IDO A DUHU

004

by @billysfari

IDO A DUHU

         NA

BILLY S FARI đź’Ž

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            4.

     A gurguje na fito daga cikin É—akina ina saĆ™ale jakar da nake zuwa makaranta da ita, Amatul-Alim cikakken sunana kenan da iyayena suka raÉ—a mani amma suna yi mani laĆ™ani da Janaam sunan da kenan akafi sani na dashi kuma ake kira na dashi, sauri nake yi riĆ™e da niĆ™af a hannuna ina Ć™oĆ™arin É—aurawa akan fuskanta don na kusa makara, na kuma tabbata Nu'aymah Ć™awata da muke wucewa tare a motarta ta fito tun É—azu ni kaÉ—ai take jira, hakan yasa ban damu na tsaya karyawa ba na nufi hanya, Muryar Mamah  baki tana cewa, "A'ah! Janaam ina zuwa bakiyi kari ba". Da sauri na juyo na Ć™araso wajen ta ina cewa, "Mamah na makara zan tafi sai na dawo, kin san halin mutuniyar tana can tana jirana, yanzun nan zaki ji tafara yimun horn idan ta gaji da jira". "To haka zaki fita baki karya ba". Na juyo kamar zanyi kuka jin muryar yayana dake fitowa daga ta sashensa yana faÉ—a, cike da girmamawa nace, "Ina kwana Ya Jameel?" Fuskarsa a sake ya amsa mani yana murmushi haÉ—e da Ć™arasowa wajen yana cigaba da cewa. "Lafiya Ć™alau Janaam, me yasa kullum bakya son yin kari kafin kifita? So kike yi wani ciwon yazo ya shige ki ki tada mu tsaye?" "Kai ma ka faÉ—a, kullum faÉ—an da nake yi da ita kenan akan fita ba kari amma bata ji!" Mamah ta faÉ—a tana kallona, sai dana daura niĆ™ab É—in dake hannuna akan fuskata sannan na É—age sa nasa  hannu cikin flate É—in da Mahmah ta zuba abun karyawar da zata ci na É—auko yankan soyayyen arish É—aya na tura abaki sannan na ciro tissue dake kan table É—in ajiye na goge hannuna ina cewa. "Afuwa ya Jameel gashi naci, in Sha Allah kuma na dena yin hakan bazan sake ba, amma dai yanzu zan tafi saboda 10 zamu shiga lecture kuma mintuna kadan ya rage ta buge, mun kusa makara kuma kasan halin mutuniyar". na faÉ—a haka tare da ficewa daga falon cikin É—an É—aga muryarya ina yiwa Mamah sai na dawo, "To adawo lafiya kiyi addu'a kiyi addu'a kafin kifita?". "Ok Mamah bye". "Bye Janam ki kula da kanki".

Ina fita kai tsaye gidansu Nu'aymah na nufa, cike da natsuwa nake tafiyata har na ƙaraso cikin gidan, dai-dai lokacin Nu'aymah na kokarin fitowa da mota ta maka maka mani harara, dariya na saki daga cikin niƙab ɗina na ƙarasa wajen ina faɗin, "Tuba nake yi muje ko?" Ina shiga sai ga yayanta Nu'aym ya fito cikin shirinsa yana gyara clip ɗin hannun rigarsa, knocking ɗin glass din ƙofarta yai ta danna glass ɗin ya zuge, "Fito ki koma baya Aymah". Ya faɗa fuskarsa ba wasa, Nu'aymah ta ɗan turo baki tana cewa, "School fa zamu je ya Aym". "Na ce baza ku je bane? Fito mana nace". Ina ganin Nu'aymah zata fita nima nafara ƙokarin fita yai saurin dakatar sani, "No ki zauna abunki". Ya faɗa yana zaunawa inda Nu'aymah ta tashi tare tada motar muka bar wajen, cike da natsuwa yake driven duk da yadda ya fahimci sauri muke yi mu isa school, dukkanin mu babu wanda ya iya cewa uffan daga ni har ita, Allah ya gani ba ƙaramar takura naji ba zamana a wajen, a hankali ya juyo yana kallona nayi saurin kauda kaina gefe, "Morning Janaam". Na ji muryarsa ta daki kunnena duk da maganar yayita can ƙasan maƙoshi tamkar baya son maganar. Ban iya amsa shi ba don nasan ya yi hakan ne saboda ban gaishesa ba. Shiriyar ajiyar zuciya ya sauke a sirrance yana sake riƙe steering wheel ɗin motar haɗe dayin gyaran murya yace.

"Aymah meke damun Ć™awarki ne? Ko azumin magana take yi?" Nu'aymah dake baya ta turo baki kamar zata yi kuka tace, "Don Allah Ya Nu'aym kabar wannan maganar ka taka mota, wallahi mun kusa makara kuma duka laifinta ne". Nu'aym ya sake juyowa yana kallona, ni har mamaki yake bani yadda yake son kallon nawa duk da rufe fuskata take, Ć™asa nayi da kaina ina wasa da yatsun hannuwana naji yace, "Wai haka ne Janam?".  A maimakon na amsa masa sai na tsinci kaina da cewa, "Please Ya Nu'aym mun makara fa?" "Am sorry". Ya faÉ—a yana É—an taka motar, da haka muka iso school, yana yin parking Nu'aymah ta É“alle marfin motar tafita tana faÉ—in, "Bye Ya Nu'aym" "Bye Aymah". Ya faÉ—a yana É—aga mata hannu, na É“alle marfin zan fita Nima yai saurin dakatar sani ta hanyar cewa, "Janaam ina son yin magana dake, gashi tun da na dawo Ć™asar nan banda wani lokacin kaina kuma jibi zan koma". "Kayi haĆ™uri muna da lecture yanzu in ba so kake a hanani shiga ba kaga Nu'aymah har ta wuce abunta ta barni". Daga haka ban jira cewar sa ba na fito na nufi cikin hall É—in da zamuyi lecture, ina jin idanuwansa akaina amma ban iya juyowa har na shige ciki, Alhamdulillah ko da na shiga har lokacin malamin da zai mana lecture bai zo ba, na zauna ina sauke ajiyar zuciya haÉ—e da mamakin to wace magana yayan Nu'aymah ke son yi dani.

Bayan mintuna biyar da zamana sai ga malamin ya shigo yana bamu hakuri akan delaying da yayi, awa biyu muka dauka muna lectures kafin ya gama ya fita, bamu fita ba sai da Nu'aymah tasa na sake yi mata bayanin karatun da muka gama sannan ta É—ago ta kalleni tana cewa, "Janaam muje capteria wlh yunwa nake ji". Kusan haka take a wajena yunwa nake ji sosai, don haka muka mike tare muka fito, muna fitowa idanuwana suka sauka akan Umar Faruk a can gefe shi da Ć™awayensu da duka mata ne sai abokinsa namiji Ć™waya É—aya riko, yan matan  sun zagaye su sai fira suke yi suna dariya shi kuma yana tafewa dasu, kallo É—aya nayi masu na janye idanuwana saboda a kaf faÉ—in makarantar babu wanda na tsana kamarsu, bani Ć™aunar abinda zai haÉ—a ni dashi koda kuwa alkhairi ne saboda yadda ya É—auki kansa acikin makarantar, baya ganin mutuncin kowa kuma baya shakkar wulakanta kowa cikin mutane, ciki kuwa hadda malamai saboda yana É—an É—an wani babban attajirin mutum dake faÉ—a aji a gwamnati mai ci yanzu, mata sune abokansa aduk inda yake baka rabashi dasu, yana taka duk wanda yaso sannan ya daukaka wanda yake so ba tare da an taÉ“a dakatar dashi ba a makarantar, duk da wuÉ—annan É—abiu nasa kuma ba kaÉ—an 'yan mata ke sonsa ba saboda kyan da Allah yayi masa da kuma iya wanka, uwa uba tarin arziki da yake dashi da kana kallonsa zaka san shi É—in ba É—an gidan Ć™ananan mutane bane. Umar Faruk wankan tarwaÉ—a ne wato chocolate colour, yana da manyan idanuwa masu launin ja kuma a shanye suke tamkar mai jin bacci, haka kuma yana da dogon hanci da loÉ“awar kumatu musamman idan yayi dariya duk da ba kasafai ya fiye yinta ba, yana da matsakaicin tsawo da kuma murÉ—aÉ—É—en jiki dake nuna yana motsa jiki, na fahimci duka hakan ne lokaci É—aya saboda yadda 'yan mata ke yawan zancensa.

A hankali na ci gaba da saukowa akan matattakalar wajen da muka gama É—aukar karatun ina ma Nu'aymah magana, jin shiru bata amsa ni ba ya sani É—ago kai da niyar sake yi mata magana, abun mamaki sai na hangota a can matakalar farko ta saki baki tana kallon gefen da su Umar Faruk suke tana faman kallonsa, takai ci ne ya kamani na É—an tsaya ina kallonta nima kafin na koma na riĆ™o hannunta muka shiga saukowa ina cewa, "Wlh Aymah bakiyi ba! Na rasa meye abun kallo a can". Nu'aymah dake yi tana juyawa tana kallonsa tace, "Baza ki fahimta ba Janaam, gayen can na matuĆ™ar burgeni wallahi, ba don nasan halinsa ba tsab zai iya disgani da na je mun zama Friends ni dashi, Allah Janaam yana matuĆ™ar burgeni sosai". TaÉ“e baki nayi bayan mun sauko ina cewa, "Lallai ba kida aiki Aymah, meye abun burgewa atattare dashi, bakya ganin dabi'unsa da halayyarsa ne? Ai sam ko kusa bai dace daya shiga rayuwarki ba don Allah tun wuri karki fara, mutum bai da aiki sai faÉ—in rai da zama cikin mata sai kace wani É—an daudu". "Hmm! Bazaki gane ba, ai Wlh ni ko gaisawa ce mu riĆ™a yi dashi hakan ba Ć™aramin faranta raina zai yi ba,". Nu'aymah ta faÉ—a tare da juyawa gefe, hango motar ta a inda mukayi parking É—azu tayi, tayi saurin taÉ“o ni tana faÉ—in."Bar wannan zancen Janaam dama ya Aym ya bar mana motar anan bai tafi da ita ba?" Na juyo na kalli motar haÉ—e da cewa. "Gashi kin gani, amma nima ban san bai tafi ba gaskiya tunda bai bani key ba yana hannunsa, kin kuma san idan yasan anan zai bar maki ita dole ya bani key É—in yace na wuce maki dashi".  "Zo muje" Nu'aymah ta faÉ—a tana jan hannuna muka nufi wajen motar, tamkar wanda idanuwansa ke kanmu muna isowa wajen ya zuge glass É—in gefensa fuskarsa É—auke da murmushi yana cewa. "Har kun fito". Nu'aymah ta zato idanuwa tana kallon sa haÉ—e da cewa, "Can't believe wai da gaske kai ne yaya ka tsaya jirana? Muna fa da lecture É—i 2-4". Ni kuwa a zuciyata mamaki ne yakama ni kar ace ya tsaya ne akan maganar daya ce yana so yayi dani? Ai kuwa sai ji nayi yace wa Nu'aymah. "Malama bake na tsaya jira ba, Ć™awarki Janaam nake son magana da ita shiyasa ban tafi ba". Nu'aymah ta taÉ“e baki tana haÉ—e rai take cewa. "Dama ai na sani, kinga Janaam bara naje na samo mana abinda zamu ci, kai kuma ya Aym gaka gata amma ka sani dole sai ka biyo ta hannuna na buga maka stamp, idan ba haka ba na hana a saurareka". Nu'aym ya saki murmushi haÉ—e da ciro kudi a aljihunsa ya miĆ™a mata yana cewa,  "Eh na dai ji, karÉ“a ki Ć™ara ki sawo maku abu mai kyau, in dai ke nasan halinki yanzun nan sai kije ki kwaso maku harkar kayan zaĆ™i da snacks, kuma sam basa maganin yunwa don haka kawai kiyi maku take away É—in abinci mai kyau". Nu'aymah na dariya ta karba ta wuce, shi kuma ya É—an leĆ™o daga cikin motar yace, "To Ranki shi daÉ—e shigo daga ciki muyi magana". "A'a ya Nu'aym nan ma ya isa". Na faÉ—a ina jin Ć™irjina na wani bugawa da karfi, murmushi ya yi ya fito daga cikin motar shima ya jingina a jikinta kamar yadda nayi sannan yace..

ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏