001
by @jeeddah3256
TAREEQ IMAM
Na
Jeeddah Aliyu
001.
Matasan samari ne su uku ke tafiya kowanne su yana sanye da kayan ƙwallo sky blue in colour ga baki ɗayansu jikinsu jiƙe yake da gumi, alamar da ke nuna daga filin ƙwallon ƙafa suka fito. Shekarun su na haihuwa ba za su gaza 14-15 ba. Tun daga nesa kake ji tashin muryoyin su suna tafe suna firar yadda team ɗinsu yai nasarar lashe gasar da suka yi a yammacin yau. Ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance a tsakiya kuma shine gajere a cikinsu ya kalli na gefen hagunsa ya ce.
"Slugger ga fa mutuniyarka can ta dawo daga islamiyya da alama hango mu da tayi ne yasaka ta ƙara sauri."
Ya ƙarasa magana tare da pointing inda ya hango ƴar matashiyar budurwa ke tafiya cikin sauri jikinta sanye da uniform ɗin Islamiyya.
Murmushin mugunta wanda aka kira da suna Slugger ya yi har yana haɗawa da shafa sumar kansa wacce ya yiwa wani irin kalar ɗan iskan haircut, da ƙarfi ya shiga kwalla mata kira.
"Ke Nana zo nan! kina jina fa ki tsaya nace."
Ko juyowa Nana bata yi ba balle yasa ran za ta amsa mai sai ma ƙara saurin da tayi wanda har da ɗan gudu-gudu ta haɗa.
Gani haka yasa ya bi ta da mugun gudu dama shi gudu ba wuya yake mai ba tana gaf da isa gate ɗin gidansu ya cimmata, da ƙarfi ya cafko purple hijab ɗinta ya yi mugun jawo wuyanta da ƙarfi ya yi baya yayin da wuyan hijab ɗin ya yage a ƙoƙarin kwatar kanta da take yi. Hannunta na hagu ya damƙe cikin nasa shiyasa ya saki yagagge hijabinta.Ya shiga ja ta da ƙarfi ita kuma tana tirjewa a fusace ta ce
"Wai me na tare maka ne a rayuwa Tareeq da duk sanda muka hadu sai ka ci zarafina?"
Tai magana cikin rawar murya wacce ke nuna kowanne lokaci za ta iya fashewa da kuka.
"Ubanki kika yi min shegiya baƙar munafuka wato ke har kin manta abin da kika yi min ɗazu a school kina zaton kin ci bulus ko?"
"Ni fa ba wani mummunan abu nace akanka ba kawai dai na faɗawa Uncle Joel ne ya shiga tsakanina da kai kadaina taɓa min jiki saboda ni ba 'yar iska bace..
"Dallah rufewa mutane shegen bakinki mai mugun ɗoyi tsiya to da kika kai faɗawa Uncle Joel uba na ne shi da zai sa na fasa yi miki abin da zuciyata ta raya min?"
"Ba ubanka bane ba amma ai kana tsoronsa."
Nana ta faɗa cikin tsiwa, har tana murguda baki.
"Iyeee! lallai slugger ka yi sake yarinyar nan ta gama rena ka. Na rantse da Allah da nine ta ke gayawa haka da tuni na gaggaurawa shegiya maruka, da bakinta zai juye ya koma keya."
Cewar Fahad wanda suke wa laƙabi da suna Rooney kuma shi ne wanda ya fara hango Nana.
"Kam bala'in nan! Nana ni kike kira ɗan iska?"
"Ban faɗa ba amma Tareeq abin da kake min miye bambanci ka da ɗan iska?"
Tana rufe baki yana ɗauke ta da mahaukaci mari a kumatunta na dama tana ɗagowa cikin ruɗewa ya sake dallawa ɗayan kumatunta, na hagu ga baki ɗaya Nana ruɗewa tai ta rasa inda za ta tsoma ranta saboda maruka sun ratsa ta ba kaɗan ba. Da ƙarfi ya finciko ta ya haɗa ta da jikin bangon gidansu yasa gwiwar hannunsa a maƙogwaronta ya danne yayin da yasa ɗayan hannunsa ya yiwa 'yan matasan boobs ɗinta baƙar damƙa ya dinga matsa su, da iyakaci ƙarfinsa yana luguiguita su wani irin tsananin azaba da ya ratsa ƙwaƙwalwar Nana yasa ta tsandara ihu sai dai ihu nata bai fita sosai ba, saboda maƙoshinta da ya dafe Rooney da Lil-prince sai kyalkyalar dariya suke yi su na kashewa.
"Ci mana ubanta ka matsi 'yan biyunta son ranka gobe ko gani wata tayi za ta kai ƙararka gun Uncle Joel da gudu za ta hana."
Lil-prince ya faɗa yana sheƙewa da dariyar mugunta.
Rooney ne ya karɓe zance ta hanyar cewa.
"Bar Shegiya yau zata koyi darasi, ba dai taƙamarta kai ƙarar BBT ba {Bad boys team} yau za ki yaba wa aya zaƙinta, shegiya mai idanuwa kamar na mujiya."
Wata mota ce baƙa wulik ƙirar Corolla new model 2023 tazo ta wuce su har tayi nisa sai gashi direban motar ya yi reverse ya dawo, hakan ne ya jawo hankalinsu har suka kalle mamallakin motar cikin sauri Lil-prince ya furta.
"Slugger sake ta zo mu tafi ga tsohon munafuki can na gidanku mai siffar ƴan daudu ya tsaya yana kallanmu...
Tun kafin Lil-prince ya dasa aya suka ji muryar Uncle Hamza yana faɗin
"Kai Tareeq uban me kake aikatawa ƴar mutane a jikin bango?"
Sakinta Tareeq ya yi ta durƙushe ƙasa tare da rushewa da matsanancin kuka, da sauri uncle Hamza ya ɓalle murfin mota ya fito.
"Me kayi wa ƴar mutane Tareeq?"
"Abin da idonka ya gane ma?"
Tareeq ya yi magana yana gallawa Uncle Hamza harara.
"Kai dai anyi mugun ɗan iskan yaro kai kenan kullum cikin ɗaukowa iyayenka magana.
Uncle Hamza ya faɗa tare da ɗago Nana wacce har yanzu take gunshaƙin kuka.
"Daɗin abin Iyayena na ɗaukowa ba na wani ƙato ɗa shan miyar gidanmu ba,kuma ubana yana da arzikin da komai girman laifin da na aikata zai tare min dan haka ka fita sabgata babu ruwanka dani."
Sosai furucin Tareeq ya ɓatawa Uncle Hamza rai wato shine ƙato ɗa shan miyar gidansu, lallai me hana yau ya cin uban yaro nan sai ALLAH. A fusace Uncle Hamza ya yi kan Tareeq ya shaƙe masa wuyan jersey har sai da idanunsa suka firfito, Nana tana gani haka ta kwasa da gudu ta shiga gida.
Da ƙarfi Lil-prince da Ronney suka shiga ɓamɓare hannun Uncle Hamza daga wuyan rigar Tareeq wanda dakyar yake iya numfashi. Yana sakinshi ya dinga tari idanunsa suka yi jajir sai dai bakinshi bai mutu ba sai maganganu banza yake fadawa uncle Hamza ɗin
"Da ku bar shi ya dake ni yau kwano tuwonshi ya ƙare a gidanmu, dama na gaji da gani wannan mummunar fuskar tasa mai saka min tashin zuciya."
Tareeq ya yi magana cikin fitsara da zallan rashin kunya.
Ronney da Lil-prince suka sheƙe da dariya tare da kashewa, cikin ƙonar zuciya Uncle Hamza ya zuba musu ido sai huci yake tsananin ɓacin rai yasa ya kasa magana kamar ba zai daina kallonsu ba. Sai kurum ya yi kwafa tare da girgiza kai ya juya da sauri ya shiga motarsa.
Cikin ɗaga murya Tareeq ya ce.
"Banza kawai ɗan maula lokaci na zuwa da zan kakkaɓe ka daga gidanmu wawa kawai mai warin bunsuru."
Duk abin da yake faɗa a kunne Uncle Hamza bai mayar mishi da martani ba ya ja motarsa ya nufi gida.
"Gaskiya slugger idan ba ka tashi tsaye akan guy ɗinan ba ka ci ubansa cin goriba, ba zai sakar ma mara kayi fitsari ba."
"Bar shi kawai Lil-prince lokaci nake jira wallahi-azim sai nai masa mummunan wulaƙancin da ko kare ba zai ci ba."
"Da kyau na wajena ni nasan BBT basa ɗaukar reni."
Ronney ya faɗa yana wani bubbuɗawa.
Tareeq ya cire rigar jikinshi ya ɗora a shoulder yana faɗar "Ba don jersey ɗinan favorite ɗina bace ALLAH da sai na cina mata wuta saboda kawai hannu ɗan shegiya nan ya taɓa ta."
Ya ƙarasa magana yana wani yatsine fuska, dariya su Lil-prince suka sa dai-dai sun iso gate ɗin gidansu Ronney shaking hands suka yi da wani salo mai nuna rashin jin su a fili tare da faɗar sai sun haɗu anjima. Gidanje huɗu ne tsakanin gidansu Ronney da na su Lil-prince gidansu Tareeq shine a ƙarshen layi, yana zuwa tangameme gate ɗin gidansu ya ja yai tsaye ya shiga knocking abin mamaki gate maigadi ya buɗe masa alhali ga ƙaramar ƙofa ya bi amma tsabar iskanci da ɗaukar magana irin nasa sai dai a buɗe masa gate a cewarshi ƙafafuwanshi sun fi kowa ce mota da ke gidan daraja da tsada, saboda haka dole maigadi ya dinga buɗe mai gate.
"Sannu da dawowa magajin Daddy."
"Yauwa Ɗan Bala kaima sannu da tsare mana ƙofar gida."
Tareeq ya faɗa yana ɗagawa Ɗan Bala hannu, yana zuwa ƙofar da za ta sada shi da main parlour kasancewar ƙofar ta gilashi ce wacce alburushi baya hudawa{bullet proof}da zarar an tura ta da ƙarfi ƙarar alarm zai karaɗe ilahirin gidan shiyasa ya fizge ta da ƙarfi ta yadda ƙararta zai isarwa da duk wanda ke cikin main parlour ɗin shigowar shi duk gidan shi kaɗai ne mai wannan ɗabi'a shi kuma yana yi ne saboda kowa ya kama kansa, gudun kada ka shiga gonarsa ya shuka ma rashin mutuncin.
Kyawawan 'yan mata su Uku ya tarar zaune cikin parlour ɗaya tana operating wayarta yayin da biyu ke kallon Big brother Naija yadda ya rufu ƙofar ne ya firgita su saboda kowacce ta shagala da abin da take yi kamar daga sama suka ji ƙarar duk dai in da sabo sun saba da iskancinsa kala daban-daban.
"Mtsss...!
Wacce ke operating ɗin waya tai tsaki.
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'un."
Ɗaya daga cikin masu kallon big brother ta faɗa can ƙasan maƙoshinta.
"Annobar gida ya dawo."
Ɗayar ta faɗa tana mishi kallon sama da ƙasa tare da jan guntun tsaki.
Folding hannuwa ya yi yana sauraren abin da kowacce su ke faɗa.
Ƙwafa ya yi har ya ɗauki hanyar corridor da zai kai shi da ɗakinshi
Ya ji an sake ja mishi tsaki a fusace ya juyo ya sauke fusatattun idanuwanshi akan wacce yake kyautata zaton ita ce tai tsaki.
"Wacce Shegiya ce mai sha'awa kwanciyar gadon asibiti ke min tsaki?"
Ya tambaya yana wani zare idanuwa kamar yana yi da sa'anninshi.
"Wai nikam Tareeq har sai yaushe za ka fara girmama na gaba da kai ne?"
Daga bayan shi ya ji muryar Umminshi ta daki dodon kunnenshi.
Cikin kumbura baki ya ce.
"Ummi ko zan girmama na gaba dani bana tunani riɗa-riɗa ƴan matan gidanan za su sami haka daga gareni, kawai dai ina so ki shiga tsakanina da Ya Zainab ta daina shiga sabgata ina shigowa ta kira ni da annobar gida, ban tanka ta ba. Hakan bai ishe ta ba sai da ta sake yi min tsaki har sau biyu."
"Rufe min baki Tareeq kafin na tsinke ma mari Zainab ɗin ce zan shiga tsakaninka da ita ƴar uwarka ta jini kayi hauka ne Tareeq?"
Ya kwana da sani Ummi ba za ta taɓa bashi gaskiya koda shine da gaskiyar, shiyasa ya yi kwafa ya wuce zuwa ɗakinshi tun kafin ya ƙarasa shiga corridor ya ji Ummi tana ci gaba da masifa.
"Kai ma saboda ɗaukar magana yasa ka biyo ta cikin parlour nan bayan akwai ƙofar shiga ɗakinka ta waje fitinane yaro kawai da baya ƙaunar zaman lafiya."
Bai ce komai ba ya ƙarasa shigewa corridor ɗin tare da shan alwashin ko ba yau sai ya karyawa Ya Zainab ƙafa ko hannu tun lokaci da ya karyawa Ya Fadila hannu ta daina shiga sabgarsa tun da ya fahimci 'yan matan gidan nasu sai yana yi yana kakkarya su zasu daina shige mishi hanci.
Ummi ta juya ta koma kitchen dama tana cikin haɗa abincin dinner ta jiyo muryar Tareeq ɗin. Ko five minutes Ummi ba tayi ba da shiga kitchen ta ji Fadila tana kwalla mata kira, da sauri ta fito hannunta riƙe da ludayin miya. Nana da Mamarta ta gani tsakiyar parlour tsaye yayin da maman Nana sai cika take tana batsewa Nana kuma sai faman gunji kuka take.
"Subhanalillah! Nana Tareeq ne ko?"
Ummi ta faɗa sa'ili da ta iso kusa da Nana dan tasan duk duniya shi kadai ne za a kawo mata ƙarar sa, tasa hannu tana jujjuya fuskar Nana tana kallon shatin yatsun Tareeq dake shimfiɗe raɗau akan manyan kumatunta.
Cikin sanyi jiki Ummi ta ɗago ta dubi maman Nana ta ce.
"Dan ALLAH maman Nana kiyi haƙuri tabbas ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinshi ba...
"Dallah Maman Fadila ya isa haka maganar ta gaskiya nagaji da cin kashin da Tareeq ke wa Nana, fissibilillahi ace iskancin shi ya tashi daga tsagwama da dukanta da yake yi ya koma taɓa mata nonuwa to wallahi ki sani ba zan lamunci ya ɓata min tarbiyyar 'ya ba. muddin ya sake taɓa ta hukuma ce za ta shiga tsakaninsu ina dalili yaro ya fitine mutane unguwa."
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'un! Nana Tareeq ne ya taɓa miki nono?"
Ummi ta faɗa cikin zallar firgici da tashin hankali.
"Eh! Ummi bama sau ɗaya ba ko yau a school ya ritsa ni a bathroom ya taɓa sai na kai ƙararshi wurin schoolteacher ɗinmu ya dake shi. Shine yanzu na dawo daga islamiyya su ka sake tare ni shi da abokanshi yai min mari biyu ya kuma sake taɓawa. ALLAH ya taimake ni sai ga Uncle Hamza na nan gidan ya kwace ni a hannunshi da ALLAH ne ƙadai yasan iya adadin abin da zai yi mi
n."
Nana ta faɗa tare da rushewa da sabon kuka.
#Soyayya
#Nadama
#Makirci
#Kiyayya.