FreeArewaPen original
RIBAR ƘAFA
- 1views
- 106chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · BABI NA ƊAYA
RIBAR ƘAFANAWattpad :-AyusherMohdArewabook:- Ayushermuhdŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️*Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku ɗaukacin masoyana a duk inda kuke, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yana lafiya. Musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, masu ciki Allah ya saukesu lafiya, wadanda ke neman haihuwa Allah ya basu. Masu neman aikin yi Allah ya taimakesu yasa su samu. Ƙasar mu Nigeria Allah ya shiga lamarin ta ya kawo mana gyara Ameen suma Ameen.* Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen..... lol duk da nasan ke ko kai ka fada.......... Dafatan za'amin uzurin jina shiru da akai. I am back!PAID BOOK SHAFI NA FARKODuk abinda ke faruwa a wannan lokacin kwakwalwarshi naji sai dai idanuwansa sun kasa buɗe wa sosai, dakyar ya iya ɗan motsa idanshi na hagu wanda yake jin nauyinshi sosai. Mutane biyu ya gani suna janshi a ƙasa, ga wani azababen ciwon kai dake damunshi wanda yake ji kamar yasa ihu ba sai an fada ba harda jan da suke mai a ƙasa yasa yake ƙarajin kan nashi kamar zai faɗo kasa. Shin ko dai mutuwa yai? Ko Mala'iku ne ke janshi? Tambayar da ya yiwa kansa kenan, sai dai sam ba shi da amsar da zai bawa kansa, abu ɗaya yake tunawa abinda ya shaka a handkerchief last kafin ya farka cikin wannan yanayin da ya ganshi a ciki. Kamar a mafarki yaji ana cewa "Eh mun ɗauko shi, noo ba wannan maganar ku bamu kuɗin da kukace zaku bamu kafin mu fita, dan wallahi sai munga alert zamu bar nan." Sai kuma yaji ance "Kai Malan karfa ka raina mana hankali, bama san hauka dan Allah! Kasan saida ran mu da muka yi akan aikin nan? Kadai san wannan ba irin aikin da muka saba bane ko?" Daga nan bai sake jin komai ba saboda wanj bacci dayai gaba dashi. Kwakwalwarshi ce ta sake dawowa hayyacinta sai dai wannan karan gudu kawai ake a cikin motar, gudu ake kamar za'a bar garin. Horn aka fara yi da ƙarfi ta bayan su, nan danan mutanen dake cikin motar hankalinsu ya tashi, tsoro da furgice duk ya kamasu, suka ƙara sa gudun motar yanaji guy ɗin ɗazu wanda ya gane muryarshi yana cewa "Munshiga uku ba dai har an san munyi kidnapping ɗinshi ba?" Ɗayan da gaba ɗaya tsoro ya rutsashi yace "Wallahi ina da mahaifiya marar lafiya, shiyasa ni bansan gangancin da yasa ka ɗau aikin nan ba kadai san dama bazamu tsira ba," ya cigaba da magana cikin rawar murya "Ka gangara gefen titi mu ajiye motar mu nufi daji kawai gwara mu tsira da ran mu sannan ya dai bamu rabin kudin?" Ɗayan yace "Eh, ya turo." Nan suka sa gudu. Sai da suka ɗan yiwa masu bin nasu nisa sannan suka gangara gefen titi, motar kawai suka ajiye suka auna a guje kai kace zaki ne ya biyosu, dan suna gudu harda faduwa suna gudu suna faɗa dan ɗayan yaso su sace motar.Saurayin nan kuwa dakyar ya mike ya iya motsa hanayensa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.