11
KURURUWA A KUNNEN KURMA🥀 🥀
A 2025NOVEL
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
(OUM AMEER)
Wattpad:@ Ummu-Ameer
Arewabooks: @Aminatuibrahimbawa
From d experience writer of:
Zaytoonah
Abarwa rai
Gudun wuce sa'a
Kibiyar so
Kulsum
Bahiyya
Nuudarr
Littafin kuɗi ne. #500 kacal, zaki iya turawa ta wannan asusun 3132703269 Ibrahim Amina Bawa, sai ki tura shaidar biya ta wannan Layin ***. 🙏🙏
Hi' everyone, gashi dai Allah ya nufa mun dawo, in sha Allah daga yau zaku ci gaba da samun update har zuwa ƙarshen free pages....Tafiyar Kururuwa a kunnen kurma cike ta ke da sarƙayayi, tausayi, ban dariya, abin takaici da kuma abin al'ajabi, ku ci gaba da bibiyar wannan alƙalamin in sha Allah ba bu dani sani.
FREE PAGE 11
Naseer dai shiru kawai yayi tare da kafe ni da ido yana kallon na,instead of ya ji haushina akan irin baƙaƙen kalamanda na shiga jifar shi da su ƙarshe tausayina ne ya kama shi, aure na soyayya daren farko na na kwana ni ɗaya dole abun ya yi min ba daɗi..... Matsowa yayi a hankali ya rungume ni zuwa jikin shi ba tare da ya furta mini komai ba, sai dai a can ƙasan ran shi ji yake yana mi shi wata irin ƙuna akan takaicin wannan irin al'amari, ta yaya wai bacci ya ɗauke sa a mota? Tare suka shi go da abokan sa guda biyu sun rako shi har bakin ƙofar ɗakin, sannan komai ya ɗauko daga mota hatta wayoyinsa suna tare da shi a wannan lokacin but how comes? Miye ya mayar da shi mota har ya kai ga yin bacci? Tunanin da ya ke ta yi kenan but har yanzu ya kasa samun amsa. Ni kuma ji na a cikin jikin sa yasa na ƙara lafewa tare da sake fashewa da wani sabon kukan wanda ya ke jin sa har cikin ransa.
Mun ɗauki kusan 5mnt a haka wanda daga ni har shi kowa da irin abinda yake saƙawa a cikin zuciyar sa, daga ƙarshe yayi breaking hug ɗin tare da sanya idonsa a cikin nawa cike da karyewar zuciya ya ce.
"Safnah! Na san yanzu ranki a matuƙar ɓace ya ke, duk abinda zan faɗa miki ba lallai ki yarda ba, amma wallahi tallahi ni ma bansan mi ye abinda ya faru da ni ba, tabbas su Edrees sun rako ni har bakin door ɗin nan ta ki suka juya suka koma but daga nan ban san ya akayi ba sai yanzu na farka na ganni a mota, ban san mi zan samu idan nayi miki Ƙarya ba, don ina son ki ne na aure ki Safnah Hayatudden, saboda haka ya rage naki ki yarda ko kar ki yarda"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali ina mai gyaɗa kai na jiki na duk yayi sanyi na kalle shi na ce.
"Na kwana a matuƙar tsora ce, kuma ban san dalilinka ba shiyasa, but kayi haƙuri, nima haka wai jiya daga gida zuwa mu iso nan ɗin bacci mai nauyi ya ɗauke ni" Wani Sabon mamakin ne ya sake bayyana akan fuskar sa ya ce.
"Ke ma kin yi bacci a mota Safnah?"
Gyaɗa kaina nayi alamar eh ba tare da nayi magana ba.
"To ki yi haƙuri, namu kalar tarihin kenan kuma in sha Allah daga wannan ya riga da ya wuce. Bari na je na yi sallah ko sallar asuba ɗin ban samu na yi ba"
Gyaɗa kai na nayi tare da komawa bakin gado na ɗan ɗosana ina mai rabka tagumi a raina ina ƙara gasgata gaskiyar sa domin mutum cikakke mai hankali in dai ba da wani uzuri ba ba ta yanda za'a yi ace ya kawo har yanxu bai sallaci sallar asuba ba.....
Gefen Xunnurain kuwa, tun da aka ɗaura auren en uwansa suka shiga kira suna yi masa Allah ya sa albarka, shi dai kawai da amin ya ke bin su domin shi kaɗai yasan abinda ya ke ransa game da wannan ƙaddararren auren nasa wanda bai san ma da wane irin suna zai kira sa ba. Duk irin yanda Bilal ya kwana yana ba shi shawara bai saurare sa ba, ƙarshe ma suna fitowa daga masallacin asuba ya kalli Bilal ɗin ya ce. "Malam ta shi mu san in da dare ya mana". Cike da mamaki Bilal ya ce "Kamar ya?" wani kallon ya sake jefa masa sannan ya ce. "I mean mu koma gida...." wata uwar harara ya jefa masa sannan ya ce "Kai malam ban son rainin hankali, taya zaka ce mu tashi mubar gidan mutane da sassafe kamar wa su marasa gaskiya" cikin halin sa na ko in kula ya ce " I'm damn Serious! Kuma ma ai mu ɗin marasa gaskiyar ne as you said because er su ba zata jima ba zata dawo gaban su..." miƙewa Bilal yayi a tsaye jiki sanyaye ya kalli Usman ɗin ya ce. "Joke apart Usman kada ka kuskura ka ce zaka yi gangancin sakin Xuhra ina baka shawara". Sharesa yayi tare da juyawa ya kwashi wayoyinsa guda biyu ya zura a aljihu sannan ya sake kallon in da Bilal ɗin ya ke tsaye ya ce "Hayar ka na ɗauko na taho da kai don haka ni ke da alhakin mayar da kai gida, so you have no choice da ya wuce ka ta Shi mu tafi ko kuma na tafi na barka a nan wallahi ka ji na rantse" Bilal dai shiru kawai yayi yana mai bin abokin nasa da kallo mai murɗaɗɗiyar rayuwa, idan ba shi ba taya za'a aura maka yarinya ka ta shi kawai tun asubar fari kace zaka bar gida ba tare da sanin kowa ba..... Katse masa tunanin sa yayi da faɗin "Malam ko sai ka tsaya kwarakar karin kumallo in yi tafiyata zaka biyo motar kasuwa daga baya?" kafaɗa Bilal ya ɗage sannan ya ce. "Mai ƙaya ya daure mai cirewa miye nasa na kuka! Ta shi mu tafi tunda haka ka ke so" Daga haka suka fito babu wanda ya yi wanka a cikin su, shi dai mai gadin gidan bai dai na mamakin su ba har ya gama buɗe musu gate ɗin suka fice zuciyar sa cike da tsoron Allah yasa ba wata ta'asar suka aikata ba. Tun da suka hau hanya Bilal ke masa bayanin yanda ya kamata a canjawa gidan na sa fenti don kawai su fita kunyar Xuhra da kuma dangin ta duk da cewa gidan ba wani babban gida ba ne, 2bedroom ne sai 1parlor mai doguwar veranda sai kitchen a tsakar gida sai toilet daban shi ma. Bilal dai sai famar zuba zance yake amma Usman ko sau ɗaya bai ɗago ya kalle shi ba... Harararsa yayi ta wutsiyar ido sannan ya ce "Wai Malam kai kurma ne ko yaya? Ni fa bana son renin hankali" wayar sa da yake dannawa ya kashe tare da jefa ta a aljihu hankali kwance ya ce. "Abinda ni ke da halin yi shi zan yi Bilal, ba ni da kuɗin yin wani fenti yanxu, idan xata shiga a haka ta shiga idan kuma ba zata shiga ba to ta fasa". Haushi ne ya ƙume Bilal shiyasa yayi shiru kawai yaci gaba da driving ɗinsa suka ci gaba da tafiya. Umar na fitowa daga ɗakin Abdulmalik in da ya kwana ya nufo ɗakin nasa in da yasan cewa ya bar baƙi a ciki wato su Usman, sai dai turus! ya ja ya tsaya ganin ba kowa a ɗakin, dube dube ya shiga yi tamkar mai neman wani abin na daban, sai dai ganin ba komai na su shi ya tabbatar mai da cewa ba sa gidan, a tunanin sa sun koma hotel ne may be they are not comfortable a nan ɗin. Aydah kuwa, ƙarfe goma dot ta gama shiri tare da Irfan ta shiga ɗakin da Xuhra ta ke kwance ta kalle ta ta ce "Xuhra Hajiya Kakale ta ce ba za'a tafi da ke gidan auren ki ba sai zuwa Monday idan an shirya miki, so idan kina da ra'ayi ki tashi mu tafi gidan Safnah yanzu can zamu tafi tare da su Aunty Rabi'ahtu da Yah Abdul" Duƙunƙune ta ke a cikin duvet,ga wani zafi da jikinta ya ɗauka alamar zazzaɓi tsabar yanda ta kwana ta na kuka, jin yanda Aydahr ke neman cika ta da surutu yasa don dole ta ɗago a hankali calmly ta ce. "I'm not interested please, you can leave". Jin yanda voice ɗinta ya sauka sosai a slow yasa Aydah matsawa ta ɗora hannun ta a forehead ɗinta ta ce. "Sis are you sick? What's wrong? Idan auren nan ne bakya so please let me know, sai a san yanda za'a ɓullowa su Daddy..." "Aydah please! Just leave, I will be fine OK..." juyowa tayi kawai ta baro ɗakin, motar ta ta wuce ta shige ita da Irfan suka nufi gidan Safnah daman ta ce ba za ta iya jiran su Aunty Rabi'ahtou ba domin su sunce sai 12pm za su je...... Ni kuma ina zaune ina jiran Naseer har kusan 9am daga ƙarshe na ta shi na shige cikin ƙayataccen banɗaki na wanda yaji kayayyakin zamani tamkar wani ɗakin bacci. wanka na yo na fito direct na buɗe closet ɗin da already na san da zaman sa, domin babu abinda Naseer bai masa vedio ya tura mini ba, daman kuma duk himilin kayan lefe na da aka haɗa a nan yasa aka shirya min komai ya zama ready tun kafin na shigo, wani irin farin ciki ne ya lulluɓe ni ganin irin sabuwar duniyar da na tsinci kai na a ciki, Dubai Exclusive lace ne na ciro wanda ya sha stones da ɗinki na musamman na sanya, na ɗauko veil ɗinsa na ɗora tare da takalmin sa sai gani cas! Na fito Safnah Matar Naseer Sani Wurno ta asali. Ina cikin jujjuyawa ina kallon kaina a mirror ya shigo ɗakin, wata irin kunya ce ta kamani wanda yasa da sauri nayi ƙasa da kaina ina murmushi,... "Ɗago ki kalle ni mana Safnah" ɗagowar nayi ba musu na kalle sa wanda har cikin rai na naji cewa wankan sa ya ƙayartar da ni ainun, murmushi ya sakar min tare da matsowa ya rungumeni ya na faɗin. "Kin yi kyau sosai cikin wannan kayan" nima dai ban yi nauyin baki ba na ce "Kaima haka" gyaɗa kansa yayi ya ce "Na gode. Zo muje muyi break fast kada zunubin yayi min yawa, an kawo amanar er mutane tun jiya na barta da yunwa" murmushi na yi na ce "Kai ma ai kana jin yunwar kuma ai ma ba laifinka ba ne" gyaɗa kansa yayi ya ce "Thank you for understanding" Daga haka ya ja hannuna muka fito ɗaki na gwanin sha'awa da mu, tunda muka sauko na ke ganin kalolin ma'aikata daban daban ma su mabanbantan uniform wanda duk wanda muka ci karo da shi sai ya tsaya ya durƙusa har ƙasa ya gaishe mu sannan ya ta shi ya ci gaba da abinda ya ke , a wani tangamemen dining area muka yi masauki wanda a ƙalla dishes ɗinda ke kan table ɗin nan sunfi guda biyar, zaunawa muka yi yayi ta ciyar da ni daman na zama kamun yunwa because tunda muka iso Sokoto da sunan bukin aure na ban san na samu wani cikakken lokacin da na zauna na ci abinci ba, yana bani abincin a hankali yana min fira na cewa wai tafiya ya ke da ita ta uxuri nan da sati ɗaya idan na amince ya tafi idan kuma ban amince ba sai ya fasa...... Sallamar Aydah ita ce ta katse mana firar wanda yana ganinta ya janye daga jikina da alama ko don saboda Irfan ne yayi hakan. Dariya Aydah ta fara har tana tafa hannu ƙarshe ta ciro wayar ta ta shiga snapping na mu tana faɗin. "Best couple of the week, wallahi kunsha kyau sosai, wannan irin wanka haka sis kamar ba za'a mutu ba" Naseer dai dariya yayi kawai sannan ya ce "Aydah how are you?" Zaunawa tayi akan kujerar da ke kusa dani tace "while! A little bit fine, because hidimar bukin kunnan ta kusa karya mini haƙarƙari na" girgiza kan shi yayi ya ce "Eyyah! We are sorry, but na yi miki alƙawari idan auren ki ya zo sai mun ninka miki fiye da yanda kika mana" Dariya tayi ta ce "Allah yasa ba daɗin baki ba ne" Kallon Irfan yayi ya miƙa masa hannu ya ce "Mutumin ba magana ne?" Matsowa irfan yayi ya ba shi hannu ya ce "Good morning Yah Naseer" "Good morning boy, how are you doing today" "I'm fine" shaking ɗin hannunsa yayi yace "That’s good to hear, have a nice day with your sisters" Daga haka ya waigo ya kalle ni ya ce "Safnah ni zan fita, kin san mutane zasu zo, so kada su zo musamman Familyn ki su cimmim a gida hakan ba zai mu su daɗin zama ba" gyaɗa kai na nayi alamar gamsuwa na ce "Allah ya tsare, a dawo lafiya" Ba Aydah ba, hatta ni kai na sai da abin ya bani dariya. Bayan Naseer ɗin ya wuce na tashi muka wuce sama, nan muka bar Irfan da kayan maƙulashe a gaban shi yana kallon TV yayin da ni da Aydah muka shige ɗaki na cike da zumuɗi ina so in labarta mata cakwakwakiyar da ta wakana tsakanina da Naseer a jiya daren farkon mu, sai dai me? Wani Babban abin mamaki shi ne, tamkar an dannawa waya formatting haka naji kai na yayi wani dum! Lokaci ɗaya naji komai ya ɓace min tamkar wani abu makamancin hakan bai taɓa faruwa da ni ba, ƙarshe ma sai muka ɓige da firar auren Xuhra da Usman. Gefen Usman kuwa, ƙarfe goma sha biyu na rana a ƙofar gidan su ta buge mu su, mamaki ne fal a ransa ganin yanda mutane suka cika farfajiyar gate ɗin gidan na su, bai gama tsinkewa da al'amarin ba sai da ya kutsa cikin gidan ya tarar da taron mata an cika gida sai kekkewa ake ana arerewa. Jin cewa hayaniyar ta fi ƙarfin sa yasa ya dawo kawai ya shige ɗakinsa ya rufe, wayarsa ya ciro ya kira Siddeeq wanda ringing ɗaya zuwa na biyu ya ɗaga ya ce. "Yah Uxman ka dawo ne?" calmly ya ce "Siddeeq miye ya ke faruwa a cikin gida?" murmushi Siddeeq yayi tamkar yana a gabansa ya ce. "Wunin bukin ka ne ake yi?" cike da mamaki ya maimaita kalmar ya ce "Wunin buki! Uban waye ya gayyato su...." Da sauri Siddeeq yana mai ƙume dariyar sa ya ce "Kai dai Yah Usman kada kayi saurin zagi Hajiya ce ta tara su..." kitt! Ya tsinke wayar ransa na yi masa wani irin suya tsabar takaici, sai da ya ja kunnen su akan kada su bari Hajiya taji zancen nan amma sai da aka samu wani ɗan iya da yaje ya sanar mata.... Ƙwanƙwasa ƙofar da akayi ne ya katse masa tunanin da ya ke, shiru yayi yana tunani, sai daga ƙarshe ya ce "Come in"... Da sauri ya miƙe daga kwancen da yake ya xauna da kyau ganin Umma ce ta shigo yana mai yin ƙasa da kansa ya ce "Hajiya Ina wuni!". Zuruu! Hajiya Sa'a tayi tana kallon sa kamar wadda tayi karo da wata baƙuwar fuska, bai ankara ba kawai ya ji saukar ɗaɗagon kukan ta kukan da ke yin matuƙar ba shi baƙin ciki a rayuwa, ko abu bai taka kara ya karya ba hajiya zata zauna tayi ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya.... "Yanzu fisabilillahi Usman ka kyauta kenan? Ace wai duk abinda ya ke faruwa da rayuwar ka daga ni har Maryam babu wanda ka ke iya samu ka faɗa masa matsalar ka, har yaushe zaka daina irin wannan Usman?" girgiza kai yayi sannan ya ce " Ba haka ba ne Hajiya kiyi haƙuri, ban san mizan faɗa muku ba shiyasa na yi shiru... " Sautin kukan ta ne ya ƙaru ta katse shi da faɗin" Amma Usman har abu yayi ƙamari bamu sani ba har a kai ga ɗaura maka aure Usman... " Safe kansa yayi cike da damuwa ya ce" Hajiya dan Allah ki yi haƙuri ki daina wannan kukan ba shi da amfani... "" Haba Usman! Wannan abun Sam bai yi daɗi ba... "" Duk da haka Hajiya abin bai kai da ki yi ta wannan kuka haka ba dan Allah". Sallama Hajiya Maryam tayi ta shigo ɗakin ita da Ramlatu, Ruƙayya da kuma Amrah sai Siddeeq wanda ya hango shigowar su shima ya biyo bayan su. Gaishe da Mami Xunnurain yayi kawai yayi shiru duk da yasan cewa ba lallai ta nuna ɓacin rai ba amma ya na ji a ransa cewa bai kyauta ba da yayi shiru bai sanar mu su ba.... Sharce hanci Umma tayi ta kalli Mami ɗin ta ce "Faɗa nike yi masa domin yanxu gaba ɗaya Usman ya ƙara canzawa, halin ko in kulansa sai ƙara gaba ya ke" jinjina kai Mami ta yi ta ce "To ai sai yayi ya gani idan hanya mai ɓullewa ce gare shi, ace an nemi aure har an saka rana lokaci kaɗan ya rage yarinya ta ce ta fasa har ta kai ga yin aure wai ba zaka iya buɗe baki ka sanarwa iyayenka da en uwan haihuwarka halin da ake ciki ba ina amfani" Umma ta ce "Ai wallahi Usman ni dai ina mi shi addu'a Allah ya canxa mi shi wannan rayuwar ta sa, yanzu dan Allah in ban da iyayen ta suna da mutunci ba haka za su bar shi a gantale yayi ta zaryar neman wani sabon auren ba. Kai! Wallahi wannan Safnahr dai an yi er banzar yarinya" Ruƙayya ta ce "Wallahi kan ta tayiwa Ummah, matuƙar ba shi da haƙƙinta sai Allah ya saka mi shi..." jinjina kai Mami tayi ta ce "Yanzu dai duk wannan ya wuce, mace ba ta taɓa auren mijin da ba nata ba, tunda har an yi haka kuma iyayen ta ba su yi ƙasa a guiwa ba suka aura masa er uwar ta ai sai da dukkan su mu yi mu su fatan alheri" Ajiyar zuciya Siddeeq ya sauke sannan ya kalli Xunnurain ya ce. "Yah Usman gidan nan akwai sauran aiki sosai a cikin sa, yanzu haka daga can ni ke na kira engineer na ce yaxo yayi estimate ɗin kuɗin da zai ci, to yana can na baro sa kafin na koma mu ji..." girgiza yayi ya ce "No! Siddeeq gidan nan ba zai gyaru ba a yanzu har a shige sa domin gaskiya bani da wannan halin, mun yi magana da Bilal cewa zan yi amfani da gidan sa kafin zuwa lokacin da zan ƙara sa gyaran..." Kallon sa Umma ta yi ta ce "Ina da rai na Usman ba zaka zauna gidan haya ko gidan aro ba har abada, gidan Mustapha wanda yake mallaki na ne na mallaka maka shi halak malak..." Sai kuma ta juya ta kalli Ramlatu, Siddeeq da kuma Ruƙayya tace "Kuji da kyau, gida na wanda na mallaka na Mustapha na barwa Usman shi duniya da lahira" Jinjina kai Siddeeq yayi ya ce "Wallahi Umma ko ni ni ke da halin da zan mallakawa Yah Usman gida zan yi hakan domin ya fi ƙarfin komai a wurin mu, ya tsaya akan mu tamkar Alhaji ne ya ke raye, akan farin cikin mu da walwalar mu ya tauye kansa ta hanyoyi da dama, saboda haka ni dai har cikin zuciya ta na yi amanna da hakan, Allah ya hore mana hanyoyin samu ma su albarka ya hana mana yi wa en uwan mu hassada " Kallon Usman Ruƙayya ta yi sannan ta ce" Umma muma Yah Xunnurain yafi ƙarfin komai a wurin mu, fatan mu Allah ya ba su zaman lafiya ya kauda fitina a tsakanin su" Godiya Mami kawai tayi mata domin ba ta isa tace zata yi magana ba, yanzu sai ta fasa kuka ta ce ta nuna cewa ba ita ce ta haifi Usman ɗin ba. Usman kuwa, wannan irin al'ajabi ya ma hana shi yin magana, gidan Mustapha? Babban gida ne flat wanda ya kashe kusan shekara biyar yana gina sa, ya narka dukiya ba er ƙarama ba daga ƙarshe bayan ya gama ginin Alhajinsu shi ne ya ƙara sa masa fenti da duk wani abinda yayi saura bai kambala ba, auren sa saura six month sukayi accident ya ra su, shi ne fa gidan ya dawo gadon Umma, en uwanta sun yi ta bibiya akan ta saida ta ƙi haka ma wani ƙaninta Hamisu yayi ta ƙwaƙwa akan ta ba shi aron gidan da zai yi aure shi ma ta ƙi amincewa amma wai yau shi ne ta ba shi da hannunta.... "Usman yaushe aka ce za'a zo da amaryar" cewar Umma tana mai samun wuri gefe ta zauna jin ƙafafunta sun gaji da tsayuwa.. Dariya Amrah tayi ta ce "Oh! Ikon Allah, ko ya kalar fuskar Amaryar Yah Usman ɗin ta ke? Wannan irin aure dai Allah yasa ya zama alheri" Da amin duk suka amsa,daga ƙarshe Usman ɗin ya ce "Hajiya na ce su bar ta har su shirya mata..." Girgiza kai Umma tayi ta ce "A'a Usman ba'a yi haka ba, gobe idan Allah ya kai mu rai da lafiya, Zamu tafi tare da Ramlah, Ilham da kuma Hajiya Halima, sai Hauwa da Hajiya fatima gefen Maryam, Siddeeq ya ɗauke mu a motar Isyaku sai ka samo mana mota muje da mota biyu...." "Hajiya har mota biyu? Ina ga ku tafi a ɗaya mana kawai mutum biyu ya isa..." "A'a Usman gwanda muje da yawa mu yi musu godiya kuma su san cewa mun amshi auren nan hanu biyu ko ba haka ba Maryam?" Gyaɗa kai Mami tayi ta ce "Hakan ma yayi. Bari na kira Sharif na ji idan za'a samu million biyu ya cika abinda zai cika idan kukaje Sokoton kuyi siyayyar kayan lefen sai ku je da su" kai tsaye ya ce "Hajiya kuɗin nan ya yi yawa, sannan gaskiya ni bani da wani kuɗi mai yawa a yanxu da zai isa na yi lefe, a dai bar shi ko zuwa gaba..." Kalma Ummah ta ɗauke ta dire sannan ta kalle shi ta ce "Usman wane lefen ne za'a bari har zuwa gaba?? Shin ko dai baka son er mutane jona maka ita suka yi?" gaban shi ne ya yanke ya faɗi, da sauri ya canza akalar zancen ya ce "Ba haka ni ke nufi ba Hajiya, naga ko iyayenta cewa sukayi ɗaura aure kawai shi ne dole duk wani abu zai iya biyowa daga baya, to kinga tunda har ba'a san da zancen auren ba zamu iya barin komai a bishi a hankali...." Kukan nan da baya so shi ta sanya masa tana faɗin " Kawai dai Usman idan baka son er mutane ka faɗa mana gaskiya tun wuri... " " A'a haka ni ban ce haka ba.. "." Bilal fa ya sanar min ko er wace irin gida ce, saboda haka komai zamu yi iya ƙarfin mu ba zamu barta a haka ba, idan kai ba kada kuɗi mu Allah ya hore mana, zan bayar da dubu ɗari biyar" "Ramlah ta ce" Yanzu zan turawa Siddeeq 200k.." kafin ka ce mi har sun haɗa 3.7m nan ta ke. Shi dai Usman mamaki ya hana shi magana, a ransa kuma cewa ya ke 'Yarinyar da zata zo ta juya zuwa gidan su ba jimawa waye zai yarda ya kashe mata kuɗin sa? Nan dai suka yi ta tattaunawa daga ƙarshe suka fita suka bar shi ya shige toilet domin watsa ruwa.......
Ni kuma muna nan da Aydah har kusan 4pm su Aunty Rabi'atou ba su zo ba, daga ƙarshe na kira wayar Yah Abdul ya ce sun fasa zuwa yau sai gobe za su shigo. Firar mu muke ta yi, idan lokacin sallah yayi mu ta shi muyi sallah idan lokacin cin abinci yayi muje muci abinci, ba su bar gidan ba sai 8pm, bayan na dawo daga rakiyar su na haye sama direct na cire kayan jiki na na ɗora towel na shige banɗaki,zaune ni ke cikin jacuzzi wanda ya ke cike da ruwan ɗumi ma su daɗin ƙamshi, ga wani engine a ciki mai fitar da wani kalar kumfa da hayaƙi gwanin sha'awa wanda ba mai cutarwa ba,zaune ni ke dirshan na yi relaxing bayana tare da extending kai na baya kaɗan yayin da idanuwana suke a lumshe domin yanayin ba ƙaramin daɗi ya min ba... A hankali na dinga jiyo sautin kuka yana karaɗe kunne ne wanda ban san daga ina yake fitowa ba, tun ina jin shi a nesa-nesa har naji sautin direct yana fitowa daga cikin ɗakina, kuka sosai murya mace kamar ta Xuhra har tana sheshsheka... Jikina na wani irin mazari na fito da gudu na janyo towel na ɗora upside down jiki na duk kumfa na buɗe ƙofar na fito, sai dai abin mamaki banga kowa ba, sannan ɗakin yayi tsit! Tamkar ba nan ne na jiyo amon sautin kuka ba..tsaye na yi zuciya ta na wani wani irin duka da ƙarfi tamkar zata fasa ƙirji na ta fito tsabar tsoron da ya kamani... A hankali na ji kukan ya dawo ta window kamar yanda ya fara daga farko a hankali daga baya sautin ya ɗaga tamkar a kunnena.. Ƙoƙarin buɗe baki na nike in yi addu'a sai dai kuma na kasa, lokaci ɗaya na fashe da kuka jikina duk ya ɗauki mazari, duk da haka kuma takawa ni ke domin zuciya ta faɗamin ta ke daga zaran na ɗaga curtain ɗin zanga ko wacece ke rusa wannan kukan...jin ƙarar an buɗe ƙofa yasa ni yin baya da ƙarfi tare da matse jikina wuri ɗaya na rufe idanuwana... "Safnah! Lafiya kuwa?" Da sauri na buɗe idona jin muryar Naseer a gabana yana magana,ai ban tsaya tankasa ba da gudu na faɗa jikin sa ina mai nuna masa window murya na rawa na ce "Ba ka ji sautin kuka ba yayin da kake haurowa nan?" Direction ɗinda hannu na ya bi ya kalla har zuwa windown, janye jikin sa yayi ya je ya yaye curtains ɗin ya leƙa gefe da gefe sama da ƙasa sannan ya rufe window ɗin daga ƙarshe baki ɗaya ya dawo ya jani zuwa jikin sa ya ce." Safnah relax your self, ba kowa a wurin windown nan, in fact window a upstairs taya kike tunanin wani zai zo..." "Wallahi tun ina toilet ni ke jiyo sautin kuka, kuka sosai a cikin ɗakin nan, bayan kuma na fito sai sautin ya koma a wurin window ɗin" "It may be tsoron da kikaji ne a daren jiya shi ne abin ya tsaya a ranki har kike tunanin akwai wani abu, amma ba komai a nan ki kwantar da hankalinki kinji ko..." Girgiza kai na nashiga yi hawaye wani na bin wani na ce "Wllhy ba wani tsoro, da kunnena na ji sautin kuka wanda tabbas ba gizau ba ne kuka ne na gaske.." cike da tausayawa ya ce "To shi kenan na ji, yanzu koma miye yazo gani na dawo ina tare da ke, babu abinda zai same ki in sha Allah" ni dai shiru kawai nayi tare da ƙara lafewa a jikin sa tamkar wata mage yayinda har yanxu nike jin sautin yana dawowa a brain ɗi ta. Mun shafe kusan 30mnt a haka, daga ƙarshe ya ce "Safnah bari na je na yi wanka kinga yanzu na dawo, ina da buƙatar wanka" da sauri na girgiza kai na na ce "Ni dai ba inda zaka je gaskiya" "To naji, tashi mu tafi ɗakina" har muka isa ɗakin nasa ban yarda na bar jikin sa ba, sai da ya ce min na zauna ya shiga toilet yanzu zai fito, da ƙyar ya samu na ƙyale sa yayinda na samu gefe guda akan gadon na takure tamkar er jaririyar mage na runtse idanuwana gam har ya fito, toilet ɗin ya raka ni na ƙara sa wankan da na fara sannan muka fito, closet ya buɗe ya ciro min wa su sleeping dress cotton Riga da wando na saka kawai na haye gadon na ƙudundune, shi kuma tsayawa yayi ya shirya sannan ya hawo kan gadon ya ce "Safnah ki zo muyi nafila mana..." Da sauri na girgiza kai tare da janyoshi ya faɗo gefena na ce "Ni dai tsoro ni ke ji dan Allah mu bar shi sai gobe..." yunƙurawa ya yi da nufin tashi yana faɗin "Ki daure ki kwantar da hankalinki..." girgiza kai na nayi ina ƙara cukuikuye shi yayin da idanuwana suka ciko da wa su sabbin hawaye na ce "Please mubar shi sai gobe, tsoro nike ji sosai har can ƙasan zuciya ta" Shiru yayi tare da ɗora kansa a kan pillow ya janyo ni sosai xuwa jikin sa na ƙara shigewa na maƙalƙale shi na lafe kamar mai bacci. Jin nayi shiru kamar bacci ni ke yasa shi ɗago fuska ta ya kalleni da kyau zuciyar sa ci ke da ruɗani yana tambayar kansa wai mi ke faruwa ne? Miye haka? Aure kwana ɗaya zuwa na biyu amma komai ya birkice mu su! Miye yake tsorata ta to?... Haka dai ya ke ta tunane - tunane barkatai wanda gaba ɗaya ya ji duniyar sa ta ƙuntata.. Ni kuma jin yayi shiru yasa na ɗago na kalli fuskar sa, kallon da ya saka ni yin dana sani na har abada domin numfashi na ne ya nemi ɗaukewa ganin wata fuska mai tsananin ban tsoro da firgitarwar a cikin fuskar Naseer, cikin ƙyaftawar ido na zabura na yi tsalle na dire ƙasa jiki na na wani irin ƙyarma... "Ko yau wannan daren ba naki ba ne Amarya Safnah!" wannan ita ce kalmar da ta shiga amsa kuwwa a cikin kunne na.. Haƙiƙa na shiga tashin hankali iya tashin hankali domin wani fitsarin wahala ne ya kufce min ba tare da sani ba..........
OUM AMEER