bane shiyasa,amma karku damu komi lokaci ne but yana ƙaunarmu sosai fa,a hankali za ku samu kulawarsa duk randa ya tattaro ya dawo ƙasarsa da zama baki ɗaya." Jannat dake saurarensu bata sanya musu baki ba sai ta dubi Arfah taga yadda ta taɓe baki kafin Arfan tace,"Lokacin mu kuma mun kama gabanmu ba,ai kawai dai ayi sha'ani Anty Khairy." Anty Khairy ta maida dubanta kan Jannat da har lokacin bata ce komi ba domin kuwa bata da abin faɗi akan mutumin da take da tabbacin baya yinta ko ƙanƙani,darajar Inna da Abbah kaɗai take ci a gidannan har yake iya amsa gaisuwarta idan suna waje.Amma idan ma babu su ko gaishesa tayi sai dai ya ɗaga mata hannu kawai,ta rasa wace iriyar tsana shi da Mamie sukai wa Ummu da har ya shafeta sam basa ƙaunarta.Muryar Anty Khairy dake faɗin,"Sis tashi mana ki shiga toilet ki watsa ruwa wannan irin zafi da ake a Abuja." Jannat sai ta saki murmushi tana kai hannu ta zare rolling ɗin dake kanta tace,"Okey Anty yanzu zan shiga,ai wanka sosai ma zanyi da ruwa mai ɗumi sabida marana sosai naji ya ɗaure yanzu." Cike da tausayinta suka haɗa baki wajen faɗin,"Sannu Jannat." Anty Khairy ta ɗaura da faɗin,"Har yanzu dai kina nan kina fama wannan azaban ciwon mara da laulayi idan kina period tamkar wata mai Yaron ciki?Allah ya baki lafiya gaskiya kina fama Sis Allah ya rabaki dashi cikin gaggawa." Jannat ta amsa kai tsaye da faɗin,"Ameen Anty Khairy thank you." Daga haka Anty Khairy ta fice daga ɗakin tabar Arfah da Jannat,Jannat na shirin tuɓewa ta wuce zuwa toilet."Bestyn Feenah kinga yadda kullum fatarki ki sake haske da glowing kuwa?Kodai kin sauya mai ne ko kuwa tsabagen gyarane ke fa mayyace wajen son gyaran jiki tamkar wata jinin shuwa haka kike jinki." Dariya Jannat ta saka kafin ta bankawa Arfah harara tana faɗin,"Waya sani ko jinin nasu ce,nidai wannan fata tawa tana shan surutu,babu wani mai dana sauya wannan dai da kika sani ne,kawai dai idanunku ne ke ganin fatata tana haske but asalin natural brown skin ɗina ne kwance saman fatar ke duk uban farin da kika ƙaro bakya gani Arfah?" Arfah ta jinjina kai tace kai tsaye," Bana gani wallahi,amma ke kam dai gaskiya kamar kullum sabunta kyawunki ake Jannat domin gani nayi kinfi sanda nazo KD har cika ma." Jannat tayi dariya sosai kafin tace cike da shagwaɓa,"Ke dallah sharrin wannan abin ne ina gamawa za ki ga na koma normal,ni wallahi da zan daina yin period da saina fi kowa farin ciki sam bani ƙaunarsa Arfah,amma idan na faɗi hakan sai su Momy suce banda hankali wai ai yin shine cikar lafiyata rashin yin matsalace,wahalar da nake sha ne bana so Arfah yanzu haka banda gasasshen fish bana jin komi gashi ku gidannan babu mai son shi sosai ina za a min ordering grilled fish mai kyau Arfah?" Arfah ta saki murmushi cike da jin tausayin yadda yanayin ke maida Jannat tace,"Karki damu bari nayo miki ordering grilled fish daga wani special restaurant sun iya fish ko wani iri ne either rousted,grilled or pepesoup." Ai jin kuma Arfah ta ambaci soup ɗin sai kwaɗayin kuma ya koma kansa,cike da zaƙuwa Jannat tace,"Yi mini ordern duka biyun Arfah duk wanda yamin shi zanci please kiyi yanzu may be ma kafin na fito na kintsa an kawo ko?" Arfah tace,"Nan da 40 minutes za a kawo In Sha Allah." Tana maganar ne tana saka order ɗin online domin sun saba yin ordering abubuwa daga restaurant ɗin a aiko musu gida musamman idan Anty Khairy ta tashi da kyuiyan yin girki idan Daddyn Manar baya ƙasar,sai kawai suyi ordering suci mai aikinta Diana kuma ta girka nasu ita da mai gadi da driver. Rigar wanka da pad Jannat ta ɗauka cikin kayanta ta nufi toilet ɗin,ganin hakan ya sanya Arfah ficewa daga ɗakin domin zuwa ta sanar da Anty Khairy cewa Diana ta samarwa Jannat wani abu mai yaji-yaji da za ta ci wanda bamai nauyi sosai ba,domin sunfi kowa sanin bata shiri da abinci mai nauyi sai kwaɗayi idan tana a halin period.Take Anty Khairy ta dannawa Diana kira ta hanyar kiran line ɗinta,bugu biyu ta ɗaga Anty Khairy ta bata umurnin dafawa Jannat ɗin slim pasta spaghetti,tace ayi amfani da tsokar kaza a kuma saka pepe sosai a ciki yadda zaiyi yaji sosai.
Tana aje wayar ta dubi Arfah tace,"Ai za ta ci wannan ɗin ko?Nifa tausayi take bani kamar wata mai ciki,gaskiya Allah ya rabata da wannan jarabar irinshi ne idan ta samu ciki da wuya bata yi fama da laulayi mai tsirfa kala-kala ba." Arfah tace cike da tausayin Jannat ɗin,"Wallahi Anty nima nasha yin wannan tunanin,nifa ban taɓa ganin irin hakan ba sai akan Jannat." Suka cigaba da tattauna batun har zuwa time ɗin da Diana ta kawo komi ta aje bisa dining table ta sanar da Anty Khairy cewa ta kammala,Khairy ta jinjina kanta tana sanar da ita abinda za ta dafa musu for dinner zuwa dare.Wayan Arfah aka kira alamun har an kawo fish ɗin,ta fice da sauri zuwa wajen bakin gate ɗin estate domin amso saƙon.
Time ɗin data shigo ta tadda har Jannat ta kammala shiri ta fito zuwa falo,tayi mata duba ɗaya tana kallon yadda light purple ɗin rigar shan iskar data saka ta amsheta."Besty ga fish ɗin fa kinji ƙamshi har ya fara cika wajen?" Arfah ta faɗi hakan tana wucewa da ledar zuwa dining area.Tashi Jannat tayi ta nufi wajen dining ɗin Anty Khairy na tsokanarta da cewa wannan karon kuma kwaɗayin fish ya zaɓa daga dirowa Abuja,murmushi kawai Jannat tayi tana isa wajen dining ɗin taja kujera ta zauna.Koda Arfah ta juye mata soup ɗin manyan catfish dake faman turiri aroma ɗin kawai ya sanya yawunta sake tsinkewa,tayi saurin saka spoon ta ɗebo takai bakinta tana lumshe idanunta sakamakon ƙamshi da taste ɗin daya tsara kwanyarta.Kular da Diana ta zubo jallof ɗin slim pasta ɗin ta buɗe,ta ɗebi kaɗan ta zuba soup ɗin fish ɗin daga gefe ta miƙe ta isa cikin falo domin su cigaba da hirarsu da Arfah da Anty Khairy.
*********
INSTANBUL
Yawo sosai Mamie sukai yau a cikin garin INSTANBUL domin Nawaf ya zaga dasu wurare da dama,musamman shopping malls domin sun yi sayayya sosai ganin kuɗin banza danƙare a asusun ajiyar A.Chiroma.
Basu dawo gida ba sai to 6pm na yammaci,sun samu gidan a buɗe ga motar Ammar Chiroma da suka gani a fake tabbacin ya dawo gidan kenan.A gajiye suke sosai hakan ya sanya Labibah yin gaba ta riga Mamie shiga daga ciki wacce ta tsaya taya Nawaf kwaso jakunan sayayyan da sukai,tana shiga cikin falon idanunta suka sauka akan Ammar Chiroma dake zaune daga ƙasan carfet ya baje takardu yana zane.TV a kunne yayi ƙasa da volume sosai alamun baya son hayaniya ko kaɗan,daga gefensa bowl ne daya zubo yankakkun Apple yana ci.Bata yi sallama ba time ɗin data sanya kanta cikin falon domin bata yi zaton ganinsa a cikin falon ba,hakan yasa koda tayi masa sannu baiko ɗaga kai ya kalleta ba bare ta sanya ran zai kulata.Itama bata zafafa ba tayi wucewarta zuwa ciki tana sakin ƙaramin tsakin da Ammar Chiroma saida ya jiyota,hakan ya sanya shi ɗago manyan idanunsa ya rakata da ido yana jin wani irin takaici da haushin Yarinyar na sake cika zuciyarsa.
Shigowar Mamie tare da Nawaf niƙi-niƙi da bags ɗin shopping ya sanya Ammar saurin miƙewa ya isa wajen Mamie ya amshi bag's ɗin dake riƙe a hannunta yana faɗin,"Mamie sannu da zuwa,gaskiya yau kun sha yawo." Mamie ta sakin masa murmushi kafin tace,"Ai Allah ya yiwa Nawaf albarka har inda ban taɓa takawa a ƙasarnan ba yau ya kaini,ai gobe babu inda za mu fita hutawa za mu yi a gida sai ana gobe za mu tafi ma sake fita yin sayayyan tsaraba." Kai kawai Ammar ya jinjina yana amsa gaisuwar da Nawaf ke masa.Ciki Mamie ta shige itama tana sanarwa Ammar cewa ta gaji sosai wanka take buƙatar yi,yayi mata a fito lafiya ya koma inda ya taso ya zauna ya cigaba da aikin zenensa.Nawaf ne ya gama shigo da duka kayan yayi sallama da Ammar Chiroma ya bar gidan,bayan wucewarsa babu jima Ammar ya tattara komi nasa ya wuce zuwa room ɗinsa domin baya buƙatar wannan mara kunyar Yarinyar ta fito ta sake taddashi cikin falon.
Tunda ya shige su Mamie basu sake jiyo motsinsa ba,domin har suka yi wankansu suka sauya shiga suka fito zuwa falon basu ji motsinsa ba.Labibah ce ta gama shigewa da kayan zuwa room ɗinsu bayan sun baje wasu anan cikin falon sun sake duba zaɓen da sukai,koda suka gabatar da sallar magriba da Isha'i suka sake fitowa falon still babu ɗuriyar Ammar Chirom.
Mamie ce ta wuce zuwa kitchen ta dafa musu jallof ɗin Macaroni data tayi amgani da niƙaƙƙen nama da veggies a ciki,girkin yayi daɗi sosai sabida yadda dahuwar yayi ruwa-ruwa ta kuma saka isasshen naman kaza a ciki bayan niƙaƙƙen naman.
Labibah ce ta biyo bayanta ta markaɗa musu fruit ta juye cikin jug ta saka ice yadda zai ɗauki sanyi sosai,kamar za ta ɗebi soyayyen naman ragon Ammar tayi masa warming sai wata zuciyar ta kwaɓeta domin tana da tabbacin gwasaleta zai yi bazai ci ba.Koda suka shirya komi bisa dining table waya Mamie ta ɗaga tayi kiransa akan ya fito suyi dinner ɗin tare,amma buɗar bakinsa sai cewa yayi bazai ci Macaroni ba nama da milk kawai zai ci shima sai zuwa can anjima yana gudanar da wani muhimmin aiki ne.Mamie ta kashe wayarta don tsananin takaici komi bata iya ce masa ba,saida ta aje wayar tukun ta dubi Labibah tana faɗin,"Halin Ammar sai shi daughter,ko anyi auren nan sai kinyi haƙuri dashi domin yana da murɗaɗɗan hali." Baki kawai Labibah ta taɓe kafin tace,"Hmm! Mamie ya zanyi tunda ina son shi ai haƙuri ya zama dole,koda muka dawo fa dana shigo ko kallo ban ishesa ba Mamie,nayi masa sannu ma amma duk da hakan banci arziƙin daya ɗaga ido ya dubeni ba,gaskiya Baby yana da damuwa." Mamie cike da takaici tace,"Allah ya shirya mini shi Labibah,gabaki ɗaya gani nake kamar ana sake sauya mini shi,wannan ziyarar dana kawo masa naga sauyin yanayi a tattare dashi sosai,amma zuciyata na bani cewa duk akan soyayyar Yarinyar da yace ta mutu ne,koma miye In Sha Allah da zaran kunyi aure zai samu cikakkiyar walwala."Suka cigaba da tattauna batun kafin suyi serving kansu su fara cin abincin cike da nutsuwa.Suna kammalawa Labibah ta miƙe tace da Mamie za ta shige ciki domin yau ba za ta tsaya yin hira ba kwanciya zatai da wuri idan ta gama waya da Momynta,Mamie ta jinjina kanta tace,"Shikenan daughter nima waya nake son yi dasu Khairy da kuma Abbah dana gama zan shigo idan Ammar ɗin bai fito ba.Labibah tayi wucewarta tana faɗi a zuciyarta cewa,"Kyadai ji dashi Mamie,nikam yau banda time ɗinku." Koda ta isa room ɗin zubewa tayi bisa bed ta fara neman line ɗin Hajiya Barirah domin ta shaida mata irin sayayyan data yo musu da uban kuɗin da aka ja.
Daga can falon Ammar Chiroma kuwa Labibah na wucewa ta gyara zamanta bisa kujerar dining ɗin ta saka kiran layin Hajiya Amina Mansur Bichi,matar da suka shafe fin shekara basu yi waya ba kasancewar tasu ba wani zuwa ɗaya yayi da Mamien ba.Ita Hajiya Amina macece mai sanyi amma kuma tana da zafi idan an taɓata,tana da tsananin kirki da son takala sam matsayinta da kasancewarta ƴar babban attajiri kuma mata ga Prof Bichi da kowa yasan Allah ya hore masa arziƙi hakan baisa ta fito a mai girman kai da ƙyamatar talaka ba.Ita kuma Mamie tana hali na disgi da ɗaukar duk wani talaka a bakomi ba,kuma ita karan kanta ƴar talakar ce domin Ubanta saida gwanjo yake a kasuwa har ya bar gidan duniya.Yanayin yadda Hajiya Amina ta karanci halayyar Mamie ya sanya take baya da ita,hakan yasa amincin dake tsakanin Prof ɗin da Abbah yafi ƙarfi saɓanin su matayensu da babu shaƙuwa mai zurfi a tsakaninsu sosai gaskiya.Tana saka kiran line ɗin ne tana fata da addu'ar cewa Allah dai yasa Hajiya Ameena na amfani da line ɗin bata sauya wani ba,sai dai cikin sa a sai gashi kiran ya shiga har ya fara ringing.Cikin sauri ta saka wayar a speaker tana sake gyara zamanta da ɗokin son Hajiya Meenah ta ɗaga kiran,sai da yayi ringing sau uku sassanyar muryar Doctor Ameena Damaturu ya doki kunnuwar Hajiya Mardiyyah.Cikakkiyar likitar Yara ce dake aiki da asibitin Mallam Aminu Kano Teaching Hospital,tana da ƙwarewa sosai a fanninta domin har ta kai matsayin cikakkiyar Consultant."Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh." Doctor Ameena ta furta kalmomin cikakkiyar sallamar addinin musulunci zuwa ga Hajiya Mardiyyah.Mamie ta amsata tana ɗaurawa da faɗin,"Doctor kina magana da Hajiya Mardiyyah ce ta Jos." Take Doctor Ameena ta shaida muryar Mamien,hakan yasa cikin sauri tace,"Ayyah! Hajiya Mardiyyah so sorry please nayi loosing contact ɗinki ne sanadin canjin phone da nayi,ya kuke ya kwana da yawa gaskiya bama zumunci hakan bai kyautu ba." Mamie ta washe baki tana ɗaukar wayarta ta miƙe tsam ta baro ɓangaren dining ɗin zuwa cikin falo,domin tana jin cewa za ta fi samun sakewa tayi wayar anan ɗin."Bari kawai Doctor wallahi mun bari sheɗan kam yayi galaba a kanmu wajen watsar da juna ko gaisuwa ta wayan ma ya garara,yanzu ɗin ma cewa nayi bari na gwada kiran line ɗin na ji ko kina amfani dashi har yanzu." Cewar Hajiya Mardiyyah tana sauraron jin ta bakin Doctor Ameena ɗin."Allah sarki aiko ina amfani dashi ai bazan iya rabuwa da wannan line ɗin ba Hajiya Mardiyyah,ya Yaran namu yasu Hajiya Inna kowa dai lafiya ko?" Doctor Meenah ta tambaya tana tuna karamci irin na Hajiya Inna ɗin a lokacin da Prof ke yawan kaita Jos ana ziyartar juna.Mamie tace cikin fara'a,"Kowa lafiya lau Doctor,Hajiya suna Umrah ita da Abban ina ga sai sun samu sati biyu za su koma Jos,nima gani a INSTANBUL na kawowa ɗanki ziyara ne tunda shi baya damuwa da zuwa ganin gida kamar wanda akaima sammu akan ya tsani mahaifarsa." Mamie ta ƙare maganar cike da marairaita.Daga ɓangaren Hajiya Aminah kuwa cewa tayi,"Subhanallah Mardiyyah ki daina faɗin hakan,kawai may be yanayin aikinsa ne kinsan aiki a irin waɗannan ƙasashen yana da wahala domin kusan dukkanin lokutan da kake dashi kake sadaukar musu musamman aiki a ƙarƙashin manyan companies irin nasu Ammar sam basa samun lokacin kansu,na sha ji Shureim na yabon irin ƙwazonsa da baiwar fikrarsa da yasa suke farautarsa a kamfononi da yawa akan yayi aiki dasu godiya za ki ma Allah ba yawan ƙorafi ba." Mamie ta sauke numfashi tace,"Hakane kuma Ameenah kin fini gaskiya,yanzu haka gashi can ɗaki yana faman aikace-aikace ko fitowa yayi dinner baiyi ba,ai kira nayi mu tattauna wani batu game da haɗin zumunci dasu Abbah ke son ƙullawa tsakanin Shureim da ƴar wajen Nuratu."Cikin sauri Mamie ta jiyo Hajiya Ameena tace,"Ƴar wajen Nuratu fa kikace Mardiyyah? Mamie ta jinjina kai tamkar Doctor Ameena na gabanta kafin ta buɗe baki tace......✍🏻