FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · BABI NA ƊAYA
*SAFEENATU*NA*UMM ASGHAR*Arewa books @UmmAsghar*BABI NA ƊAYA*Sunana Safeenatu Ahmad Yunus (Feenah) kamar yadda mafi yawancin kawayena suke kirana. Asalin mahaifina mutumin Karamar hukumar Kazaure ne dake jihar Jigawa. Gidan kakanni na yana nan a unguwar Sha'iskawa. Mahaifina tsohon ma'aikaci ne da NMDPRA wato Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority. Yanzu da yayi retire kuma sai ya tsunduma a harkar kasuwanci.Shine mamallakin sanannen gidan man nan wato AYK PETROLEUM AND GAS wanda keda rassa a ko'ina a cikin fadin kasarmu Nigeria.Haka nan yana da company da ake yin granite tiles a gunduwawa yana kuma da Company da ake sareafa shinkafa a Kakara. A taƙaice dai Baba cikakken ɗan kasuwa ne. Gidanmu na nan a unguwar Lamido Crescent dake garin Kano.Kasantuwar Mahaifina mamallakin mata biyu bai sa mun taso kanmu a rarrabe ba, mahaifina jarumin mutum ne da yayi tsayin daka wajen ganin ya samar da kyakkyawar alaƙa a cikin iyalinshi. Duk da matsanancin kishin dake tsakanin iyayenmu mata Baba bai yi saken da suka sanya mu a ciki ba.Mu goma sha shida ne ƴaƴan Babanmu maza goma mata shida amma ba'a taba rarrabe ɗan wannan ɗakin da ɗan wancan saboda yadda kanmu yake a haɗe, sam bamu san wani abu wai ƴan ubanci ba. Uwar gida Hasiya da muke kira Mama tana da 'ya'ya goma maza bakwai mata uku, itama mutuniyar Kazaure ce don abokan wasa suke da Baba, mahaifinta ƙani ne a wajen mahaifiyarshi.Yaya Aminu ne babba sai Yaya Usman, Yaya Aisha,Yaya Zainab, Yaya Umar, Khadija wacce muke sa'anni ni da ita sai dai ta girme ni da watanni huďu, Abdulkarim, Mustapha, Huzaifa da kuma Kabir.Sai mahaifiyata Maryam da muke kira da Anty wacce ta kasance amarya. Anty ta fito ne daga ƙabilar Wolof daga ƙasar Senegal, sun haɗu da Baba ne a garin Abuja anan gidan mahaifin ta inda ya amsa gayyatar cin abinci da mahifin nata yayi mishi a lokacin yana Ambassador kasar Senegal anan Nigeria..Ganin farko da yayi mata yaji ta kwanta mishi a rai, bai bar gidan ba sai da yayi magana da mahaifinta shi kuma yace ya nemi soyayya a wurinta idan har ta aminta dashi to ya bashi.Bai sha wata wahala ba wajen yaɗa manufar shi ga Maryam inda aka yi dace ta aminta dashi don haka ba'a ɗauki dogon lokaci ba aka yi aurensu inda ta tare a cikin iyalinshi a garin Kano.Nice babbar ƴa a ďakinmu sai ƴan biyu da suke bina wato Hassan da Hussein, sai Jiddah, Zahra da kuma auta Imaduddeen.Nayi makarantar primary ɗina har zuwa secondary a GATEWAY INTERNATIONAL SCHOOL, yanzu haka na kammala degree ɗina a Bayero University Kano inda na karanci Business Administration. Yanzu haka an saka ranar aurena watanni biyu masu zuwa.A gajiye na shigo gida daga wajen aiki wato inda nake yin primary assignment kasancewata ƴar bautar ƙasa. Sai dana fara shiga ɗakin Anty na sanar mata da dawowata kafin na wuce ɗak...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.