ƳAR KARUWA PART 1

ƳAR KARUWA Chapter 25

by @ayshadansabo

Arewabook@ayshadansabo

Paid book

***

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Chapter 25

"Eh Hajiya Ameena ita ɗin fa,kinsan har an kawo kuɗin gaisuwa da kayan saka rana aka fasa batun auren nata da Yaron wajen Sanata Wase na nan Jos,sabida Uwarsa tace bazai auri ƳAR KARUWA ya haɗa jininsa da jinin fasiƙa ba." Mamie ta dakata da maganar tana son jin me Hajiya Ameena za ta ce?Ga tsanin mamakinta numfashi Doctor Ameena taja kafin tace,"Ikon Allah!Amma Prof bai sanar dani cewa ɗiyar Nuratu bace,yana dai ta yabon nutsuwar Yarinyar kamar yadda shima Shureim ɗin naji yana yabon Yarinyar a wajen Mahaifinsa,kinsan Shi ma naso muyi haɗin zumunci ne ya auri ɗiyar Yayata to sai akai rashin sa a da akai gwajin jini sai aka samu akasi idan sukai aure za su yi ta haihuwan sicklers ne sai kawai aka haƙura domin haƙura da junan shi yafi." Mamie da duk ta ji bata ji daɗin yadda Hajiya Ameena bata nuna jin zafin cewa ƳAR KARUWAR data tsana ce za a haɗa Shureim aure da ita ba sai ta wayance da faɗin,"Allah sarki Doctor gaskiya haƙura da junan shi yafi,nima so nake Arfah su je ayi gwajin jinin ita da Yaron da za ta aura don musan matsaya idan akwai damuwa tun kafin a tsaida lokaci sai su haƙura da juna." Hajiya Ameena ta ƙarfafa Mamie akan cewa lallai kam ayi gwajin genotype gabannin tsaida ranar aure,sukai sallama da juna bayan Hajiya Ameena ta tabbatar wa da Mamie cewa za ta yi magana da Shureim ɗin shima akan maganar gwajin jinin,amma kasancewar Jannat ɗiyar Nuratu ce ita bakomi bane a wajenta tunda Yarinyar ta samu kyakykyawar shaidar cewa kintsatstsiya ce.

Jiki a mace Mamie ta kashe wayarta bayan sunyi sallama da juna tana sake jin zazzzafar tsanar Yarinyar na cika zuciyarta,domin taso ace Doctor ɗin ta nuna rashin goyan bayanta domin ta samu hanyar rura wutar ƙiyayyar abin har sai maganar ya rushe,amma sai gashi Doctor ɗin ta gwasaleta.Tana shirin saka kiran Aminiyarta Hajiya Barirah domin labarta mata komi sai ga Ammar Chiroma ya fito,wannan karon da alamu ya sake yin wanka ne ya saka kayan bacci masu taushi.Kalar kayan sea blue ne da yayi masifar yi masa kyau,daddaɗan ƙamshinsa kawai ke tashi a jikinsa yana buɗe duk inda ya gifta.

"Mamie barka da hutawa." Ya faɗi hakan yana zama kusa da Mamie idanunsa akan fuskarta yana karantar yanayi na damuwa dake kwance a saman fuskarta.Ta dubesa a nutse tace,"Sai yanzu ka kammala aikin ka fito,meyasa kake wasa da cin abincin dare Ammar? Yau ma kana nufin nama da Madara kaɗai za ka ci ka kwanta bacci anya kuwa Ammar?" Murmushi kaɗan Ammar Chiroma ya saki kafin ya furta,"Mamie zan haɗa da noodles amma da kaina zan dafa." Ya faɗi hakan ne domin baya buƙatar ma Mamie tace za ta janyo masa wannan Yarinyar tace ta dafa masa don bazai ci ba.Tuni Mamie ta gano manufarsa hakan ya sanya ta taɓe baki tace,"Hmmm! Duk dai kayi ka gama Ammar,sai ka tashi kaje ka dafo ai ina nan ina jiranka kayi warming naman har dani zanci." Kai kawai Ammar Chiroma ya jinjina yana miƙewa tsaye ya nufi hanyar kitchen.Mamie ganin hakan ya sanya ta fara neman layin Abbah vedio call,sun jima suna magana da Abban ya sanar da ita cewa next week za su koma gida 9ja.Itama Mamie ta shaida masa cewa nan da 3days za su koma Jos domin Ammar baya maraba da zuwanta,dariya kawai Abbah yayi mata yana tsakonarta da cewa sunfi kusa da Yaron nata ai.Mamie ta aje wayarta tana sakin murmushi zuciyarta cike da kewar mijin nata,sosai taga ya ƙara mata wani irin kyau da yin fresh.

Ammar ne ya shigo cikin falon hannunsa ɗauke da tray ƙarami daya ɗauro plate dugu biyu na noodles da kuma naman da yayi warming,daga gefe guda kuma kwalin milk ɗinsa ne da yayi sabo da shan abarsa babu dare babu rana matuƙar yana gida ne a zaune.

Daga tsakiyar kujerar 3seater da Mamie kekai ya aje tray ɗin tare da zama yana faɗin,"Mamie ko in sauke mana daga ƙasan carpet ne?" Mamie ta jinjina kai tana faɗin,"Gaskiya kam zai fi." Sauka yayi da tray ɗin zuwa ƙasan tsakiyar carpet ɗin yana ɗaukan plate ɗin noodles ɗinsa daya dafa ya fara ci domin baya buƙatar ya huce bai ci ba,Mamie sakkowa tayi ta iso wajen ta zauna tana jin wani daɗi da ƙaunar tilon Yaron nata na sake mamaye zuciyarta.Tunda suka zo yaune karon farko da sukai irin wannan zaman za su ci abu tare kuma fuskar Ammar Chiroma ɗin na cike da annuri ba kamar ɗazu da suka dawo yadda ta samesa yayi ciɗin-ciɗin da fuska ba,ta kai hannu ta ɗauki yankan naman da yayi rau da zafi tamkar yanzu aka soya shi takai baki.Daɗin suyan da kuma na yajin da Ammar Chiroma ya baɗa a samansa ya ratsa har kwanyarta time ɗin data tauna naman ta haɗiye tana aje ganinta akan Ammar tace,"Son nan da 3days za mu wuce tunda naga alamar baka yi farin ciki da ziyarar dana kawo maka ba wannan karon." Ammar Chiroma ya wani shagwaɓe face kafin yayi magana cike da zallar aji da yin ƙasa da muryarsa sosai yace,"Mamie nifa nayi farin ciki kawai dai naso ace ke kaɗaice kika taho,ina laifin ma idan ƴar rakiyar kike nema kizo da Auta ko Khairy nasan mijinta bazai hana ba Mamie." Mamie tace cike da taɓe baki,"Hmmm! Sai kace kana sakewa Autar fuska kaida ko fara'arka bata gani,to tana skull kuma suna dab da fara exam na final year ɗinsu shiyasa bance zan taho da ita ba,Khairy kuwa itace bata yi sha'awar zuwa ba amma karka damu za mu dawo tare kafin ayi bikinku da Labibah domin na ga shagunan saida Abayas daya kamata ace munzo mun sayi na sakawa a lefe." Ammar ji yayi kansa ya wani sara masa domin ko kaɗan baya son Mamie tana tuna masa da zancen cewa wai ya amince da batun auren Labibah,cike da son abar zancen yace,"Mamie yaushe Abbah za su koma gida daga Umran yau duk bamuyi waya dasu ba daga shi har Inna." Mamie data gano so yake abar wancan batun sai ta danna masa harara tana faɗin,"Next week yace,za ka je ne idan sun dawo ɗin?" Da sauri Ammar ya girgiza kansa kafin ya buɗe baki yace,"No Mamie ba zan je 9ja nan kusa ba." Takaici ya sanya Mamie yi masa shuru ta cigaba da cin namanta shi kuma ya ƙarisa cinye noodles ɗinsa.Falon ya ɗauki shuru kafin kiran Khairiyyah ya shigo cikin wayar Mamie domin tunda suka taho duk dare sai sunyi waya da Khairyn,ganin ba vedio call bane ya sanya Mamie saka wayar a speaker ta aje a saman laps ɗinta tana amsa sallamar Khairiyyah.

Sassanyar muryar Khairy ya sake ratsa kunnuwarsu time ɗin da take faɗin,"Mamie Auta ce take son yin magana dake gata kusa dani." Mamie tace,"Lafiya dai ko,badai wata rigimar bace nifa bana son rigimar Arfah bata wayar." Muryar Arfah ta jiyo a maimakon na Khairyn Arfah na faɗin,"Mamie bafa wata rigima ina yini ya ISTANBUL and Yaya A?" Mamie tace a taƙaice,"Lafiya ya kuke?" Arfah sai ta shagwaɓe murya tace,"Lafiya lau Mamiena maganar kuɗin da kika ce za ki turo ne naji shiru Mamie gobe nefa Dinner ɗin,baki ga yadda ɗinkinmu yayi kyau ba ɗazu Jan ta iso mana dashi,gaskiya ba ƙaramin kyau za mu yi ba." Mamie ta taɓe baki tamkar Arfah na gabanta kafin tace a zafafe,"Kedai kika sani da jaye-jayen tsiyarki sakarya kawai,kuma wallahi ina sake jaddada miki idan Nuratu tazo garin nan kika bi Ƴar Karuwarnan zuwa wajenta ban yafe ba,kuɗi kuma ba Abbah yace shima kin amshi kuɗi hannunsa ba?" Arfah nan da nan ta sake shagwaɓe murya tace,"Mamie kuɗin make-up ne fa ya turo mana kinsan dai yadda komi ke tsada a Abuja,please Mamie ki turo min ko 30k ne kinji?" Mamie tace,"Naji ba Khairiyyah wayarta mai ya hana ki kira da wayarki ke?" Arfah ta narke murya tace,"Jannat ke amsa call dashi ta bar wayarta a ɗaki ne shine Feenah ta kira ta line ɗina suke magana gashi nan ta gama bari ku gaisa ma Mamie." Kafin ma Mamie ta kaiga hana Arfah baiwa Jannat wayarta har ta riga ta miƙa mata domin dama suna zaune ne dab da juna.Sassanyar muryar Jannat mai wani irin zaƙin amo ne ya doki kunnuwar su Mamie time ɗin da take faɗin,"Mamie ina yini ya Turkey dasu Yaya Ammar?" Mamie ta haɗiye takaicinta tace,"Lafiya lau,dama ina so in miki gargaɗin cewa ko Karuwar Uwartaki tazo karki sake kice za ki ɗaukar mini Arfah ki kaita wajenta kina jina ko?" Jannat cikin rawar murya tace,"Ina ji Mamie In Sha Allah hakan bazai faru ba Allah ya baki haƙuri." Daga haka Jannat ta miƙawa Arfah wayar.Muryar Arfah Mamie ta jiyo tana faɗin,"Mamie why? Don Allah meyasa hakan?" Mamie tsawa ta dakawa Arfah tana faɗin,"To Uwata tuhumata kike? Maza baiwa Khairy wayarta shashasha kawai." Muryar Khairiyyah da Mamie ta jiyo shiya bata tabbacin Arfah ta bata wayar,Khairy cike da kwantar da murya itama tace,"Mamie why?Meyasa zaki ce mata hakan,gashi yanzu ta bar mana falon ta nufi ɗaki kuma nasan kuka take,don Allah Mamie ki rage ci mata fuska akan Ummu please!" Mamie cike da zallar takaici tace,"Au kema tuhumata kike Khairy?Anya ko Nuratu bata lashe min kurwarku ba kuwa? Tunda naga tamkar mayya haka take duk zuciyar data kama bata sakinsa cikin sauƙi,to bari kuji har abada bazan taɓa ƙaunar Nuratu da jininta ba,don haka Kudai da kuka ga za ku iya nunawa shegiyar Yarinyar ƙauna ku da Ubanku sai kuyi tayi,kuma wallahi idan kika bari Arfah ta je wajen Nuratu duka ke da ita ban yafe muku ba." Yadda Mamie tayi furucin a matuƙar kausashe ba ƙaramin baiwa Khairy tsoro tayi ba.Ba kuma Khairyn kaɗai ba hatta da Ammar Chiroma dake sauraren komi furucin ya doki zuciyarsa matuƙa,Khairy haƙuri kawai taba Mamie sukai sallama da juna.Koda Mamie ta kashe wayar idanunta ta mayar kan Ammar Chiroma tana kallon yadda mood ɗinsa ya canza,domin ya haɗe face babu wannan annurin dake saman face ɗinsa a ɗazu.Cike da mamaki ta tambayesa,"Ammar lafiya naga ka wani haɗe face?"Cikin ƙasaitacciyar muryarsa can ƙasa ya furta,"Mamie meyasa Arfah ke da rawar kai har haka ne,kece kike shagwaɓata da wani kalmar Auta tana rashin kunya ko?" Mamie tace cikin sauri,"Ka barni da ita indai akan Ƴar Karuwarnan ne zan bata mamaki,na rasa meyasa take jarabar son Yarinyar kodan tare suka tashi tun suna ƙananu? Ammar bana son Nuratu bana son duk wani abu daya danganceta don haka bana fata kabi sahunsu wajen nunawa ɗiyar cikinta ƙauna har abada." Ammar ya dubi Mamie da wani yanayin da ba za ta iya fassara shi ba kafin ya jinjina kansa yace,"Okey Mamie karki damu,kema kinsan bana yinsu ko ƙanƙani,but Mamie basai kin dinga nunawa a zahiri ko kina yawan magana ba,ki daina kula Yarinyar da maganganu irin yadda kikai za ta rainaki ne watarana."Mamie tayi kasaƙe tayi tana duban Ammar Chiroma wanda yaci serious alamun tabbatar da kalamansa,kwanyarta ta tafi tunani na wucin gadi kafin ta jinjina kanta tana faɗin,"Barirah tasha faɗa mini hakan Ammar amma na kasa dainawa,sam ban iya ɓoye ƙiyayyar abu a cikin zuciyata ba musamman na ƳAR KARUWARnan wacce Abbanku ya ɗauki son duniya ya ɗaura a kanta,gabaki ɗaya soyayyar da yake gwada mata ko kai da kake first born baka samu kulawa irin yadda yake bata ba,na tsaneta tsana irin wacce bazan taɓa iya misaltawa ko gogeshi daga cikin zuciyata ba Ammar." Ammar ya jinjina kansa yana jin wani irin ɗaci na cika zuciya da maƙoshinsa,cikin wani irin sanyin murya ya furta,"Mamie kiyi haƙuri ki koyi danne komi a ƙarƙashin zuciyarki wannan shine koyarwa ta addini,domin babu kyau zurfafa ƙiyayyar mumini ɗan uwanka,ko Abbah ki daina nuna masa bakya ƙaunar jinin ɗan uwansa domin Abbah Kabeeru ya nuna mini ƙauna Mamie ke kinsan hakan,don Allah kiyi haƙuri ki ɓoye komi a cikin zuciyarki please Mamie kinji?" Cike da gamsuwa da kalamansa Mamie ta jinjina kanta tace,"Naji Ammar Allah ya bani ikon iya yin hakan,yanzu dai mu koma kan batunka da Labibah ka amince a haɗa aurenku tare da nasu Arfah ko kuwa da zaran mun koma a aje magana a fara gabatar da naku?"Mamie ta ƙare maganar tana zubawa fuskar Ammar Chiroma data sake haɗewa tamkar baƙin hadari idanu.Tamkar bazai ce komi ba sai kuma ya numfasa tare da haɗiye wani abu mai ɗaci a maƙoshinsa,cikin zuzzurfar muryarsa da wani yanayi ya sake maida shi can ƙasa sosai yace,"Mamie abar shi a haɗa gaba ɗaya domin Abbah ma hakan yace,kuma ina da buƙatar na sake nutsuwa nayi nazarin yadda zan koyawa zuciyata yadda za ta amshi wata mace bayan Angel Mamie." Yadda ya ƙare maganar cikin wani irin karyayyen sauti ba ƙaramin dukan zuciyar Mamie hakan yayi ba.Ta ƙuresa da kallo tana tambayar,"Ammar wacece kuma wata Angel?" Sai kuma data jefa masa tambayar ta tuno da zanen data gani a ɗakinsa da kuma kalaman da suka tattauna dashi akan zanen.Muryarsa ta sake jiyowa can ƙasa yana faɗin,"Mamie itace wacce nace miki ta mutu." Ya ƙare maganar yana maida idanunsa ya lumshesu wani zazzafar yanayi na sake bin jinin jikinsa.Cikin kwantar da murya Mamie ke rarrashinsa da kalamai na ban haƙuri tana sake nusar dashi cewa da zaran anyi aurensu da Lalibah zuciyarsa za ta manta da waccan ta amshi Labibah,don haka yayi haƙuri ya baiwa zuciyarsa damar da za ta so Labibah koda rabin son da yayi ma matacciyar data riga tabar gidan duniya ne.Ammar Chiroma da har lokacin idanunsa suke a lumshe baisan lokacin daya buɗesu ya sauke ganinsa akan Mamien ba,ganin yadda idanunsa sukai wani irin kaɗawa sai da ya baiwa Mamie tsoro.Cikin wani irin murya mai cike da rauni yace,"Mamie i can't,idan nace zan iya buɗewa wata zuciyata taso wata halitta bayan Angel nayi ƙarya Mamie,just pray for me kawai Allah ya rage mini zafin soyayyar da nake mata domin bana fata na cigaba da rayuwa ba tare da ragowar soyayyarta a cikin zuciyata ba." Kalamansa sukai masifar dukan zuciyar Mamie tare da ɗaure kanta ta shiga mamaki da tambayar kanta wace iriyar soyayyah ce Ammar Chiroma kewa Yarinyar haka?Shi kuwa Ammar yunƙurawa yayi ya miƙe tsaye yana jin yadda kansa ke wani irin sarawa da matsanancin ciwo,ya dubi Mamie data kasa sake cewa komi yace,"Mamie zan je na ɗan ƙarisa wani zane a computer gabannin na kwanta good night." Bai jira cewarta ba kuma ya nufi hanyar room ɗinsa cikin takunsa a nutse ya bar Mamie da bin bayansa da kallo tana mamakin wani irin so Ammar kewa Yarinyar,domin ta gano cewa da gaske zuciyar Ammar Chiroma ke ƙaunar Yarinyar data mutu.Jikinta a mace ta miƙe tare da haɗa plate ɗin da suka ci nama ta wuce dashi zuwa kitchen,koda ta fito wutar falon ta kashe ta nufi room ɗinsu tana mamakin yadda Labibah bata fito falon ba yau.

Shi kuwa Ammar Chiroma yana shiga cikin ɗakinsa direct wajen frame ɗin zanensa ya nufa,zama yayi daga bakin bed ɗin ya ɗakko frame ɗin yana sumbatar fuskar zanen gently.Wani irin yanayi ne ya shiga ratsa bargon jikinsa yana ji tamkar ana sake kewaye jinin jikinsa da soyayyarta ne,"When zan mallakeki Angel?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin wani yanayi mai zafi na sake hautsina zuciyarsa.Ya jima riƙe da hoton yana sumbata kafin ya aje ya nufi toilet,kansa ya sakarwa shower ɗumin ruwan na ratsa har kwanyarsa.Ya jima a haka yana gwama numfashi kafin ya ɗauro towel ya fito,kansa ya tsane da ƙaramin towel gabannin ya sauya wasu kayan baccin yayi light off yabi lafiyar gado.

********

ABUJA, NIGERIA.

"Besty don girman Allah kiyi haƙuri ki tsaida wannan kukan da kike yi,sai kace yau kikasan halin Mamie ko jin ire-iren Waɗannan cin fuskar data yi miki? Kiyi haƙuri Jannat wallahi zuciyata zafi take yi sosai,da ace Mamie ba Uwata bace tabbas da kinga irin action ɗin da zan ɗauka amma ni da ke duka dole haƙuri za mu yi mu cigaba da yi mata addu'a har Allah ya ganar da ita gaskiya ta gane cewa abinda take yi ba daidai bane Jannat,so please stop this crying kada kanki yayi ciwo please!" Arfah ke wannan maganar tana riƙe da hannun Jannat dake kuka sosai.Tunda ta shigo cikin ɗakin take kuka domin zuciyarta ta fara gajiya da irin ƙiyayya da cin fuskar da Mamie ke mata,me ta tsare mata cikin wannan duniyar data kasa ƙaunarta? Jannat ta tambayi kanta tana sake sakin wani irin kuka cikin low voice mai taɓa zuciya.Cikin muryar kukan ta dubi Arfah tace,"Arfah meyasa Mamie ta kasa ƙaunata ne wai,me muka tsare mata cikin wannan duniyar ni da Ummu da ba za ta iya yafe mana ta ƙaunaceni koda ba za ta ƙaunaci Ummu ba? Nayi danasanin zuwa Abuja yau Arfah domin kalaman Mamie sun doki zuciyata ban taɓa zaton ƙiyayyar da take mana ni da Ummu har ta kai za ta iya buɗe baki taja miki Allah ya isa idan har kika raɓi inda Ummu take ba,nasani Arfah,tabbas nasan Ummu mai laifi ce amma ina sonta a hakan Arfah,ina sonta duk girman zunubin da take aikatawa domin bani da tamkarta har abada,zan cigaba da yi mata addu'ar samun shiriya,but am sorry to say gobe zan juya inda na fito domin bazan so a kaina ace Mamie na furta za ta iya miki Allah ya isa ba Arfah,tunda dai na samu na halarci Kamun da akayi a ɗazu to basai nayi attending Dinner da yinin ba." Jannat ta kai ƙarshen kalamanta wasu zafafan hawaye na sake sulmiyowa daga cikin idanunta.Da gaske take yi har cikin zuciyarta take jin danasanin zuwanta Abuja ɗin,in don ta Ummu ce tasan cewa za ta iya binta har Kaduna suga juna kafin ta juya Lagos.Arfah da zuciyarta takai ƙololuwa wajen ɓaci da jin zafin Mamiensu ta dubi Jannat tana sake riƙo hannunta tace,"Wallahi Jannat babu inda za ki tunda har kika riga kika taho sai munyi bikinmu,don Allah kima daina faɗin hakan tun kafin ma Anty Khairy ta ji,nidai na baki haƙuri kan haƙuri don Allah ki yafewa Mamie ki daina saka damuwa a cikin zuciyarki akan irin ƙiyayyar da take gwada miki watarana sai labari Jannat,ta cigaba da cin darajarmu mu da Abbah please!" Jannat kanta kawai ta jinjinawa Arfah alamun taji ɗin.A hankali Arfah ta zaro tissue da kwalinsa ke aje saman side drawer ta shiga sharewa Jannat hawayen fuskarta,suna a haka kiran S.M Bichi ya shigo cikin wayar Jannat ɗin.Da fari cewa tayi ba za ta ɗaga ba saida Arfah ta rarrasheta sannan tayi receiving call ɗin,tashi Arfah tayi ta fice daga ɗakin zuwa wajen Anty Khairy tabar Jannat na amsa sallamar daya doko mata a narke.Da ƙyar ta iya bashi 20 minutes ta sanar dashi cewa bacci yazo kwanciya zatai,ba don ransa yaso ba ya barta bayan ya shaida mata cewa zai zo nan gidan Khairyn gobe kafin su wuce gidan su Farry ɗin.Amsa masa kawai Jannat tayi ta kashe wayarta tana sakin ƙaramin tsaki,domin zuciyarta zafi kawai take mata Mamie ta riga ta gama rusa duk wani farin cikin data shigo dashi garin Abuja....✍🏻

Assalamu alaikum!

*Masoya Labarin ƳAR KARUWA duka anan na kawo ƙarshen part 1 na labarin,wanda yazo muku a matsayin free pages.* Naso ƙwarai yafi haka yawa pages ɗin,but a hakan ma na duba nayi ƙoƙari lol

Basai Nace komi ba duk wanda yake bin labarin yasan cewa yanzu ne za a fara labarin da gasken gasken,don haka ku taho ayi tafiya ARCH.AMMAR CHIROMA AND HAFSAT KABEER CHIROMA tare daku masoya alƙalamin Aysha Ɗansabo.Kada ku bari ayi wannan tafiyar babu ku domin labari ne da nayi muku alwashin cewa zai ƙayatar tare da ilmantar daku ya kuma faɗakar akan tarin darussa na rayuwa dake cikinsa,sannan akwai zazzafar soyayya gami da zazzafar ƙiyayyar da zai taɓa zukata ya kuma nishaɗantar.

Part 2 na book ɗin wanda zai kasance paid pages zai fara zuwa muku on 20th of this month In Sha Allah,sai ku hanzarta domin ayi tafiyar tare daku.Masu bibiyar arewabook paid pages za su fara sauka bada jimawa ba,don haka aje ayi refill a cika wallet domin nunawa labarin ƙauna😍

Taku Aysha Dansabo ke cewa mu haɗu a part 2