CHEF ZEEY (Love in the Kitchen)
9
by @azizat
CHEF ZEEY
*Love In The Kitchen*
Topnotch season 4
©AzizatHamza2025
ArewaBooks @Azizat Hamza
9-Last Free Page
JAYKAY
Hajiya tana dawowa daga gidan ƙawarta ta kira Jalal da ke supervision Plaza ta ce masa ta samu Chef da za ta musu aiki a restaurant. Shi duk yadda ta ke ta bayanin abincin gargajiya bai fahimci inda ta dosa ba. Restaurant ɗin da za su buɗe fine dining ne ba wai shagon abinci kamar na Mama put ba. Ya dai ce mata idan ya shigo gidan zai sameta su yi magana.
Completely shi yama manta da maganar da suka yi. Amma yana shigowa da ya gaisheta sai ta ke ce masa me ya ke gani gameda hiring Chef Zeey su mayar da Restaurant ɗin wajen yin traditional food.
"Hajiya, akwai plan a ƙasa, mun riga mun yi nisa, I don't think it's a good idea mu chanja tsarinmu a wannan gaɓar" ya faɗa a nitse kamar ba ƙorafi ya ke ba.
"Daɗina da kai kenan, idan ka kafe a abu shikenan. Ɗan'uwanka is more open to new ideas" hakan da ta faɗa zafinsa dai-dai yake da ta ɗau guduma ta buga masa a dai-dai ƙirjinsa.
Everytime ta auna shi da Jamal haka yake ji.
"Ni dai na inviting ɗinta za ta zo gobe, ka yi tunani akai. Ka gwada jin idea ɗin daga wajenta ka gani ko abu ne da za ka yi aiki da shi. Yanzu ni sau nawa nake tashi da marmarin abincin gida in rasa wajen siya sai dai ko a taho da shi daga family house. I think her idea is very creative"
So yake ya ce mata ba creative idea kaɗai bane zai tafiyar da restaurant amma sai ya yi shiru. Duk abinda zai faɗa ba fahimta za ta yi ba musamman da ta riga ta nanata cewa Jamal yana son new ideas.
"Zan yi magana da ita" ya faɗa bayan dogon shiru.
"Ko kai fa. Allah ya sa a dace". Ƙasa-ƙasa ya amsa da Amin sannan ya tashi ya fita.
Da safe bai yi mamaki ba da Hajiya ta sake nanata masa cewa ya dawo da wuri saboda su yi magana da Chef Zeey.
Yana jin Janan da Saudah suna yiwa Hajiyar tsiya wai tun jiya da ta ci abinci a gidan Hajiya Maryam take ta waƙar Chef Zeey.
Ya kaɗa kai ya fita. To ko suma za su taya shi jimamin wannan lamari ai.
Lokacin da ya samu sarari a office sai ya shiga Instagram dan ya ga wacece Chef ɗin da Hajiyar ke maganar a damƙa wa restaurant. A bayanan Hajiyar ya fahimci a Instagram ta santa tun ma kafin su haɗu a gidan ƙawarta.
Video ɗaya ya kalla ya fita daga wajen yana mamakin me ya hau kan Hajiya haka take ƙoƙarin kawo masa tarkace cikin harkarsa.
Videon da ya gani ba da waya mai kyau aka ɗauka ba, it was blurry. Wajen da ake girkin duk ƙasa da su randa su rijiya, typical gidajen ghetto.
Ta ina mai irin wannan content ɗin za ta heading restaurant ɗin da ya ke son buɗewa.
Anya ma Chef ɗin ce kamar yadda Hajiyar ke ta faɗa. Koda zai yi amfani da maganar Hajiya ya mayar da restaurant ɗin strictly traditional cuisine, to ba zai iya ɗaukan wannan matar ba, dan bata dace da shirinsa ba.
Bai bari maganar ya jima a ransa ba ya watsar da komai akan koma wacece ya riga ya gama assessing ɗinta tana zuwa zai ce mata ba zai yi aiki da ita ba. Ba sai Hajiya ta gane ba ya san me zai yi ya koreta a rufe maganar.
Ƙarfe huɗu saura ya dawo daga Masallaci kenan zai koma office Hajiya ta kira shi, wai yana ina, ya zo Chef Zeey ta jima a gidan, ta gama abinda ya kawota shi ta ke jira. Ya ce mata yanzu zai zo.
***
ZEEY
Gidan Hajiya Layla ya ninka gidan su Hayfa girma da kyau. Ban zama 'yar ƙauye ba sai dana shiga kitchen ɗinsu. Allah ina ga sashen Kaka tsulum zai shiga kitchen ɗin har a samu sauran space. Babu abinda babu a kitchen ɗinnan. Irin kitchen dana ke gani a Pinterest da manyan food bloggers ɗin kudu ne.
Da ni ke da kitchen ɗinnan ai katifa kawai zan shimfiɗa na rinƙa kwana a wajen. Idan za ka kwana kana girki a irin wannan haɗaɗɗen kitchen ɗin Allah ba za ka gaji ba.
Hajiya da ta lura na faɗa kogin soyayyar kitchen ɗinta sai ta ce "gashi duk kyan kitchen ɗinnan ni da Janan ba girki muke a ciki ba"
Hangame baki nayi da ta faɗi hakan. Idan ina da irin kitchen ɗinnan ai babu abinda zai hanani girki sai ciwo.
"Lokacin da zan yi aure aka kaini wajen Kakata wai ta koya mini girki muka yi ta faɗa na gudo. Da na je London kuma su ba irin abincinmu suke ci ba dama bana son wahala sai na koma cima irin tasu. Kin san a lokacin Alhaji idan ya ji ta cin Tuwo ko wani abu sai dai ya siya a African restaurant ko kuma ya yi da kansa"
Na zaro ido ina mamaki. Cabɗi! Wai sai shi 'ya yi da kansa'. Har na hango Baffa Lawalli ko Baffa Zakari suna tuƙa tuwo. Abinda ba zai taɓa faruwa ba kenan, ko a mafarki.
Haka ta riƙa nuna min komai na kitchen ɗin. Ta haɗa ni da mai aikinta ta ce ta gwada min inda ake saka komai da yadda ake konna burner ɗin. Akwai wata ma da ta shigo, na ji Hajiyar ta kirata da Saudah. Tana kallona ta ce "ke ce Chef Zeey da Hajiya ke ta maganarki tun jiya?" na gyaɗa mata kai.
Na fahimci kallon reni a idanunta. Wato irin ban worthing Hajiya ta yi maganata ba ɗinnan.
Lokacin da mai aiki ta buɗe min freezer inda suke ajiye frozen foods ɗinsu sai dana nemi tsari da talauci sau goma a zuciyata. Wato nama ne da kifi danƙare a ciki sun yi ƙanƙara. Akwai naman Sa, Akwai gudar Akuya da aka yanka gida takwas, ga naman rago, ga naman Kaji. Hassana mai aikinsu ta ce min akwai naman Talo-Talo dana Zabi, ba wai Kaza kaɗai bane a wajen. Ni sai na rasa ma wanne zan ɗauka. Ba ni zan ci abincin ba amma ni ke ruwan ido. Su kam na san nama bai damesu ba.
Hajiya Layla ta ce na yi mata Tuwon Biski da miyar Kuka amma gaskiya zan haɗa da wani abun.
Yadda kitchen ɗin yake ƙal-ƙal da tsari sai na rasa ma a ina zan haɗa kurho ɗin gawayi da zan turara tuwon kamar yadda na yi a gidan Hajiya Maryam.
Ai kuwa ina tambayar Hassana ta ce sai dai mu fita ta baya ina kunna gawayi a nan zan fara jin ƙara winwinwin. Ta nuna min wani abu wanda na fahimci smoke detector ne.
Muka fita ta baya na je na haɗa wutan. Cikin tsari da ƙwarewa na fara komai. Ina tuwo ina prepping miyan kukan da zan yi, ina so shima sai ruwan kukan ya dahu da kyau kamar yadda Kaka ta koya min kafin na zo na kaɗata.
Kafin na ƙare girkin Janan 'yar Hajiya ta dawo. Ita da Saudah ne suka shigo kitchen ɗin wai tana son ganina. Itama irin kallon da Saudan ta mini ɗazu shi take min, in fact nata ma ya fi muni. Ko kaɗan bata da daraja mutum kamar Hajiya. Kallon 'yar aiki ta ke mini ba Chef ba.
Ta yatsina fiska ta ce "Yanzu wannan ɗinne Hajiya ke cewa za ta koya mini girki. Thank God Mi Amor baya son Tuwo balle ta ce saboda shi in koya"
Saudah dai dariya ta yi ta bi bayanta suka fita daga kitchen ɗin.
Gwiwata sai ya sace iissssssss kamar an sace balon-balon. Ashe dai yadda Hajiya ta ke da fara'a ba haka sauran 'yan gidan suke ba. Da alama dai daga yau idan na fita ba zan ƙara zuwa ba. Kafin su fara min kallon 'yar Maula. Halal nake nema ba roƙo na zo yi ba.
Lokacin dana gama wanke kitchen ɗin ni da Hassana sai na koma falo na zauna ina jiran ɗan Hajiyar da zai zo mu yi maganar restaurant.
Ina zaune ina kallo a falo sai ga wani yaro ya shigo falon sanye da Uniform ɗin Makaranta a jikinsa. Yaron kyakykyawa da shi, daka ganshi ka ga ruwa biyu. Ga gashin kansa baƙi siɗik a kwance lub irin na Turawa.
"Hi, Sannu" ya faɗa yana ɗaga min hannu.
"Sannunka handsome boy, an dawo daga Makaranta?" Ya gyaɗa kai sannan ya wuce sama da gudu.
Yaron ya burgeni, dan ban ɗauka ya iya Hausa ba.
Can ina zaune duk na ƙagu mutumin dana ke jira ya zo sai Hajiya ta sauko ita da yaron ɗazu wanda nake da tabbacin jikanta ne ta ce yau za ta koya masa cin Tuwon Biski.
Wajen dining suka nufa ta dishing masa. Ina ji tana tambayarsa ko abincin ya yi daɗi, na leƙa na ga yaron yana gyaɗa mata kai.
Har yaron ya gama cin abinci wanda na ke jira bai dawo ba.
Hajiya ta zo ta zauna ta kira shi a waya. Ban san me ya faɗa ba, na dai ga ta cire wayar ta ɓata fuska.
"Hajiya barin je na tattara kayana idan ya so yana zuwa ɗin sai na wuce"
"Ki yi haƙuri na riƙe ki Ziyadaah. Ki shiga kitchen ki ɗauki duk abinda kike so kin ji"
Na miƙe ina mata godiya. Tun ɗazu ta tura min alert ɗin kuɗin aikin dana yi. Nauyin alert ɗinne ma ya sa na shirya jiran ɗan nata ko zai kai ƙarfe takwas na dare bai dawo ba.
Da zan wuce kitchen ɗin sai ta ce na buɗe freezer na ɗebi naman da zai isheni. Allah Sarki matar arziƙi, kamar ta san naman nan dana gani yana raina.
Babu kowa a kitchen ɗin. Tunda muka tattare kitchen Hassana ta koma ɗakinta. Itama duk yadda ta ke ganin wai ban kai ta girki ba da ta ci tuwon dana yi sai data ce dole Hajiya ta kirani na zo na mata girki.
I think waccar Saudar ma ta ci amma ita Janan bata ci ba, ban ma sake ganinta ba tun da ta leƙoni ta min kallon banza.
Talaka ya samu ganima dole yai bushasha. Ni da Hajiya ta bani damar ɗiban nama ba sai na buge da cika leda ba. Sai dana cika leda mai yellow da baƙi da nama amma still idona bai haƙura ba. Hassana ta ce idan naman yai wata bai ƙare bama ita da sauran ma'aikatan gidan suke rabawa a sake kawo wasu.
A yadda na ke ganin naman nan kuwa, ko kullum za a riƙa girki da shi zai iya kaiwa wata uku ma.
Wannan greed ɗin ya tunzurani na sake ɗauko wani baƙin ledan cikin tarkacen dana zo da shi daga gida na sake sa hannu ina ƙoƙarin ɓanɓaro gudar kazar saboda ta yi ƙanƙara. Da ƙyar na cirota na ɗago zan sata a leda
"U'u'um"
"Wayyo!" Na saki ledar hannuna a tsorace saboda gyaran muryan da na ji a bayana babu shiri.
A hankali na juyo cike da kunyar abinda aka kamani ina yi. Ga nan leda cike da nama a saman island ɗin kitchen ɗin ga ni nan kuma ina shirin cika wata ledar.
Hannunsa ɗaya riƙe da baƙin suit ɗinsa, ɗayan hannun kuma yana cikin aljihun wando.
Kallon-kallo muka tsaya yi ni da shi. Na san kallon ɓarauniyar nama yake mini. Sai na ji wani kunya ya rufe ni. Ina so na ce masa Hajiya ce ta ce na ɗiba amma bakina ya kasa maganar sai rarraba idanu kawai na ke yi.
Juyawa yai zai tafi na ce masa "Ha, Haajiya...Hajiya ce ta ce..."
A nan muka kawo ƙarshen Free Pages na littafin CHEF ZEEY: Love in the Kitchen