39
by @oumfatima33
💞💞💞💞💞💞💞💞
AMATURRAHAMAN
*By*
OUM FATIMA
*(Hakimar D. A. W. A)*
💞💞💞💞💞💞💞💞
*DASHEN🌲ALLAH*
*WRITER'S📚ASSOCIATION*
*TEAM*
*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*
BOOK 1
PAGE 39
*بسم الله الر حمن الر حيم*
Bacci yayi sosai sai ƙarfe 12:00am ya tashi ya shige bathroom kai tsaye domin shirin tafiya masallaci wanda ana gama sallah za'a ɗaura auren. Bai wani jima ba ya fito saboda lokaci daya fara ƙurewa, shiryawa yayi tsaf cikin dakakkiyar farar shaddar data lashe kuɗaɗe wurin sayenta. Hula ƙube ya murza a saman kansa ta zauna ɗas gwanin sha'awa tamkar ka sace shi ka gudu.
A gaggauce ya fito saboda ƙurewar lokaci ya shiga wurin Ammah ya mata sallama, yana fitowa yaci karo da su Abba suma sun fito cikin shirin wucewa. Sojojinsa da suka taso suna ganin fitowarsa suka buɗe masa motar tsakiya cikin waɗanda aka fitar za'a yi tafiyar dasu. Bai shiga ba sai da ya buɗewa Abba ya shiga ya zauna a tasa motar sannan ya koma ya buɗe ma Baba Alhaji wacce za'a tuƙashi ya zauna sosai kafin ya zagaya inda Samuel ya buɗe masa ya shiga kusa da Baba Alhajin ya zauna.
Lokacin da motocin nasu ke ƙoƙarin ficewa Salim ya fito shima cikin shiri ya shiga tasa motar ya take musu baya domin Hajiya Ruƙayya ta saka shi dole ya shirya yaje ɗaurin auren, haka jerin motocin suka fice reras cikin tsari abin birgewa.
Cikin tsari motocin ke wucewa har suka ƙarasa babban masallacin juma'ar da zasu yi sallah kafin a gudanar da ɗaurin auren, da gudu sojojin Zayyad suka firfito suka shiga gyara masa hanya don tabbatar da tsaronsa shida familynsa kasancewarsu manyan mutane ba zasu rasa maƙiya ba. Sannan shi Zayyad ɗin kansa aikinsu ne tabbatar da tsaronsa.
Sun samu iyalan Alhaji Abba gana suma sun zo don haka ana gama sallar juma'a aka shiga gudanar da ɗaure-ɗauren aurarrakin da za'a gudanar a ranar. Auren ANISA MAINA MUHAMMAD DOKAJO dana angonta ABDULMAJID ABBA GANA aka fara ɗaurawa kafin sauran suka biyo baya.
Bayan an kammala daga nan kai tsaye Dokajo Mansion aka wuce inda Iyayen amarya suka shirya ƙayatacciyar walima aka ci aka sha aka gudanar da lecture daga bakunan manyan Malamai kafin aka tashi.
Ana gama walimar ya zame wa mutanen da suke ta zuwa domin gaisawa da shi da sanya albarka a auren ƙanwarsa da aka yi ya nufi ɓangarensa sabo da kansa ke masa ciwo sosai hutu yake buƙata. Samuel ɗaya fuskanci haka da sauri yayi gaba yana buɗa masa hanya Siddiq kuma na take masa baya suka shige, sai da suka tabbatar ya shige ciki suka tsaya bakin ƙofa saboda yace baya buƙatar a bar kowa ya shigo masa.
***** Amarya Anisa sai da akayi da gaske aka samu tayi wanka mai make up ɗin da Mammah ta ɗuko tazo ta fara shiryata cikin ƙwarewa a aikinta, ƴanmatan kuwa su Haneen tuni sun shirya abinsu sun ci kwalliya sun yi kyau masha Allah sai kai-kawo suke na kula da ƙawayensu harma dana Anisar wanda sune suka gayyato su.
"Tabarakallah, masha Allah." Shine abinda mutane ke furtawa lokacin da aka gama shirya amarya domin kuwa Anisa itama kyakykyawarce saboda Ahalin Dokajo gaba ɗayansu kyawawa ne. Sai dai rashin walwalar dake saman fuskarta ita ke ragewa kwalliyar tata armashi domin kuwa fuskar ta ɗan kumbura idon yayi ja saboda kukan data kwana tana yi na tabbatarwar da tayi ta rasa masoyinta gidan wani za'a kaita da ban.
Mai make up ɗin tayi matuƙar ƙoƙarin ganin ta ɓoye kumburin fuskar tata da tsadaddun kayan make up ɗinta. A ɓangaren Hajiya Sha'awanatu itama hakan take, sai dai ita tayi matuƙar ƙoƙarin danne nata yanayin tana gudanar da bikinta cike da karfin hali saboda tabbacin da aminiyarta kuma ƴar'uwarta ta bata na cewa tana da shiri daga baya.
Sanarwar isowar tawagar ango gaisuwar Iyaye da kuma yin hotuna da amarya da ƙawayenta ce tasa Anisa jin wani ƙullutu ya tare mata maƙoshi, ji take tamkar ta ɗauko wuƙa ta luma masa kowa ya huta. Oho shi bai ma san tana yi ba saima farin cikinsa da yake na kasancewarsa angon daya auri wacce yake tsananin so, ba ruwansa da iya shegen da take yi domin kuwa ya shirya tsaf domin koya mata hankali da maido ta kan hanyar data sauka.
Ɓangaren Baba Alhaji suka fara zuwa suka gaisar da Kakanni sannan suka nufi ɓangarensu Anisar inda Momy da ƴan'uwanta suka tare su da fara'a tamkar ba komai a zuciyar Momy haka ta dage tana ta yaƙe har suka fice suka nufi sauran sassan suka gaishe su kafin suka nufi inda amarya take da ƙawayenta.
Duk inda suka je mai ɗaukar hotonsu na biye dasu yana aikinsa har suka je wurin amarya da ƴanmata. Da mutuntawa su Haneen, Fatima, Ameerah, da Nadiya suka tarbe su banda Najma da suke tif da taya ita da Anisa. Sai da sukayi rantsuwar zasu je su sanar da Dady sannan ta fito tana ɓata rai haka aka yi musu hotunan, Abdulmajid tsabar jan magana har wani rungumeta yake yi duk yanda take zillewa.
Bayan sun tafi kuka ta shige ɗaki tana yi na baƙin ciki har ta rasa kalar da zata yi don jin sauƙin raɗaɗin da zuciyarta keyi.
***** Zaheera kuwa ranar ji take tamkar an mata gafara don gani takeyi kasancewar Anisa ta furta cewar tana son Zayyad ɗin a gaban kowa zai iya zama matsala a gareta, don haka yau data samu aka kawar da Anisa sai take jin farin ciki mai tsanani.
Ado taci sosai saboda so take ta burge Zayyad ɗin ko ta wani hali yau don haka taje wurin kwalliya na musamman akayi mata, shaddace ta saka ɗinkin fitet gaunt wacce tamkar a jikinta aka ɗinka ta tsabar kama jikinta da tayi. Don kyau tayi kyau sosai saboda itama dai kyakykyawar ce masha Allah.
Gida suka wuto ita da ƙawarta Samra data nace mata tunda taji labarin zuwan Zayyad ɗin a bakin Zaheera, don haka itama kwalliyar tayi sosai suka wuce saboda ta kira Teemah a waya ta tambaye ta Zayyad ɗin tace mata sun dawo daga wurin ɗaurin auren yana shashensa.
"Kinga Samra ki jirani a nan zanje can part ɗin nasa don kwalliyar nan ba zata tashi a banza ba." Zaheera ta faɗa tana dafa kafaɗar Samra. Wani kallon kin gama raina ni Samra ta jefa wa Zaheera kafin ta waske ta saki wani munafikin murmushin tace "Haba ƙawata ya za'a yi in barki kije ke kaɗai ban san me zai faru ba, ai gara dai in raka ki zaki fi samun ƙwarin gwiwa kema." Ta ƙare maganar cike da makirci a ranta tana raya cewar 'hauka ake zan bari ki tafi ke kaɗai wato ni inyi asarar wannan damar da samunta sai tsananin rabo kuma'.
"Lafiya ƙawata tunanin me kike?." Zaheera ta faɗa ganin Samra tayi nisa a cikin tunani har tana mata magana bata ji ba. Murmushin yaƙe tayi tana cewa "Ba komai ƙawata, muje ko." Ba dan ta gamsu ba ta miƙe tana gyara zaman yalolon mayafin data ɗora saman kafaɗarta suka fice zuwa part ɗin Zayyad duk da yanda zuciyarta ke bugu da tsoron abinda zasu tarar saboda ko su ya hanasu zuwa sashensa bare harda wata da ban.
Har suka ƙarasa gabanta bai bar dukan tara-tara ba, amma sai dai tana dakewa ta danne tsoronta suka ƙarasa ƙofar da zata sadaka da ainahin sashen nasa. Wani mugun birki suka ci lokacin da suka ci karo da Samuel da Siddiq a ƙofar zaune saman plastic chairs suna shan shayi suna hira.
"Madam lafiya?." Siddiq ya faɗa ganin yanda sukayi tsilli-tsilli da ido suna magana ƙasa-ƙasa, "Zan je wurin Yaya ne akwai saƙon da zan amsa a wurinsa." Zsheera tayi ƙarya saboda a barta ta wuce. Gano abinda take shirin yi ne yasa Samra saurin cewa "Eh saƙo zamu amso." Ta ƙare maganar tana riƙo hannun Zaheera don tabbatar musu da tare suke.
"I'm sorry Madam Boss yace baya buƙatar ganin kowa." Samuel ya faɗa yana cin magani gudun kar ma ta kawo musu wargi saboda ya san yarinyar bata da kunya. Ai kuwa cike da fitsara tamkar ba jinin Dokajo ba tace "Amma dai banda ni ya hana, kai kasan matsayina a wurin Ya Zayyad kuwa? To inma baka sani ba ka sani yanzu, nice matar da zai aura inzo a matsayin shugabarku kuma dole kuyi min biyayya in ba haka ba mutum ya gane kurensa!." Ta ƙare maganar tana wani yatsina fuska.
Kafin Samuel ya bata amsa Samra tayi saurin cewa "Ƙwarai kuwa, idan kuna son ci gaba da zama s kusa da uban gidan naku to ku gaggauta bamu hanya mu wuce!". Ta ƙare maganar da ƙwarin gwiwarta.
Siddiq ne ya buɗe baki zai yi magana Muhsin da yazo wucewa ta wurin yaji hayaniya ya ƙaraso don ganin meke faruwa. Ya katse shi ta hanyar cewa "Meke faruwa a nan wurin?." Ya faɗa ba wasa. A zabure Zaheera ta juya tana kallonsa saboda ta san shi, shima bashi da wasa tamkar Marshal ɗin haka yake.
In ina ta fara ya daka mata wata muguwar tsawa ya nuna musu hanya, ai kuwa a sukwane suka wuce. Samuel ya bisu da mugun kallo yana jin zuciyarsa ta sojoji na motsawa tamkar ya musu dukan tsiya haka yaji. Haƙuri Muhsin ya basu kafin ya wuce inda zashi yana mamakin haukan daya kai Zaheera sashen Yayan nasu har da wata mai kama da karuwan bariki, ya tabbata da ace ya fito ya same su a wurin ba abinda zai hana ya saka a zane masa su.
******* Haka yinin biki ya ƙare zuciyar amarya da mahaifiyarta babu daɗi, ana gama sallar magriba Dady ya saka Momy ta shirya Anisa ta rakota wurinsa, nasiha yayi mata mai ratsa jiki kafin ya sauƙaƙa murya ya rarrasheta sosai. Da kanshi ya kaita part ɗin su Baba Alhaji suka haɗu da sauran ƴan'uwansa suka yi mata nasiha sosai kafin kowa ya bata kyautar daya tanada mata ta aure wacce ba wanda ya bata ƙaramar kyauta a cikin Iyayen da yayunta, a barma batun kyautar da Babban Yaya ya bata. Muzaffar, Muhsin da kuma Sageer su Dady ya wakilta suka kai Anisa har ɗakinta suka danƙa amanarta a hannun Abdulmajid bayan sun musu nasiha sosai suka kuma roƙeshi akan ya riƙeta amana ya kuma yi haƙuri da ita saboda har yanzu ita ɗin yarinya ce. Alƙawari yayi musu akan zai kula da ita zai kuma riƙeta amana.
Itama basu barta ba nasiha sukayi mata suka nuna mata matsayin da mijinta ke da shi a kanta a yanzu. Sallama suka yi musu suka tafi cike da tausayin Anisa da suka bari tana ta kuka tamkar ranta zai fita.
Duka yanda Abdulmajid yaso shareta bayan tafiyarsu kasawa yayi saboda tausayinta daya kama shi, yana son Anisa har cikin zuciyarsa soyayya kuma ta gaskiya. Sai dai ba zai ɗauki iskanci da raini daga gare ta ba don ya lura tana da rainin wayo dole sai ya nuna mata shima mai zafn ne zasu dai-daita.
Ajiye komai yayi a gefe ya fara rarrashinta da ƙyar ta iya tsagaita kukan tayi shiru ba don taki rarrashin nasa ba sai domin abinda zuciyarta ta saƙa mata, gabatar mata da kazarta yayi da drinks ya fita zuwa ɗakinsa don ya shirya ya dawo. Da wannan damar Anisa tayi amfani yana fita ta miƙe ta sakawa ƙofar key ta barshi a jiki kafin ta koma ta bararraje taci kazarta ta more ta haye gado ya kwanta tana tunanin ta inda zata fara ta samu ta kashe wannan alƙaƙai ɗin auren da aka manna mata.
Koda Abdulmajid ya dawo ya murɗa ƙofar yajita a rufe murmushi kawai yayi ya koma inda ya fito yana raya wa a ransa 'lokacinki ne yau yarinya kiyi yanda kike so kafin nawa lokacin ya fara.
____________&
Zaheera kuwa bayan sun bar wurin kai tsaye ɗakinta suka koma suna jin baƙin cikin rasa wannan damar da suka yi, ji take tamkar ta zauna tayi ta rusa kuka hakan yasa ko fita batayi ba wurin bikin ta cire kwalliyar ta jefar ta zauna tana kukan baƙin ciki.
Samra kuwa tsabar takaici bata ko zauna ba tayi tafiyarta gida tana jin haushin abinda ya faru. Zayyad ɗin da sukeyi domin sa bai san meke faruwa ba don tunda ya shige bai fitoba sai da lokacin Sallar magrib yayi ya fito suka wuce Masallaci shida Siddiq da sauran masu yin sallar.
Bai shigo cikin gidanba sai da yayi isha'i kai tsaye kuma sassan Ammah ya nufa a can ya samu Muzaffar suka zauna suna tattaunawa a kan maganar Amaturrahaman da yanda ya baro ta bai kuma koma ba bare ya san halin da take ciki......