Chapter 002
by @jeeddah3256
TAREEQ IMAM
Na
Jeeddah Aliyu
002.
Cikin tashin Ummi ta buɗe baki da idanuwa tana kallon fuskar Nana. Da ka kalle cikin idanuwan ummi za ka gano irin tsananin tashin hankali da ta shiga. Tabbas tasan Tareeq ba ya jin magana ga tsokanar faɗa kamar me ko su dake zaune dashi ya fitine su, domin yaro ne mai kiriniya da taurin kai ga baƙar zuciya amma duk da wannan ko kusan ba taɓa kawowa zuciyarta rashin jinsa ya kai haka ba. Dukka Tareeq guda nawa yake yaushe ma ya balaga da zai dinga ɗauko mata masifa irin wannan?"
Tuni idanuwan Ummi sun canza kala cikin yanayi na wanda ya shiga damuwa ta ce.
"Dan ALLAH ba don ni ba kiyi haƙuri maman Nana nai miki alƙawari ko hannun Nana Tareeq ba zai sake taɓawa bare nononta. Sai na hukunta shi bisa laifi da ya aikatawa ƴarki."
Kafin Maman Nana tai magana suka tsikayi sautin muryar Ayya daga bayansu tana faɗin
"Amma gaskiya Amina kin bani mamaki haka kawai wata banza bazara zata ɗauko gantalalliyar ƴarta, su shigo har cikin gidanmu tai wa jikana ƙazafi ke kuma ki yarda, wallahi da dani ku ka fara cin karo da tuni nasa securities sun watsa ku waje masu baƙar aniya."
Ayya ta ƙarasa magana tare da makawa Maman Nana da Ummi harara.
Tun sanda ta shigo parlour har ta ƙarasa magana Ummi tana kallonta, ko kusa ba ta ji mamakin fitowar waɗannan kalaman daga bakin surukarta ba. Saboda ta kwana da sani tana ɗaya daga cikin mutane da suka jagoranci taɓarɓarewar tarbiyyar Tareeq.
"Haba Ayya wannan wacce irin magana ce?" miyasa a duk sanda aka kawo korafi akan Tareeq sai kin nemi kare sa alhali kinsan rashin jin sa duk abun da aka faɗa akansa bana kwakwato zai aikata?"
A fusace Ayya ta ce "To ai ni ba sakarya bace da zan amince da wannan shatin faɗe ba."
"Lallai yau na gasganta abin da ake yaɗawa akanki Ayya, yanzu ke ko kunya bakya ji a matsayin ki na uwa jikanki ya aikata mummuna laifi irin wannan sannan ki goyi bayan sa?"
"Na goyi bayan sa ɗin daga nan in kin fita ki zarce gidan alƙali dan ALLAH dan Annabi kafin wayewar gari mu ga sammaci.
"Ai dole ki faɗi haka saboda kina taƙamar ɗanki mai ƙudi ne, amma ba komai ALLAH na nan shi zai bi mana haƙƙinmu da mahaifin Nana yana raye jikanki har isa ya taba masa ƴa wallahi da sai inda ƙarfinsa ya ƙare duk kuɗin ku ba zai zuba ido yana kallo ana cin zarafin 'yarsa ba."
Cewar Maman Nana tana watsawa Ayya mugun kallo.
"Dallah rufe min baki manufukar mata da alama ba nonon ƴarki aka taɓa ba kawai munafuci da tsugudidi ne ya kawo ki gidanan maza ja gantalalliyar ƴarki ku bar mana gida. Wa ma yasani ko da amincewar ta suke ƴan taɓe-taɓensu, na kuruciya kin zo kina so tayar mana da hankali a wofi."
Ayya karasa magana tare da nuna wa Maman Nana ƙofar fita
Sosai ran Ummi ya ɓaci da furucin Ayya sai dai ba ta da yadda zata yi, ci gaba da ba wa Maman Nana haƙuri tayi tare da rarrashin Nana.
"Ba komai Maman Fadila na haƙura amma ki tabbata ki ja masa kunne babu shi babu ƴata ya fita sabgarta, ki kuma ɗage da wa ɗanki addu'a shiriya tun tafiya ba tai nisa ba ya fara shuka tsiya irin wannan ba a san me anan gaba zai aikata ba. Na barku lafiya"
Daga haka Maman Nana ta ja hannu Nana suka fice daga gidan, yayin da Ayya tabi Maman Nana da baƙaƙken maganganu.
Zazzafan numfashi Ummi ta sauke kafin cikin kwantar da murya ta ce.
"Haba Ayya miyasa za ki dinga goyon bayan Tareeq bayan kinsan ba shi da gaskiya musamman irin wannan mummunan
laifi da ya aikata?"
"Na sani Amina amma jinin kaine da baya taɓa tsallake wuya duk yadda Aliyu ya kai da lalacewa ba zan ji daɗi wata ta zo daga waje har cikin gidanmu ta aibanta shi."
"Amma Ayya abin da ki ka yiwa Maman Nana ba dai-dai bane. Tunda ita aka wa laifi kamata ya yi mu taru mu dukka mu bata haƙuri."
"Ya isa dallah Amina yawan maimaita zance shi ke kawo ɓacin rai, kawai mu ci gaba da bin Tareeq da addu'a.
"Ki fahimci ni Ayya...
"Dallah rufe min baki wallahi Amina da Tareeq bai ɗebo kamaninki ba da nace ba ke kika haife shi ba.
Ayya ta katse Ummi cikin tsawa da fusata. Sannan ta cigaba da fadin "Amma ba abin mamaki bane kiyayyar da kike wa mahaifinsa ce kika tattaro kika dawo da ita kansa."
Jiki a mace Ummi ta juya ta koma kitchen dan bata da saura abin faɗa, Zainab ta miƙe tare da ja siriri tsaki, ta kalli Ayya rai ɓace ta ce "Wallahi-tallahi Tareeq ya fita zakka a gidanan, kullum da kalar masifar da zai jajibo mana yaro sai kace jinin fir'auna."
"Ahir! Zainabu kada na sake jin kin aibanta ɗan uwanki, abun da ya yi Tareeq ai shi ya yi ki idan shi jinin fir'auna ne kema jininsa ce dan kuwa jini irin ɗaya ne ke yawo a jikinku. Duk abin da kika ga yana yi ƙuruciya ce idan mu ka bi shi da addu'a sai ki ga watarana ya natsu ya daina kowanne yaro da irin tashi kalar ƙuruciya."
Fadila da Baby suka kalli junansu tare da taɓe baki, sun kan tuni suka daina shiga sabgar Tareeq duk da uwa ɗaya uba ɗaya ne ya haife su hakan bai sa ya raga musu ba.
Ayya ta maida ganinta akan su Fadila ta ce.
"Ku kuma tsofaffin munafukai naga sai wani tattaɓe baki ku ke gara ku fito fili ku faɗi abin da ke cikin zuciyoyin ku kada ya kashe ku."
Daga Fadila har Baby ba wanda ko kallon arziki yai mata, hakan ya ƙara tunzirata, ta koma ɗakinta rai ɓace.
Ummi tana shiga kitchen a fusace ta zari muciya kai tsaye ɗakin Aliyu tai wa tsinke tana shiga dai-dai ya fito daga wanka waist ɗin shi ɗaure da brown towel yana fito, a fusace Ummi ta nufe shi tana zuwa ta rufe shi da duka duk inda ta samu sauke masa muciya kawai take tana haɗawa da zagi
"Ɗan iska yaro kawai marar jin magana tsabar rashin jin naka har ya kai ka dinga taɓa wa yaran unguwa nono, to wallahi bari ka ji duk ranar da ka sake taɓa wa Nana nono sai na illata ka a gidanan. Sai dai ubanka ya tsinka igiyoyin aurensa dake kaina."
Tsaye kawai Tareeq ya yi yana kallonta da girar ido ɗage duk duka da take masa ko gizau bai yi ba. Tamkar tana dukan itace, Ummi sai haki take yi da kyar take jan numfashinta alamar da ke nuna ciwonta na Asthma ya tashi duk da haka bata fasa kai mishi duka ba gani ta fara galabaita yasa Tareeq ya fizge muciyar hannunta ya jefar ya kama kafaɗunta ya zaunar da ita gefen gadonsa da gudu ya fita zuwa parlour.
"Ya Baby ina inheler Ummi Asthma ta ya tashi."
Tareeq ya faɗa hankalinsa a mugun tashe.
Baby ta zabura da sauri ta nufe bedroom ɗin Ummi.
Fadila ta ɗago cike da takaicin Tareeq ji take kamar ta tashi ita ma ta rufe shi da ɗan banzan duka, cikin ɓacin rai tace.
"Wallahi Tareeq idan ka sake ka zama silar da hawan jini ya kashe Ummi ba za mu taɓa yafe ma ba. Idan kai Daddy shine gatanka mu kuma ita ce gatanmu."
Fadila ta ƙarasa magana mai tattare da karayar zuciya.
Shiru Tareeq ya yi yana sauraren abin da Fadila take faɗa, yayin da fusatattun idanuwanshi ke yawo akan fuskarta fitowar Baby daga bedroom ɗin Ummi riƙe da inheler yasa Tareeq ya bi ta da sauri, da taimakon inheler numfashin Ummi ya daidaita ta ɗago idanuwanta da suka canza launi ta watsa su akan fuskar Tareeq da ke jingine da bango, mugun kallo da take aika masa yasa Tareeq yai saurin kauda fuskarsa.
"Ummi Dan ALLAH ki yi haƙuri ki daina biyewa fushin zuciya, kina dukan Tareeq da duka zai sa ya gyara halinsa da tun kafin ya kawo girman haka ya daina Ummi ki sani duka baya taɓa gyara tarbiyya face ya ƙara jagorantar taɓarɓarewar ta.
Hawaye da Ummi take ƙoƙarin dannewa ne suka silalo akan kumatunta, cikin rawar murya da karayar zuciya ta ce.
"Baby ba za ki gane hali da nake shiga a duk lokaci da aka kawo min ƙarar Tareeq gidanan ba. Lamarin Tareeq kullum gaba-gaba yake yi a maimakon yana girma ƙiriniyarsa ya ragu amma sai daɗa ƙaruwa take."
"Ummi addu'a za ki ci gaba da masa, ni wallahi a wasu lokuta idan naga Tareeq yana wani abu sai naga kamar ba shi ƙadai bane, kamar wani mai shafar aljanu."
Cike da takaicin furucin Baby na ƙarshe Ummi ta galla mata harara, don ba ƙaramin haushi ta bata sai kawai ta ture hannuwanta da ke jikinta ta fice daga ɗakin a daidai ƙofar fita taga Fadila jingine jikin bango.
Ummi ba ta tanka ta ba ta wuce zuwa bedroom ɗinta. Bin bayanta Fadila tai har Ummi ta nufi bathroom jin motsin Fadila a bayanta yasa ta tsayawa tare da waigowa.
Cikin rauni murya Fadila ta ce "Dan ALLAH Ummi ki daina saka damuwar Tareeq a zuciyarki kada hakan ya zo ya shafi lafiyarki mu shiga uku."
"Fadila iskanci Tareeq ya isheni duk wanda ya ga yadda yake tafiyar da rayuwarsa ni za a zarga da rashin bashi kyakkyawar tarbiyya, Kuma Ubangiji shine shaidata ina iya bakin ƙoƙarina."
"Haka ne Ummi amma kowanne ɗan adam da irin jarabawar da Ubangiji yake jarabtarsa da ita domin gwada ƙarfin imaninsa. Kar ki fasa ko nuna gajiyawa wajen yi masa addu'a ubangiji yana sane da halin da kike ciki."
Kyakkyawar ajiyar zuciya Ummi ta sauke a kodayaushe cikin godewa ALLAH take da ya bata, ƴaƴa mata masu hankali da natsuwa lokuta da dama suke kwatar mata da hankali a duk lokaci da irin wannan ta faru.
"ALLAH Ubangiji yai muku albarka Fadila ALLAH ya shirya min Tareeq ya ganar dashi illolin da ke tattare da abin da yake aikatawa.
"Amin ya Rabbil'izzati."
Murmushi Ummi tai kafin ta buɗe ƙofar bathroom yayin da Fadila ta fice .
"Yanzu Tareeq jin daɗin ka ne ka dinga ƙunsawa mahaifiyar mu baƙin ciki?"
Kauda fuska ya yi da bari kallon Baby yana gunguni ƙasa-ƙasa. Duk da Baby ta ga yadda ya yi hakan bai sanyaya mata gwiwa ba, ta ci gaba da faɗin.
"Na tabbata ba za ka so ka zama silar da hawan jini ko ciwon zuciya su kashe ummi ba, saboda haka ka saka kayanka ka je ka bata haƙuri kai mata alƙawarin ba za ka sake aikata kwatankwacin abin da ka aikata yau ɗinan."
Baby ta ƙarasa magana cikin tausasa murya tana kallon gefen da Tareeq ɗin yake jingine ya wani harɗe ƙafafuwanshi wurin ɗaya, yayin da ya yi folding hannuwanshi a ƙirji. A fusace Tareeq ya ce.
"Dan ALLAH Ya Baby ki fita ki bani wuri inaso na saka kayana kada ki ɓata min lokaci."
Waro idanuwa Baby tai tana kallon Tareeq kamar zata sake magana sai kuma ta haɗiye abarta, ta girgiza ta fice abinta.
"Mtsss! Haka kawai Ummi ta bi ta tsangwame ni, ta taƙurawa rayuwata sai kace ni ƙadai ne ɗa. Ita kuma Nana za mu gauraya da ita gobe a school sai naci uwarta wallahi."
Da wannan mita Tareeq ya shirya cikin blue jeans da white colour t-shirt ya ɗora blue p-cap a kansa ƙafafuwansa cikin white trainers, ya bi jikinsa da turaruka masu ƙamshin gaske, bedside drawer ya buɗe can ƙasan wani dictionary ya ɗaga ya ɗauko buddle na one-one thousand ya kirga 50k ya mayar da raguwar kuɗi inda ya ɗauko, kana ya soke wanda ya kirgo cikin aljihun wandonsa, har ya kusa fita daga ɗakin ya tuna da wristwatch ɗinsa da bai saka ba da sauri ya dawo ya janyo drawer mirror ya buɗe wani maidaidaci box ya dauki ɗaya daga cikin tarin agogayen shi. Yana tafe yana saka agogo daidai yana buɗe ƙofar main parlour yaci karo da wata farar yarinya wacce shekarunta na haihuwa ba za su wuce bakwai ba tana zuwa da gudu yayin da take kyalkyalar dariya duk yadda taso ta kauce masa hakan ya ci tura dan sai da ta bangaje shi agogon da yake ƙoƙarin sakawa ya faɗi ƙasa, cikin tsananin tashin hankali ta duƙa ta dauƙo mishi agogo daidai shi ma cikin azama ya duƙa tsoronshi ɗaya idan agogon nashi bai fashe ba. Bai lura da Lokacin da ta duƙa ba sai jin ya yi kanta ya buge bakinshi, sosai ya ji zafin bugun shiyasa ya ɗago a fusace tuni cikinta ya murɗa ko bata yi mishi laifin komai ba ya dake ta balle yau ta shiga komarsa. Ma
i ceton ta hannunsa sai ALLAH.
#Tareeq
#Nana
#Ummi
#TeamTareeqImam.