BABI NA ƊAYA
by @ayushermuhd
RIBAR ƘAFA
NA
Wattpad :-AyusherMohd
Arewabook:- Ayushermuhd
ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️
*Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku ɗaukacin masoyana a duk inda kuke, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yana lafiya. Musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, masu ciki Allah ya saukesu lafiya, wadanda ke neman haihuwa Allah ya basu. Masu neman aikin yi Allah ya taimakesu yasa su samu. Ƙasar mu Nigeria Allah ya shiga lamarin ta ya kawo mana gyara Ameen suma Ameen.*
Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen..... lol duk da nasan ke ko kai ka fada..........
Dafatan za'amin uzurin jina shiru da akai. I am back!
PAID BOOK
SHAFI NA FARKO
Duk abinda ke faruwa a wannan lokacin kwakwalwarshi naji sai dai idanuwansa sun kasa buɗe wa sosai, dakyar ya iya ɗan motsa idanshi na hagu wanda yake jin nauyinshi sosai. Mutane biyu ya gani suna janshi a ƙasa, ga wani azababen ciwon kai dake damunshi wanda yake ji kamar yasa ihu ba sai an fada ba harda jan da suke mai a ƙasa yasa yake ƙarajin kan nashi kamar zai faɗo kasa. Shin ko dai mutuwa yai? Ko Mala'iku ne ke janshi? Tambayar da ya yiwa kansa kenan, sai dai sam ba shi da amsar da zai bawa kansa, abu ɗaya yake tunawa abinda ya shaka a handkerchief last kafin ya farka cikin wannan yanayin da ya ganshi a ciki. Kamar a mafarki yaji ana cewa "Eh mun ɗauko shi, noo ba wannan maganar ku bamu kuɗin da kukace zaku bamu kafin mu fita, dan wallahi sai munga alert zamu bar nan." Sai kuma yaji ance "Kai Malan karfa ka raina mana hankali, bama san hauka dan Allah! Kasan saida ran mu da muka yi akan aikin nan? Kadai san wannan ba irin aikin da muka saba bane ko?" Daga nan bai sake jin komai ba saboda wanj bacci dayai gaba dashi.
Kwakwalwarshi ce ta sake dawowa hayyacinta sai dai wannan karan gudu kawai ake a cikin motar, gudu ake kamar za'a bar garin. Horn aka fara yi da ƙarfi ta bayan su, nan danan mutanen dake cikin motar hankalinsu ya tashi, tsoro da furgice duk ya kamasu, suka ƙara sa gudun motar yanaji guy ɗin ɗazu wanda ya gane muryarshi yana cewa "Munshiga uku ba dai har an san munyi kidnapping ɗinshi ba?" Ɗayan da gaba ɗaya tsoro ya rutsashi yace "Wallahi ina da mahaifiya marar lafiya, shiyasa ni bansan gangancin da yasa ka ɗau aikin nan ba kadai san dama bazamu tsira ba," ya cigaba da magana cikin rawar murya "Ka gangara gefen titi mu ajiye motar mu nufi daji kawai gwara mu tsira da ran mu sannan ya dai bamu rabin kudin?" Ɗayan yace "Eh, ya turo." Nan suka sa gudu. Sai da suka ɗan yiwa masu bin nasu nisa sannan suka gangara gefen titi, motar kawai suka ajiye suka auna a guje kai kace zaki ne ya biyosu, dan suna gudu harda faduwa suna gudu suna faɗa dan ɗayan yaso su sace motar.
Saurayin nan kuwa dakyar ya mike ya iya motsa hanayensa, nan ya fara tattaro duk wani karfi da yasan yana dashi, motar sa ce dan kuwa ya ganeta. Kai ya shiga girgizawa wanda ke mai nauyi kamar an ɗaura masa dutse, yana dafa jikin kujera a haka dakyar ya zauna a gun driver, kansa ke sake sarawa gashi ko gani sosai bayayi sai dai da ya bari mutanen nan su sace shi gwara yaja motarshi yabar wajan. Kunna motar yai ya jata zuwa kan titi, ko gama hawa kan titin bai yi ba yaji ana juyashi, tun yana san sanin meke faruwa har yaji ya hakura sakamakon ɗauke komai da akai daga cikin kwakwalwarshi.
Jikin bishiyar dake gefen titi ɗayar motar da sukai gware ta bugu nan fa itacen dake bayan motar kur-kurar suka hau zubowa ƙasa. Dattijon dake zaune cikin mota ne ya rike wuyansa da ya bugu yana ƙoƙarin fitowa bakinshi banda "Inalilahi wanina ilaihi raji'un," babu abinda yake fita.
Ba Ƙaramin tashin hankali ya fuskanta ba ganin yanda motar data kuno kai ta gangara, kafafunsa ne suka shiga karkarwa a haka ya ɗin ga jan ƙafar shi har sai da yazo inda motar ta ke. Ihu ya saka da karfi ganin saurayi a kwance cikin jini, ya dinga salati yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Wayarsa ya ɗauko ƙirar nokia jikinsa na rawa ya ƙira waya sai dai harta katse ba'a ɗauka ba. Tsaki ne ya fito daga bakinsa dan dama yasan indai shashashan yaran can ne ba ɗauka zai yi ba. Yana tsaka da ƙoƙarin buɗe ƙofa sai ga wata mota ta taho, ganin halin da suke ciki yasa tai parking nan suka taimaka aka buɗe ƙofar aka ciro yaran wanda gefen kansa keta zubar da jini. Hankali a tashe suka nufi asibiti dan kuwa tsoro bazai bar mutumin nan ya iya jan motar nan tasa ba. Saboda gabaki ɗaya a rude yake.
Har suka shiga asibitin yana sake gwada wayarsa ko Allah zaisa wannan mashiriricin yaron ya ɗau wayar. Suna shiga mutanen asibitin suka fara gaidashi sai dai ganin halin da yake ciki yasa hankalin nurses ɗin ya tashi. Hankali a tashe suke tambayar shi inda yake mai ciwo, ya kalli nurse ɗin hankalinsa a tashe yace "Accidents mukai ga mara lafiyan nan." Da sauri suka kalli baya dan sai a lokacin sukaga samarin dake rike da saurayin da aka shigo dashi jini na ɗiga daga gefen kansa da hannunsa. A guje suka turo gadon aka ɗora shi tare da yin ciki dashi. Dattijon ya kalli samarin da suka temaka masa yai musu godiya sannan suka tafi suka barshi domin Dattijon garinsu yana kusa kuma duk mutane sun sanshi dattijon kirki ne sosai. Addu'a kawai dattijon nan keyi dan gaba ɗaya jikinshi rawa yake, fatanshi kawai Allah ya tashi kafaɗun yaran nan. Wayarsa ya sake ɗauka a karo na ba adadi ya ƙara ƙiran wayar yaran da yaketa nema tun ɗazu. Kamar daga sama yaji an ɗauka sai jiyai ance "Baba ina kwana bacci nake yi."
A fusace yace "Kai dai wallahi bakaji da ɗin halinka ba shashasha kawai, to ka hanzarta zuwa ina asibitin kan kwana, kuma yanzu dare ne ba safiya ba." Da sauri saurayin da aka ƙira yace "Baba bakada lafiya ne? Naga badai suma kai ba tunda gashi kana ƙira na a waya."
Wani kululun takaici ne ya kamashi yace "Kabir ka tashi kayi abinda na saka ko sai ranka ya ɓaci?" Yana kaiwa nan ya kashe wayar takaici duk ya isheshi, yaro ace banda shirme da sakarci bashida aikin yi.
KB yai mika tare da yin hamma kamar zai haɗiye ɗakin, sannan ya tuture himilin shirgin dake cikin ɗakin nashi ya miƙe. Fitowa yai tsakar gida ya fara kwalla ƙara kamar wani sabon kamu yana cewa "Kursum! Kursum! Kina ina?"
Budurwa ce wacce bata fi shekara 16 ba, doguwa siririya wacce kana ganinta zakasan siririyar ce, baka ce, tana da manyan idanuwa da kuma tsayi, ta fito daga ɗaki sanye da dogon hijab ɗinta kalar ruwan ƙasa alamun fita zatai. Jitai anja hijab ɗin nata ta baya wanda yasata saurin riƙe inda wuyanta yake tace "Ya Kabir menene hakan?"
Gabanta ya dawo ya ware mata hannu yace "Nikam Kursum kin rainani ko? shikenan ba abinda za'a miki a gidan nan sai dai kice nine? To ga hannaye na ina hannun dake janki da zaki ce ni? Yarinyar nan duk kin gama rainani wallahi. Bari kiji, in na gama tama ki sai na ji miki ciwo a gidan nan zaki fara bani girma na."
Waigawa tai baya ganin matar dake tsaye a bayanta tana kifta mata ido yasa tai saurin sauke ajiyar zuciya ta koma ciki a hankali tare da maida kofar ta rufe. Gurin matar taje ta riƙe hanayenta tare da janta ta zauna a bakin gado tace "Umma yanzu zanje na amso litattafaina na dawo, an bamu aiki ne a makaranta inban kai ba gobe duka za'amin."
Matar dake zaune kallo ɗaya zaka mata kasan batada lafiya irin ciwon nan daya shafi kwakwalwa ke damunta, dan kuwa yanda take kallanta baki a sake kaɗai zai baka wannan amsar. Sannan kuma kana ganinta zakasan akwai alaka tsakaninsu da yarinyar dan kuwa suna kama sosai. Kursum ta saki hanayenta a hankali tace "Yanzu zan dawo kinji? Kafin ki kirga hamsin na dawo. Ko kuma a'a ɗari zaki ƙirga zakiga na dawo kinji?"
Kai ta ɗaga mata a hankali, maida zaman hijabinta tai sannan ta fito tsakar gida, ganin bataga Kabir ba yasa ta fita da sauri dan batasan Ummanta ta fara borin nemanta bata nan.
A can asibiti kuwa an gama yiwa saurayin nan treatment sai dai har yanzu bai farfaɗo ba. Kuɗin da aka lissafawa dattijo ya tattare duk kuɗin cikin account ɗin shi ya biya ba tare da ya damu da ƙarewar da suka yi ba dan yasan sun mai ragi sosai saboda girma da matsayinsa. Sai ma daɗi da yaji ganin sun ishe shi. Shiru yai tare da zama gaban yaran dake kwance akan gado yana tunanin abinda ya faru. Shi kam har yanzu baisan daga ina motar yaran ta fito ba sai hatsarin da sukai kawai yaji, lalai ita rayuwar nan in mutuwarka tazo haka zaka tafi ba tare da shiri ba. Kamar daga sama ya jiyo muryar Kabir yana tambayar inda yake, labulen ɗakin ya yaye tare da cewa "Baba kana ina? Innalillahi na shige su nidai ka taimaka kar ka mutu." Ido huɗun da sukai da Baban ne yasashi yin murmushi tare da ajiyar zuciya yace "Kai Allah ya ceceni ai gaba ɗaya hankalina ya tashi." Fuska a tamke yake kallansa kafin yace "An buɗe islamiyar daren?"
Kabir ya ƙarasa shigowa yana kallan saurayin dake kan gado yana cewa "Eh na faɗawa Malam Munir, Baba wannan kuma fa?"
Ajiyar zuciya yai zai yi magana sai ga Dr ya shigo dan kana kallansa zakasan likitane sakamakon farar coat ɗin dake jikinsa, ya mika mai hannu tare da cewa "Alhaji Nuhu Ɗanbatta dafatan duk abinda ya kamata ayi an yi maka?"
Murmushi Dattijon yai cikin jin daɗi yace "Dr sai dai Allah ya biyaku amma komai lafiya kalau."
Ajiyar zuciya Dr yai yace "Amma na sanar kar a amshi kuɗinka kuma ance ka biya."
"Ba'a haka Dr sana'a kukeyi in ba ana biya ba ya za'ai kusamu ku cigaba da aikin ku?"
Murmushi Dr yai tare da cewa "Allah ya ƙara haskaka rayuwarka, amma ina so in ba damuwa kaima mu dubaka dan hatsari ne kaima zai iya yiwuwa ka bugu hankalinka ne baikai gun ba."
Kallan Kabir yai yace "Ka zauna anan naje na dawo karka kuskura kabar gurin nan."
A tare da Dr suka fito suna tafe yana sake nuna mai asibitin nasu, dan Alhaji Nuhu Ɗanbatta mutum ne wanda ake girmamashi da darajashi a garinsu da kewayensu. Yana fita Kabir ya fara bin saurayin nan dake kwance da kallo yana zagayashi kai kace aikin da aka sakashi kenan, har yayi gaba sai kuma ya dawo da sauri ya kafe saurayin da ido yace "Ɗan saurayi wanene kai? Daga alamunka dai bakai kama da yaran garin mu ba. Hmmm ba dai ɗan fafa bane ba ko? Dan dai wannan kayan na jikinka na tabbatar fake ne, dan ko ni nan nasan kayan jikin nan naka ba kayan kananun mutane bane, faɗa min ina ka samesu?" Sai kuma ya fara ɗaga rigar yanasan gane ta gaskiyar ce ko ta bogi ce wai da gaske rigar Nike ce? Idansa ne yakai kan takalmin ƙafar saurayin, da sauri ya ware ido tare da zabura ya sauko gun da sauri yana kallan warin takalmi ɗaya dake ƙafar saurayin. Zaman jeans ɗinsa ya gyara tare da shafar ɗan karamin sajensa yace "Ha ha ha karya kake wallahi, daga gani wannan takalmin satoshi kayi, idan ba haka ba ina warin takalmin? kutt eh lalai guy ɗin nan kaci uwar rainin wayau. Wallahi tallahi ina nan harsai ka farka ka sanar dani inda ka sato shi nima inje in dan sato ko sau ɗaya ne tab New Balance eh lalai yaran nan kazo da iskanci." Zama yai a gefe ya ɗau ra ƙafa ɗaya kan ɗaya yana girgiza ƙafa yana tunanin inda Babanshi ya samo yaran nan, badai shima taimakonshi yai kamar yanda ya saba ba? Amma yayi kalar wanda aka taimaka? Kayan jikinsa yake sake bi da kallo tare da kuramai ido har Alhaji Nuhu ya dawo yana nan zaune yana kwancewa da warwarewa.
Wayarsa ya ɗauko da sauri ya fara duba kuɗin takalmin kafin yai tsaki yace "Da alama satowa kai shi yasa aka samu wani yaran ya mazge ka, kai inbanda wawancinka duk san gayunka bakasan akwai inda ba'a zuwa ba?" Yana nan yanata ƴan maganganunshi Alhaji Nuhu Danbatta ya shigo ɗaure da hannunsa na hagu da gudu ya mike yace "Baba meya samu hannun?"
Kallan saurayin dake kwance yai yace "Kabiru duba aljihunshi ko akwai wani abu da zai nuna koshi wanene, sannan ka wuce kaje kan titin bayan gari wajen gonar Badaru anan mukai hatsarin, motar yaran nakeso kasa a janye zuwa gefen titi sannan ka duba ciki ko akwai wani abu dazai nuna inda yaran ya fito, ga key ɗin motarsa da mutanen da muka taho suka bani."
Ki kifta ido Kabir yai yace "Baba tsaya nai recording maganarka kasan Babban yaro irina doguwar magana wahala takemin na riƙe ta cikin kai na."
Wani banzan kallo Baban nashi yai masa yamai yace "Baban yaro ko babban dakiki dan dai wannan abin naka alamu ne na dakikanta ba gayu ba."
Shidai Kabir bai damu da me Alhaji Nuhu Ɗanbatta yake cewa ba sai ma kuna wayar dayai haka ya sake mai bayani sannan ya amshi key din motar ya fita yana wani kumbo na tafiyar nigogi, kai kawai Alhaji Nuhu Danbatta ya girgiza sannan ya kalli hanunsa da akace ya sa mu targade aka gyara masa, kallan saurayin yai wanda har yanzu bai farfaɗo ba, fatan shi dai Allah ya tashi kafaɗun yaron.
Yana nan a zaune bacci ya fara ɗaukar shi, wayarshi ce tai ƙara da sauri ya farka tare da sawa a kunnensa yace "Kabir ka isa?"
Daga can ɓangaren Kabir yace "Baba nifa gani nazo inda kace kunyi hatsarin ga motarka nan amma babu motar yaran, da mamaki yace "A'a kamar ya babu motar kuma? Ka duba dakyau motarshi na nan gun sai dai in ko gangarawa motar tai, mutanen da suka kawomu su suka taimaka aka ciroshi daga motar."
Kabir ya kalli abokansa da suka fito dan tayashi dubawa yace "Wallahi Baba babu duk mun duba." Kabir yai maganar yana sake dubawa ko zai hangota.
"Badai bigeshi nai yana tafiya da ƙafa ba? Kai ba yanda za'ai na manta abimda ya faru sai dai in ko kaina ne ya bugu nima? Amma ya akai na samu key din motar da ba tawa ba?"
"A'a Baba a mota ne dan ga fitilar mota a ƙasa wacce kuma nasan ba ta motarka bace, amma dai babu motar guy ɗin nan babu alamunta a gun nan duk mun duba."
Mamaki sosai ne ya bayyana akan fuskar Alhaji Shehu Ɗanbatta. Toh wani ne ya ɗauke motar kenan? Sa ce ta akai? Ko me?
Ayusher Ce🏌🏻♀️