SAFEENATU

BABI NA ƊAYA

by @ummasghar

*SAFEENATU*

NA

*UMM ASGHAR*

Arewa books @UmmAsghar

*BABI NA ƊAYA*

Sunana Safeenatu Ahmad Yunus (Feenah) kamar yadda mafi yawancin kawayena suke kirana.

Asalin mahaifina mutumin Karamar hukumar Kazaure ne dake jihar Jigawa.

Gidan kakanni na yana nan a unguwar Sha'iskawa.

Mahaifina tsohon ma'aikaci ne da NMDPRA wato Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority. Yanzu da yayi retire kuma sai ya tsunduma a harkar kasuwanci.

Shine mamallakin sanannen gidan man nan wato AYK PETROLEUM AND GAS wanda keda rassa a ko'ina a cikin fadin kasarmu Nigeria.

Haka nan yana da company da ake yin granite tiles a gunduwawa yana kuma da Company da ake sareafa shinkafa a Kakara. A taƙaice dai Baba cikakken ɗan kasuwa ne.

Gidanmu na nan a unguwar Lamido Crescent dake garin Kano.

Kasantuwar Mahaifina mamallakin mata biyu bai sa mun taso kanmu a rarrabe ba, mahaifina jarumin mutum ne da yayi tsayin daka wajen ganin ya samar da kyakkyawar alaƙa a cikin iyalinshi. Duk da matsanancin kishin dake tsakanin iyayenmu mata Baba bai yi saken da suka sanya mu a ciki ba.

Mu goma sha shida ne ƴaƴan Babanmu maza goma mata shida amma ba'a taba rarrabe ɗan wannan ɗakin da ɗan wancan saboda yadda kanmu yake a haɗe, sam bamu san wani abu wai ƴan ubanci ba.

Uwar gida Hasiya da muke kira Mama tana da 'ya'ya goma maza bakwai mata uku, itama mutuniyar Kazaure ce don abokan wasa suke da Baba, mahaifinta ƙani ne a wajen mahaifiyarshi.

Yaya Aminu ne babba sai Yaya Usman, Yaya Aisha,Yaya Zainab, Yaya Umar, Khadija wacce muke sa'anni ni da ita sai dai ta girme ni da watanni huďu, Abdulkarim, Mustapha, Huzaifa da kuma Kabir.

Sai mahaifiyata Maryam da muke kira da Anty wacce ta kasance amarya. Anty ta fito ne daga ƙabilar Wolof daga ƙasar Senegal, sun haɗu da Baba ne a garin Abuja anan gidan mahaifin ta inda ya amsa gayyatar cin abinci da mahifin nata yayi mishi a lokacin yana Ambassador kasar Senegal anan Nigeria..

Ganin farko da yayi mata yaji ta kwanta mishi a rai, bai bar gidan ba sai da yayi magana da mahaifinta shi kuma yace ya nemi soyayya a wurinta idan har ta aminta dashi to ya bashi.

Bai sha wata wahala ba wajen yaɗa manufar shi ga Maryam inda aka yi dace ta aminta dashi don haka ba'a ɗauki dogon lokaci ba aka yi aurensu inda ta tare a cikin iyalinshi a garin Kano.

Nice babbar ƴa a ďakinmu sai ƴan biyu da suke bina wato Hassan da Hussein, sai Jiddah, Zahra da kuma auta Imaduddeen.

Nayi makarantar primary ɗina har zuwa secondary a GATEWAY INTERNATIONAL SCHOOL, yanzu haka na kammala degree ɗina a Bayero University Kano inda na karanci Business Administration. Yanzu haka an saka ranar aurena watanni biyu masu zuwa.

A gajiye na shigo gida daga wajen aiki wato inda nake yin primary assignment kasancewata ƴar bautar ƙasa. Sai dana fara shiga ɗakin Anty na sanar mata da dawowata kafin na wuce ɗakina, ina shiga na jefar da jakata akan gado na hau cire kayan jikina saboda yadda nake jina a takure. Zafi ake yi sosai gashi ni kuma idan akwai abinda jikina baya so to yanayin zafi ne, yanzun nan zan haɗa gumi ƙurajen gumi kuma su fara feso mini shi yasa ac'n ɗakina kullum a kunne take bana taɓa kashewa. Toilet na faɗa nayi wanka haɗe da ɗauro alwalar sallar la'asar. A gaban dressing mirror na tsaya na goge jikina kafin na ɗauki body lotion na love nature (Oriflame) na shafe dukkan jikina dashi sannan nabi da oil perfumes na sandalia intense da vip luxury oil duka daga Lush_Scents. Ina son ƙamshi sosai shi yasa duk kuɗaɗena a wajen sayen turare suke ƙarewa.

Bayan na gama dukkanin wasu shafe-shafe na sai na buɗe wardrobe na ciro wata doguwar english gown ta shan iska mai hannun shimi na saka bayan na feshe ta da turaren Essenza Supreme (oriflame). Hijab ɗin sallahta na saka na tayar da sallar la'sar. Na jima akan sallayar ina addu'a kafin na tashi na ninke hijab ɗin na ajiye, yunwa nake ji sosai don rabona da abinci tun breakfast da nayi kafin na fita shima ba wani abun kirki naci ba, toasted bread ne slice biyu sai orange juice cikin tumbler ɗaya shikenan abinda ke cikina har yanzu da ake neman ƙarfe biyar saura na yamma. Fita nayi zuwa main kitchen na ɗebi abinci  a cikin ƙatuwar warmer da ake zuba abincin gidan, hardly kazo gidanmu ka rasa abinci don mafi yawancin lokuta abincin rana yana tarar da na dare sai dai a fitar dashi a bayar. Masu aiki ne ke girkin abincin gidan sai dai kowacce mace ranar girkin ta ita ke girka abincin Baba. Nazo fita daga kitchen ɗin muka kusa yin karo da Ya Umar. Da sauri na kauce ina tura baki ganin ya kawo hannu zai ranƙwashe ni. A duk ƴan gidanmu idan da akwai wanda bama shiri dashi to Ya Umar ne, banda yana tsoron Baba kuma a tsaye yake akan iyalin shi to da shi zai wankewa Mama takaicin haɗin kan da muke dashi wanda a bayyane yake tana adawa da hakan sai dai dole tayi haƙuri tana kawar da kai don tasan Baba ba zai ɗauki rarrabuwar kan iyalin shi ba.

A fusace yace "me kike cewa?"

Ƙasa-ƙasa nace "to ni nayi maka magana ne," Ina cigaba da ƴan ƙunƙuni.

Nuna ni yayi da yatsa yana cewa "Idan kika ce zaki yi mini rashin kunya wallahi sai naci uwarki, baƙale kawai."

Ban ƙara tanka mishi ba na wuce duk kuwa da raina ya ɓaci da zagin da yayi mini. A rayuwata ina son Anty ina kuma girmama al'amarinta don haka bana ganin mutuncin duk wanda ya nemi ya raina mini ita, shine kuma dalilin rashin shirin mu da Ya Umar tun farko, duk cikin ƴaƴan Mama shine yake da aƙida irin tata kamar wani mace, ko kusa baya ƙaunar Anty baya ganin girmanta, akan dole yake yi mata magana shima don yasan Baba ba zai ɗauki rashin arziƙi daga wurin shi bane shi yasa, sai dai kuma hakan bai shafi ƙaunar da yake yiwa ƴaƴanta ba idan ka cire ni to kyakkyawar alaƙa ce sosai tsakanin shi da su Hussein. Nice dai na fita daban a cikinsu, koda yake hakan baya rasa nasaba da tsananin kamar da nake yi da Anty, duk cikin ƴaƴanta nice nake kama da ita na kuma ɗauko kalar fatar ta. Kowa yasan ƙabilar wolof baƙaƙe ne sai dai kuma kyawawa ne, to haka nima na ɗauko baƙar fatar Anty duk da ma na ɗan fita haske kaɗan amma duk cikin ƴaƴan gidanmu ni na fita daban don kuwa dukkansu farare ne kasancewar daga Baba har Mama suna da hasken fata, to ƴan ɗakin namu ma farin Baba suka ɗauko idan ka cire ni.

A bayyane yake Mama bata ƙaunata don ko dariya take yi idan ta ganni zata gimtse fuska, a cewarta wai idan ta ganni sai gabanta ya faɗi saboda babu ta inda na baro uwata, ita kuwa yadda take jin tsana da kishin Anty yasa ko me kama da ita bata son gani. A parlour na zauna ina cin abimcin, remote na ɗauka na canja channel zuwa BBC BRIT ina kallon tipping point. Gaba ɗaya attention ɗina na mayar ga kallon don ni kallon films bai dameni ba amma ina kallon irin waɗannan programs ɗin sosai ko babu komai they are educative so akwai ƙaruwa a ciki. Ina gama cin abinci wayata ta fara ƙara, ajiye plate ɗin nayi akan center table kafin na ɗauki wayar fuskata ɗauke da murmushi don tunda naji ringtone ɗin nasan Albi ne wato fiance ɗina Hamza. Da sallama na amsa wayar farin cikin dake ƙunshe a muryata ya kasa ɓoyuwa don yau thruout bamu yi waya ba sai yanzu.

"Hello baby laifin me nayi duk yau aka shareni?" Murmushi na saki mai sauti jin abinda yace, duk ranar da bamu yi waya ba dama haka yake yi mini don kada nayi mishi ƙorafin rashin kirana da bai yi ba tun kafin nayi magana zai yi sauri yace na share shi. A shagwaɓe cikin muryar da shi kaɗai nake yiwa magana nace "kai dai ka shareni shine zaka wani ce na shareka, ai dai wallahi na kusa nayi fushi."

Dariya ya saki mai cike da nishaɗi yace "sorry baby, wallahi yau ayyuka ne suka sha kaina sai yanzu na samu na yakice da ƙyar don bazan iya cigaba da komai ba idan har ba naji voice ɗin ki ba." Tunda muka fara wayar nake sakin murmushi don Albi akwai iya sakin kalami, yasan yadda zai tsara mace taji kamar duk duniya baya da wani abu mai daraja bayan ita. Fitowar Anty daga ɗaki yasa nayi mishi sallama akan zamu yi magana after magrib. Tashi nayi na bita kitchen inda take haɗa abincin Baba na tayata, muna aikin muna hira wadda yawancinta nasiha ce take yi mini akan kyautata mu'amala da duk wanda Allah ya haɗani zama dashi. Zai yi wuya ƙwarai da gaske ki zauna da Anty baki tsinci wani abu na ƙaruwa a tattare da ita ba, walau ka samu ƙaruwa akan ilimin addini ko na boko, harkar girke-girke da zamantakewa ta yau da kullum, ko yaya ne dai baza ki tashi ba ba tare da kin ƙaru da zaman da kuka yi da ita ba.

Lokacin da muka gama aikin magriba tayi don haka ɗakina na wuce don nayi sallah, na idar kenan Khadija ta shigo. Duk yau bamu haɗu ba saboda ita a banki take primary assignment ɗinta ba kuma sa tasowa da wuri don kusan kullum ina rigata dawowa gida. Kwanciya tayi akan gado na tace "tun ɗazu na dawo ina taso na shigo wurinki sai dai na gaji da yawa wallahi, Honey ne zai zo ranar friday me kike ganin ya kamata mu tanadar mishi?"

Kallonta nayi nace "abinci ko snacks? Wane a ciki?"

"Abinci dai ko tunda kinga daga wani gari zai zo." Nace "haka ne, to amma me zai hana ayi mishi traditional food tunda ya daɗe baya nan amma me kike gani?"

Gyara kwanciyarta tayi tace "hakan yayi, sai dai fa ni kin san ba wani iya abincin gargajiya nayi ba sai dai kuma idan zaki tayani." Ta ƙarashe maganar da alamar roƙo. Girgiza kaina kawai nayi don nasan dama ni zata barwa aikin don Khadija bata son girki, malalaciya ce anan ɓangaren sai ya zame mata dole take shiga kitchen, ita ɗin complete opposite of me ce don ni i derive pleasure in cooking, sosai yake sakani nishaɗi shi yasa duk lokacin da Anty ta shiga kitchen to za'a tarar dani a wurin ina tayata, ni har masu aikin main kitchen ina zuwa ina tayasu girki ina kuma ƙara koyon wasu abubuwan a wutin su tun ma ba girke-girken gargajiya ba.

"Please Feenah, kin ji?" Ta ƙara roƙona. "Naji Allah ya kaimu friday ɗin, amma wallahi tayaki zan yi baza ki sakar mini aiki gaba ɗaya ba don nasan halin ki."

Tasowa tayi ta rungume ni tana cewa "naji na yarda." Hira muka cigaba dayi har lokacin da Anty ta turo Zahra ta kira mu. A ɗaki muka tarar da ita zaune a gaban dressing Mirror tana kwalliya. Kallon juna muka yi muna ƙunshe dariya don mun san kwalliyar zuwa wurin Baba take yi. Wani abu dake burgeni da Anty kenan akwai ta da iya tattalin miji, kullum cikin gyaran jiki take da kwalliya, bata taɓa yarda Baba ya ganta cikin mummunar shiga koda kuwa ba ranar girkinta bane. Zama muka yi a bakin gado Khadija tace "Anty gamu Zahra tace kina kiranmu." Sai da ta gama shafe-shafenta sannan ta nuna mana wasu jarkoki guda biyu tace "gashi nan kowa ta ɗauka kuje ku dinga sha safe da yamma, maganin sanyi ne." A tare muka yi mata godiya muka tashi muka ɗauka muka tafi. Ba yau Anty ta fara bamu maganin sanyi ba, from time to time tana bamu don tace ba lallai mu san muna ɗauke da ciwon ba idan ma kuma babu to yana da kyau ace muna detox lokaci bayan lokaci.....

*UmmAsghar*