MAKIRIN IKO
by @mrsisham12
☠️☠️ MAKIRIN IKO ☠️☠️
The hunted house 🩸
Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩
MALLAKIN
MRS ISHAM
03
Tafiya yake yi a cikin falon cikin nutsuwa kamar me neman wani abun ko ina na cikin falon har izuwa kitchen se da ya kare wa kallo amma be ga wani abu ba hakan yasa ya samu guri ya zauna a kujera yana jiran Mahmoud tare da jinjina abinda ya faru.
A bangaren wayannan aljanun yaran kuwa suna tsaye a cikin falon suna masa dariya amma shi sam baya kallon su.
“Ya Mahmoud na gaji da zaman gidan nan kullum abubuwan da nake ji nake gani sake Ƙaruwa suke”
Siyama ta faɗa cikin damuwa
Mahmoud dake riƙe da duka hannayenta ne ya ce
“Su menene din ki ke gani?meyasa ni bana ganin su?me yasa ke kadai suke tsoratarwa? Tun jiya na rasa gane kan ki Siyama. amma in sha Allah gobe zan ɗauke ki muje asibiti kin ji ko?”
Wani irin kallo ta masa kawai domin ta ma rasa me zata ce mai dan duk abinda ta faɗa ta san ba yarda ze yi ba. Hakan yasa ta cire hannunta cikin nasa.
“Yanzu bari in je in sallami Bilal se in dawo in dafa ko in siyo miki abinda zaki ci”
Bata ce masa komai ba har ya fita Kwanciya tayi tana me rungume pillow gaba daya abin duniya ya haɗu ya mata yawa ga cikin da take fama dashi ga abubuwan da take gani a gidan nan ga shi duk yanda tayi Mahmoud yaƙi yarda da abinda take faɗa masa.dafe kan ta da ta ji yana mata ciwo tayi tana lumshe idanunta.
Saukowa ya yi ya samu Bilal na zaune a falo yana jiran sa,zama yayı kusa dashi yana
“Am so sorry about what happened earlier “
Murmushi Bilal yai yace “bakomai abokina,na san Siyama ba haka take ba kuma wannan ba dabi’ar ta bace. Tabbas akwai abinda yake faruwa da ita. Abokina ka tsaya ka yi bincike sosai ze iya yuwa abinda take faɗa maka na abubuwan da take gani da gaske ne saboda kai ba zama ka ke yi a gidan nan ba in ka fita tun safe se yamma ko dare ka ke dawuwa. Ita kadai take zama babu wanda yasan abinda ke faruwa cikin gidan nan se ita tun da ita ce mai zama cikin sa. Kar ka mayar da wannan matsalar bakomai ba mu zo muna cizon yatsa a gaba.”
Jinjina kai Mahmoud yayi saboda ya yarda da maganar abokin nasa hakan yasa shi futar “hakane ni ma nayi wannan tunanin in sha Allah gobe tare zamu fita ni da ita zamu je asibiti a duba ta”
Cike da mamaki Bilal yake kallon Mahmoud jin sunan asibitin da ya kira “ban gane zaku je asibiti ba? Ya zaa yi yarinya tana fama da spiritual problem kazo kana maganar za ka kai ta asibiti Mahmoud are you okay ?”
“Nooo Bilal babu wani maganar spiritual problem anan. Ta ya ma zaa yi a ce wannan sune signs nashi ?you know ni ban yarda da irin wayannan chamfe-chamfen ba,wasu aljanu da wasu fatalwa duk karyane they doesn’t exist,kawai it lives in people’s mentality ne amma duk karyane,see gobe zan kai Siyama asibiti zan nema mata professional Therapist “
Zallan mamaki da al’ajabi ya hana Bilal dauke idon sa akan Mahmoud bakin sa kawai yake kallo shi se yanzu ma yake tunawa tun suna secondary school Mahmoud be yarda da wayannan abubuwan he always denied the fact that ghost and evil spirits exist in this world.
“Hmmm Allah ya kyauta”shine iya abinda Bilal ya iya furtawa dan ya san duk abinda ze faɗawa Mahmoud akan abinda ya shafi maganar abinda Siyama take fama dashi ba abinda ya shafi asibiti bane to ba yarda ze yi ba hakan yasa yace shi ze tafi.
Har bakin motar sa ya masa rakıya yayında ya dawo ya shiga kitchen ya musu toasting bread ya hada kayan tea ya wuce bedroom tana kwance ya same ta.
“My love tashi ki sha tea bana son ki kwanta haka”
“Ya Mahmoud am not hungry “
Ɗaura tray da ya shigo dashi yayi akan table ya jawo sa kusa da gadon sannan ya sa hannu ya dagota
“Kına son babyn mu ya zauna da yunwa ne?please ki ci abinci kinji “
Bata son masa musu hakan yasa ta sha tea da bread din ta je tayi alwala da wanka tafito ta shimfida sallaya tayi sallah isha da basu yi ba tana idarwa ta hau gado ta kwanta ko da kwanciyar ta bata dau lokaci ba bacci yayi gaba da ita.
Shima bayan ya gama ne yayı wanka yayi alwala yazo yai sallah ya fara duba muhimman abubuwan aiyukansa kamar kullum se kusan 11:00 bacci ya fara ɗaukan sa hakan yasa ya ajiye komai ya kwanta yana musu addua tare da kashe wutar dakin.
Karan buga kofa da ake yi ne ya tasheta yasa ta farka a firgice tana dafe kirji tana “Innalillahi wainnailaihi rajuun” buga kofa ake yi kamar za'a ɓallasa da karfin gaske. kunna hasken dakin tayi ta kai idonta kan agogo ta ga karfe biyu da yan mintuna,mutsuke idonta tayi tana zuro kafafunta ƙasa tare da kallon fuskar Mahmoud yana sharan baccin sa sabanin ita da bazata iya yin bacci ba saboda karar buga kofar da ake yi kuma da duka alamu kofar dake downstairs ake bugawa. Hula ta sanya akan ta sannan ta miƙe tana riƙe cikinta ta ficewa a dakin. Tana tafiya a hankali a hankali har ta sauko ƙasa wannan kofar da yake a garkame din shine ake bugawa ta ciki har kofar yana jijjiga kamar ze ɓalle. Kirjinta na bugun tara-tara ta nufi bakin kofar tana ɗaura hannunta akan kwaɗon tunani ta fara ta ina zata samu ɗan mukullinsa.
Wasu saututtuka da gurnani haɗe da ihu take jiyowa a cikin dakin marasa dadin ji haka yasa ta kai idonta gurin wani ɗan ƙaramin ɓuli dake jikin kofar,dakyar ta iya gano tarkacen dasu ke ciki tsofoffin kujeru ne da su gidan sauro ga yanan gizo da ya mamaye ko ina a dakin iya abinda ta iya gani Kenan hakan yasa ta kyalla idonta wani gurin daban fuskar wata mata tacı karo dashi tana sanye da fararen kaya gashin kan ta a hargitse idonta bakikirin abun tsoro da hanzari ta ja baya tana kokarin faɗuwa ta ji an riƙe ta ta baya kamshin turarensa ne yasa ta fahimci shine ɗago kai ta yi suka haɗa ido.
“Ya Mahmoud..”
“Naam siyam me ya fito dake da wannan daren sannan me ya kawo ki bakin wannan kofar?”
Ya tambayeta yana tsareta da idanu yana mata kallon da tunda suke be taɓa mata irin sa ba domin idanunsa a tsaye suke ya kafeta dasu ko kyaftasu baya yi.
Cikin in ina tace “ya Mahmoud ina bacci shine na ji ana buga kofar da karfi shine na zo dubawa “
Kallon kofar ya yi kafin ya dubeta gently yace “okay amma daga yau kar ki sake tunkaran inda wannan kofar take wannan ya zamo karon ki na farko kuma na karshe, in kuma kin ƙi ɗaukan shawarata za ki yi danasani mu je ki kwanta “
Ya faɗa yana riƙe hannunta suka soma tafiya,maganganunsa sun tsaya mata arai matuka,tana son tambayansa menene yasani dangane da wannan daki kuma me yasa yace zata yi danasani amma bata ga fuskar tambayan sa haka ba saboda fuskarsa a haɗe yake babu alamar wasa tamkar ba Mahmoud din ta ba.
Yana rike da ita suka haura upstairs sun zo dede bakin kofan dakin su Kenan ta ji ya sake hannunta ko da ta ɗago zata kalle sa taga wayam babu shi babu alaman sa a gurin ita kaɗai take tsaye a wajen babu shi. Kalle-kalle ta fara daga inda take tsaye amma babu kowa ko inuwar mutum babu hakan yasa ta shiga dakin tana shiga ta ci burki ta tsaya saboda hango Mahmoud da ta yi yana kwance yana baccin sa peacefully akan gado. Dakyar kafafunta suka ja ta izuwa kan gadon ta zauna tana kurawa fuskarsa ido tabbas Mahmoud yana da nauyin bacci ba kasafai abu yake tayar dashi ba,fahimtar da tayi baccin sa yayi nisa ne ta yasa ta gane wanda suka hauro sama dashi har ya rike ta suka yi magana ba Mahmoud bane,nan wani sabon tsoro ya rufeta,lalubo Mahmoud tayi ta kwanta a jikinsa tana kamkamesa wasu hawaye me zafi suna saukowa a kumatunta ita yanzu komai ya fice mata a rai duk yanda take so da ɗaukin gidan nan yanzu ya fice mata arai tama fi kaunar kurkuku akan gidan nan.
Rufe idanunta kawai tayi bawai dan tana jin bacci ba saboda abinda ta gani yanzu baze bar ta ta iya runtsawa ba.haka yau ma tana jin sa ya je yayi alwala yazo yana tashin ta seda ya tabbatar da ta tashi kafin ya tafi masallaci. Sallah ta yi ta dawo gado ta kwanta dan yau bata jin tana da kuzarin da zata iya girka komai. Se karfe bakwai Mahmoud ya dawo hannun sa riƙe da kula dubansa tayi bayan ya shigo tana tambayarsa
“Ya Mahmoud wannan fa?
“Gida naje na karɓo mana kayan karyawa yau base kin mana breakfast ba tunda zamu je asibiti”
Bata ce komai ba ta zuba musu suka ci ya shiga wanka ya fara shirin fita tana kallon sa kuma bata tashi ba. Ta cikin madubi ya kalle ta yace
“Ki tashi mu shirya muje asibiti baby”
“Ya Mahmoud se ka dawo ni kam ba asibitin da zan je” ta faɗa murya a sanyaye.
Juyowa ya yi yana duban ta da kyau “but why?hun? meyasa bazaki je ba? Na samo mana appointment da doctor fa”
Kan ta a ƙasa ta ce “ya Mahmoud please ka yi hakuri amma ni lafiyata kalau”
Ba irin lallashin da be mata ba amma ta ƙi yarda. ya yi-yayı har ya gaji ya hakura.
Jakan zuwansa wajen aiki ya ɗauka ya je bakin gadon ya manna mata kiss a kumatu sannan ya mannawa cikin ta. Sallama ya mata ya fita Kwanciya ta yi tana jin Motar sa yana barın gidan. Ajiyar zuciya ta sauke,wani tunani ne ya faɗo mata hakan yasa ta miƙe kamar wacce aka mintsina tana saka doguwar hijab. Musa me gadi yana zaune yana jin redio ya ji sallamanta.
“Hajiya ina kwana”
“Lafiya lau musa me ka ke yi yanzu?”
Ta tambaye sa tana gyara tsayuwarta
Musa na washe baki kamar gonar auduga yace “hajiya babu komai kawai redio nake saurara za'a yi miki wani abun ne?"
“Eh,akwai guduma ko kuma gatari zaka fasa min kwadon dakin ƙasa ne na ɓatar da ɗan mukullinsa”
Tashi ya yi yana “to hajiya ina da guduma” cikin dakin sa ya shiga ya ɗauko guduma ya fito gaba tayi ya bita a baya suka shiga nuna masa wannan kofar dakin tayi nan musa ya fara aikin fasa kwaɗo sun kusa mintuna talatin yana abu daya se daga karshe dakyar-dakyar kwaɗon ya ɓalle ya faɗo ƙasa.
“Yawwa musa na gode maka zaka iya tafiya”
“To hajiya” tana tsaye a bakin kofar se da ta tabbatar da ya bar falon yayi waje tukun ta dawo da hankalinta kan kofar.
A hankali ta tura kofar tana faɗin “Bismillah “ shiga ta yi tana tura kofar karo ta fara ci da kwanukan samiru na zamanın da wanda aka yi amfani dasu tsawon shekaru hamsin,tsallake su tayi ta wuce tana toshe hancinta da hijab din ta saboda kuran dake tashi a dakin hannu dayan kuma tana yaye yanar gizon da ya rufe ko ina.
Dakin ta ƙarewa kallo komai nasa na nan ga kujeru na zamanın da da suka sha kura da yanar gizo su table ga agogo da kana gani kasan da zinari aka yi sa,ga su kumbo a watse a ƙasa. tafiya take a dakin tana dube-dube ta ji karar faɗuwar abu hakan yasa ta nufi inda ta ji ɗaran labule ta gani a wajen hannu tasa ta yaye labulen ta ga kofa ce a gurin buɗewa tayi ta shiga. tun daga bakin kofa ta fara cin karo da wasu irin kayayyakin da wasu zane da kana gani base an faɗa maka ba kasan na matsafa ne, ga kwarangwal din mutane da ya kusa cika dakin an tara su a gefe daya, a kasan dakin kuwa an yi wata zane da jan gari kamar tambarin wani abu tsakiyar sa ga kwaryar karfe cike da jini ya daskare,ga su kofuna cike da jini. Ga kwarangwal din kan mutum shine a tsakiya.hakan ya tabbatar mata da duk ma wanda yayi rayuwa a wannan daki to tabbas cikakken matsafi ne.
Idonta ne ya sauka akan wani katon akwatin glass wanda kana ganin duk abinda yake ciki ta waje. Wasu irin turnakakkin hayaki ne a ciki kala-kala masu yawa suna ta yawo a cikin akwatin da alamar hanyar fita suke nema hayakin nan babu kalan da babu daga ja,fari,shude,Kore,baki kala-kala suna ciki. a hankali kafarta ya fara jan ta izuwa wajen akwatin ta tsaya a gabansa hannunta ne ya fara rawa wata murya ta ji me girma da ban tsoro yana fadin
“Ki buɗe mu!ki buɗe akwatin nan “
Runtse ido ta yi cikin jarumta ta sa hannunta ta buɗe murfin akwatin ya faɗi ƙasa da sauri ta ja baya tana ɗaga kanta sama tana ganin yanda wayannan hayakin suke shawagi a saman dakin dariya me sauti yana tashi muryoyi na faɗin
“Ruhikan mu sun samu ƴancin,ruhin mu ya samu ƴancin da ya jima yana so”
Abinda ruhikan suka dinga faɗa Kenan suna dariya kafin daga bisani suka dungule guri daya suka zama abu daya.
Zare idanu kawai take yi jikinta da kafanta rawa kawai yake yi ta ga abinda bata taɓa gani ba,guduwa take son yi domin ceton rayuwarta amma kafafunta bazasu iya ɗaukan gangan jikinta ba. Wannan ruhin da suka dungule guri daya ne suka nufota suka nufo fuskarta da gudun gaske tana tsaye babu abinda take iya yi se girgiza kan ta kafin ta ankara dungulallen ruhin ya shiga bakin ta gaba dayan sa. Wani irin kara ta sa me amo ta faɗi akan guiwowinta jikinta na jijjiga tana sa hannunta abakinta kamar ze shige ciki,nan take muryarta ya soma canzawa yana koma wa mara dadin ji da saurara ga fatar jikinta da ya soma sauya kala izuwa fari fat kamar toka duk inda ya kasance mazaunin jijiya se da ya fara tsatstsagewa yana fitar da jini, ko ina na jikinta se da ya tsage idonta ya koma baki wuluk babu ɗigon fari a cikin sa kafafunta suka lankwashe suka koma baya,takai mıntuna goma tana ihu da kururuwa tare da janzawa izuwa abubuwa da dama,hannu tasa ta keta hijabin jikinta gida biyu ta yatsar a ƙasa tana huci kamar zaki ƙarewa dakin kallo ta yi da idanunta masu ban tsoro da firgitarwa kafin ta fashe da wani irin dariya me sautin gaske da se da ilahirin daki ya ɗauka.
Musa na zaune har karfe uku saura yunwa gaba daya ya soma nukurkusar shi,ga shi ya ji hajiyar tasa shuru hakan yasa ya je bakin kofar falo ya tsaya yana ta kwala sallah ma amma shuru babu wanda ya amsa shi yafi mintuna biyar tsaye amma shuru hakan yasa ya koma bakin gate ya zauna.
Karfe bakwai Mahmoud ya dawo gida musa ya bude masa gate ya shigo
“Sannu da zuwa yallabai”
“Yawwa sannu de musa “ ya faɗa yana zaro dubu biyu a aljihunsa ya basa karba yayi yana kwararo godiya
Kai tsaye falo ya shiga yana kiran “my siyam where are you am back baby”
Shuru ya ji hakan yasa ya yi tunanin tana daki a kujeran falo ya wurga jakansa ya haura.ko da ya shiga dakin nan ma wayam babu ita babu alamar ta. Ajiye jakarsa yayi ya fara tunanin to ina ta shiga ko wani daki dake upstairs din nan se da ya duba da cikin toilet amma bata ciki,hakan yasa cikin sauri-sauri gudu-gudu ya sauko ƙasa ya shiga kitchen shuru babu ita. downstairs ma haka ya gama duba ta babu ita amma be shiga wanann dakin ba saboda be lura abuɗe yake ba fita a compound yayi yana nufan inda musa yake
“Musa ina Siyama take ko ta fita ne?”
“Ah ah alhaji hajiya bata fita ba tana cikin gidan nan rabona da ita tun 9 na safe wato bayan ka fita,to karfe uku naga banga abinci ba kin kofa ba na je nayi ta sallama amma shuru “
“Kuma ka tabbata bata fita ba”
“Kwarai alhaji bata fita ba gaskiya “
Be kuma bi ta kan musa ba ya sake komawa cikin falon nan ya sake dubata a karo na biyu amma babu ita a ko ina wanann dalilin yasa ya fito suka fara neman ta shida Musa a cikin gidan amma ba inda ba su duba ba babu ita.
Hankalin Mahmoud in ya yi dubu tofa ya tashi domin ga wayar ta na kan gado ɓalle yace ze Kira ta dawuwa daki yayi ya zauna yana buga uban tagumi. Ƙarar buɗe kofan toilet yaji wanda hakan yasa ya ɗago kai a sukwane yana kallon ta kamar yau ya fara arba da ita tana sanye da daguwar riga ya jiƙe jagaf.. daga sama har ƙasa ɗiga take yi da ruwa hatta gashin kan ta a jike yake kamar wacce ta shiga teku ta yi wanka
Da sauri ya nufeta “thank goodness..Siyama ina ki ka shiga gaba daya kin tayar min da hankali “bata ko kalli in da yake ba ta nufi gado tana kokarin hawa ta kwanta ya yi saurin riƙe kafadarta
Wani kallo ta masa wanda be san lokacin da ya janye hannun sa a kafadan na ta ba,kallon fuskanta yayi ya ga yanda ta haɗe girar sama da na kasa tamkar bata san me ake Kira da kalmar dariya ba.
“Siyam what’s wrong with you ko ba ki da lafiya ne?me yasa ki ke min irin wannan kallon na miki laifi ne ?”tana tsaye ki kam kamar gunki ba Uhmm ba uhm uhmm.
“Yau ya Mahmoud din na ki kema rowan jin muryarki? Yanzu de ki cire wannan wet cloth din in ba haka ba ze sa ki mura”
“Dagaske ya Mahmoud?”ta yi maganar kamar yar karamar yarinya
Gyada mata kai yayi yana zuwa bayanta ya soma Jan zip din rigar na ta,kamar an ce masa ya kalli mirror yana kallon madubi ya ga wata iriyar halitta me ban tsoro da razanarwa a tsaye a gaban sa a maimakon Siyamarsa. wani irin shaking jikinsa ya fara da kyar ya ɗago ya kalli fuskar Siyama yaga tana masa murmushi kamar bakomai. Sake kallon ta cikin mudubin yayi yaga wannan halittar ce tsaye a gabansa wani irin fitsarine ya zo masa wanda saura kaɗan ya saukosa a wando a maimakon ya karasa ja mata zip din kasa se ya zuge mata shi sama ya juya ze bar dakin simi-simi har ya kai bakin kofa ya gan ta a gabansa
“Ya Mahmoud dina ina ne ka ke kokarin zuwa”
“Ba..baa babu ko ina siyamata zan ɗauko jakata ne a ƙasa” ya faɗa cikin in inan da be san yana da ita ba.
“Ba se ka je ba ni zan ɗauko maka “ ta faɗa tana miƙa hannunta yayi tsayi dogo kamar igiyar shanya ya sauka ƙasa se ga hannun ya ɗauko jakan nasa da ya baro a falo.
Karɓan jakar yayi kamar ze yi kuka yace “my siyam dan Allah ki bar ni in je in dawo”
Noke kafaɗa tayi tana masa murmushi “ah ah ban inda zaka “
“To to to” ya faɗa yana komawa cikin dakin. shigar sa yayı dede da soma ringing wayansa da sauri ya je ze sa hannu ya ɗauka ta rigasa, matse wayar a hannunta tayi nan take wayar ta lankwanshe. Duban wayar sa da ya siya million daya da rabi yayi ya ga yanda ya koma yasa shi furta
“Siyama meye ki ke yi haka dan Allah in ma wasa ki ke yi dan ki tsorata ni ki bari wlh cikina ya kunshi ruwa”
Sake wayar tayi ta mayar da hannunta a wuyansa ta masa shaka bana wasa ba ta ɗaga sa sama kafafunsa na lilo a ƙasa,hannu yasa yana buge hannunta amma ko gizo bata yi ba tana shake dashi ta je stairs na farko tana sakin murmushi ta wurga shi tsakiyar falon da karfin gaske,ƙaran tim kawai kake ji tun da ya faɗo be kuma motsi ba saboda suman da ya yi. Cikin İsa da takama take saukowa ƙasa musa dake tsaye yana leken su jikinsa na rawa ne yaji an taɓa sa ta baya yana juyawa ya ga ita ce tsaye a bayansa idanunta sun koma baki kirin suna haɗa ido ya yankı jiki ya faɗi a sume.
Se karfe tara Mahmoud ya samu damar farfaɗowa zama ya yi yana jin kansa na wani irin sarawa saboda ba ƙaramin buguwa ya yi ba riƙe kan ya yi yana miƙewa tsaye hanyar fita a falo ya gani a buɗe hakan yasa ya soma tafiya yana ɗangyasa kafarsa. Muryar ta ya ji tana
“Ina ne inda ka ke tunanin zaka je?”
Slowly ya ɗaga kansa saman celling falon saboda a sama yake jiyo muryar nata ganin ta yayı zaune a saman celling up side down.
“Dan Allah ina me baku hakuri ku kyaleni ku Kyale min matata ba mu yi muku laifin komai ba”
Ya faɗa yana haɗe hannayensa guri guda alamar roƙo,dirowa a gabansa ta yi tana ɗaura hannunta a goshin sa
“Kune ku ka shigo mana har muhallin mu,ku ne ku ka biyo mu domin ku takura mana”
“Wallahi ah ah na rantse da Allah ba mu yi hakan da nufin cutar da kowa ba”
“Ohhhh hakane ? To shikenan mu yi wani wasa” ta faɗa tana buɗe tafin hannunta lemon tsami ne guda uku suka bayyana a hannun nata.
“Wannan lemon tsami guda ukun,a cikin su zaka zaɓi wanne ne asalin lemon tsami. Matukar ka canki asalin lemon tsami to tabbas zamu bar ku kai da matar ka har abada amma muddin baka canka daidai ba..” ta karishe kaganar tana tsare sa da idanunta da suka kara girma,zufa ne kawai yake ketowa Mahmoud domin kuwa yasan wannan wasan yana da matukar hatsari shin me ze faru in be zaɓa dede ba?cikin tsoron abinda ze faru yace
“Dan Allah ku yi hakuri ku rabu damu a bar maganar wannan wasan na roƙe ku”
Lankwasa kan ta tayi tana zare masa ido ta ce
“Wato bazaka yi ba Kenan “ girgiza kai yayi cikin tsoro ya furta
“To in ban zaɓa daidai bafa mai ze faru?!”
“Matar ka da ɗan cikinta ruhinsu ze zama mallakin mu”
Cikin tashin hankali jin abinda ta faɗa ya zube a kasa yana rike kafafunta yana
“Ku yi hakuri su kadai ne farın cikina kar ku rabani da matata “
Kamar gilmawar walkiya ya ganta zaune a gabansa tana turo masa hannun nata me ɗauke da lemon tsamin kusa dashi
“To maza ka zaɓi wannene me kyau din. Saboda shi ne kawai hanyar ceton matar ka da ɗanta. Saura lemon tsami biyu din daya ruhin matar ka ne a ciki daya kuma na ɗanka. Matukar baka yi zaɓi me kyau ba a gabanka zan dagargaza ruhikansu “
Jiki na rawa Mahmoud ya miƙa hannu yana kallon fuskarta. Hannunsa na rawa ya fara raba ido yana tunanin wanne ne ze zaba wanda baze zame masa matsala ba..
“ ya Allah ina me rokon ka da ka bani saa in zabi asalin lemon din,ya Allah ka sani kasan yanda nake son matata siyama bazan taɓa barın wani mugun abu ya same ta ba” wannan sune addua da yake ta yi a zuciyarsa a yayinda hannunsa ke rawa runtse ido ya yi ya dauki lemon tsamin da ya kasance shine a tsakiya.
Da hankali ya ɗaga kai suka haɗa ido da ita yaga irin kallon da take masa wani irin kugi cikin sa ke masa gaba daya jikinsa ya jike da zufa sharkaf har diga yake yi tsabar masifar da yake ciki.
Zuba lemon tsamin tayi a kasan carpet ta wura musu iskan bakinta nan take na farko ya rabe biyu wato shine asalin lemon tsami na tsakinya da ya zaɓa kuma ya koma kwai kana kallon abinda ke ciki hayyaki ne ke ta yawo cikin Kwan haka na karshen shima hayaki ne cikin sa. Tunda yake a rayuwarsa be taɓa shiga tashin hankali ba kamar yau fahimtar ba asalin lemon din ya zaɓa ba,wani irin ja idanunsa suka yi suka fara zubo da hawaye danasani da kuma haushin kansa ne ya dabaibayesa tabbas yasan ya aikata kuskure da ace ya yarda da kalma daya da ya fito daga bakin Siyama to tabbas da baa zo wannan gabar ba.
Maketacin dariyar da take yi ne ya dawo dashi hayyacin sa.
Wani irin kara ne da be san dagan ina ya fito ba ya cika falon wanda se da yasa hannu ya toshe kunnensa. Yana daga kasan domin ganin yanda gangan jikin matarsa Siyama yake yawo a saman iska tana masa murmushi tare da faɗin
“ kayi bakwana da ita” ta na faɗin haka ruhin ya fita a jikinta Siyama dake sume ta nufo ƙasa da wani irin speed ya ware hannayensa ta faɗa a jikinsa. Rungume ta yayi yana hawaye,kafin ya ɗago fuskanta kallon innocent face dinta yayi da ya koma ja saboda rauninka da taji yai ya daura hannunsa akan cikinta dake harbawa.
“Am so sorry siyam is all my faults da ace na yarda dake da duk wannan abun basu faru ba ki yafe min matata ki yafe min “ ya gama maganar yana fashewa da kuka kamar yaro karami. A hankali ta bude idonta da suka kumbura murya a hankali ta ce
“Ya Mahmoud ka dena kuka.biyan bashin wasu muke yi wasu sun aikata laifi daga karshe mu muke biyan bashi”
“Da na yarda dake da duk bata kai ga haka ba,bana son wani abu ya same ki ko abinda ke cikin ki zan yi iya kokarina na kawo karshen wannan abun “
Murya suka ji yana faɗin “baza ka iya ba,bazaka taɓa iya kawo karshen komai ba yakai Mahmoud Ibrahim alkali” muryar na yin shuru wutan gidan gaba daya ya soma kawuwa yana ɗaukewa. tare da wani irin guguwa da yake tashi a falon kankame juna suka yi shi da Siyama kamar zasu zama abu daya.
“Ya Mahmoud Ina jin tsoro “
“Babu abinda ze faru in sha Allah “ yana rufe bakinsa wanda basu san ko waye ba ya damki gashin kan Siyama da karfi da ya ji aka rabata da jikin Mahmoud aka fara janta a kasa kamar kayan wanki,ihu kawai take yi tana kiran sunan Mahmoud haɗe da jujjuya kanta saboda azabar da take ji. Da gudu Mahmoud ya bi ta yana kwala kiran sunanta amma ya gagara cin mata saboda da mahaukacin gudu ake janta,kofan guest toilet dake falon ne ya bude da kansa aka wulla Siyama ciki sannan kofan ya rufe kan sa kirif da karfi koda Mahmoud ya isa ga kofar da iya karfin sa yake dukan kofan amma yaki budewa ga kukan siyamansa da yake ji a ciki. Wutar gidan ne ya dauke gaba daya duhu ya damaimaye ko ina na gidan wanda Mahmoud ko tafin hannunsa baya iya gani.
Tun yana jin kukan Siyama har yaji shuru ko ina na gidan yayi tsit baka jin motsin komai ga duhu kamar cikin rami.
A hankali ya fara jin sautin kukan jariri a upstairs da kuma sautin kukan Siyama tana kiran sunansa. Cikin sanda ya fara tafiya yana lalube a cikin duhu har ya rike jikin stairs din haurawa ya fara yi yana tafiya a hankali yana kuma kasa kunne domin sanın takamammen inda sautin kukan na su ke fitowa,wata kofa ya yawuce ya ji an bude kofar hakan yasa ya dawo baya yana motsawo kusa da kofan ya ji ana kuka kasa-kasa a hankali ya tura kofan candles ne guda biyu a kunne su suka dan haskaka cikin dakin babu komai a dakin hakan yasa ya shigo ciki yana shiga kuwa kofar ta rufe kanta
“Ya Mahmoud “ kallon inda ya ji muryar nata ya fito yai nan ya hango Siyama tsaye a bakin window dake bude iska me karfi na shigowa tana sanye da rigar jikinta se kuma hannunta rike da jariri nannaɗe cikin towel da ya ɓaci da jini haka itama jikinta duk ya ɓaci da jini gashin kanta ya hargitse kamar kan mahaukaciya. Sannan babu ciki a jikinta.
“Ya Mahmoud zan tafi in ba mutuwa na yi ba bazasu Kyale mu ba” ta faɗa tana hawa saman window ta tsaya
“Nooo Siyama dan Allah kar ki yi haka ki dakata Siyama “ya faɗa yana tunkaro ta tana riƙe da baby ta zura kafarta daya waje.
“Noo Siyama don’t do this “ ya faɗa yana girgiza mata kai suna a haka har Allah ya bashi saa ya iso ta a lokacin da take kokarin yin tsalle ta fada ya damƙo hannunta yana damƙota,ta marmashe ta koma ganye ja baya yayı ganin abinda ya faru da gudu ya bude kofan ya fita duk da ko ina duhu baya ganin gaban sa amma gudu kawai yake yi,ji yayi ya ci karo da abu kamar dutse hakan yasa ya daga Kai ya kalli abinda ya buge wani irin katon halitta ne baki kırın idanunsa ja ga kahon dake kan ta tsaye a gabansa da hannu daya wannan dodon ya daga Mahmoud sama da karfi kofar falo ya bude inda wannan dodon yayi wurgi da Mahmoud wanda seda ya fita a gidan gaba daya ya faɗi a tsakiyar titin anguwar da babu kowa kamar matacce yana wurgasa waje kuwa kofar falon da gate din gidan suka rufe kansu.
Karfe hudu na asuba sanyin iskan dake tashi ya kaɗasa nan ya fara dukunkune jikinsa guri daya kafin daga bisani ya buɗe idon a hankali nan ya gansa kwance a tsakiyar titi da sauri ya mike zaune yana karewa anguwar nasu kallo.yafi mintuna biyar yana zaune ya rasa inda ze nufa domin kan sa gaba daya ya gama kullewa hakan yasa zuciyarsa ya basa shawaran zuwa wajen hajiyarsa. Tashi yayi ya karkaɗe jikinsa duk da kuwa kayansa sun yi futu-futu kamar Wanda ya yi wasa da kasa ga jikinsa da ya kukkuje.
Your comments means a lot to me,in bakwa comment zan yi tunanin bakwa jin dadin book din ne
Don’t forget to share,comment and like 👍
Se mun haɗu jibi in Allah yakaimu da rai da lafiya❤️🙏🏻