ƊAYA CIKIN BIYU

ƊAYA CIKIN BIYU

by @mrsisham12

3–4⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️

🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥

🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)

(*Yar lelen jarumai writers*).

Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩

❤️🔥Page 3____4

BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR

A wannan shekaru goma sha biyar da suka shuɗe, MUZNA TAIFUR RAHMAN da kuma MUZAINA TAIFUR RAHMAN basu taka ƙafarsu a kasar Kuwait ba,suna nan suna rayuwar su ne a nan Russia.a tankamemen gidan su da mahaifin su Sarki Taifur Rahman ya mallaka musu, anan suka girma suka yi karatun su da komai kamar yanda Mai girma Sheikhy ya basu umarni kar a dawo dasu gida.har se bayan shekarun nan,to tabbas basu dawo ba,sede dangi ana kai musu ziyara can ƙasar Russia domin dubo lafiyar su,,a yayinda sarki ya damka musu ragamar wani shahararren company sa da yake ƙasar. domin su tafiyar da komai yanda ya dace,se de Muzna ta ƙi bayarda yardar ta, saboda abin da ya shafi sarauta dasu kasuwanci duk baya gabanta hasalima baya burgeta ko kaɗan .mafarkinta shine ta zama jarumar finafinai,kuma burinta ya cika domin yanzu ta zama cikakkiyar model kuma jarumar finafinai da ake ji da ita, yawancin poster ko magazine ko tallan manyan products za'a ga hoton ta a jiki, Muzaina kuma yanzu ita ce wacce ragamar Company sarki Taifur yake hannunta. ita ke juya komai domin duk wani abinda ze d’aga mata daraja tana so,ga shi ta taso da masifar kaunar sarauta.

THE INTERNATIONAL HOTEL CHAIN IN RUSSIA.

Babban hotel ne me girman gaske a Ƙasar Russia,babban dakin taro wanda girmansa baze taɓa iya misaltuwa ba cike yake makil da al'umma mabambamta .daga wajaje masu nisa da kuma kusa. Taro ne wanda ya amsa sunan sa taro,mutane masu mabambamtan addini da kuma a kida suna ciki,musulmai da kuma wa'yanda ba musulmai ba,suna a zaune a high table.kuma in ka duba zaka ga manyan governors ne da presidents ,haɗe da manyan attajirai na manyan ƙasashe. duk sun hallara, harma ka san ba wajen k’ananan mutane bane.

Kama daga larabawa, turawa, indiyawa, africans da de sauran su.

wannan taro yanda ya tara manyan masu faɗa a ji a duniya ya isa ya nuna cewa gomnatin babban ƙasar Russia ce ta shirya sa. domin,taro ne da ake yin sa lokaci zuwa lokaci kuma ya samo a sali ne domin tantance sarauniyar kyau na ƙasar.

Wani Bature ne riƙe da mic a hannun sa,dayar hannun kuma na riƙe da jerin list din sunayen yan matan da suka ci wannan gasa ta kyau na ƙasar Russia, kyawawan yan mata ne jere bisa kan dandamalin ko wacce tasha ado da kaya me ɗaukan hankali tana jiran sakamakon gasar.face mutum daya da kanta ke kallon k’asa,tana tsaye so calmly ba ta wannan rawan kan da sauran suke yi hakan ne yasa ban samu damar ganin fuskarta ba.

Wannan Baturen ne ya soma kiran wacce ta zo ta hudu,tafito taƙarbi roses haɗe da wani dogon kyalle da ke rubuce da miss Russia fourth position,haka aka dinga kira har ya rage saura a kira ta farko, wa'yanda suke tsaye a gun ko wacce kirjinta se lugude yake suna addu'ar Allah yasa a zabe su.

Mutumin ne ya sa'ke furta

" The winner is............"Ya yi Shuru kowa ya matsu so yake kawai a ji wacece wannan wacce ta lashe wannan gasar kyau din.

Se da ya ɗauki mintuna uku kafin da karfi ya ce

" And the winner is......... MUZNA TAIFUR RAHMAN Miss Russia".

Kaurewa wajen ya yi da tafi, yan matan suka soma tafi. wannan kyakyawar matashiyar da kanta ke kallon k’asa ne ta d’ago Jin an ambaci sunanta. Allahu akbar,kyakyawace ta k’in k’arawa domin kuwa tafi ko waccen su kyau.

Tsalle ta yi sannan cikin jin dadi ta rungume wacce ta ke kusa da ita, ta soma tafiya cikin cat walk,tana nufan wajen wannan baturen,jikinta na sanye da doguwar riga me masifar kyau,riga ce tsukekke daga sama zuwa cikinta,kasan kuma ya bazu sosai launin pink da launin baƙi,yasha ado da wasu azababbun duwatsu k’ananu daga sama har kasa.yana da doguwar hannu da yanka-yanka,kafarta na sanye da doguwar takalmi me masifar tsini.ga wuyanta da ke daure da yar siririyar sarka wanda Kai da kanka in ka gani batare da an faɗa maka gold bane zaka fahimci hakan.Haka d’an kunnen shima bayi da hayaniya komai dinta so simple and breath taking. ko ina na jikinta a rufe yake se dogon gashinta da aka mayar dashi curl hair style,fuskarta yasha adoh .kyakyawa ce sosai ta ajin farko matashiya ce yar shekara ashirin kuma model and actress,.tana tafiya cikin burgewa tana daga hannunta fuskarta ɗauke da murmushi har ta isa gaban wannan mutumin yai shaking hand dinta yana faɗin

" Congratulations MUZNA".cikin zazzakar muryarta ta ce " thank you".

Wannan dogon kyalle da yake rubuce da winner miss Russia,aka rataya mata a wuya wani juyi ta yi sannan ta soma tafiya irin na models har ta isa tsakiyar stage din,ta ɗan jujjuya cike da farin ciki.ta koma wajen da ta baro aka saka mata crown a kai tare da bata wani hadaddiyar roses masu kamshi da kyau.nan wajen ya kuma ƙaurewa da tafi ga hasken Cameras ta ko ina ana ɗaukan ta a hoto,ba ta waje a ka yi ta yi godiya sannan ta sa'ke da bayar da ɗan takaitaccen tarihin ta,sannan aka bata kyautar makudan kuɗaɗe,abokan gasan nata daya bayan daya suka zo suna rungumeta domin tayata murna,ita kuwa bakinta ya kasa rufuwa murmushin dake kan fuskarta ya kasa gushewa wanda shine yabada damar fito da azababben kyawu da Allah ya mata me kid’ima duk wani dan adam.

Fara ce sol Jajajir da ita,farin ta yana d’aukan ido na fitan hankali,kun san yanda farin larabawa yake base na muku dogon jawabi ba,amma duk da haka farin fatarta ya zarce misali.tana da tsayi dede gwargwado domin baza'a sakata a sahun gajeru ba,haka zalika tana da jiki haɗe da diri me daukan hankali. idan muka dangana zuwa fuskarta kuwa,tana da dogon fuska matsakaici, me ɗauke da manyan idanu masu haske sosai,kalar kwayar idonta light brown,sun kasance lumsassu,ga dogayen gashin ido da suka yi wa idon kawanya,tana da dogon hanci wanda ya kasance bangaren hagu a ɓule yake an saka masa nose pin,gashin giranta kamar wanda aka yi caving dinsa alhalin a haka yake,idan muka gangaro zuwa bakinta kuwa tana da cute small lips da suka kasance pink sosai gwanin burgewa da ɗaukan hankali.wasu kwantaccun suma ne kwance a gaban goshinta da yai luf luf,tana da tsawon gashi wanda ya kawo har kunkuminta duk da kuwa an mayar mata da gashin nata din zuwa curl hair style.kalar gashin kuma se aka mayar da shi light brown color.in takaice muku dai kyakyawa ce ta kin ƙarawa domin duk yanda zakuyi tunanin kyawun Muzna to ta wuce nan, idan masu karatu basu manta ba, sarauniya Fatima wato mahaifiyar su da kanta ta shaida kan cewa kaf faɗin ahalinta da kuma ahalin Sarki Taifur Rahman babu wanda ya kai su kyau.

Kallon danƙareren agogon hannunta ta yi ta ga lokaci nata wucewa,turo baki tayi tana kallon cikin wajen ko zata ga wacce take nema,amma bata ganta ba hakan yasa ta sadakar bazata zo ba.nan take ta ji wajen ya isheta gida kawai take da bukatar komawa.

" MUZAINA ba ta zo ba ko!?,ai dama wannan yar uwar ta ki ba lallai ta zo ba,na kuma faɗa Miki".

Wata kyakyawar budurwa ta faɗa wacce ta kasance kawarta.

Sa'ke kallon agogon ta yi a karo na biyu.se sannan ne ta ɗan taɓe fuska kana cikin nutsuwa da kwantar da murya ta furta " Haseena!,ke kin san yanda MUZAINA take sona kawai nasan wani babban uzuri ne ya riƙe ta shisa bata zo ba,amma......".kasa karasa maganar ta yi ta riƙe fuska da hannun ta daya alamar mamaki.

" Meyafaru kuma,ke fa ko kaɗan bakya son a ce Muzaina ta yi laifi, ko yaushe ke ce ke mata uzuri uhmmm lallai kam". cewar Haseena.

" Ke kin san meye!?, na yi babban mantuwa wallahi,yau da safe kafin in fito naga ta min text, kan cewa tana da meeting yau in ta gama da wuri zata zo, in kuma bata gama ba,bazata samu zuwa ba"..

Ta faɗa tana sakin murmushi,ko gama jiran jawabin da ake yi bata yi ba ta ja hannun Haseena suka fito a wajen, murmushi itama Haseenar ta yi tana mamakin irin son da ita Muzna take yiwa yar uwar'ta Muzaina.

Farfajiyar hotel din suka fito bayan sun bar hall din nan suka samu yan jarida da kuma masu ɗaukan hoto suna ganin fitowar su, suka musu caa,haɗe da fara ɗaukar ta a hoto, tambayoyi suka fara yi mata kamar haka.

" Sarauniyar kyau shin za ki iya faɗa mana wani irin farin ciki kike ciki yau!?,shin kin taɓa tunanin za ki yi nasara a wannan waje duk da kin kasance model,kuma jarumar finafinai!?".

Tambayoyin de kowa da nasa .amma basu samu attention din ta ba, ga securities se tare yan jaridar suke domin rakasu zuwa Motar.

Wata baturiya a cikin yan jaridar ce ta soma yiwa wata dake kusa da ita magana

" Ita din fa yar Sarkin Kuwait ce, ai dole ma a bata lamba daya !, kin san su ya'yan manyan nan duk abinda suke so suna samu.as far as kudi yana aiki,tofa babu abinda ze gagara,ga ta da shegen kyau kamar ita ce ta halicci kan ta".

Daya na kusa da ita ta ce " haka ne kam,amma naji labarin cewa ba ita kaɗai bace,yaran Sarkin su biyu ne,akwai twin sister din ta komai din su iri daya babu abinda ya raba su,se de wancan she has a attitude mugun girman kai ne da ita ga kuma wulakanta yan adam, shisa Muzna take burgeni, domin ina yawan kallon finafinan ta".

Cikin gulma suke wa junansu wannan maganar, sede abinda basu sani ba gaba daya abinda suka faɗa ta ji yo su. hakan yasa ta dakatar da tafiyar da take yi ta dawo baya zuwa gare su.

" Ba kowa ni ɗan masu kuɗin bane yake neman abu kuma ya samu a lokacin da yake buƙata ba,domin a wannan rayuwar ba komai ne muke nema mu samu ba,ze yu ku kun san gidan ku,to mu har yau bamu san ya kalar masarautar mu yake ba, sede a nuna mana a hoto,idan akwai wanda yake tunanin cewa saboda ni yar sarki ce yasa na samu wannan damar, to kuyi gaggawan goge wannan a kwakwalwar ku. kokarina da kuma jajircewa na haɗe da taimakon Allah shine ya kawo ni wannan waje,in har kana son abu tofa bawai kana daga kwance bane zaka samu,put your efforts and energy.anan ne zaka samu abinda ka ke so.ka kuma haɗa da neman taimako a gun Allah,dan ina yar sarki ba shine ze sa ina kwance akan gado na in samu abubuwan da nake bukata ba fatan kun fahimta!?, sannan dangane da yar uwata Muzaina,kar ku sa'ke magana mara dadi akan ta,ita din macece me zuciyar zinari,wanda be Santa bane ze mata kallon arrogant amma she's so simple".

Tana gama maganarta ta juya ta barosu tsaye a wajen,ta ci gaba da tafiya tana manna sun glass a kyakyawar fuskar ta,har ta bar wajen yan jaridar suna bin bayanta da kallo suna jinjina self confidence da take dashi,isa inda ta bar Haseena da kuma securities tayi. suka k’arasa inda aka tanadar musu motar suka shiga suka dau hanyar zuwa gidan su dake cikin Rublyovskoye highway.

Wani danƙareren gida suka shiga bayan gate man ya buɗe musu.komai na cikin gidan abin burgewa ne, a tare suka fito suna takawa har suka isa cikin falon, da baki baze taɓa iya fasalta irin kyawun da yake dashi ba,a cikin wannan hadaddiyar falon suka tadda ita da wasu turawa zaune suna tattaunawa da gani magana suke yi akan kasuwanci,tana sanye da wando pencil na jeans ya kamata sosai se riga madaidaiciya me dogon hannu kan ta kuwa tayi donot da gashinta ,masifar kamar da suke yi da ita ne yasa Turawan suke ta kallonsu,. domin in bawai don kayan da ya bambanta su ba to babu abinda ze hana su ce mutum daya ne,.

Ɗago kai ta yi suka haɗa ido da juna kafin ta miƙe ta nufesu ta rungume ta tana faɗin

" Na tayaki murna sosai my Muzna ina matukar alfahari dake". Ta yi maganar tana shafa bayanta duk da fuskarta babu murmushi akai, murmushi Muzna ta yi ta ce

" Nagode,duk da ina fushi dake na rashin halartar wannan babban rana a gare ni,amma bazan iya dena sanki ba my Muzaina".

Dan murmushi ta yi kaɗan kafin ta sake ta,ta kalli turawan ta gabatar musu da ita suka gaisa.

Haseena na gefen su ba ta ce musu komai ba,da ta gaji da tsayuwar ne ma ta shige ciki ta bar su a falon.

Batare da ta zauna ba ta sa'ke furta " mun gama wannan tattaunawar se mun haɗu wani lokaci".

Tana gama faɗar haka bata jira amsar su ba ta rike hannun Muzna suka shiga ciki,a hanyar su ta zuwa bedroom din su se labarin abinda ya faru a wajen take bata .ita kuma bata ce mata komai ba domin ba me yawan son magana bace sosai.

Se da suka shiga ciki ne ta kalleta ta ce " My Muzna!.,ko da yaushe ina yawan ce miki ki rage wannan yawan surutun naki amma bakya ji,wa ya faɗa miki jinin sarauta suna dogon magana ko dogon jawabi!?,ko ni be zama a ce na zamo miki misali ba!?, haba mana in aka ga kina yawan yin abu kamar gama garin mutane za'a rena ki. wanda hakan kuma ze taɓa min carrier na, saboda nan gama in na zama sarauniyar masarautar Bayaan za'a dinga cewa yar biyun sarauniya bata da kamun kai,bayan ke kuma zan sakar miki ragamar Company din Aba,duk da ma yanzu kin ƙi yarda ki soma aiki tare da ni a company. kin mayar da hankali akan carrier ki na gasar kyau da films,anyway ina tayaki murna da kuma miki addu'a ".

Ta gama maganar ta tana warware gashinta da ta hade tayi donot dashi.

Muzna da wannan maganar ya zamo mata kamar ruwan sha ne ta sauke a jiyar zuciya domin in wannan karatu ne ya ci a ce ta haddace sa .domin kusan kullum se Muzaina ta mata wannan maganar yanzu har ta ga ji da saurara.

Cikin ko oho da maganganun nata domin ta gaji da jin su ta furta " to shikenan sarauniya Muzaina kar ki damu nima zan koma kamar ki har ma in fiki .se de ze dau lokaci kafin in koma haka, saboda abinda bawai ka tashi da shi ba yana da wahalar koya,. bari in yi wanka yanzu in fito".

Ɗage mata kafaɗa ta yi alamar she doesn't care,ko da Muzna ta fito daga wanka sanye da rigar towel bata iske Muzaina a ciki ba,hakan yasa ta yi zamanta a kan mirror tana busar da gashin kanta da ya kasance me matukar tsawo ta gyarasa, sannan ta yi shafe-shafe, ta saka riga da wando.sak irin kayan Muzaina ta sanya sede ita ta yi ɗan kwalliya,wayar ta da ya soma ƙara ta nufa domin ganin me kiran nata. number sakatarenta ta gani ɗauka tai ta soma magana,.

" Mubeen ya a ke ciki !?". Ta faɗa tana gyara tsayuwar ta,a bangaren wanda ta kira da suna Mubeen ya ce

" Ran ki shi dade, gobe akwai show din daukan hoto da ki ke dashi, wanda za'a sa a magazine,se kuma contract din da zakiyi signing na Film din THE GANG,wanda director din yake ta bin ki,kiyi sign amma kin ƙi amincewa".

" To shikenan se goben " ta faɗa tana kashe wayar ta, kafin ta fice a dakin ta nufi bedroom din Haseena, kwance akan gado ta sameta tana matsa waya.

" Ya Allah, yanzu ke Haseena shine da ki ka yi wanka ba ki taho dakin mu ba!?".

Ta faɗa tana zama a gefen ta, Miƙewa zaune ta yi tana " afuwan!,na baku damar yin magana ne ke da Muzaina,shisa na ɗauke ƙafa ". Girgiza kai kawai ta yi dan tasan saboda Muzaina ne yasa bata je ba,domin sam Muzaina bata son Haseena kamar yanda itama bata son ta,a cewar Muzaina Haseena yar talakawa ce be kamata ta ɗinga tarayya dasu ba,se de ƙawance yayi karfi sosai a tsakanin Muzna da kuma Haseena, wanda hakan yasa ta dawo da ita zama a gidan su,saboda dama su biyu suke rayuwa a cikin wannan makeken gida se kuma masu aikin su, hakan sam be yi wa Muzaina dadi ba tayi faɗa har ta gaji amma Muzna sun ƙi rabuwa da Haseena.

" Yanzu duk ba wannan ba kira min Aba a waya na san suna tare da Ummi" Muzna ta faɗa.

Video call ta kira su ta system aikuwa Kamar yanda ta yi tunani hakan ne ya kasance, sarki TAIFUR RAHMAN na tare da sarauniya Fatima, bakaramin farin ciki suka yi ba ganin fuskar Muzna. Saboda murmushin dake kwance a fuskarta ne yasa suka fahimci Muzna ce,sosai suka sha hira sannan suka tayata murna haɗe da faɗin ai sun gani a labarai hakan ya faranta musu rai matuƙa.

Dariya ita da Haseena suka yi,ta ce " Aba ya jikin naka!?, fatan ya yi sauki sosai!?,kana shan magani ma kuwa!?,kaima kar ka zama irin Muzaina, itama in bata da lafiya duk yanda zan yi da ita bata yarda ta sha magani". Dariya suka yi kafin,sarki Taifur Rahman ya ce

" Kar ki damu Muzna ina shan magani sosai, Ummin ku na ta min ɗure,ina ita Muzaina take!?, kai mata ko ki kirata ".

Ɗaukar system din ta yi ta fice a dakin ,suna ci gaba da wayar har ta isa falo anan ta iske Muzaina dake zaune kamar wata me yin bacci.

Ɗaura mata system din tayi akan cinya hakan yasa ta ware kyawawan idanunta ta ɗaura su akan iyayen nasu.

Hira suka ɗan taɓa saboda babu wani shakuwa sosai tare da ita da kuma su, ita abinda yake gabanta kawai take yi bata taɓa kiran su, in ba wai Muzna ce ta yi kiran ba,ko kuma in su suka kira,tun dabi'un ta na damun su har suka watsar,se de suna sonta kamar yanda suke son Muzna.

" Aba shin yaushe ne za mu zo Kuwait!?,ko da yaushe se de ku yi ta ce mana lokaci na zuwa lokaci na zuwa, se yaushe ne lokacin ze zo shi!?,ina son in zo in ga yanda ake gudanar da al'amuran masarautar saboda ko da na zama sarauniya ba se nasha wahalar koya ba ".

Ɗan jimantawa sarki Taifur Rahman da sarauniya Fatima sukayi jikinsu yayi sanyi,cikin karfin hali sarauniya ta furta

" Kar ki damu Muzaina lokaci na zuwa,kuma in sha Allah zamu kawo muku ziyara a ƙarshen wannan wata "".

" Allah yasa" ta faɗa tana miƙawa Muzna system din ta soma kiran baturiyar yar aikinsu.

Sosai ta ƙara yin hira dasu domin ko kaɗan bata gajiya da jin muryarsu haka zata ta basu labarai masu dad'i da ban dariya kuma suna samun nishadi sosai hakan yasa kullum se sun yi waya.

Bayan ta kammala wayar ne ta ajiye laptop din akan Centre table, ta je ta kira Haseena domin cin abincin dare da aka tanadar musu a dinning,har suka kammala cin abinci babu wanda ya yi magana,se da suka gama ne suka koma falo yayinda Muzaina ke zaune a dinning tana latsa wayarta.

" Elizabeth" ta kira me aikin tasu cikin rawar jiki tazo domin tana tsoron duk wani abinda ze haɗa ta da Muzaina domin yanzu zata ci mata mutunci ita ba wani abu bane a wajenta.

Cikin bada umarni ta ce " je ki kawo min hot coffee kar sugar ya yi yawa".

Dasauri ta shiga kitchen ta haɗa mata coffee din ta kawo har in da take zaune,kusan mintunan ta biyar da tsayuwa amma Muzaina bata daga kai ta kalleta ba,ɓalle ta karbi kofin coffee da ta kawo mata,hannun Elizabeth har ya gaji ya fara rawa,se da ta gama shan kamshin ta kafin nan ta sa hannu zata ƙarba cikin rashin sa'a kuwa coffee ya ɗan zuba mata a hannu, da sauri ta miƙe tana yarfa hannunta da hot coffee din ya zuba.

" Am really sorry ma'am". Ta faɗa muryar ta na rawa domin ta san yau na lahira se ya fita jin dadi,wasu kyawawan tagwayen mari masu zafi ta wanka mata a kumatu wanda se da wannan yar aikin ta ji komai ya tsaya mata cak,su Muzna dake zaune a falo ne suka waigo da sauri jin sautin marin da ta sauke mata.

Da mamaki suke kallon su,kafin su miƙe Muzaina ta watsawa yar aikin sauran coffee me bala'in zafi a jiki.

Ihu ta soma yi tana yarfa hannu cike da radadin zafi,Muzaina ko a jikinta ta dau wayarta ta bar dinning din,da hanzari suka isa inda take tsaye tana kuka,suka riƙe ta suna bata hakuri.

" Gaskiya Muzna ni abinda twinning din ki take yi bana jin dadi, wannan ai wulakanci ne, tsakani da Allah akan me zata watsa mata tafasasshen coffee ta konata,ko ta manta Allah ne kaɗai yake yin hukunci da wuta ?". Haseena ta faɗa cikin tausayin Elizabeth,jiki a sanyaye Muzna ta furta

" Kin san halinta ai, yanzu de mukai Elizabeth din bedroom din ta se a kira doctor ya duba ta".abinka da farar fata nan take inda coffee din ya taba ya yi jajir sosai. Da taimakon su suka kaita dakinta aka kira doctor ya duba ta ya basu magani.

" Muzaina gaskiya yakamata a ce i zuwa yanzu kin sauya hali domin wannan ba hali nagari bane,ni nagaji da dabi'un ki haba mana, yanzu yarinyar nan bata miki komai ba kin kona ta,in da a ce ya taɓa fuskarta fa? ". Ta faɗa rai a ɓace dan lamarin yar uwar'ta ta ya soma guduran ta.

Hankali a kwance kamar babu abinda ta aikata tana zaune akan gado ta ɗaura daya kan daya tana kallon yanda ta titsiyeta tana mata masifa,.

" Da ya taɓa fuskarta da hakan ya fi min dadi., ke baki ga yanda take kokarin la'anta min fatar jikina bane?,ko za ki fifita wacce take matsayin baiwa akan yar uwar ki ne!?".

Cike da takaici Muzna ta girgiza kai dan ta rasa abin faɗa,kawai ta bar mata dakin ta nufi nata asalin bedroom din dama kowa da nasa bedroom din amma sukan kwana a daki guda.

Ko da ta shiga dakin ranta a ɓace wanka ta yi ta yi duk abinda ta saba yi sannan ta saka kayan bacci ta hau gado haɗe da ɗaukan wani towel yar karama wanda aka yi sa domin rufe fuska ta rufe fuskarta haɗe da yin addu'a,tana me tuna cewa gobe tana da bukatar tashi da wuri domin tana da zuwa wajen daukan hotuna da wannan tunanin bacci yayi gaba da ita.

washe gari da misalin karfe takwas ta yi breakfast din ta duk da ba wani abinci taci sosai ba saboda bata cin abu me nauyi, bayan ta kammala ne,ta je ta yi wanka. ta gyara style din gashinta sannan ta fito da cout na mata riga da wando blue color. da riga fari na ciki,wandon ba yi da tsayi har can sosai kafarta ya sha high hill white color.ta yi kyau sosai ta fito kamar yar teddy handbag kawai ta ɗauka da wayarta se sweet lollipop da ta , a bakinta ta fita tana kallon falon,da babu kowa tasan duk suna ciki suna bacci a farfajiyar gidan ta iske driver ta karbi car key a hannunsa ta shiga cikin wani aniyar motar ta fice a gidan.

Tana isa industry din na su ta samu ana ta shige da fice,tana fitowa a motar ta aka soma tayata murna har ta shige ciki,nan ta samu wa'yanda zasu mata kwalliya da taimaka mata wajen shiryawa suna jiranta hakan yasa suka shige make up room,kayan jikinta ta cire ta daura towel ta zauna nan suka soma tsantsarawa kyakyawar fuskar ta kwalliya da ya dace da fuskar. Bayan sun gama yi mata kwalliyar suka mata gyaran gashi aka haɗe sa gu daya bakaramin kyau ta yi ba tun kafin ta ma saka kaya ta yi kyau na fitina,. Su kan su wa'yanda suka mata kwalliyar se yaba kyawun da tayi suke yi wani breath taking gown irin na amare suka bata sede bashida wani hayaniya sosai kuma color din sa baki ne da kuma golding hakan ya sake fito da kyawunta nan take ta koma kamar wata amarya ko ma in ce fiye da amarya,wani takalmi da yake da tsini kamar tsinken kara kalar golding ta saka, ɗan kunnen da ke kunnenta na gold yana da tsayi,se ɗaukan ido yake yi, babban dakin photo room suka shiga ana riƙe mata da jelar rigar nan aka soma ɗaukanta zafafan hotuna. Se da aka ɗauke ta hoto da mabanbantan kaya sau kusan huɗu sannan aka gama shooting din. Producer su ne ya tura domin a kira yo masa ita.

Cikin office din sa dake industry din ta shiga ta same sa zaune yana jiranta farin Balarabe ne wanda ya soma manyanta.

" Barka dai Abu Xalib" ta faɗa tana zama fuskarta da ɗan murmushi.

" Yawwwa Muzna ina miki murna,tun jiya bamu samu lokacin magana ba".

Shuru ta yi tana jinsa tana ci gaba da murmushi.

Ci gaba da magana Abu Xalib yayi.

" Wato abinda yasa na bukaci ganin ki shine, mahaifin ku sarki Taifur Rahman ya sanar dani kuna daf da komawa gida wato cikin masarautar ku,wanda hakan kuma ze kawo karshen zaman ku a wannan ƙasa bansaniba ko in zaku dinga kawo ziyara,.bari muje kan maganar da nake son faɗa miki kai tsaye,yanzu kece tauraruwa me haskawa a wannan ƙasa da kike kan ganiyar daukakar ki ta wannan matsayi,ke yanzu sarauniyar kyau Russia ce. wacce ta lashe wannan gasa,ga finafinai da kike yi.in har ki ka tafi yanzu ban san ya wannan abu ze kasance ba.,abu ne da ze wahalar damu kafin a samu wacce zata maye gurbin ki”.

Kallon sa take yi babu ko kyaftawa har ya gama maganar sa,can kuma ta fashe da dariya tana mayar da maganar ta sa wasa,zuba mata ido yay har ta tsagaita da dariyar.

Ta ce " haba Abu Xalib, wannan maganar sam ba gaskiya bane,nasan Aba wasa kawai yake maka.amma ba yanzu ne za mu koma gida ba.yau tsawon shekaru goma sha biyar muka yi a wannan ƙasar da a ce za'a kai mu tushen mu da an jima da yin haka.se kawai rana tsaka Aba ya faɗa maka haka,yanzu mu yi wani abu daya ni zan kira sa a gabanka za ka ji irin amsar da Aba dina ze baka ".

Da ido kawai Abu Xalib yake binta ,har ta kira layin sarki Taifur Rahman, bayan ya daga ne ta soma faɗin

" Aba dina,shin kasan me Abu Xalib yake ce min kuwa !?".

Daga ɓangaren Sarki Taifur Rahman ya ce.

" Ah ah ƴata se kin faɗa".

" Cewa yay ka ce masa wai mun kusa dawuwa gida,shine ya ke tunani akan carrier dina,yanzu ka ba sa amsa mu ji wayar tana a handsfree".

Gwauron numfashi sarki ya ja kafin ya ɗan yi jim sannan ya furta

" Abu Xalib, magana ce wacce yara irin Muzna ko Muzaina bazasu fahimta ba,amma tabbas Ina da yakinin Kai nasan za ka fahimta, tabbas sun kusa zuwa gida amma a wasa hahahaahahh" ya ƙarishe maganar yana dariya,dariya itama ta yi tana faɗin

" Abu Xalib ka ji abinda ya ce ko?,wasa yake yi,Aba akwai sa da son wasa".ta katse kiran domin abinda take so ya ji kenan.

Dariyar yaƙe Abu Xalib yayi,domin maganar da sarki yayi ya tabbatar masa da tabbas akwai abinda yake boyewa yaransa,hakan yasa ya ɗan yi dariya domin kar Muzna ta kawo komai a ranta.

Bayan ta kashe kiran ne ta kuma sake tabbatar masa da suna nan a Russia babu inda zasu je daga nan ta masa sallama ta fice.

Ko da ta dawo gida nan take bawa Haseena labarin yanda suka yi ita da Abu Xalib, Muzaina da ta tafi gurin aiki ne ta shigo kunnenta manne da waya tana tafiya haɗe da yanga da alamar tana jin dadin wayar da take yi,wani ƙayitacciyar murmushi ta saki haɗe da faɗin

" In sha Allah,kin san nice nan wacce zata zama sarauniyar masarautar Bayaan domin ina da duk wani quality da ake buƙata, sannan Muzna ta, wannan abun sarautar duk be da me ta ba,just watch and see yanda zan fara mulkar Bayaan cikin kwarewa.kamar de yanda Aba yake yi domin kuwa jininsa ne yake yawo lungu da sako a cikin jikina ".

Ankara da su Haseena da tayi zaune a falon ta yi suna hira,hakan yasa ta karaso tana me mannawa Muzna kiss a goshi kafin ta shige ciki tana wayarta cikin kasaita.

Murmushi ta yi ta bi bayan Muzaina da kallo kafin ta mayar da dubanta zuwa ga Haseena ta ce

" Burinta a har kullum be wuce ta zama sarauniya wacce zata gaji Aba ba, gaskiya can't wait in ga my twinning ta fara mulkar Bayaan " ta faɗa cikin annashuwa.

Girgiza kai Haseena ta yi " hmmm da kuwa an shiga uku ai,Muzaina da bata kallon kowa da mutunci in ta zama sarauniya ya kenan!?,nide gaskiya bana fatan hakan saboda bana tunanin zata sauya".

Langwabe kai ta yi tana turawa Haseenar baki " ohhhhh, Haseena meyasa ki ke faɗar haka ne?,na san in sha Allah my Muzaina za ta sauya sosai ".

" Uhmmm Allah yasa".

Miƙewa ta yi tsaye daga ita se wando boom short da kuma riga t-shirt me dogon hannu ta bi bayan Muzaina din,.

Samunta ta yi ta gama wayar tana fitar da wasu muhimman files daga cikin briefcase,dagowa ta yi ta kalleta taga yanda ta tsaya mata akai tana murmushi.

" Wannan murmushin duk na menene my Muzna?".

Se da ta zauna a kusa da ita kafin ta ce " bana komai bane fa ce na farin cikin ganin ki abar kauna". Batare da ta ce komai ba ta yi mata murmushi kawai.

Ci gaba da magana Muzna ta yi " amma ya naga yau kin dau lokaci ba ki dawo ba ,shin lafiya kuwa domin ba ki taɓa kaiwa goma na dare a waje ba".

Ajiye file din ta yi ta maida hankalin ta gareta, kafin ta riƙe hannunta daya ta ce " My Muzna yau meeting mu ka yi game da wannan kamfanin da kuma hanyar da za'a sa'ke fadada shi,kin ga wannan takardun duk nasu ne,yanzu ki yi wanka ki zo mu yi bacci".

Gyada mata kai ta yi sannan ta yi wanka ta saka kayan bacci kala daya sak dana Muzaina din,babu abinda zaka kalla kace wai ze banbanta su,fa ce yanayin style din gashin su,ko wacce da kalar adon da tayiwa gashinta.kwashe komai suka yi suka a jiye akan mazauninsu sannan suka kwanta haɗe da kashe wutar dakin.

Haseena jin Muzna ba ta dawo bane yasa ta gane sun kwanta ita ce ta kashe komai na wutan lantarkin gidan, sannan ta shi nata dakin ta kwanta.

Koda ta shiga tunanin Muzna da Muzaina ta soma yi wato babban abinda ta fahimta da ko wannensu shine.

" Muzna yarinyace wacce ta mayar da kanta ba kowa ba,bata d’auki duniya da zafi ba. komai din ta tanayi Kamar yanda sauran gama garin mutane sukeyi ,ko da wasa ba ta nuna cewa ita yar sarki ce balle me arziki . tana so way’anda suke tare da ita su saki jiki sosai, Kar su dinga la'akari da matsayinta har yasa su yi tunanin ta kerewa a Jin su.

Hakan ne ya sa tadawo da kanta low level. Ta kasance tana gudanar da rayuwarta cikin farin ciki,tana da sakin fuska sosai akwai ta da fara’a.ga barkwanci,duk in da ake neman shagwababbiya tofa in a ka samu Muzna magana ya k’are.duk da ta kasance me hankali da sanin yakamata had’i da tausayi sede wani lokaci akwai shiririta.Tana da matukar tausayi sosai Wanda hakan ya zama shine rauninta ga tsoro kamar farar kura.musamman kyankyaso Tana masifar tsoron sa sosai.

Wanda a bangaren Muzaina kuma ya zama sab’anin haka,Muzaina ta kasance wata iriyar baudaddiyar mutum ce komai na ta ya fita daban.bata fiya son yin mu’amula da mutane ba in ba wai kasuwanci ne ya had’a ku ba,ko kad’an bata da saurin sabo musamman in ka kasance ba kowan kowa ba. Domin ta tsani had’a wani alaka da talaka.kad’an daga cikin halayenta.wulakanci,rashin kunya,tsiwa,rashin tausayi dan ita babu abinda ya shafeta da Jin tausayin mutum.bazata maka dariya ba sede murmushi shima seda dalili.Sam bata son wani ya rabesu.ga son girma da son a darajata a matsayinta ta CEO kuma royal blood. Wannan sune kad’an a ciki.

“ Allah me iko wannan shine Allah daya gari bambam “ Haseena ta fad’a kafin tayi addu’ar bacci.

1:00am na dare,kira ya shigo wayar Muzna da ta mance bata saka sa a silent ba,farkawa sukayi Muzaina na jan tsaki,haɗe da soma mata masifar menene ya hanata sanya wayarta a silent. bata ce da ita komai ba ta zura ƙafafunta kasa ta miƙe tana hamma ta isa gaban mirror da basu rufesa da komai ba,zare ido ta yi tana ganin me kiran nata duban agogon dake manne akan bangon dakin yana harbawa dik!dik!dik! A hankali,kuma hankali tashe ta ce

" Ya Salam kiran Ummi a wannan lokacin kuma!?, Allah de yasa komai lafiya",dan haka kawai ta tsinci kanta na masifar sarawa

Jin abinda ta faɗa ne yasa Muzaina itama saurin tasowa ta iso gabanta duk sun gagara picking din kiran se kallon junansu da suke yi.

Hannu na rawa ta dau kiran ta sa a kunne

" Assalamualaikum ya Ummi".

Muryar sarki Taifur Rahman ne ta ji yana amsa sallamar.

" Aba lafiya ka kira mu a wannan kurarren lokacin? fatan kowa na cikin koshin lafiya hankalin mu ya tashi sosai ".

Sautin murmushin sa suka ji yana faɗin " lafiya lau kawai ina son jin muryar ku ne kafin in kwanta bacci,fatan kun yafe min na tayar da ku danayi daga bacci?".

A tare suka sauke a jiyar zuciya jin komai lafiya,hannu Muzaina tasa ta karbi wayar tana ƙara volume

" Aba naji muryarka wani iri ko ka soma bacci ne, sannan kuma ina Ummi shin Idonta biyu ne!?".

" Babu komai y’ata, kawai mura nake yi, sannan Ummi din ku ga ta nan amma tayi bacci. shine na saci wayarta hahahahaha" ya karasa maganar yana yar dariya. Suma dariyar suka ɗan yi kana cikin raha Muzna ta ce

" Kar ka manta kafin kayi bacci ka tabbatar da kasha magani,in kuma ka manta se na zo na maka dure da kaina ".

Dariya sarki yayi ya ce " in sha Allah bazan mance ba,ku kwanta ku yi bacci, Allah ya muku albarka ya kauda idon mugun abu akan ku ya'yana,ku kula da junan ku sosai,ko min rintsi kar ku bar wani abu ya shiga tsakanin ku,ina matukar kaunar ku ".

" Mu ma muna son ka sosai Aba ka yi bacci cikin aminci da yardan Ubangiji ".

A haka suka yi sallama ya kashe wayar sannan suka kwanta bayan Muzna ta sanya wayarta a silent.

2:30Am

Tsakar dare jikinta ya dau zafi sosai ga wani irin zufa da ke tsatstsafowa a jikin ta gaba daya ya jikata,se girgiza kai take yi ga uban kerma da jikinta ya dauka,wasu irin munanan mafarkai take yi masu razanarwan gaske, bakinta da yake ta kokarin yin magana amma ko kalma daya ya kasa fitowa a ciki se yunkuri da take yi,can ta samu ta iya soma magana

" Ah ah,ah ah,karya ne, hakan sam baze taɓa yuwa ba". Wannan sune abinda take faɗa a sambatun da take yi.

Kamar a mafarki Muzaina ta soma jin maganganun ta,hakan yasa ta farka daga baccin da take yi ta ɗaura Idonta akan muzna dake jijjiga.

Da hanzari ta miƙe tana riƙo ta haɗe da kiran sunanta amma bata tashi a baccin da take yi ba.

Hankali a tashe Muzaina ta ci gaba da kiran sunanta

" My Muzna,ki tashi haka,mafarkin meye ki ke yi haka?".

Ta faɗa tana kunna light din dake gefen gadon nasu haske ya gauraye dakin,hasken na kunnuwa ta buɗe idanunta da suka cika da hawaye ga jan da suka yi.

Ganin Muzaina ce riƙe da ita yasa ta sa'ke rungumeta sosai tana faɗin

" Muzaina ina jin tsoro,tsoro nake ji Muzaina".

Ganin tana a tsorace sosai ne yasa ta rungumeta tsam jikinta tana shafa bayanta

" Ki kwantar da hankalin ki mafarki ne kawai".

Numfashi me zafi kawai take saukewa domin mafarkan da ta yi bana wasa bane mafarki ne me matukar tsoratarwa,da ta rasa dalilin yin su.

Se da ta tabbatar da ta dawo hayyacinta sannan ta kwantar da ita a gadon, ta ɗauko mata maganin zazzaɓi ta bata saboda zafin da taji jikinta ya ɗauka.

Dakyar bacci ya dauke su har kusan karfi huɗu saura sannan zazzaɓin ya sauka suka samu runtsawa.

Koda gari ya waye bayan Muzaina ta farka bata yi sallah ba, saboda ba ta damu da yin Sallah ba tana yi ne a lokacin da ta gadama. hakan yasa bayan ta farka ta dubi Muzna da har lokacin bacci take yi dukunkune cikin bargo,wanka ta yi ta fito ta shirya cikin shirinta na zuwa office ta yi kyau sosai cikin matsatsun cout dark brown ta gyara gashinta tai donot dashi,.

Gadon ta nufa ta zauna haɗe da shafa kan muzna dake bacci sannan tayi kissing forehead dinta ta miƙe cike da tafiyarta na yanga ta fice a dakin ta bar gidan zuwa office. Haseena dake falo taga fitowarta ne tabi bayanta da kallo.

Tana Miƙewa dan zuwa duba Muzna dan tasan bata baccin safe sosai har haka ba ta farka ba.

Tadda dakin ta yi a ƙulle tayi knocking nan ma shuru ba'a buɗe ba.

Wannan yasa tayi tunanin ita muzna ce ta rufe kofar hakan yasa ta juya ta koma falo.

" Shugabar masarautar Bayaan me kawar da zalunci yar Sarkin Kuwait,ke ce kaɗai za ki iya kawar da mummunar ƙaddara dake tattare da wannan masauratar dake daf da shiga cikin ha'ula i, sarauniya ce keeeeeeeeeeeeeee ". Da sauri ta farka tana kallon dakin, ga muryoyin da take ji suna mata kuwa a dodon kunne kuma bawai na mutum daya ba.

Da karfi ta toshe kunnenta tana runtse ido da karfi ta furta " ya isaaaa hakaaaaa bana son jin komai ku kyale ni".

" Ke ce,ba kowa ba, kulawar Bayaan na karkashin ikon ki, sannan daga yau za ki fara taka matakin hawa sarauta ko kina so ko bakya so babu yanda ki ka iya ".

Duk da ta toshe kunnenta da tsananin karfi amma har tsakiyar kanta take jin wa'yannan muryoyin suna mata magana ga cikin dakin da yake ta girgiza haɗe da tashin guguwa.

Da karfi ta ce " su wayeee ku !? ".

Ko ina na dakin tsit ya yi komai ya koma dede kamar babu komai,a hankali ta sauke hannunta a kunnenta tana kallon cikin dakin a tsorace sauka Idonta yayi akan kofar dake a buɗe,da matsiyacin gudu ta bar dakin ta faɗa falo,iske Haseena ta yi zaune dakatawa ta yi tana goge fuskarta haɗe da dedeta nutsuwar ta,dan bata son hankalin ta ya tashi. Jin ana tsaye a kanta ne yasa ta kallon ta

" Muzna lafiya baki da lafiya ne naga fuskar ki ta kumbura?,kuma kamar ba'a cikin nutsuwarki ki ke ba?". Ta faɗa tana Miƙewa zuwa gareta,riƙe ta tayi tana shanye tsoron dake tare da ita

" Haseena mu je dakin ki in yi wanka mu bar gidan nan ".

Da mamaki take kallon ta ganin yanda take magana kamar wacce bata cikin nutsuwa

" Muzna kin tabbata kina lafiya sannan meyasa ki ke magana kamar wacce take cikin tashin hankali".

Jan hannunta kawai tayi zuwa dakinta batare da ta amsa mata ba.

Wanka ta yi ta tura Haseena zuwa dakin kayan su ta dauko mata kayan sawa yau ko yar kwalliya ba ta yi ba,

Kawai ta saka dogon pencil gown da ya tsaya mata a iya a guiwan sahu.fakin gashinta tayi ta saka hill din takalmi, Haseena da ita ma ta shirya cikin rigar da wando suka fice a gidan a motar muzna din amma dake bata cikin yanayi me dadi yasa tabarwa Haseena take driving din su,yau ta rasa menene abinda yake damun kawarta ta, har suka isa industry babu wanda yace komai.

Ko yan industry da abokan aikinta sun fahimci yau bata cikin yanayi me kyau domin ita me faram-faram da mutane ce ,tana da kyakkyawar alaƙa da mutane.

Ko da ake shooting ma jikinta a sanyaye sosai hakan yasa Haseena ta jawo ta gefe ta ce

" Wai Muzna menene yake damunki yau ne!? ,na tambaye ki har na gaji amma kin ƙi amsani".

Numfasawa ta yi tana dafe goshin ta da zara-zaran yatsunta da suka sha cotes.

" Haseena wani mugayen mafarkai nayi jiya a cikin su guda daya ne kawai nake iya tunawa dayan kuma ko ina so in tuna amma bana iyawa".

" Wani mafarki ne haka!?"Haseena ta tambaya.

" Naga Aba da fararen kaya masu haske da daukan ido sosai kan sa sanye da hular sarautar sa, yana yi mini murmushi haɗe da yi min bye-bye,se kuma ya ce ƴata nasan za ki iya,ina da yakini akan ki sosai".

Ta karasa maganar tana jingina jikinta,Shuru duk sukayi Haseena na nazartan maganar ta da ta faɗa amma tasan ba ya wuce shirmen mafarki ne kawai.

" Yanzu saboda wannan ne yasa duk ki ka sauya yau!?, hankalin ki ya kwanta, ina me tabbatar miki da kawai mafarki ne,ku ma kin san shirmen mafarki wani lokacin".

Da wa'yannan kalaman Haseena ta ɗinga kwantar mata da hankali, har ta ɗa saki jiki aka ci gaba da shooting da ita har yamma liris suna can.

Yau ta ɗan gaji sosai ga bata jin cin komai kamar wata mara lafiya haka take ji. shisa ko da ana aikin karfin hali kawai ta saka se kuma kwarin gwiwa da Haseena ta ƙara mata,suna tsaye da Abu Xalib a bakin motar sa ya bata wani file zata yi signing contract din gasar kyau da za'a yi na duk duniya bayan ta yi signing din ne suna tsaye yana mata magana, Mubeen ya taho hannun sa riƙe da wayarta ya furta

" Ran ki shi dade ana kiran ki a waya kuma wayar an ce me matuƙar muhimmanci ne "

Batare da ta lalle sa ba ta ce " waye ne yake kiran!? ".

" Wayar daga can masarauta ne,yarima Farasat ne yake kiran ki yanzu ya kira kusan sau goma kenan".

Se a sannan ne ta kallesa tana me cewa " ka yi picking sannan ka sa min a handsfree ".

Kamar yanda ta basa umarni hakan kuwa ya yi,yay picking din kiran.

Se da aka kusa mintuna biyu kafin nan a bangaren yarima Farasat ya soma magana

" Gimbiya Muzna ina me baƙin cikin sanar dake mun rasa wanda ya fi soyuwa a gare mu,ina mana baƙin cikin rasa Aba Allah ya ɗauke sa " ya faɗa muryarsa a dashe.

Wani dim ta ji kanta ya ɗauka se ta ji komai na duniyar ya tsaya mata baya yawo kamar yanda yake mata,.

" Innalillahi wainna'ilaihi rajuun " shine kawai abinda Abu Xalib da Haseena, Mubeen suke faɗa wanda shine ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi

Cikin kasa yarda da abinda ya faɗa ta kwace wayar a hannunsa ta ce " Farasat bana son wasa ka faɗamin abinda ka faɗa yanzu karya ka ke min dan Allah ".

A raunane Yarima Farasat ya soma cewa " babu karya ko kuma bayanin wasa a cikin zantukana gimbiya Muzna.sarki Taifur Rahman Allah ya masa rasuwa a sakamakon ciwon daji da yayi fama dashi na tsawon shekara huɗu,zuwa gobe da safe za'a turo jirgi ya dawo daku gida domin a yi jana'izar mahaifin ku a kan idon ku, Allah ya kara mana juriyar rashi". Yana gama faɗin haka ya katse kiran.

Yanzu labari ya soma tafiya in har kun bani haɗin kai tofa zamu tafi,in kuma kuka ki bani haɗin kai se mu hakura da wannan daddadar labarin,yawan comment din ku yawan read more din ku.

Comments,like and share fisabilillahi.🥰🥰🥰🫶