AJNABIYYA

Ajnabiyya page 3

by @hajjace22522

AJNABIYYA...

NA

*HAJJA CE* 👈

Arewabook@Hajja22522

Wattpad@Hajjace

Facebook@Hajjace

Page 3

Ameerah ta tashi da safe tana jin wani irin sanyi na ratsawa ta cikin bargon da bai ishe ta ba. Idonta na kallon rufin ɗakin su zuciyarta na cike da mafarki mai daɗi.

"Da ace ni kuwa na taso cikin gidan masu kuɗi." Ta faɗa a cikin ranta.

"Hmmmm! Da yanzu wayar tashi daga bacci ce zata farkar da ni. Gefe guda kuma ga abinci mai rai da lafiya yana jere a kan dining. Ruwan wanka ma an surka min a lafiyyan banɗaki da zakaji kamar kayi bacci a ciki. Amma kuma kashhh..."

Ta lumshe ido hawaye ya gama kankama a gefen idanunta. Su ɗin talakawa ne fitikkk. Ko mafarki na alfarma ki ka yi sai dai ki tashi da baƙar yunwa. Tun jiya dama bata ci komai ba bayan furar da ta shanyewa Inno, hakan yasa ta ke ta jin ta wani iri, jiri yana kamata, rashin karfin jiki dana zuciya sun mamaye ta. Da kyar ta miƙe tana kallan jikinta. Yo tana wanka da ruwan famfo wanda shi ɗin ma idan sun samu sai ai ta yi maka iko ana hanaka ɗibar shi, kuma idan tayi wankan ma sai ta yi ta haki saboda sanyi, taya ya fatarta zata yi kyau Sabulu kuwa sai kayi ta faman nemowa a cikin kasko baka samu wanda zaka ɗan saɓe jiki dashi ba. Da kyar ta iya samun wanda zata ɗan wanke wajajan da tasan suna buƙatar wankewa. Bayan ta shirya cikin doguwar rigar uniform ɗinta, ta fito suka yi sallama da Mama ta nufi makaranta da zummar mantawa da damuwar gidan su.

A makaranta ta samu su Meenal da Yaseer abokanta da kuma ƴan ajinsu a karkashin wata bishiya. Meenal na shirin cire littafi daga jaka Yaseer yana dariya yana ta zuba hira wacce da alama akan jarabawar da aka ɗauki sunayen su ne. Ta isa wajan su cikin gajiya saboda ta wahala ga yunwa ga rashin isasshen bacci ga tahowa a ƙafa.

"Kin kwana lafiya Ameerah?" Meenal ta tambaya tana murmushi.

"Alhamdulillahi." Ta amsa da ɗan ƙaramin murmushi akan fuskarta. Amma zuciyarta na bugawa ba don komai ba sai don mafarkin da ta tashi da shi. Uhmmm! Duniya ce dai kowanne na da nasa labarin a cikin ta. Bata daɗe a wajan ba duk aka tashi suka shiga cikin class bayan sun gana tabbatar da kowanne ɗaliba ya shiga ajin shi. Zaune suke su ukun a ƙarshen aji yayin da malaman suka ɗauki lokaci kafin su iso. Yaseer ya ɗaga takarda yana gyara wani lissafi. Meenal na ƙoƙarin karanta wani labari daga cikin wani littafin Hausa tana karkaɗa baki kamar mai shirin yin drama.

"Meenal ki daina karatun nan kamar mai wasan kwaikwayo." Yaseer ya faɗa yana dariya.

"Yaseer wallahi kai dai ba ka fiye sa ido, ina ruwanka ita?." Ameerah ta ce tana ƙoƙarin ɓoye murmushinta dan itama shirin yiwa Meenal ɗin magana ta keyi, sai kuma taji mutumin nasu ya rigata. Yaseer ɗin ne ya kalleta yana cewa.

"Toh yau kuma ke me kike ji dashi da safen nan? Kuma me kika ci dan kar ki zo ki ci ruwa da burodi kamar jiya." Ameerah ta kau da kai gefe, ta ɗan yi murmushi kaɗan tana cewa.

"Ka bar ni Yaseer. Kai ne har yanzu ba ka girma ba." Meenal ta saka dariya tana kallonsu su biyun ta ke faɗin.

"Wallahi ku biyu idan kuna tare ana samun dariya." Yaseer ya ce cikin murmushi.

"To Meenal ke ki tsaya bakya sanarwa kanki farin ciki, mu duka dai mun fi ki wayo." Wani irin shiru ne ya biyo baya, amma cike da nishaɗi. Ameerah ta duba bangon ajin zuciyarta cike da wani tunani da bata iya furtawa. Sai dai idan tana tare da Meenal da Yaseer tana samun nutsuwa da dariya sosai. Su ne abokanta na gaske masu fahimta da nuna kulawa ba tare da sun nuna iko ko wadatar da suka fi ta ba. Duk da halin rayuwa da ta ke ciki, makaranta ita ce wajen da ta ke jin kamar ta na da matsayi mai girma a rayuwarta. Ta san ba kowa ke da irin wannan damar ba musamman ƴaƴan talakawa irin ta.

Malamin Chemistry ne ya shigo ajin na su Dr. Abubakar. Tsaye yayi a gaban ajin yana dube-duben fuskokin su. Kamar kullum ya cika da kamala da tsauri. Ɗaliba suka tsaya da dariyar da suke yi kowa ya ɗauki littafin da suka san shi zai yi musu amfani dashi.

"Ku buɗe littattafanku shafi na 67. Zamu ci gaba da darasin mu Hydrocarbon." Ya faɗa da murya mai ɗan ƙarfi yadda kowa zai iya jiyo shi. Ameerah ta buɗe littafin amma zuciyarta tana ɗauke da abinda ya faru da ita na tunanin da ta ke yi da safe. Yanzu haka tana zaune a cikin aji tana ƙoƙarin fahimtar darasi. Amma zuciyarta na kulle da tambayoyin da ita kanta ba ta da amsar bayarwa. Ta kalli biro da takardarta ta ce a ranta.

"Da ace ni ba ƴar talakawa bace...! Da watakila yanzu ina da calculator mai kyau ba irin hakan nan ba da nake bugawa da gefen biro ba."

Gabaki ɗaya ta shagala, ji ta ke yi kamar rayuwarta a tauye ta ke, babu walwala babu rahama a cikin ta. Bayan wani lokaci sai taji Meenal ta latsa hannunta akan disk tana dariya a hankali. Ameerah ta dubeta da mamaki ta ke cewa.

"Ke dai Meenal ko." Ameerah ta ce tana kafeta da ido.

"Wane abun dariya ne yanzu aka yi?"

"Wallahi wannan Yaseer ɗin ne wai yaje makarantar su Hammad ana training na debate ya kasa cewa komai kamar wanda aka cire masa murya." Meenal ta ce tana dan bushewa da dariya. Yaseer ya juyo da sauri yana cewa.

"Ni kuma? Anya ni ne? Meenal Allah ya baki hankali, ai ni shi yasa nake ƙoƙarin duba me za ku faɗa kafin na ɗauki maganar ku." Ɗalibai suka kwashe da dariya ciki har da Dr. Abubakar wanda ya ɗan kalli Yaseer da murmushi yace.

"Yaseer idan ka gama sha'aninka sai ka ci gaba da ƙoƙarin Hydrocarbon ba humorcarbon ba." Dariya ta sake cika ƴan ajin suka dinga yi.

Ameerah ce ta ɗan saki fuska. Wannan karon kuwa ba sabida dariyar Yaseer ba ne ba. Nooo! kawai dai ta lura da wani abu ne. Duk da halin talaucin da take ciki, tana da abokai masu kwantar mata da hankali. Kuma a hankali makarantar nan tana zame mata mafaka ta wajen da zata gina kanta dama rayuwarta anan gaba kaɗan. Tana rage mata takaici da bakin cikin abubuwan da ta ke gani ko kuma ta ke yi a rayuwar gidan su. A ranar karatun ba ƙaramin daɗi ya yiwa Ameerah ba, dan har aka tashi wani irin farin ciki ta ke ji.

  

*****

Ranar wata Alhamis ne rana mai zafi da iska mai ɗauke da ƙura tana kaɗawa a hankali. Bayan sun fito daga makaranta, Meenal da Yaseer suka jira Ameerah a ƙarƙashin ɗaya daga cikin manyan itatuwan da ke bakin ƙofar makarantar su. Suna ta dariya suna sharhi kan darasin Biology da suka gama.

"Ke Ameerah." Meenal ta kira sunanta tana ɗaga mata hannu.

"Ki dinga tafiya da sauri mana, wallahi yau zuciyata ta ƙone da explanation ɗin Mr. Iliyasu akan Photosynthesis." Ameerah ta ƙaraso tana murmushin da yake cike da kasala tana cewa.

"Toh ai ke ce baki daina tambaya ba sai da na rasa inda zan saka kaina wallahi." Yaseer ya sosa kai yana dariya yake faɗin.

"Kuma duk da haka sai da Malam ya ce ‘very good Aminatu!’ Ai kunga kowa da irin yadda yake gane abubuwa." Suna ta dariya haka suka kama hanya a tare suna tafiya a ƙafa kamar yadda suka saba. Kowa yana jefa tsokaci wani lokacin kuma su yi shiru na ɗan ƙanƙanin lokaci kaɗan, sai kuma su ci gaba da hira. Tafiyarsu ba ta cike da damuwa ba saboda kowa da nashi tunanin.

Ameerah dai ba ta da wani abu da ya fi damunta banda cewa idan tana gidan su, tana son ta dinga yin karatu sosai da kuma samun kwanciyar hankali. Amma akasin hakan ne kullum yake samun ta idan ta koma. Yau ma tana tunanin yadda zasu shiga gidan da suke da ƙarancin wutar lantarki, wasu gidajen kuma ta ke kyallewa kamar fitsari a damina. Ga dafa abinci a kan murhun duwatsu, wanda idan ruwa ya sakko sai dai su haƙura su koma gefe suna jiran yadda Allah zai yi dasu. Sannan tazo ta fara wanke kayan makarantar ta kafin sannan tayi karatu a ƙarƙashin fitilar solar da kusan bata da haske sosai. Meenal ce ta juya ta kalleta tace.

"Ameerah yau ma kina tunani ne?" Ameerah ta yi dariya kaɗan tace.

"A'a kawai ina lissafin aikin gida ne. Kinsan fa da sauƙi idan rayuwa tana da sauƙi." Yaseer ya juyo yana tafiya a baya yana kallonsu yace.

"Ai rayuwa kullum da sabon challenge ta ke zuwa. Amma dai ku duba muna da lafiya wannan ma babban arziki ne." Duk suka amsa da cewa.

"Haka ne, amma idan ka samu abubuwan jin daɗi rayuwar zarafi daɗi sosai." Duk suka jinjina kai suna ci gaba da tafiyarsu. Ana ƙarasowa cikin unguwa kowannensu kamar kullum suka yi sallama. Lumshe idanuwa Ameerah tayi iska na shigar mata cikin jiki tana jin wata irin ni'ima da nutsuwa da ɗan hasken rana da ke shigowa tsakanin rassan itatuwa da ke gefen hanya.

Ameerah ta shiga gida cikin ƙarfafa zuciya, amma cikin ranta akwai ƙarancin jin daɗin abinda zai biyo baya yadda taji gabanta na dukan uku uku akan tunanin ta na me aka dafa. A ɗan wajan girkin su ta tarar da wani kwano mai ɗauke da tuwo da miyar kuka wanda da alama shi aka ajiye mata. Sai dai lokacin da ta ga wannan abincin zuciyar ta fara bugawa cikin ranta tana cewa. Wannan ba shine abincin da ta saba tunanin na ci ba. Saboda haka sai ta fuskanci wani tunani a cikin zuciyarta wanda ya rufe duk ilahirin jikinta da gumi. Ameerah ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon abincin da aka ajiye mata wanda kusan kullum shi suke yi, idan kaga anyi canjin abinci toh bako aka yi a gidan. Miyar kuka ce koriya sharrr da tuwon dawa. Ji tayi duk ƙarfin zuciyarta sai da ta hautsine ta fara jin tashin zuciya kamar zatayi amai. Sai ta ji hawaye suna zuba daga idanuwanta. Wannan ba sabon abu ba ne a gare ta, amma yau sai ta ji kamar ba zata iya ci ba duk kuwa da yadda taji cikin nata yana neman agajin bashi wani abun. Ta ƙara jin takaici na rufe fa.

Ta ɗakko ta riƙe kwanon a hannu tana jin motsin da zuciyarta ke yi. A cikin tunaninta tana ganin kanta a wani gidan masu kuɗin inda abinci irin su chips da egg ko noodles da meat suke a teburin cin abinci mai kyau. Ta riga ta yi mafarkin cewa tana cikin gidan wanda ba ta damu da ƙarancin abin da zata ci ba, tunanin ta sai hasaso mata taliya da nama ko dankalin turawa da kwai yakeyi. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kallanta ta sake kaiwa cikin kwanon tuwo da miyar kukar dake ɗauke da ƙamshin daddawa mai shegen wari.

Hawaye ne suka ƙara zuba a fuskar ta. Zuciyarta ta riga ta gama kissima mata abincin masu kuɗi mai rai da lafiya shi yasa a yau wannan abinci ya zama kamar wani cikas a cikin zuciyarta. Ɗaki ta shiga wanda ya cika da gumus na daddawa da warinta. Wannan yana ƙara tursasa mata haushi a  zuciyarta, tana jin kamar kar taci tuwon da har ya gama sandarewa saboda rashin samun kwano mai riƙe zafi. Tana hawaye ba tare da wani fashi ba ta ɗauki cokali tana jin ƙin ci, amma ta fara ci cikin ranta tana tunanin cewa wannan ne rayuwar su, wannan ne ƙaddarar su a halin yanzu da suke ciki. Amman nan gaba kaɗan rayuwar su zata sauya daga halin rashi zuwa halin samu.

"Ashe kin dawo?" Mama ta faɗa tana kallanta. Ameerah da ke tauna tuwon bakinta kamar mai cin maɗaci tace.

"Eh Mama na dawo da wani irin ciwon kai." Ta faɗa dan kar ace zata je ɗebo ruwa. Ba zata iya fita ba a halin yanzu saboda ƙuncin da ke addabar ruhinta.

"Ayya! Toh ki gama cin abincin sai kisha magani ga ragowar paracetamol can da na sha ɗazu. Da har Inno tana cewa idan kin dawo zaki yi mata wanki." Ameerah ta turo baki, ita fa ta lura a gidan nan nasu ba ta da wani ƴanci na jin daɗi. Kullum daga wannan aikin sai wancan babu maganar ta huta. Bata ce komai ba sai danna lomar tuwo cikin baki tana dauke numfashi dan rage shakar ƙamshin miyar. Tana kammala cin abincin ta fitar da kwanon ta dawo ɗakin ta rage kayan jikinta. Kwanciya tayi tana sakin murmushi a ɓoye, yau itace zata huta, itace zata kwanta bayan ƙaryar ciwo da ta jibgawa kanta. Ehh mana idan ba haka tayi ba Mama da Inno sun dunga wijijjiga ta kenan kamar ƴar kwallo. Da yake baccin ta ke ji, kuma hutun ta ke so. Bata daɗe ba bacci ya yi gaba da ita.

*****

Duk wanda ka gani a cikin hall ɗin yana cikin farin ciki yake, sai dai farin cikin da Ameerah ke ciki za'a iya cewa yafi na kowa dake wajan dan da ka ganta zaka tabbatar da hakan. Kowa ka gani a wajan da partner ɗin da yake magana, ko wa gang amman banda Ameerah da ta ke rungume da littafi hannunta riƙe da biro tana wani irin blushing kai kace tana cikin shauƙin soyayya ne.

"Hello student, please kowa ya samu waje ya zauna. Muna fatan kowa ya shirya?" Gabaki ɗaya mutanan hall ɗin aka amsa da.

"Yesssss sir."

"Very good. Muna fatan kuyi wannan jarabawar ku samu ku dace. Idan kuka yi Allah ya baku sa'a akwai waɗanda zasu iya tafiya ƙasar waje ƙaro karatu. Dan haka a dage a kuma maida hankali." Ameerah ta ware ido jin an ambaci ƙasashen waje. Dagaske idan ta samu ta haye zata bar Nigeria? Ba ma gidan su zata bari ba ƙasar duka? Ta rintsa ido tana jin wani abu yana yawo mata cikin jikinta. A fili ta ke furta.

"Ya Allah ka cika min buri na." Tana faɗa ta sake crossing hands ɗin ta saman kirjinta tare da sakin wani ƙayataccen murmushi da yake fitowa tun daga can ƙasan ranta. Daga nan kowa aka bashi questions dan suna da yawa kusan su saba'in ne a hall ɗin jarabawar. Su ukun duka suna tare duk da cewa ba kusa suke zaune ba, kowanne da seat ɗinsa. Yaseer yana daga gaban seat ɗin Ameerah. Yayin da Meenal ke bayanta ya kasance tana tsakiyarsu. Kowannen su sai da ya yi Bismillah kafin su fara karanta questions ɗin. Tun da ta ɗora idanunta kan takardar murmushi ta ke da alamar tambayoyin ba zasu yi mata wahala wajan tsargewa ba......

Shin Ameerah zata cika mafarkin nan nata? Aka ce wai rai da buri. Ita kuma duniya labari ce. Muje zuwa.✍️